Shugabancinmu Da Cigabanmu: A Tsarin Kasarmu


    Mahalicci halitta da Ya nufi Æ™aga halittocinSa da Ya shimfiÉ—a su a duniyarmu da muke zaune, a kan tsarin shugabanci ya tsara abinSa. Buwayayye Ya wanzu gabanin kowa da komai. Tun a nan, mai hankali ya san ana karantar da shi muhimmancin gabaci. Ya mamaye komai da komai bayan da Ya halicci komai da komai. A nan, ana yi muna hannunka mai sanda, ga martaba irin ta gabaci. Zai ci gaba da wanzuwa bayan fakuwar duk wani wanzajjen abu a bangon duniya. Wannan ishara ce ta tabbatar mana da cewa, umurnin gabaci na aiki da furuci sun cancanci su soke aiki da furucin duk wani….
    ---------------------------------------------
    Daga
    Aliyu Muhammadu Bunza
    Sashen Koyar da Harsunan, Nijeriya
    Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’adua, Katsina
    Jahar Katsina, Nijeriya
    --------------------------------------------

    Takardar da aka gabatar a taron  Æ™ara wa juna sani na ‘yan’uwa Musulmi Æ™arÆ™ashin Jama’atul Muslimin, jagorancin Malam Muhammadu Bello ÆŠanmalam a makarantar Nana Asma’u ranar Alhamis ta Æ™arshen Safar, 1435 daidai da  2 ga Junairu, 2014 da Æ™arfe takwas na yamma
    Da suna Allah mai rahama mai jinƙai. Tsira da aminci su tabbata ga Manzon Allah Muhammadu ɗan Abdullahi (SAW) da iyalansa da sahabansa da waɗanda suka yi koyi da su ya zuwa ranar sakamako.
    Gabatarwa:
    Mahalicci halitta da Ya nufi ƙaga halittocinSa da Ya shimfiɗa su a duniyarmu da muke zaune, a kan tsarin shugabanci ya tsara abinSa. Buwayayye Ya wanzu gabanin kowa da komai. Tun a nan, mai hankali ya san ana karantar da shi muhimmancin gabaci. Ya mamaye komai da komai bayan da Ya halicci komai da komai. A nan, ana yi muna hannunka mai sanda, ga martaba irin ta gabaci. Zai ci gaba da wanzuwa bayan fakuwar duk wani wanzajjen abu a bangon duniya. Wannan ishara ce ta tabbatar mana da cewa, umurnin gabaci na aiki da furuci sun cancanci su soke aiki da furucin duk wani mahaluƙi. Da Allah bai kasance haka ba, muna da damar mu zaɓa wa kanmu tsarin da ya dace da son zuciyarmu. kasancewarSa yadda Ya kasance, Ya rufe muna kowace ƙofar tunanin kanmu ga abin da ya shafi siyasar rayuwarmu face sai mun tuntuɓe Shi domin ta yau muka sani, ta jiya wajenSa aka samu labarinta, ta gobe kuwa Ya keɓanta ga ilminSa. A bisa ga wannan salo, za mu gina tattaunawarmu. Allah Ya yi muna jagora.
    Mene Ne Shugabanci?
    Shugabanci ya Æ™unshi abubuwa biyu manya-manya a tsarin tafiyar da rayuwar É—an Adam. Na É—aya shi ne, shugabanci kansa. Na biyu shi ne “mulki” wanda yake É—a ne daga cikin ‘ya’yan shugabanci. Sunan jikansu “Iko” shi ya sa suka fi jikansu hankali da sanin ya kamata. A kowace irin fasara ta addini ko ta zamani waÉ—anan abubuwa uku: shugabanci da mulki da iko jejjere suke tafiya kamar kashin awaki.
    A luga shugabanci na da ma’anar rigaya ko gabacin abu na haihuwa ko shekaru ko sani ko Æ™warewa a sana’a ko a fahimtar wani abu. A wata luga yana iya É—aukar ma’anar “Jagora” kamar makaho da majayi. Ba kuskure ba ne a fassara shi da “Zagi”, domin a Hausance sarki “Uban Zagi” ake ce masa. An yi daidai idan aka ce masa “Madugu”, domin ayarin fatake ba su san wani ba shi ba. A dabin caca shi ne “Kartagi” ba wanda ya isa ya buÉ—a bajau ba da umurninsa ba. A fassarar jinsi a kira shi “Maduga” saboda mata ba su san kowa ba sai ita. Idan ta hau karagar mulki ita ce “Magajiya” a fagen bori take da suna “Inna”.
