Ticker

6/recent/ticker-posts

Matsayin /N/ Da /R/ A Karin Harshen Sakkwatanci (2)

Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami'ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato, Nijeriya

NA 

SHAMSUDEEN BELLO HAMMA’ALI

BABI NA ‘DAYA: GABATARWA


1.0 GABATARWA


A wanann babi na farko, za a dubi yadda magabata suka gudanar da aikinsu a game da tsarin ginin jumlar Hausa, sannan a dubi yadda tsarin ginin yadda yake a karin harshen sakkwatanci. Musamman ta ‘bangaren nazarin k’wayar ma’ana wadda wannan aikin zai duba. Ta hanyar bitar ayyukan da magabata suka gudanar, an dubi yiwuwar gudanuwar aikin, za a bayyana dalilin binciken da kuma yadda aka kafa hujjar ci gaba da nazartar wad’annan k’wayoyin ma’anar na –n da –r a karin harshen sakkwatanci. Za a bayyana hanyoyin da ake bi domin gudanar da wannan binciken daga k’arshe a nuna muhimmancin gudanar da wannan aikin.

A babi na biyu kuma za a bayyana ma’anar k’wayar ma’ana tare da kawo rabe-rabenta sannan a gabatar da matsayin k’wayoyin ma’anar -n da -r a karin harshen sakkwatanci. A babi na uku kuma aikin ya nuna yadda masana suka raba jumlar Hausa a daidaitacciyar Hausa sai aka kawo yadda rabon yake a karin harshen sakkwatanci, tare da kawo fasalin sassauk’ar jumlar Hausa ta daidaitacciyar Hausa, don ta zama makamin kwatancin da za a yi tsakanin daidaitacciyar Hausa da karin harshen sakkwatancci.

Sannan a bayyana yadda yankin suna yake wanda a nan ne wad’annan k’wayoyin ma’anar suka fi fitowa.

Babi na Hud’u a nan ne gundarin aikin yake, don haka yana k’unshe da abubuwa kamar haka: za a nuna ire-iren yadda wad’annan k’wayoyin ma’anar suke a karin harshen sakkwatanci, haka kuma a wannan babi za a yi magana a kan yadda k’wayoyin ma’anar suke fayyace suna dangane da jinsi, sannan kuma a nuna yadda suke fito da manunin nasaba da na mallaka, a karin harshen sakkwatancci. A cikin babin ne za a nuna yadda k’wayoyin ma’anar suke zamantakewa da ajin sifa, sai a nad’e aikin. Sai babi na Biyar inda za a tak’aita aikin tare da kawo jawabin kammalawa sai kuma manazarta ta biyo baya.

 

1.1 BITAR AYYUKAN DA SUKA GABATA


Masana da dama sun gudanar da ayyuka a kan nahawun Hausa, tun daga masanan farko wad’anda Turawa ne suka yi aikin rarraba ‘bangarorin nazarin nahawun harshen bisa tsarin harshen Ingilishi har ya zuwa ga masana ‘yan gida da suka gaji Turawan, kusan duk abu guda ne. Ire-iren wad’annan ayyukan ne tare da na masanan zamani musamman wanda aka gudanar da ya shafi yankin suna da ajin sifa da kuma ajin kalmomi masu aiki irin na nahawu. Inda wannan aikin zai baje kolinsa shi ne, a kan irin wad’annan ayyukan ne da ake son tattarowa a jera su a wannan babin domin samun fito da yadda aikin zai kasance.

Da farko kafin a fara wannan aikin sai da aka waiwayi ayyukan da aka gudanar wad’anda suka shafi wad’annan k’wayoyin ma’anar a harshen Hausa.

Galadanci (1976), ya wallafa littafi mai suna “An introduction to Hausa Grammar”. A cikin wannan littafin an ta’bo zancen wad’annan k’wayoyin ma’anar ta fuskar jinsi da nasaba da adadi da sifa na daidaitacciyar Hausa. Amma wannan nazarin zai dube su ne a karin harshen sakkwatanci.

