NA
ABUBAKAR ZAHARADEEN MAINIYO
07031168630
BABI NA DAYA: GABATARWA
1.0 Shimfid’a
Wannan bincikecike mai taken Fassarar Wasu Kalmomin Kiwon Lafiya: Nazari a kan Asibitin Koyarwa Ta Jami’ar Usmanu ‘DANFODIYO (Usmanu ‘DANFODIYO University Teaching Hospital UDUTH) da Asibitin K’wararru ta Sakkwato (Specialist Hospital Sokoto) Asibitin Daji daga harshen Ingilishi zuwa harshen Hausa. An gudanar da shi ne a kan asibitoci biyu wad’anda ke cikin garin Sakkwato. Asibitin Koyarwa ta Jami’ar Usmanu ‘DANFODIYO Sakkwato da kuma Asibitin K’wararru ta Sakkwato (Specialist Hospital). Binciken zai taimaka wajen sauk’ak’a sadarwa da kuma samar da fassara mai inganci ta wasu kalmomin kiwon lafiya.
Binciken ya gudana ne a cikin babi biyar. Babi na d’aya wanda shi ne gabatarwa, ya kawo bitar ayyukan da suka gabata da hujjar ci gaba da bincike da manufar bincike da hanyoyin da aka gudanar da bincike da kuma farfajiyar bincike.
Babi na biyu ya kawo tak’aitaccen tarihin samuwar fassara da ma’anar fassara da nau’o’in fassara. Bugu da k’ari babin ya tattauna muhimmancin fassara. Babi na uku ya kawo tak’aitaccen tarihin Asibitin Koyarwa ta Jami’ar Usmanu ‘DANFODIYO Sakkwato (Usmanu Danfodiyo University Teaching Hospital) da kuma Asibitin K’wararru ta Sakkwato (Specialist Hospital Sokoto). Babi na hud’u ya kawo fassarar wasu kalmomin kiwon lafiya. Babi na biyar shi ne tak’aitawa da kammala aikin.
https://www.amsoshi.com/2017/09/30/zumuntar-bahaushe-a-zamanin-gsm/
1.1 Bitar Ayyukan Da Suka Gabata
Malamai da manazarta sun yi ayyuka daban - daban a kan fassara wasu daga cikin ayyukan da wannan bincike ya ci karo da su su ne,
Mahmud (1976) a littafinsa mai taken “Shawarwari ga mai Fassara” Mawallafin ya raba littafin ‘bangare biyu. ‘Bangare na farko ya bayar da shawara ne ga mai aikin fassara a Ingilishi zuwa Hausa. ‘Bangare na biyu ya k’unshi jerin kalmomi daban-daban da aka fassara da suka danganci aikin fassara.
Wannan aikin yana da alak’a da nawa aikin saboda a kan fassara aka yi shi amma ya bambanta da nawa aikin domin zan gudanar da bincike ne a kan fassarar wasu kalmomin kiwon lafiya ne.
Mamman (1985) a kundin digirinsa na farko wanda ya gabatar a Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya a Jami’ar Usmanu ‘DANFODIYO Sakkwato mai taken “Matsalolin Fassara labarai Ingilishi zuwa Hausa a Kafafen Yad’a Labarai” Problems of English Hausa News Translation in Media Establishments. Manazarcin ya tattauna matsalolin fassara a kafafen yad’a labarai na arewacin Nijeriya. Bugu da k’ari ya kuma yi bayanin hasashen masana dangane da fassara da matsalolin fassara dangane abubuwan da ya tattara ya kuma yi bayani a kan matsalolin fassara ta fuskar kalmomi. Duk da yake wannan aiki na da kama da nawa domin an yi nazari ne a kan fassara sai dai ya bambanta domin nawa aikin fassara wasu kalmomin kiwon lafiya ne.
Misau (1987) a kundin digirinsa na biyu mai taken “Matsalar Fassara Bak’in Kalmomi a Kafafen Yad’a Labarai” wanda ya gabatar a Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya Jami’ar Bayero Kano. Ya tattauna matsalar yanayin fassara bak’in kalmomi a kafafen yad’a labarai. Marubucin ya bayar da misalan yadda gidajen Rediyo guda biyu na Kano da Bauchi suke fassara labarai, musamman yadda ake fassara kalma d’aya ta fuskoki daban-daban.
Akko (1976) a wata mak’ala mai taken “Fassara Hanyoyinta da Matsalolinta” wadda ya gabatar a Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya ta Jami’ar Bayero Kano. Malamin ya yi k’ok’arin bayyana irin matsalolin da ake cin karo da su wajen gudanar da aikin fassara da kuma hanyoyin da za a bi wajen kauce musu.
Yahaya da wasu (1998) a kundin digirinsu na farko mai taken “Wasu Bayanai a Kan Tasirin Ma’ana da K’a’idojin Gudanar da Fassara”. Wad’annan manazarta sun yi bayanai daban-daban a kan aikin fassara a cikin bincikensu. A cikin wannan aikin sun yi bayani wane ne mai aikin fassara da yiyuwar fassara kalmomi masu alak’a da juna ta fuskar ma’ana da kuma bayani a kan kalmomi masu nuna dangantaka ta ma’ana a aikin ginin jumla kazalika kuma sun yi magana a kan k’a’idojin gudanar da aikin fassara.
Ko shakka babu akwai kama a tsakanin wannan aiki da nawa aikin domin sun yi bincike a kan fassara amma sai dai sun bambanta da nawa aikin don kuwa nawa fassarar wasu kalmomin kiwon lafiya ne.
Suleman (1999) a kundin digirinsa na farko mai taken “Hangen Dala Ba Shiga Birni Ba” wanda ya gabatar a Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya Jami’ar Usmanu ‘DANFODIYO Sakkwato, fassarar littafi ne na Adabi na Ingilishi mai suna. “The Still Born”
Hauwa (2000) a kundin digirin ta na farko wanda ta gabatar a Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, a Jami’ar Usmanu ‘DANFODIYO Sakkwato, ta fassara littafin “The ‘Birtuous Woman” wanda ta kira "Mace ta Gari" wannan ma fassara ce ta Adabi.
Muktar (2002) a kundin digirinsa na farko mai taken “Bijirewar Mabarata” wanda ya gabatar a Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya Jami’ar Usmanu ‘DANFODIYO Sakkwato, fassara ce ta littafin “Beggers Strike”.
Malumfashi da Yakasai (2004) a cikin littafinsu mai suna “Translation An Introductory Guide” Marubutan sun tattauna a kan fassara a fagen ilimi da kuma ci gaban fannoni. Bugu da k’ari sun kawo ra’ayoyi da gudummuwar fassara wajen yad’a labarai da matsalolin fassara da ilimin furuci da naso na harshen Ingilishi da Larabci a kan aron kalmomi a harshen Hausa.
Sar’bi (2005:128) ya gabatar da wata mak’ala mai taken "Are Idioms Translatable?" Shin ko ana iya fassara adon harshe Marubucin ya tattauna ire - iren fassara da k’warewa ko cancanta a aikin fassara ko rashin k’warewa a kan fassara.Bugu da k’ari ya kawo abubuwan da ake buk’ata ga mai aikin fassara domin kasancewarsa k’wararren mai fassara daga harshen Ingilishi zuwa Hausa.
Abdullahi (2010) a kundin digirinsa na farko mai taken “Matsalolin Fassara a Kafafen Yad’a Labarai: Ke’ba’b’ben Nazari A Kan Rediyon Jihar Zamfara” wanda ya gabatar a Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya a Jami’ar Usmanu ‘DANFODIYO, Sakkwato. Manazarcin ya tattauna matsalolin fassara da ma’anar fassara da ire-irenta da matsalolin fassara bak’in kalmomi a Gidajen Rediyon Jihar Zamfara.
Yakasai (2012) ya gabatar da wata mak’ala mai taken “Tasirin Fifikon Fassara a Cikin Harshen Uwa Bisa Harshe Na Biyu a Hausa” Wadda aka gabatar a Taron Gabatar da Mak’alu na Tsangayar Fasaha da Addinin Musulunci Jami’ar Usmanu ‘DANFODIYO, Sakkwato.Malamin ya yi tsokaci ne a kan fifikon fassara cikin harshen uwa bisa ga harshe na biyu a aikin fassara da ingantacciyar fassara da sigar fifikon fassara da gudummuwar al’ada da harshe wajen aikin fassara .