    A wajen Bahaushe, kalmar “Sarki” baÆ™uwa ce, wadda aka sani “Gogarma”. Da aka É—an ja zango kalmar “Shugaba” ta karÉ“e tuta. Kalmar “Shugaba” ita ta haifar da “shugabanci”. Dukkaninsu sun Æ™unshi kalmomi biyu ko uku a doguwar fassara. Kalmar farko ita ce “sha” wadda ta koma “shu” a gaÉ“oÉ“in. Kalma ta biyu ita ce “gabaci” ko “gaba” da “ci”. “Sha” É—in nan ko “shu” an gajarta su ne, ga alama ma’anarsu “shiga” idan aka haÉ—a da “gaba” sai a samu “shiga gaba”. Haka kalmar Larabci “ra’is” daga kalmar “kai” na É—an Adam aka cirato ta. Dalilin Larabawa ke nan na yi wa kai kirari “sayyidul jasadi” shugaban jiki. Turawa su ce da ita “President” a ma’ana su ce: The elected head of a republic ko The head of an organization. A kowace fassara daga fasarorin an samu kalmar “head” wadda ta yi canjaras da ma’anar Bahaushe da Balrabe, don a fuskar “shugabanci”, za mu ce, shi ne jagorar jama’a wanda suka aminta da shi wajen jiÉ“intar al’amuransu na siyasa, zamantakewa da addini. Don haka shugabanci shi ne tafiyar da al’amuran jama’a bisa ga yardarsu da amincewarsa ga dokokin da suka yi imani da su. Shugabanci shi ne waÆ™iltar mutane ga abin da suka miÆ™a wuya gare shi bisa ga tafarkin da zai ciyar da su gaba ga manufofinsu da daidaita tunaninsu. Wanda aka damÆ™a wa shugabancin shi ne “shugaba” don haka ala tilas shugaba ya kasance:
    i)       WaÉ—anda yake jagoranta suka zaÉ“e shi shugaba.
    ii)      WaÉ—anda yake jagoranta sun yarda da shugabancinsa.
    iii)     Yana jagorantar mutane bisa ga abin da suka yarda a kai.
    iv)     Ya yi imani da aikin da aka waÆ™ilta shi ba wanda yake so na ransa ba.
    v)      Ya É—auki waÉ—anda yake jagoranci iyalansa domin da haÉ—in kansu ya kasance shugaba.
    vi)     Idan aka rasa É—aya daga cikin (i-v) matsala ta tashi daga shugabanci ta koma mulki.
    Mene Ne Mulki?
    A hankalin tuwo muna hangen mulki a matsayin wani zamani na shugabancin wani shugaba. A bayyananiyar magana mulki ya fi da haka. Mai mulki shugaba ne amma ba mai shugabanci ba. WataÆ™ila yana shugabancin bisa irin tsarin da ya Æ™irÆ™iro da kansa. A wani lokaci a same shi bijirarrare ga buÆ™atun mutanensa. Wanda ya hau gadon da Æ™arfin tuwo ko Æ™arfin maguÉ—i ko yaudara mulki yake yi ba shugabanci ba. A tsarin mulki, ba a kula da bin wata doka ta addini ko ta hankalin tuwo ba, shugaba shi ne wuÆ™a, shi ne nama, shi ne É—an doka, shi ne alÆ™ali, shi ne yari kuma shi ne ma’ajin baitalmalin hukuma. WaÉ—anda duk ake gani da waÉ—annan muÆ™amai a tsarin shugabanci na mulki, hoto ne kawai je ka na yi ka. Shugabancin irin na mulki ba a sassauta wa adawa, na Æ™asa bai isa ya ci gyaran na sama ba. A kujeran mulki ganin mai mulki shi ne gani, ganin waninsa makafta ne. Dalilin Larabawa ke nan na kiransa muluuku Turawa su ce dictator don haka Hausawa ke kiransa Iko.
    Wane Ne Shugaba?