Skinner, da Ibrahim, (1976) sun wallafa wani littafi mai suna”Hausa a sauk’ak’e”, (Jagoran Nahawun Hausa). A cikin wannan littafin an kawo bayanai dangane da azuzuwan kalmomin Hausa da k’a’idojin rubutu, sai dai ba a ta’bo wad’annan k’wayoyin ma’anar ba. Don haka wannan aikin zai sami damar gudanuwa.

 

Umar, (1985) ya gudanar da aikinsa na kundin digiri na farko a sashen harsunan Najeriaya na Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo Sakkwato, a kan “Bishiyar Li’irabi a cikin Nahawun Hausa” ya dubi k’wayoyin ta fuskar ajin nasaba da mallaka, amma a daidaitachiyar Hausa. Don haka ba zai hana wannan aikin gudanuwa ba, saboda shi wannan aiki zai dube su ne a karin harshen sakkwatanci.

Lawal, (1985) ya gudanar da nasa bincike a kan ajin sifa “Gurbin sifa a cikin jimlolin Hausa” a sashen harsunan Najeriya na Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo Sakkwato. Inda ya dubi wad’annan k’wayoyi ta fuskar zamantakewar sifa da suna, a tsarin daidaitaciyar Hausa. Sai dai wannan aikin zai dube su ne a karin harshen sakkwatanci.

 

Zarruk’ da wasu (1988) sun gudanar da wani aiki a kan wad’annan k’wayoyin ma’anar, cikin wani littafi da suka wallafa mai suna “Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa: (don k’ananin Makarantun Sakandare)”. Sun ta’bo wad’annan k’wayoyin ma’ana ta la’akari da ajin sifa da manunin mallaka, a daidaitaciyar Hausa. Amma wannan aikin zai dube su ne a tsarin karin harshen sakkwatanci.

Zaria (1981) ya wallafi littafi mai suna “Nahawun Hausa” Inda ya yi tsokaci a kan k’wayoyin ma’anar ta fuskar ajin sifa da adadi a jinsi. Shima yayi aikin nasa net a la’akari da matsayinsu a daidaitacciyar Hausa. Wannan nazari zai dube su ne a tsarin karin harshen sakkwataci.

Skinner, (1977) ya wallafi littafi mai suna “A Grammar of Hausa” (For Nigerian Secondary School and College). Ya yi Magana a kansu ta ‘bangaren nasaba ne. Don haka wannan aikin zai bi sawun su a guraben da suke fitowa a karin harshen sakkwatanci.

Jinju (1988) ya wallafi littafi mai suna “Rayayyen Nahawun Hausa”. Shi kuwa ya yi magana ne a wad’annan k’wayoyin ma’anar ta ‘bangaren jinsi da mallaka da yadda suke a ajin sifa. Amma a daidaitaciyar Hausa. Inda wannan nazarin zai dube su a karin harshen sakkwatanci.

 

Galadanci da wasu (1992). Sun tofa albarkacin bakinsu a cikin wani littafinsu mai suna “Hausa: (don k’ananan Makarantun Sakandare)”. Sun dube su ne ta fuskar manunin nasaba da na mallaka, a daidaitaciyar Hausa. Wannan nazarin zai dube su a karin harshen sakkwatanci.

Hassan (1999) shi ma ya ta’bo wannan k’wayoyin ma’anar ta fuskar mallaka kad’ai. A cikin littafe mai suna “Hausa Language”. Shi ma ya nazarcesu ne a daidaitaciyar Hausa. Inda wannan nazarin zai dube su a karin harshen sakkwatanci.

Sani (1999) ya yi bayani a cikin littafinsa mai suan “Tsarin sauti da Nahawun Hausa”. Dangane da wad’annan k’wayoyin ma’anar ta fuskar ajin siffa da nunau da mafayyaci da tsigalau da mallaka da kuma madanganci. Amma a daidaitaciyar Hausa.Wannan Binciken zai dube su ne karin harshen sakkwatanci.

Sani da wasu (2003) sun ta’bo k’wayoyin ma’anar ta fuskar zamantakewar sifa da suna da kuma manunin mallaka, a cikin littafinsu mai suna “Darussan Hausa (don Manyan Makarantun Sakandare)”.

 

Amfani (2004) ya gabatar da muk’ala mai taken “Waiwaye Adon Tafiya”. Inda ya yi bayanin wasu daga cikin gurbin da wad’annan k’wayoyin ma’anar suka samu aka nazarce su bisa tsarin nazari na ci gaban zamani. Shi ma kamar sauran magana a daidaitaciyar Hausa, ya gudanar da nazarin wad’annan k’wayoyin ma’ana na –n da –r.

 

1.2 DALILIN GUDANAR DA BINCIKE


Hausawa kan ce “Ruwa ba ya tsami banza”, wannan karin maganar haka take, domin kuwa babu wani abu da zai iya gudanuwa a rayuwa, ba tare da wani k’wak’k’waran dalili ba. Sanin haka ya sa ake ganin ya dace da a bayyana dalilin gudanar da wannan binciken.

Babban dalilin da ya sa aka buk’aci aiwatar da wannan aiki shi ne don tattaro dukkanin guraben da wad’annan k’wayoyin ma’ana na –n da r suke bayyana a cikin jumlar karin harshen sakkwatanci sannan a fito da irin gudummawar da suke bayar wa ta fuskar ginin jumlar, da niyyar sauk’ak’a wa mai sha’awar nazartar wad’annan k’wayoyin ma’anar a wani Karin Harshen na Hausa dangane da su a wannan karin harshen. Wani dalilin kuma shi ne domin cika gurbin sharud’d’an kammala digiri na farko (B.A. Hausa) a Sashen Harsunan Nijeriya, na Tsangayar Fasaha da Nazarin Addinin Musulunci, a Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo Sakkwato.

 

1.3 HUJAR CI GABA DA BINCIKE


Duk da cewa masana sun gudanar da aikace-aikace da dama dangane da wad’annan k’wayoyin ma’anar a daidaitacciyar Hausa kamar yadda aka nuna a bitar ayyukan da suka gabata, duk da haka ba zai hana a ci gaba da binciken ba, hujjat a nan ita ce, babu wani aiki da aka gudanar dangane da wad’annan k’wayoyin ma’anar na –n da -r a tsarin karin harshen sakkwatanci, a kan wannan dalili ne aikin zai ba da gudummawa wajen nuna yadda suke a karin harshen sakkwatancci, ta hanyar kwatanta su da yadda suke a daidaitacciyar Hausa.

 

 

 

1.4 MUHIMMANCIN GUDANAR DA BINCIKE


Wannan aikin burinsa shi ne na nuna duk wani gurbi da k’wayoyin ma’ana na -n da -r suka ba da gudummawa wajen ginin jumlar Hausa musamman a karin harshen sakkwatanci.

Abin lura a nan shi ne wad’annan k’wayoyin ma’ana sun fito a wurare daban-daban a cikin jumlar daidaitacciyar Hausa. Domin taimakawa wajen fito da ma’anar da take a cikin jumlar, tare da nuna manufar abin da ake magana a cikin jumlar.

 

Babban mahimmancin wannan bincike shi ne domin sauk’ak’awa mai buk’atar sanin yadda wad’annan k’wayoyin ma’anar suke a karin harshen sakkwatancci musamman a ginin jumlar karin harshen sakkwatanci. Ta hanyar tattaro guraben da suke gudanar da ayyukansu a cikin sassauk’ar jumla.

 

1.5 HANYOYIN GUDANAR DA BINCIKE


Wannan bincike za a gudanar da shi ne ta hanyoyi da dama. Hanya ta farko ita ce duba irin ayyukan da masana suka yi ta fuskar rubuta da wallafa mujallu da litattafai da muk’alu a fagen harkokin ilimi. Hanya ta biyu ita ce bin cibiyoyin nazarin harsunan Najeriya da d’akunan karatu da shiga yanar gizo domin fito da ayyukan da za su taimaka wajen kammaluwar wannan nazarin.

Wata hanya kuma ita ce neman shawarwari daga manyan malaman nahawun harshen Hausa, musamman wad’anda suka fahimci ilimin ginin jumlar Hausa.

Hanya ta k’arshe ita ce, kuma ziyartar d’akunan karatu na manyan makarantu da jami’o’i domin samun nasarar kammalawar nazarin.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Post a Comment

0 Comments