Ticker

6/recent/ticker-posts

Sansamin Gamji Mai Cika Bakin Akuya: Bitar Littafin Sanyinna District: Events, Trends and Turning Points



Ficen mutane da ɗaukakarsu a duniyar zamaninsu yana cikin tarihinsu. Tarihinmu wani madubin ƙyallaro asalinmu ne da ɗabi’unmu da dangantakarmu da zamaninmu. Wanda ya taskace tarihinsa, ya kundace shi, ya hutar da al’ummarsa, ya agaza wa ƙasarsa, ya rage wa zuriyarsa dawarar kalato gutsattsarin labarin kunne ya girmi kaka na taliyon sama wa kai tushe cikin ƙila-wa-ƙala. Tsaftatacciyar hanyar da za a yi wa Turawan mulkin mallaka zanga-zanga, da tawaye, da ature, ga bahaguwar fahimtar da suka yi wa Daular Sakkwato cikin ƙazantaccen harshe a rubuce, ita ce, ma’ilmantar kowace ƙasa, da gunduma, su sake kakkaɓe kundin tarihinsu. Tabbas, babu…
Sansamin Gamji Mai Cika Bakin Akuya:
Bitar Littafin Sanyinna District: Events, Trends and Turning Points

Edited by
The Maina Research Committee
Published by Wali Foundation, Sanyinna.


Mai Bita
Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya,
Jami’ar Umaru Musa Yar’adua, Katsina.
Katsina-Nijeriya.

An gabatar da bitar ranar Asabar 10th ga Mayu, 2014 a makarantar GSS Sanyinna da ƙarfe goma na safe a ƙarƙashin jagorancin Right Honourable Speaker Kakakin Majalisar Tarayya Alhaji Aminu Waziri Tambuwal.

Gabatarwa
Ficen mutane da ɗaukakarsu a duniyar zamaninsu yana cikin tarihinsu. Tarihinmu wani madubin ƙyallaro asalinmu ne da ɗabi’unmu da dangantakarmu da zamaninmu. Wanda ya taskace tarihinsa, ya kundace shi, ya hutar da al’ummarsa, ya agaza wa ƙasarsa, ya rage wa zuriyarsa dawarar kalato gutsattsarin labarin kunne ya girmi kaka na taliyon sama wa kai tushe cikin ƙila-wa-ƙala. Tsaftatacciyar hanyar da za a yi wa Turawan mulkin mallaka zanga-zanga, da tawaye, da ature, ga bahaguwar fahimtar da suka yi wa Daular Sakkwato cikin ƙazantaccen harshe a rubuce, ita ce, ma’ilmantar kowace ƙasa, da gunduma, su sake kakkaɓe kundin tarihinsu. Tabbas, babu mai nunin gidansu da hannun hagu (hauni). A fahimtarmu, da dahuwa, da suya, da banda, duk gashi ya fi su sanin asirin wuta. Ga zatona, tunanin haka ne ya sa Sanyinnawa suka yi wa tarihin ƙasarsu taron dangi. To! Ga wuta ga masara.
Gadam-Gadam
Tsananin zumuɗin zuwa gona, da kwana da takaicin aiki, da yini jin haushin kasala, da mantasala, ya sa zarumi yini neman gatarinsa cikin gona alhali yana a wuyansa rataye bai ankara ba. Haka ko aka yi, tsananin ɗokin kare mutuncin Sanyinna da Sanyinnawa, ya shagaltar da ‘yan bokon Sanyinna suka yi ta fafitikar rubuta tarihinsu cikin Turanci suka manta cewa, babu Bature ko baƙo a cikin garin Sanyinna. Idan aka bi fassarar, “lokacin abu a yi shi” ba su yi laifi ba. In aka harari nassin kowane tsuntsu kukan gidansu yake yi, rafkannuwar da suka yi ba ta fi ƙarfin ba’adiyya ba. Taken littafin a Turanci shi ne: SANYINNA DISTRICT: Events, Trends, and Turning Points:Gundumar Sanyinna Jiya da Yau”. Tun a sunan littafin, mai karatu ya san mazajen da suka tsara aikin hannu ya iya jiki ya saba. Tun a sunan littafin an gayyato masu iya karatu da su buɗa su gani, ruwa na ƙasa sai ga wanda bai tona ba. A wajenmu ɗalibai, idan sunan littafi ya zaunu da gindinsa, to komi ya yi, an ba gwauro ajiyar mata.
Fuskar  Littafin
        A ganin Bahaushe, ajin hular daƙiƙi daban yake, karin hular wawa, ba sai an tambaya ba, ɗaurin yaba/walkin raggo ɗuwawu ka ba da labarinsa. A fuskar bangon littafin, an kauce wa ado na ƙawata shi da launuka domin kauce wa Bafulatanin ra’ayi. Ba a zana tamburan yaƙi da makamai ba, domin sanin ko ba a faɗa ba sunan mijin iya baba. Tarihin Sanyinna ba ya buƙatar barazanar jan bango (makari) tun tuni take da kirarin “Gambun Yamma” ga masu jihadi. Da dakarun Kabawa suka taya ta, su da kansu suka ce, “Ana shaggu ƙasa” in ji raƙumi da ya taki kunama. An dai tsara bangon littafin bisa fasahar shimfiɗar fuska ya fi shimfiɗar tabarma. Ba barazana, bale kirari ko bugun gaba, ko ba a faɗa ba karatun Farfesa Ibrahim Maidangwale Tubali (Narambaɗa) ya ratse su, a faɗarsa:
Jagora: Ƙarya ce sukai
Yara  : Wanda duk ka faɗin za shi yi
          : Ba shi yin komi
Gindi: Amadun Bubakar gwarzon Yari
          : Dodo na Alƙali
Goshin Aiki
        Bangon farko na littafin an mamaye shi da hoto da tarihin shugaban bincike. A shafi na biyu aka maimaita taken littafin. A shafi na uku aka zo da ƙawataccen taswirar ƙasar Sanyinna domin sai an san nauyin kaya ake jingar ɗaukar su. Bisa ga adalcin marubuta bincike, shafin da ya mara wa taswirar Sanyinna baya, yana ɗauke da hoton Arɗon Sanyinna Alhaji Shehu Garba, aka yi gambu da shi domin mai shirin ratsa kundataccen tarihin Sanyinna ya ga surar mai Sanyinna. A bango na biyar, aka jero bishiyar li’irabin tsarin siyasar ƙasar Sanyinna a kan ginshiƙi ɗaya, reshe shida, da saiwowi arba’in da huɗu. Abin ban sha’awa, Arɗon Sanyinna ya yi wa littafin gabatarwa ga jama’a. A tsarin godiyar littafin, marubutan sun nuna ƙwarewa da taka-tsan-tsan da kaffa-kaffa gudun hawa dokin zargi, don haka suka gode wa Arɗo, da iyayen ƙasa shida na Sanyinna, da dukkanin Sanyinnawa, kana suka kwakkwahe ga waɗanda aka nemi sa hannunsu a matakai daban-daban . Hatta da haƙƙin mallakar littafin ga kwamitin Maina, wanda ya haɗa littafin aka rataya shi tare da cikakkiyar lambarsa ta zama tabbataccen littafi wallafaffe ISBN978-931-521-5. Dattiɓen da suka yi limancin wannan gagarumin aiki su ne:
1 Alhaji Umar
2 Alhaji Muhammadu Modi Ɗandare
3 Malam Muhammadu Sajo
4 Dr. Muhammadu Arzika Ɗanzaki PhD
5 Marafan Garam Alhaji Usman Umar
6 Alhaji Sani Abdullahi
7 Malam Bala Kada Gudum
8 Malam Adamu Musa Gudum
9 Alhaji Sahabi Ɗanfari
10 Madawakin Sanyinna Alhaji Bello Mailato
11 Alhaji Sahabi Muhammad
12 Magajin Saida Alhaji Bello Muhammad
13 Alhaji Yusuf Ladan
14 Wali Foundation (Mawallafa Littafin)
Ƙunshiyar Littafi
          Tun ba a shimfiɗa buzun karatu ba, sunayen waɗanda suka jagoranci wannan bincike ya tabbatar da cewa, ba kwasan karan mahaukaciya aka yi wa tarihin Sanyinna ba. Da jin sunayen, an san, kumbu ya gamu da marfi ta bakin Zamfarawa sun ce, “Gumi ta gamu da Anka”. Ban yi wa littafin dubin tsoro ba, ba kuma shan ruwan tsuntsaye na yi masa ba. Don haka, ga hisabin ƙididdigar ƙunshiyarsa kamar haka:
 ● Shafukan tsurar aikin littafin ɗari biyu da arba’in da bakwai (247)
● Yawan babukansa takwas (8)
● Kowane babi yana ɗauke da fasula kamar haka:
 Babi na 1 fasali 6
Babi na 2 fasali 5
Babi na 3 fasali 13
Babi na 4 fasali 9
Babi ba 5 fasali 15
Babi na 6 fasali 10
Babi na 7 fasali 14
Babi na 8 fasali 5
Adadin fasula sittin da bakwai (67)
Taken Matashiyar Babukan Littafi
1 Farfajiyar ƙasar Sanyinna da tarihinta, shafi na 1-9
2 Dabashirin mazaunin Sanyinna a zamanin Jihadi, shafi na 10-18
3 Cigaban walwala da tattalin arzikin Sanyinna, shafi na 19-42
4 Fitattun daba da daulolin shawagin birnin Sanyinna, shafi na 43-55
5 Jagororin masarautun ƙasar Sanyinna, shafi na 56-78
6 Tsarin siyasar sarautun ƙasar Sanyinna, shafi na 79-208
7 Haɗin kan addini da ‘yancinsa a ƙasar Sanyinna, shafi na 209-230
8 Haihuwar boko a garin Sanyinna, shafi na 231-242
9 Fihirinsa, shafi na 243-247
10 Bangon ƙarshe hoton Magatakardan Bincike da Tarihinsa
Sanyinna Gamji Matattarar Tsuntsaye
        Duk wani gari da ke bangon ƙasa, mutanen da ke cikinsa daga wani wuri suka fito. Mahalicci bai taɓa ruwan mutane a wata ƙasa ko wani gari suka tsiro ba. Haka kuma, bai taɓa ruwan mutane a wata karkara ba. Komai taƙamar mutum, akwai wurin da kakanninsa suka fito, domin Bahaushe cewa ya yi, “kowa ya yi ƙarya ana samun ɗan garinsu”. Garin da ya samu tagomashin baƙi ya yi arziki. Ga al’ada, mutane tsuntsaye ne, ba su taɓa tabbata a ice ɗaya ba. Idan gari ya samu amincewar mutane ‘yan zuriya daban-daban, ƙabila daban-daban, ana sa ran masu gaskiya suka kafa shi, domin ƙarya ba ta taɓa haɗa kan mutane suka yi gari ba. Ku rake ni Tubali mu tambayi Farfesa Ibrahim Maidangwale Tubali (Narambaɗa) ga yadda ya yi fashin baƙin:
Jagora : Na hore ki gaskiya bari tsoron ƙarya
Yara  : Mai ƙarya munahuki Allah su yaƙ ƙi
Jagora : Har yau ba mu ga inda an ka yi mai ƙarya ba
Yara  : Amma ita gaskiya gari da mutane tay yi
Gindi : Gwarzon Shamaki na Malam toron giwa
          : Baban Dodo ba a tamma da batun banza 
          Madalla! To, mu dawo Sanyinna. Yau ƙimanin shekara takwas da aka yi ƙididdigar adadin yawan jama’a a Nijeriya (wato shekarar 2006). Sanyinna na da yawan mutane dubu sittin (60,000). Da yake, Sanyinnawa ba raggaye ba ne ga noman rani bale ga na damina. Haka kuma, a addinance ba su da aljihun baya duka mabiya sunnar Annabi (SAW) ne aƙidance da aikace, musamman a gefen aure. Idan aka duba, cikin tazarar shekara takwas, an gwamatsi dubu saba’in zuwa tamanin (70,000-80,000). Garin Sanyinna na da ƙasashe shida (6), da Uban ƙasa shida (6), da ƙauyuka talatin da ɗaya (31). Babban birnin Sanyinna na da unguwowi goma sha uku (13).
1 Shiyar Malle
2 Shiyar Wanzamai
3 Shiyar Tsibiri
4 Shiyar Sakkarawa
5 Shiyar Dutsi
6 Shiyar Fulani
7 Shiyar Maƙera
8 Shiyar Ƙofar Yamma
9 Shiyar Illela
10 Shiyar Sabon Gari
11 Shiyar Baichi
12 Shiyar Tudu
13 Shiyar Nasarawa
Kallon waɗannan unguwowi da idon al’ada, da tarihi, ya isa ya tabbatar da zuman Sanyinna sansamin gamji mai cike bakin akuya. Ba a yi kure ba idan aka ce, gari ne da ya tattaro al’ummomin Afirka ta Yamma musamman Hausawa da Gobirawa da Adarawa da Kabawa da Fulani da Zabarmawa da Zazzagawa da Arawa da Azbinawa da Wolof da Katsinawa da Barebari. Danƙari! Ko da ganin kan kura ya ci mutum. Tattara ire-iren waɗannan ƙabilu wuri ɗaya, a samu mubayi’arsu gaba ɗaya, wani tsintuwar guru  a cikin suɗi ne. Cewa wasu mazaje sun yi wa irin wannan gari barazana, labarin ƙanzon kurege ne. Irin nagartattun mutanen da suka yada zango garin Sanyinna, yi mata cin daƙuwar makaho labari ne sai dai a yi wuta-wuta haɗiyar kunamar kwaɗo tun ba a haɗe ba kai ya yi zufa. A yaƙin Alƙalawa Sanyinnawa sun yi wa rundunar Gobirawa a ƙarƙashin jaruminsu Kusu kwancin ɓauna. A shekarar 1851 Sanyinnawa sun yi wa Sarkin Kabi Yakubu Nabame bindigar ‘yan tauri, wato ke gawa, mai ke gawa, abin da an ka nuna gawa, gawa uku jere ga juna.
          A fagen noma Sanyinna ta yi wa yunwa ƙofar raggo. Ta fuskar gwagwarmayar jihadi, Sanyinna manyan kashi iyayen ciniki ce, domin mujaddadi Ɗanfodiyo ya limanci jama’a da La’asar a Sanyinna cikin dakon jiran abokan gaba. A ilmin boko, suna gaba an ka yi baya. Malam Umaru Ɗanboko ya fara rage wa alli tsawo a matsayinsa na shugaban makarantar Firamre ta Yabo, 1932. Ƙazantaccen tarihin boko, da dasisarsa, da zurmuguɗɗun Yahudu da Nasara da ke ciki bayyane yake a fafatawar Giginya da Sarkin Musulmi Attahiru Cimmaula, da turnuƙun gumuzun Satiru na shekarar 1906. Waɗannan abubuwa suka ba masu hankali tsoron boko, Sanyinnawa na daga cikinsu. Shekarar boko talatin (30) yana dawarar wurin aje kaya a birnin Sanyinna. Sanyinnawa ba su ba shi masauki ba sai a shekarar 1962. Ban ga laifin Sanyinnawa ba, domin kakansu Ɗangaladima Ibrahim na cikin shuhada’un shekarar 1903 da suka ce wa Turawa komi taka zama ta zama! Yana basaraken Sanyinna ya aje rawani ya kai wa Allah zubin adashin da ya yi musu alkawalin kwasan ƙarshe a Firdausi.
Ginshiƙan Ƙasar Sanyinna
        Babban abin da ya mamaye ƙunshiyar littafin shi ne babi na biyar da ya yi darzajen Sarakunan ƙasar tun daga Muhammadu Garo-Hawaye (1808-1893) ya zuwa Alhaji Shehu Garba (1999-Yau). Gari-Hawaye ya rasu a Sanyinna, 1833. Muhammadu Maidoro ya rasu 1846. Abubakar Bube ya rasu 1886. Haliru  Ɗankogi ya rasu 1889. Ibrahim ya yi shahada 1905 a Burmi. Arabu ya rasu 1905. Mu’alleyiɗi an cire shi 1907. Muhammadu Kaka, ya yi murabus 1922. Shehu, ya yi murabus 1953. Malam Umaru an yi masa murabus 1975. Alhaji Garba ya rasu 1999. Alhaji Shehu Garba ya hau karaga 1999.
          Ya zuwa yau (2014), Sanyinna ta albarkatu da Sarakuna (12). Biyar sun rasu a karagar mulki. Ɗaya ya yi shahada a gumuzun Burmi. Huɗu sun ci karo da ƙaddarar shugabanci, (ɗaya ya yi murabus, uku an cire su). Fatarmu Allah ya ba da zama lafiya. Bisa ga tsarin littafin, duk wani mai haƙƙi a ƙasar Sanyinna an ambace shi da matsayinsa da irin gudunmuwarsa. A koyaushe Sardauna Amadu na gaya wa shugabanni, ba a gamawa, ba a iyawa, ba a yabawa. Farfesa Ibrahim Maidangwale Tubali (Narambaɗa) cewa ya yi:
Jagora: Yau mai ashararu ya kaɗe
           : Duniya ta yi mai fashi
Yara   : Ya san ba a kwarjini ga mutanen Hausa
           : Kowac ce shina iyawa ga fili nan
           : Sai ya ƙetare gidanai ba ban kwana
Gindi:  Gwarzon Shamaki na Malam toron giwa
          :  Baban Dodo ba a tamma da batun banza  
Gyara Kayanka
        Na tabbata, mutum duk ɗan tara ne. Tilas cikin ayyukansa a ci karo da mantuwa, nan da can. A ganina, irin su maƙera Umaru ɗan shekara ɗari ba biyu (98) wata babbar hujja ce ga tarihin ƙasar Hausa ba ma Sanyinna kawai ba. Na tabbata ba a rasa irin sa cikin mata ba. Ba mu ji wurin da aka ziyarce su ba. An dogara ga ayyukan da Turawa suka yi da yawa. A nan, an yi saki zari kama tozo. Daga cikin sarakunan sana’o’i, ban ji zarmoɗon Makaɗan Sanyinna da Sarkin Ruwa ba. Ko kun manta da makaɗan kokuwa da yaƙi aka yi wa Kabawa barazana suka ji tsoron mai da gamin gumuzun Taushin Gilme? Idan dai ba a manta da a share jini a koma wasa ba, ya kamata sana’ar kamun kifi da sarakunansu su samu fasali a Littafin. A da, a fagen dambe, da an ce: “Ga Ɗansanyinna” ko an fitar da takensa naira ta gama yawo. Na tabbata an ɗan manta ne, domin aikin Magaji ba ya hana na Magajiya. Wajibi ne ga Sanyinnawa su tashi tsayin daka su nemo jerin mazajen Sanyinna da suka kwanta dama a Taushin Gilme da cikakkiyar salsalarsu. Muna nan muna bin ku bashin fassara wannan littafi zuwa Hausa.
Naɗewa
          Mun dai ji Sanyinna, mun ji irin nata matsayi a rubuce. Kiran da nike yi ga dukkan ‘yan Nijeriya shi ne, ƙasar duk da babu zama lafiya ta tsahi da aiki. Fitinar ƙabilanci da siyasa da addini alamomin naɗe duniya ne. Duk da haka, yanayin da ake son a sa ƙasarmu ciki, Musulmi da Musulunci ake son a yi wa kashin mahaukacin kare. Sarakunanmu sun sa baki, an yi biris da su, ka ce kare ya taki sisi. Gwamnoninmu sun yunƙuro, an yi tsayin dakan yi musu haihuwan guzuma ɗa kwance uwa kwance. An raba kanun malamanmu da kwabon gishiri. An tarwatsa mabiya da taɓa-ka-lashe. A yau, sai a sallar jana’iza kawai fuskokinmu ke kallon juna da rahama. An girke tsoro a zukatan ‘yan siyasarmu kowanensu jam’iyyarsa ita ce kalimar shahadarsa. Yau ƙiri-ƙiri Musulmi ne ‘yan dako da alaro a Abuja. Su ne marayu a manyan kujerin gwamnatin tarayya. Su ne ‘yan tsaron gadirum a gidan soja da ‘yan sanda da ma’aikatun tsaro. Shekaran jiya ban da jiya, da sunan Maitatsine aka karkashe mu. Shekaran jiya, da sunan ‘yan Izala da Ɗariƙa aka yi muna kisan kiyashi. Jiya da sunan ‘yan ta’adda aka yi wa ‘yan uwanmu ruwan wuta. Yau, da sunan Boko Haram aka yi muna taron dangi da ba a taɓa yin irinsa muni a Nijeriya ba. Gobe da sunan ‘yan Allahu Akbar! Ko masallata za a ƙarƙare abin da ya rage. Wawaye, dolaye, daƙiƙu, takkwalai, ‘yan siyasa da ‘yan boko da ma’aikatan gwamnatinmu na ta sake leɓo suna jiran gawon shanu. Da kwance Sanyinnawa suka yi, yau wa ka tsayi sauraron tarihinsu? Allah wadaran naka ya lalace in ji ɓauna da ta ga shanun noma, wai ji wurin da mawaƙin marasa gaskiya ya fi masu gaskiya hankali! Malam Gambo ke kiran wani ƙwaronsa da cewa:
Jagora: Me kaka shakka
           : Ga ni ga ka!
           : Ɗauri kaka shakka ko macewa?
           : Komi adadinai na tahowa
           : Mai rai wada Allah ya’aje shi
           : Ba hurce iyaka za shi yi ba.  

Post a Comment

2 Comments

  1. […] Sansamin Gamji Mai Cika Bakin Akuya: Bitar Littafin Sanyinna District: Events, Trends and Turning Po… […]

    ReplyDelete
  2. […] Sansamin Gamji Mai Cika Bakin Akuya: Bitar Littafin Sanyinna District: Events, Trends and Turning Po… […]

    ReplyDelete

ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.