Ticker

6/recent/ticker-posts

Wakar Alhaji Aliyu Magatakarda Ta Alhaji Musa Danba’u Gidan Buwai

Sauraro Da Rubutawa

Hirabri Shehu Sakkwato

08143533314

Amshi: K’i sake bajini gwarzon maza,

Ali sarkin Yamman Sakkwato.
 

Jagora: Ka yi biyu yau saura biyu,

Ga ka difiti gwamna ga ka sarkin Yamma,

Sai in ka zama gwamna a Sakkwato,

Yara:   Sannan a ba ka Barade cikin gida.

 

Jagora: Sai in ka zama gamna a Sakkwato,

Yara:    Sannan a ba ka Barade cikin gida.

 

Amshi: K’i sake bajini gwarzon maza,

Ali sarkin Yamman Sakkwato.

 

Jagora: Ka ga sarautar sarkin Yamma,

Ba fa sarautar yaro ce ba,

Ba ko sarauta wargi ce ba,

Sai an za’bi mutum mai kirki,

Yara:    A ba shi sarkin yamman Sakkwato.

 

Amshi: K’i sake bajini gwarzon maza,

Ali sarkin Yamman Sakkwato.

 

Jagora: Na yi mahwalki jiya mai dad’i,

Amma hwa ban magana sai yaz zamo×2

Yara:    Allah ya sa ya zame ma gaskiya.

 

Amshi: K’i sake bajini gwarzon maza,

Ali sarkin Yamman Sakkwato.

Jagora: In Allah ya so ya yarda,

Tutawuzan sabin in ta zo,

Yara:    Kai za ka gwamna jaharmu ta Sakkwato.

 

Jagora: Ko mu masu adawa mun bari,

Yara: Saboda mun ga alamun gaskiya.

 

Amshi: K’i sake bajini gwarzon maza,

Ali sarkin Yamman Sakkwato.

 

Jagora: Ran Juma’a na kwan mamaki,

An yi sarautu Sakwkato bunni,

Mai kurin shi ad da mutane,

An yi nad’i kowa ya watce,

Mai jama’a ya kwashi abinai,

Sai nib biya garkar wani sarki,

Ni ishe ‘yan banga sun taru,

Yara:    Da haka ‘yan sholi d’ai nig gani.

 

Amshi: K’i sake bajini gwarzon maza,

Ali sarkin Yamman Sakkwato.

 

Jagora: Wannan duk aka ci da hak’k’i nai,

Allah shi kai mai sakayya,

Makircin da sukai ma Sakkwato,

Aliyu kar ka ji tsorran komai,

Yara:    Bar su akwai Allah shi ya gani.

 

Amshi: K’i sake bajini gwarzon maza,

Ali sarkin Yamman Sakkwato.

 

Jagora: Aliyu kai ka gadi sarauta,

Ka yi nad’i daidai da sarauta,

Wanda duk bai gadi sarauta ba,

Yara ko ga nad’i sai mun ganai,

Yara:    Wane nad’inai ya cika girma,

Wanga uban huni sai ‘yan dako.

 

Amshi: K’i sake bajini gwarzon maza,

Ali sarkin Yamman Sakkwato.

 

Jagora: I tak’amarka Alu daidai,

Tak’ama sai d’an sarki,

Jan biri in dai ya yi tak’ama,

Yara:    Tabbata hwadaman nan ya gani,

Yana nuhwa ya kare geron wani.

 

Amshi: K’i sake bajini gwarzon maza,

Ali sarkin Yamman Sakkwato.

https://www.amsoshi.com/2018/01/12/na-tinkari-tsautsayi-da-shirin-yaki-tawakkali-ta-tsai-da-ni/

Jagora: Na gaishe ka Italin Nasiru,

Shugaba na matasan Sakwkato,

Kai ne anka sani duk Sakkwato,

Duk wanda anka nad’a shirme ne,

Yara:    Nasiru naka nad’i ag gaskiya.

 

Amshi: K’i sake bajini gwarzon maza,

Ali sarkin Yamman Sakkwato.

 

Jagora: Bello na Gwiwa masoyin Ali,

Ni na gane kana k’aunatai,×3

Yara:    Alhaji tun ga nad’i nit tabbatar.

Amshi: K’i sake bajini gwarzon maza,

Ali sarkin Yamman Sakkwato.

 

Jagora: Ahmed Aliyu ku gaisai,

Ahmad Aliyu ya ban mota,

Yara:    Saboda Sarkin Yamman Sakkwato.

 

Jagora: Nasiru Itali ba mu sitalet,

Yara:    Saboda sarkin Yamman Sakkwato.

 

Jagora: Kai bari dai in tada gwanina,

Bari dai in wasu ubana,

D’an Barade jikan umar,

Baba gizago ba ka da sabo,

Yara:    Masassak’i ya tsara hannu k’warai.

 

Amshi: K’i sake bajini gwarzon maza,

Ali sarkin Yamman Sakkwato.

 

Jagora:  Musa Damo ya ban gero,

Musa Damo ya ban dawa,

Musa Damo ya ban kud’i,

Da riguna Musa ya ba ni×2

Kaf Illela Lokal gamun

Yara:    Duk wanda ke son sarkin Yamma,

Alhaji babu irin Musa Dama.

 

Amshi: K’i sake bajini gwarzon maza,

Ali sarkin Yamman Sakkwato.

 

 

Jagora: Magatakarda Difiti Gwamna,

Maza su k’ara shiri sai ka zamo,

Hankalinka ya kwanta Sakkwato,

Tun mulkin gargajiya Aliyu don Mulkin ga,

Na zamani inda duk Allah ya ce a yi,

Yara:    Babu wanda ka ce ba a yi.

 

Amshi: K’i sake bajini gwarzon maza,

Ali sarkin Yamman Sakkwato.

 

Jagora: Dole in yi yabon gogana,

Tunda garinmu guda da shi,

Shehu Adamu birnin Rana,

Yara:    Irin abin da yakai man ya yi d’a.

 

Jagora: Shehu na sani d’an Adamu,

Yara:    Irin abin da ya kai man ya yi d’a.

 

Jagora: Gwamnan jahar Yobe,

Gwamnan jahar Yobe,

Abba Bukar d’an Ibrahim,

Yara:    Irin abinda ya kai ma.

 

Jagora: Matiamakin sifika Sakkwato,

Rai ya dad’e Alhaji Maigwandu

Yara:    Irin man ya yi da.

 

Jagora: Nasiru mai mai birnin Wurno,

Yara:    Irin abin da yakai man ya yi d’a.

Jagora: Haji Mu’azu Zabira ka yi d’a,

Yara:    Irin abin da yakai man ya yi d’a.

 

Jagora: Mustapha Haji Maigandi,

Yara:    Irin abin da yakai man ya yi d’a.

 

 

Post a Comment

0 Comments