Yakasai (2012) bugu da k’ari ya gabatar da wata mak’ala mai taken “Ingantacciyar Fassara: Fasaha ko Kimiyya?” Malamin ya kawo tarihin gwagwarmaya d’an Adam ta amfani da hanyoyin sadarwa ta hanyoyi daban-daban da ma’anar fassara da yanayinta da tsarin ingantacciyar fassara tare da bayyana fassara a matsayin aikin fasaha da kimiyya.
Funtuwa (2016) a kundin digirinta na farko mai taken “Fassarar Ke’ba’b’bun Kalmomin Tattalin gida guda d’ari (100) daga harshen Hausa zuwa harshen Ingilishi” wanda ta gabatar a Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya a Jami’ar Usmanu ‘DANFODIYO, Sakkwato. Ta kawo kalmomin tattalin gida guda d’ari (100) na Hausa ta kuma fassara su a cikin harshen Ingilishi.
Dukkan wad’annan ayyuka da suka gabata suna da dangantaka da nawa binciken domin sun yi nazari a kan aikin fassara amma sai dai sun bambanta da nawa domin nawa aikin zai gudana ne a kan fassarar wasu kalmomin kiwon lafiya daga harshen Inglilishi zuwa Hausa domin kyautata sadarwa a tsakanin al’umma.
https://www.amsoshi.com/2017/09/27/nahawun-ke%c6%83a%c6%83%c6%83un-kalmomin-intanet-na-hausa/
1.2 Hujjar Ci Gaba Da Bincike
Abin da ya haifar da yin wannan binciken shi ne k’ok’arin samar da k’arin ayyuka da ake da su a wannan fage na fassara. Samuwar sababbin tunani na kimiyya da cututtuka da kayan aiki shi ne ya haifar da tunanin gudanar da wannan bincike wanda ake hasasshen zai bayar da gudummuwa wajen sauk’ak’a sadarwa da inganta ayyukan kiwon lafiya.
1.3 Manufar Bincike
Babban manufar wannan bincike ita ce fassara sababbin tunani na kimiyya da cututtuka da kayan aiki da kuma ‘bangarorin asibiti domin sauk’ak’a sadarwa tsakanin al umma. Haka ma akwai bayar da gudummuwa ga masu aikin fassara ayyukan kiwon lafiya da d’alibai masu bincike a kan cututtuka musamman a jihohin Sakkwato da Zamfara da kuma Kebbi a tsakanin ma’aikata da marasa lafiya.
1.4 Hanyoyin Gudanar da Bincike
Daga cikin hanyoyin da aka bi wajen gudanar da wannan bincike akwai tattaunawa da ma’aikatan kiwon lafiya a kan yadda suka fassara bak’in kalmomi na cututtuka da kayan aiki da sassan da ke cikin asibitocin da kuma d’akunan bincike. Haka kuma an ziyarci asibitocin Asibitin Koyar da ta Jami'ar Usmanu ‘DANFODIYO da Asibitin K’wararru ta Sakkwato (Usmanu ‘DANFODIYO Uni’bersty Teaching Hospital UDUTH) da (Specialist Hospital Sokoto) don samun bayanai da suka zama fitila a kan wannan bincike.Bugu da k’ari an yi amfani da wasu ayyukan fassara da suka gabata da k’amus – k’amus na Hausa zuwa Ingilishi.
1.5 Farfajiyar Bincike
Wannan bincike ya gudana ne a garin Sakkwato a asibitin Koyarwa Ta Jami’ar Usmanu ‘DANFODIYO (Usmanu ‘DANFODIYO University Teaching Hospital) da Asibitin K’wararru Ta Sakkwato (Specialist Hospital Sokoto) kuma ya ke’banta ne kawai ga fassara wasu kalmomin kiwon lafiya. An fassara kimanin kalmomi guda d’ari (100).
1.6 Nad’ewa
Wannan babi na d’aya shi ne gabatarwa. Babin ya kawo bitar ayyukan da suka gabata da hujjar ci gaba da bincike da manufar bincike da hanyoyin gudanar da bincike da kuma farfajiyar bincike.
[…] Fassarar Wasu Kalmomin Kiwon Lafiya: Nazari Kan Asibitin Koyarwa Ta Jami’ar Usmanu Danfodiyo (Usma… […]
ReplyDelete[…] Fassarar Wasu Kalmomin Kiwon Lafiya: Nazari Kan Asibitin Koyarwa Ta Jami’ar Usmanu Danfodiyo (Usma… […]
ReplyDelete