Ticker

6/recent/ticker-posts

Wakar Sardaunan Hamma’ali Malami Maigandi Ta Alhaji Musa Danba’u Gidan Buwai

Sauraro Da Rubutawa

Hirabri Shehu Sakkwato

08143533314

Amshi: Sardaunan Hamma’ali zaki,

Malami Maigandi bi da arna. 

Jagora: Hamma’ali mukai mu kwan biyu,

Yara:    Malami Maigandi na bid’ata.

 

Amshi: Sardaunan Hamma’ali zaki,

Malami Maigandi bi da arna.

 

Jagora: Abin da kai man hamdullahi,

Malami Maigandi ba mu ramma.

 

Amshi: Sardaunan Hamma’ali zaki,

Malami Maigandi bi da arna.

 

Jagora: Malami ka ima shirya dambe,

Malami ka ima shirya dambe,

In ka bugi baki da zuciya,

Ka tabbata k’ato ya suma,

Yara:   Sai ka yi wajen wuya ka isai.

 

Amshi: Sardaunan Hamma’ali zaki,

Malami Maigandi bi da arna.

 

Jagora: Kada ka ce ni ina gama ni,

Kada ka ce ni ina gama ni,

Kowa na gaya maka da zahi,

Yara:   To kai ma gaya masa da zahi.

 

Jagora: In kowa na gaya maka da zahi,

Yara:   To kai ma gaya masa da zahi.

 

Jagora: Don zaki in ya kai k’arhi,

Yara:    Bai jin tsoron karo da giwa

Jagora: A d’an sarki in ya gawurta,

Yara:    Bai jin tsoron karo da sarki.

 

Amshi: Sardaunan Hamma’ali zaki,

Malami Maigandi bi da arna.

 

Jagora: A Hamma’ali na tafi yawo,

Ga wani nai muna kurin banza,

Ya ce shi aka wa Sardauna,

Sai nac ce kauce da nesa,

Yara:   Kusun kusumi ba ya kyau da sarki.

 

Amshi: Sardaunan Hamma’ali zaki,

Malami Maigandi bi da arna.

 

Jagora: Cikin ‘yan sarki na Hamma’ali,

Akwai wani sata yakai da rana,

Shi wannan ya zame muzuru×2

Yara:   ‘Yan kaji bai bari su girma.

 

Amshi: Sardaunan Hamma’ali zaki,

Malami Maigandi bi da arna

 

Jagora: Na sauka Kware don in ga ciyaman,

Na tahi ofis sai nig gaisai,

Sai ya ce ba ni kud’d’in mai,

Da ya ce a ba ni kud’in mai,

Ni yi jira ba a mik’a min ba,

Ni mamaki ya kama ni,

Ga rijiya ta ba da ruwanta,

Yara:   Sai guga ta hana a d’ebo.

 

Amshi: Sardaunan Hamma’ali zaki,

Malami Maigandi bi da arna.

 

https://www.amsoshi.com/2018/01/15/wakar-ciyaman-din-shagari-alhaji-madu-galadima-horo-ta-alhaji-musa-danbau-gidan-buwai/

Jagora: A D’anmaliki na Kware dwatijo,

Haji Hayatu na gode mai,

Yara:   ‘Danba’u ya yaba da girma.

 

Jagora: D’anmaliki na Kware mai nera,

Ka ga ta kowa d’an dattijo,

Sun kauce maka ko don dole,

Im Haji Hayatu na gode ma,

Yara:   ‘Danba’u ya yaba da girma.

 

Jagora: A Alhaji Arziki D’ankwangila,

Yara:   ‘Danba’u ya yaba da girma.

 

Jagora: A D’annayintin ban rena mai ba,

Yara:    ‘Danba’u ya yaba da girma.

 

Jagora: Alhaji Aminu gaida D’ankabo,

‘Danba’u ya yaba da girma.

 

Jagora: A ni D’ankabo Alhaji Aminu,

Yara:    ‘Danba’u ya yaba da girma.

 

Jagora: A ni Bello tihwa ba rana mai ba,

Yara:    ‘Danba’u ya yaba da girma.

 

Jagora: A ga Bushiya mai naman rago,

Yara:    ‘Danba’u ya yaba da girma.

 

Jagora: A Bagobiran nan ta D’antasakku,

‘Danba’u ya yaba da girma×2

 

Jagora: A ni shugaba Raha na gode,

Yara:   ‘Danba’u ya yaba da girma.

 

Jagora: Rai ya dad’ewa mai tayoyi,

Mai kamfanin taya na gode.

Yara:   ‘Danba’u ya yaba da girma.

Post a Comment

0 Comments