    Masu zargin Musulunci da rashin wayewa ga tsarin shugabanci adawar gado ce suke son su tabbatar da ƙarfi da yaji. Gabanin a samu kyakkawan shugabanci sai an samu shugaba nagari nagartace da ingatattun nassoshi suka ce a kula da:
    i)                   Yadda ya shigo majalisa. ZaÉ“ensa aka yi a addinance bisa ga shura? Ko zaÉ“ensa aka yi a al’adance bisa ga gadon-na-gaje ka? Ko zaÉ“ensa aka yi bisa ga kafirtaccen tsarin da ya ce (wai!) babu ruwansa da kowane addini? Ko shugaban Æ™addara ne irin na juyin mulki ko mulkin mallaka? A tsarin shari’a zancen “shura” kawai ta sani. Sauran fuskokin ba su da sahihin nassi, sai dai ba ta ce, a yi fito-na-fito da su ba idan sun kai ga karaga. Yi musu É—a’a wajibi. Gaggauta neman mafita daga tsarinsu wajibi ne. Wane tsari ya fi shari’a ido biyu na hangen lamari?
    ii)                Addinin Musulunci ya shafe dukkanin addinan da ke gabaninsa. Don haka, a wajen Allah babu wani addini sai shi. Wanda duk ba shi yake yi ba, ya kafirta sunansa kafiri. A sahihin nassi dole shugaban da Musulmi zai zaÉ“a wa kansa ya kasance Musulmi. Komai saÉ“on Musulmi yana nan tare da sunan matuÆ™ar bai halasta saÉ“on Allah ba. Komai adalci da natsuwa da Æ™ima da fasaha da basirar kafiri yana nan kafiri matuÆ™ar bai miÆ™a wuya ga saÆ™on Manzo (SAW) ba. Duk wata jam’iyyar da Musulmi ya shiga ba ta soke Musuluncinsa, kamar yadda duk wata jam’iyyar da kafiri ya shiga ba ta goge kafircinsa. MiÆ™a wuya ga dokar da ta yi takin saÆ™a da dokar Allah kafirci ne Æ™arÆ™ashin kowace jam’iyya yake.
    iii)             A mahangar shari’a, shugaba dole ya kasance baligi mai diwani a wajen Allah. A hankalin addininmu dole ya zamo “namiji” ba mace ba, ba mata maza ba, ba zulumbu ba. Kasancewarsa daddaÆ™aƙƙe masana sun daÉ—a juna sani. Bisa ga wannan tunani ne nassi ya kawo kasancewarsa mai cikakken hankali domin wanda bai balaga ba ruwan faranti ne, mace kuwa hankalin bai rinjayi tunani da wayo ba. Wanda ya rasa al’aurar da za a tantance shi ba ya da madogara ga nassi. A umurnin addininmu zaÉ“en mace ko yaro yin fito-na-fito da dokokin da Allah Ya aiko Manzo (SAW) da su ne.
    iv)              Sahihan nassoshi sun ce, a kula da hankalinsa da ilminsa da wayonsa da lafiyarsa. Babban hankali a wajen nassi shi ne gane Allah a tauhidance. Jagoran ilmi a nasshi shi ne sanin littafin Allah a tsaftace. Wayo shi ne rarrabe halas da haram a tsanake. Lafiyar jiki ta haÉ—a da gaÉ“É“ai manyansu da Æ™ananansu domin samun damar waÆ™iltar al’umma a mutunce.
    FaÆ™ihun Shugabanci A Nassoshin Shari’a:
    A ganin addininmu ba dole sai shugaba ya fi kowa komai zai zama shugaba ba. Haka kuma, mai da shi abin gado bai tabbata ga sunna ba. Ƙabilantar da shi, da ɓangarartar da shi, da jinsartar da shi, fitina ce babba, dole a kiyaye da haka. A fiƙihun shugabancinmu akwai:
    i)       Shugaba mai cikakken iko: A nan, ba mu ce mai cikakken shugabanci ba ko mulki, “Iko” muka ce. Nassi ya tabbatar da Allah kawai ke da wannan matsayi a sammai da Æ™assai. Shi kaÉ—ai ke halastawa da haramtawa dokokinSa tsalkakakku ne hukuncinSa ba ya tashi. Duk hukuncin da ya saÉ“a wa nasa Æ™etare haddi ake kiran sa. Hukuncin miÆ™a wuya gare shi “ridda”. YaÆ™ar masu tabbatar da cikakken ikon Allah shi ne fasadi da ta’addanci da shisshigi mai kai ga hushin Allah ga makangara.
    ii)      Manzanci da Annabci: WaÉ—annan nau’in shugabanci daga shugaba mai cikakken iko suke. Wanda duk aka zaÉ“a Manzo ko Annabi naÉ—aÉ—É—e ne daga Allah, bin sa wajibi ne. Adawa da shi da yaÆ™arsa da Æ™in bin tsarin da ya zo da shi kafirci ne a sahihin nassi. Wanda Allah Ya aiko, da aikinsa da furucinsa da yin shirunsa da kau da kansa da inkarinsa da yardarsa duk hukunci ne saukakke. Don haka, duk wani tsari da za a yi na gyaran fuska ga nasa ko soke shi gaba É—aya ko soke sashensa ko faÉ—aÉ—a shi wurin da ba a faÉ—aÉ—a ba ko taÆ™aita shi wurin da ba a taÆ™aita ba shisshigi ne da ta’addanci. Shugaban duk da ya hau karaga a irin wannan tsari cikin duhu ya hau, cikinsa yake tafiya, ciki ake yi masa rakiya, yaya zai dace da kyakkyawan shugabanci?
    iii)     Allah bai taÉ“a aiko Manzon da ba ya mutuwa ba: Idan ya mutu tsarin da an ka ba shi yana nan sai mamaya su bi kawai. Ashe! A tsarin kyakkyawan shugabanci ana son ci gaba da dogewar dokoki da tsare-tsare. SaÉ“a wa dokokin da tsare-tsaren da Allah Ya aiko bayan wucewar manzaninsa shi ya sa Yake aiko wasu manzani su jaddada. Tsarin duk da ba bisa na Allah yake ba safe duk cikin gyara yake kamar na tsohuwar mota a hannun tsohon bakanike. Shugaban da aka É—ora a kansa an wahalar da shi domin ba a ba shi tazarar yin kyakkyawan shugabanci ba.
    Ayyukkan Shugaba:
    Daga cikin ayyukkan shugaba akwai kariya. Ya kare rayuwar mutanensa da lafiyarsu da dukiyarsu da Æ™asarsu ta fuskar tanada mata kyakkyawan tsaro. A tsari, shugaba na da ikon zartar da kowane hukunci da shari’a ta ba shi. Haƙƙensa ne tsare dokokin Æ™asa ga ‘yan Æ™asa da masu shigowa Æ™asarsu. Yana da hurumin tabbatar da dokoki da hukunce-hukunce da aka tabbatar. Ba dole ne sai ya fi kowa zalaÆ™ar magana ba. Babu tilas ga kasancewarsa mai iya rubutu ko karatun rubutu ba. WaÉ—annan duk yana daga cikin ayyukansa samar da su. Ƙasa duka shugabanta ne fuskarta, dole ne ya yi tsayin daka na fito da ire-iren martabobinta da kare mutuncin mutanenta na ciki da waje da tsare musu al’adunsu da addininsu da bunÆ™asa tattalin arzikinsu.
    Shugabancin Yau A Sikelin Jiya:
    Turawan mulkin mallaka suka fara É—ora turbar akalar shugabancinmu a kan yaudara. Sun tarar da tsari gawurtacce ya riga ya cika jama’a sun miÆ™a wuya gare shi, sun yi imani da shi, a kansa suna dadaukar da rayuwarsu. Da tsarin aka yaÆ™e su, aka fatattaka su, aka murÆ™ushe su, aka gargaÉ—e su, aka yi musu koran kare a farfajiyar bilad as-Sudan. Da suka ga ruwan masu yawa ne, kuma masu zurfi, suka  yarda da Limancin makaÉ—a NarambaÉ—a:
     
    Jagora: In ka ishe gulbi ya cike,
              : In ba kowa ko ka iya.

    Yara : Koma ka tsaya ganga ka kwan
    Gindi: Ya É—au girma ya san yabo
    : Mu zo mu ga Alƙali Abu.
    Turawa bayan da suka kwana a ganga, sai suka ci gaba da shirin yadda za su sake shiga ko ba kowa. Cikin dasisarsu ce aka É—ebe zancen addini ga tsarin shugabanci. Don haka zance zama Musulmi ko ba Musulmi ba, bai taso ba. Batun jinsi mulkin mace ko namiji ba matsala ba ce. Yarda da wani tsari saukakke daga kowa ya fito a watsar da shi a zauna a sake tunani. WaÉ—annan abubuwa duk a munafunce aka tsara su, domin masu tsarin ba su shafa da kare aÆ™idojin addininsu a cikin tsarin ba. Shi kansa tsarin nasu ne. Masu zartas da su da kare su nasu ne. Duk wani mataki da aka É—auka na kare haƙƙi da ‘yanci da doka daga cikin addininsu aka cirato su. Tsarinmu bai yarda a laÉ“e ga wani abu a kare shi ba, sai dai a laÉ“e gare shi a kare. Yau yaya ake?
    A tsarin shugabancin yau, adalcin shugaba da nagartarsa kare Fatin jam’iyyarsu da manufofinsu. Jam’iyyoyin nan an tsara su bisa ga sharaÉ—i babu zancen wani addini ko wata aÆ™ida in ba tata ba. Bin wani hani ko horo na wani addini ko wata fahinta irin ta addini saÉ“a wa jam’iyya ne mai haranta wa É—an jam’iyya zama cikinta. A ciki ba a yarda wani addini ya fi wani ba don haka babu kafiri babu Musulmi bale mushariki maganar fasicci ba ta taso ba. Dokokin jam’iyya su ne nassi abin dogaro wani ba su ba abin watsarwa ne. Kowace Æ™ungiyar jam’iyyar siyasar demokraÉ—iyya da wannan manufa aka kafa ta. Ta wace hanya za a bi a samu kyakkyawan shugabanci irin wanda Allah da ManzonSa suke son mu yi alhali mun riga mun ce a aje su gefe É—aya? Wannan mugun rutsi da Æ™angi shi ya tilasta wasu bayin Allah tawaye ga tsarin demokraÉ—iya ‘yan bokon da ke cin gajiyarta suka dinga yi musu sunaye daban-daban na halastar da jininsu.
    A gajeren tunaninmu, adalcin tsare dukiyar mutane da zaman lafiyarsu da bunÆ™asar tattalin arzikinsu da zamansu kara zube kowa yana da ‘yancin kansa wai shi ne kyakkyawan shugabanci. Masu wannan makahon tunani a koyaushe Æ™asashen Turai da ‘yan barandarsu ne abin ba da misalansu. Idan za a waiwayi kundin tarihi na jiya da yau da muke ciki, wace al’umma ta fi al’ummar da addini ke shugabanta ci gaba da zaman lafiya? Wace Æ™asa ta rungumin addinin demokraÉ—iyya ba ta shiga cikin fitinonin da suka fi Æ™arfinta ba? Shugabanci nagari ba ya taÉ“a shimfiÉ—uwa sai da tsari nagari. Wanda ya yi mutane shi ya fi kowa sanin tsarin da ya dace da su. ƘirÆ™iro wani tsari saÉ“anin nasa shi ne zalunci. Komai adalcin mutum aka É—ora shi a kan zalunci aka ce ya yi aiki da shi a matsayin shugaba, wane suna ya kamata mu kira shi da shi?
    A baÆ™auyen tunaninmu ilmin boko da wayon zama da mutane da fuska biyu, da wayon ci da ceto da ci da addini da Æ™abilanci da É“angaranci da samun farin jini ga ‘yan dandin zamaninmu, wai, shi ne tafarkin hawa karagar mulki! Wanda duk ya jahilci addininsa ya rasa hankali da basirar jagorantar mutane sai dai a yi kama-kama. Tun farkon duniya zuwa yau, ba a samu wanda ya shugabanci mutane da hankalin tuwo da wayon adana dukiya ya gama lafiya ba. Shugabanni uku ne: wanda aka yi wa wahayi, da wanda ke biyar abin da aka yi wahayi da wanda ke biyar son ransa da son ran jama’arsa. Duk shugaban da ya samu kansa cikin na uku ya yi ban kwana da adalci ya ba fitina maÆ™ulin buÉ—e Æ™ofar shiga Æ™asarsa. Da shi, da waÉ—anda suke É—ora shi a kan karaga, da waÉ—anda ake shugabanta, da tsarin da ake ciki, duk sun shiga É—emuwa. Kowa ya zama mai laifi, wane laifi za a tsawatawa?
    Taliyon Tarihi:
    A zamanin Annabi Ibrahim (AS) addinan gargajiya ke tashe da jagorantar mutane aka aiko shi da gaskiya ya rusa su. Tattalin arzikin Masar ya bunÆ™asa bisa ga tsarin sarautun gargajiya, aka aiki Yusuf ya daidaita shi. Babu irin cigaban da Fir’auna bai kawo ba a shugabanci aka aiko Musa (AS) ya gyara masa tsari. BilÆ™is ta kai duk wurin da sarauniya ke kai, aka sa Sulaiman (AS) ya yi mata kakkaÉ“an gara. Cigaban Samudawa ya É—ara namu ban al’ajabi aka sa Shu’aibu ya kafa musu harsashe. Makka ita ce cibiyar duniya da wayewa da bunÆ™asa, duk wani gari da ita ba, sunansa Æ™auye, sunan jama’arsa Æ™auyawa, aka ba Muhammadu (SAW) hasken da ya fi wayon mai wayo wayo. Wannan wata ishara ce gare mu cewa, da dabarunmu da fasahohinmu da ilminmu na cin tuwo suna iya tserar da mu, da ba a turo annabawan da suka gabace mu ba. Ashe! Yanzu wanda duk ke ganin mun ishi kanmu don ‘yan takardunmu na shaidar zur wasa yake yi. Wannan ita ce matsalar shugabancin Æ™asarmu Nijeriya ta yau (2014).
    Kundin tarihi ya tabbatar muna da cewa, sarakunan gargajiya da aka yi tun gabanin Musulunci a Æ™asar nan zalunci ya rusa su. Daulolin da aka yi bayansu ba su kai labari ba. An yi Æ™arnin da addini ya shugabanci Æ™asar nan, ba a taÉ“a yaÆ™i na Æ™abilanci da yanki da É“angaranci ba a farfajiyar Æ™asarmu. Mulkin mallaka ya zo, ba da shiri ba ya gangame ‘yan kwalayensa na kunya ya san inda dare ya yi masa. Jamhuriyya ta farko ba ta sallame salla a zaune ba. Mulkin Soja na Oransi faÉ—aÉ—a maÆ™abartu kawai ya yi. Mulkin soja na Yakubu Gawon da Murtala dutse hannun riga aka Æ™are. Obasanjo ya zo, ya yi muna kashin mummuÆ™e ya assasa harsashen bambancin addini da Æ™abilanci makamai suka fara tsada. Shagari na batun miÆ™e Æ™afa aka sallame shi. Buhari ya goge allo ba a fara rubutu ba aka sallami ‘yan makaranta. Babangida ya rubuta huÉ—uba aka tilasta shi ba Shonikan ya karanta. Shonekan bai Æ™are muÆ™addima ba, Abacha ya yi iÆ™ama. Abacha na batun a daidaita sahu aka sallame salla. Abdussalam ya zo amincin bai samu ba, Obasanjo ya shigo da bababr riga. Cikin Æ™oÆ™ari na ta miÆ™e ta miÆ™e da shi, ‘Yar’aduwa ya zauna. Babban guzurin ‘Yaraduwa gare mu ba da izni a kashe mu da sunan da ba mu sani ba wai! BOKO HARAM. Jonathan ya yi garkuwa da wasiyyar ‘Yaraduwa aka girke bala’i a ko’ina Musulunci yake a Æ™asar nan. Da wanda ya ce, a kashe ka, da wanda ya ba da umurni a saka maka wuta tun ba ka ida shurewa ba, wane ne ya fi Æ™iyayya da kai? DanÆ™ari! Sunan wasu littafai Ku Yi Karatu, Ku Ƙara Karatu, Ku Yi Ta Karatu, Ƙaramin Sani ƘuÆ™umi ne.
    Baya Ta Haihu:
    A iya fahimtar duk wani mai hankali a Nijeriya. A tarihi tsarin mulkin soja ya kasa fitar da suhe wuta. ÆŠan lokacin da talaka ya san akwai hukuma shi ne zamanin Gowan da Murtala da Buhari. Mulkin farar hula, a koyaushe gara jiya da yau. Su Sir Ahmadu Bello sun É—ara su Shagari. Su Shagari sun fi su Obasanjo. Obasanjo sun gota ‘Yar’aduwa. Yar’aduwa shi ya haifi bala’in da muke ciki a yau, ka da Allah Ya maimaita muna. Har ‘yan Nijeriya sun fara mantawa da batun yaÆ™in Æ™abilanci da É“angaranci da addini da siyasa yau ga su a cikinsa tsamo-tsamo. Jin tsoron haka wasu ke ganin baya ta haihu.
    Ga tsarin shugabancin da muke ciki a yau, an fito Æ™iri-Æ™iri an nuna akwai addinin da ba a son kowane fati ya fitar da shugaban Æ™asa a ci. Akwai yankin da ba a son shugaban Æ™asan ya fito ko shi waye? Akwai Æ™abilar da ake son komai farin jininta ka da a samu shugaban a ciki. Akwai addinin da ake so dole shi zai ja akalar wannan Æ™asa, in ba haka ba, sai dai a tashi baram-baram in shataf-shataf in jina-jina. Allah Ya kare mu. