Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami'ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato, Nijeriya
NA
MAINASARA ABDULKADIR
BABI NA UKU: JUMLOLI A KARIN HARSHEN SAKKWATANCI
3.0 SHIMFI’DA
Wannan babi shi ne babin da ya ke d’auke da nazari kan karin harshen Sakkwatanci, kuma a cikin sa ne za a ga ire-iren kalmomi da jumlolin da karin harshen Sakkwatanci yake da su. Wad’anda suka had’a da azuzuwan kalmomi da Sassauk’ar jumla a karin harshen Sakkwatanci, da kuma jumlar tambaya da ta umarni, tare da jumlar korewa duk a cikin karin harshen Sakkwatanci. Za a kawo su ne kamar yadda aka kawo na daidaitacciyar Hausa a babi na biyu. Kafin a yi duk wad’annan bayanan sai an waiwayi abin da masana suka ce game da karin harshen Sakkwatanci.3.1 KARIN HARSHEN SAKKWATANCI
Idan ana maganar karin harshen Sakkwatanci za a ga cewa karin harshe ne mai babban kaso wanda ya k’unshi karuruwan harsunan yammacin k’asar Hausa. Idan aka yi la’akari da ra’ayoyin wasu daga cikin masana wad’anda ke ganin cewa, karin harshe ya kasu kashi biyu wato Karin harshen gabas wanda ya k’unshi Kananci, Zazzaganci, Katsinanci da makamantansu, sai kuma karin harshen yamma wanda ya k’unshi Sakkwatanci, Kabanci, Zamfaranci, Arewanci, da sauran kare-karen harshen yamma. Saboda kasancewar garin Sakkwato a matsayin babbar mahad’a ga sauran karuruwan harsunan yamma. Saboda haka sai masana ilimin kimiyyar nazarin harshe suka za’bi karin harshen Sakkwatanci ya zama jagora ga sauran karuruwan harshen Hausa da suke da alak’a da juna ta fuskar furuci da tsarin sauti da yanayin gini jumla da ma’ana. Akan samu dangantaka ta fagen karin harshe da al’adu da auratayya, addini da kuma kasuwanci. Wasu kad’an daga cikin masanan da suka tofa albarkacin bakinsu game da karin harshen Sakkwatanci su ne:
Hamma'ali, (1985), ya nuna cewa "Sakkwatanci Karin harshe ne na Sakkwato. An samo kalmar Sakkwatanci ne daga sunan garin Sakkwato. Sakkwatanci karin harshe ne na mutanen Sakkwato. Sai dai kuma ba ana nufin Jihar Sakkwato gaba d’aya ba. Wasu na ganin tsagwaron Sakkwatawa su ne, wad’anda ke garuruwan da ke kusa da Sakkwato, wato Zamfarawa, Kabawa da Arawa, musamman wad’anda aka kafa ko ciyar da su gaba, bayan jihadi.
Wasu masana na ganin cewa, Sakkwatanci karin harshe ne na mulki. Dalilin da ya sa suke ganin Sakkwatanci a matsayin karin harshe na mulki shi ne, saboda kasancewar Sakkwato cibiyar daular Usmaniyya. Wadda bayan k’are jihadi ita ce ke fad’a a ji a k’asar Hausa, har zuwan Turawan mulkin mallaka. Bisa la’akari da ra’ayin wannan manazarci ana iya cewa karin harshen Sakkwatanci ya samo asali ne daga ginuwar garin Sakkwato a zamanin jihadin Shehu ‘Danfodiyo, inda aka za’bi garin Sakkwato don ya zama babbar fadar mulki ta masu jihadi. Wannan za’ben da aka yi wa Sakkwato sai ya samar da dama ga mutanen garin Sakkwato na mallakar kalmomi da k’wayoyin sautukan sauran kare-karen harshen da suke mak’wabtaka da garin Sakkwaton wajen ginin kalma da samar da jumla zuwa fahimtar ma’ana da take k’unshe cikin zantukan yau da kullum.
3.2 KALMOMIN KARIN HARSHEN SAKKWATANCI A ZAUREN SAKKWATANCI NA VISION F.M.
Wad’annan kalmomi da za a gabatar a nan kalmomi ne, da ake tattaunawa a kan su cikin shirin zauren Sakkwatanci na gidan rediyo vision F.M. wad’annan kalmomin za a adana su ne don gudun salwantar su nan gaba. Ga jerin kalmomin:
Kalmomin Sakkwatanci A Zauren Sakkatanci Ma’ana a Daidaitacciyar Hausa
Al’amurra al’amura
Agalemi buzu
Akaihwa farce
Alkwato dodon kod’i
Alloba annoba
Anka aka
Arbik’i unguwarzoma
Assibit asabar
Awo Ee
Batu magana
Basilla allura
Bid’a nema
Burgu gafiya
Bugu duka
Rwarwaka raraka
Hwara fara
Wanga wannan
Wargi wasa
Shigihwa d’aki
Bid’a nema
Ragaita shiririta
3.2.1 KALMOMI MASU BAMBANCIN FURUCI AMMA MA’ANA ‘DAYA
Bargery (1934) shi ne ya yi k’ok’arin kawo wad’annan kalmomin na Sakkwatanci tare da kwatanta su da na Daidaitacciyar Hausa. Saboda haka, ga wasu kad’an daga cikin su bisa tsarin gidan rediyon Vision F.M. tare da ma’anar su cikin daidaitacciyar Hausa. Ga misalin su:
Kalmomin Zauren Sakkwatanci Daidaitacciyar Hausa
Agalemi buuzuu
Alkwatoo Katantanwa
Akaihwa Farcee
Arbiik’ii Ungoozoma
Badaraa Tsuntsu
Bagajaa Kwatamii
Bundii Wutsiyaa
‘bartakee Abaawaa
‘baaci Zaagi
‘baace-’baace ‘baatayyaa
Hwarcee Yaatsaa
Gabaa Girtsi
Gambuu k’yaure
Gulbii Koogii
Gujjiyaa Gyad’a
Guroo Ku’beewaa
Gidan bisa Beenee
Habd’ii Tookaa
3.2.2 KALMOMI MASU MA’ANA ‘DAYA, AMMA SAUTI BAMBAN
A nan k’asa, in an za a ga Sakkwatatun kalmomi wad’anda ma’anarsu d’aya da na Daidaitacciyar Hausa, amma sautin su ya bambanta da na Daidaitacciyar Hausa. Ga misalan kad’an daga cikin su:
Sakkwatanci Daidaitacciyar Hausa
Allooba Annooba
Al’amurraa Al’amura
Attanin Litinin
Anguwaa Unguwaa
Assibit Assabar
Bahwaadee Bafaade
Bushiyaa Bishiya
Bukii Bikii
Ciyyoo Ciiwoo
Jibjii Juujii
Laahiyaa Laafiyaa
Lak’yas Lak’was
Lallai Lalle
Mussai Mushee
Sabkaa Saukaa
Saashee Saashi
Shibkaa Shuukaa
Shidda Shida
Sihilii Sifirii
Suuraa Suumaa
Swa’baanii Saa’baanii
Swaahwaa Saafaa
Sakkwatanci yakan yi amfani da wad’ansu kalmomi wad’anda shi kad’ai ya ke’banta da su, sai wasu daga cikin kare-karen harshen yammaci wato ‘yan dangin Sakkwatanci, wad’anda su ma ba kowace kalma ce daga cikin kalmomin suke amfani da ita ba. Amma wannan ba ya haddasa bambancin ma’ana a kan ire-iren wad’annan kalmomi da sauran kare-karen harshen Hausa ke amfani da su.
Wannan na nufin idan Sakkwatanci ya yi amfani da wata kalma, to akwai irinta a Daidaitacciyar Hausa da sauran kare-karen harshen Hausa sai dai akan sami bambancin k’wayoyin sautuka a tsakanin su. Sannan kalmar ba ta da bambancin ma’ana da takwarar ta, da ke samu a cikin sauran kare-karen harshen Hausa ko a Daidaitacciyar Hausa. Alal misali, Sakkwatanci yakan yi amfani da kalmar ‘katattara’ wato wani sashe na k’afar mutum mai tattare da nama, wanda ya taso daga guiwa zuwa d’uwawu). Amma a Daidaitacciyar Hausa da wasu kare-karen harshen Hausa sukan yi amfani da kalmar ‘cinya’ a maimakon katattara. A nan, ma’anar katattara da cinya ba bambanci. Akan iya a sami bambancin tsarin kalmomin, amma ma’anarsu d’aya. Ko kuma bambancin furuci, amma ma’ana d’aya tsakanin Sakkwatanci da Daidaitacciyar Hausa ko ma da sauran kare-karen harshen gabashi.
3.3 JUMLOLIN KARIN HARSHEN SAKKWATANCI
A babi na biyu an kawo nau’o’in jumlar daidaitacciyar Hausa, tare da misalan su, har nazarin ya fitar da tsarin azuzuwan kalmomin da kowace jumla ta k’unsa. A wannan babin an kawo jerin wasu daga cikin kalmomi mallakar karin harshen Sakkatanci tare da tak’aitaccen bayani dangane da karin harshen Sakkwatancin kansa. Sannan an waiwayi yadda tsarin nau’o’in ginin jumlolin karin harshen Sakkwatanci tare da nazartar su daki-daki. Ga yadda nazarin ya gudana:
3.3.1 SASSAUK’AR JUMLA A KARIN HARSHEN SAKKWATANCI
Kamar yadda Sassauk’ar Jumlar daidaitacciyyar Hausa ta k’unshi yankin Suna da kuma abin da aka fad’i a game da suna; haka ma Sassauk’ar jumlar Sakkwatanci ta k’unshi yankin suna da kuma yankin abin da aka fad’i a game da suna. Misali wasu daga cikin jumlolin Sakkwatanci.
a- Bala ya c canye abinci.
Sn aik maf lokt Aik Sn k’b
S A K
b- Musa na ya s sha ruwa
Sn aik maf lokt Aik Snk’b
c- Musa ya k kaama Zaki
Sn aik maf lokt Aik Sn k’b
S A K
d- Ali ya k kashe Kare
Sn aik maf lokt Aik Sn k’b
S A K
3.2.2 JUMLAR TAMBAYA
Jumlar tambaya ita ce jumlar da ake yi domin tambaya. Saboda haka Sakkwatanci yakan canja wasu daga cikin kalmomin na tambaya, amma kuma wasu basu canjawa, kamar yadda daidaitacciyar Hausa take fad’insu haka Sakkwatanci shi ma yake fad’insu. Ga wasu daga cikinsu.
- Ina Maryam tat tahi ?
- Waa aŋ ka aika ?
- Yaushee na za a dawo wa aiki ?
- K’ak’aa za a yi ?
- Yayaa Audu yah hwad’i jarabawa ?
- Mii Ali yas saye ?
- Wa suŋka zo d’azu ?
3.2.3 JUMLAR UMARNI
Jumlar umurni kamar sauran jumloli ita ma jumlar umurni ta karin harshen Sakkwatanci daidai take da jumlar umurni ta daidaitacciyar Hausa. Haka ma takan zo da kalma d’aya rak, a matsayin jumla, kuma ta ba da ma'ana cikakkiya, kalmar da take zuwa da ita, itace kalmar aikatau. Ga kad’an daga cikin misalan jumlar umurni a karin harshen Sakkwatanci.
- Ali tashi !
- Kabiru rubuta !
- Musa Karanta !
Haka jumlar ya kamata ta kasance amma saboda wasu dalilai sai ta koma kamar haka:
Misali:
Tashi !
Rubuta !
Karanta !
3.2.4 JUMLAR KOREWA
Jumlar korewa ta karin harshen Sakkwatanci ita ma daidai take da jumlar korewa ta Daidaitacciyar Hausa. Sai dai kuma ita wannan jumlar ta korewa ta d’an bambanta da ta daidaitacciyar Hausa a wasu bak’ak’en haruffa na Sakkatanci da suka sa’ba da na daidaitacciyar Hausa. Ga wasu daga cikin su:
- Baa Ali yas sayee ba.
- Rabi ba ta tahi makaranta ba.
- Baa kud’d’i banki.
- Agwagwa ba ta tashi sama sosai.
- Baabu ruwa a randa.
- bai dace a hana bara ba.
- Kaada kaa tahi/kar ka a tahi.
- 3
NA’DEWA
Wannan babi wato babi na uku inda aka bayyana karin harshen Sakkwatanci a bisa ra’ayoyin masana da kuma ire-iren jumlar Hausa karin harshen Sakkwatanci, tare kuma da kawo wasu misalai daga ciki. A sassauk’ar jumlar Hausa ta karin harshen Sakkwatanci an yi bayani cewa ita ma jumlar ta k’umshi yanki biyu wato yankin suna da kuma yankin abin da aka fad’i a game da suna, haka ita ma jumlar karin harshen Sakkwatanci tana bias tsarin S.A.K, kamar haka sassauk’ar jumlar daidaitacciyar Hausa. Jumlar tambaya ta karin harshen Sakkwatanci ita ma kamar jumlar tambaya take ta daidaitacciyar Hausa, jumla ce da ake yi domin tambaya. Jumlar umurni ta karin harshen Sakkwatanci, ita ma kamar jumlar umurni take ta daidaitacciyar Hausa, ana gina ta ne akan umurni. Jumlar korewa ta karin harshen Sakkwatanci, ita ma kamar jumlar korewa take ta daidaitacciyar Hausa, ana gina ta ne a kan korewa sai dai ta bambanta da ta daidaitacciyar Hausa kad’an.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.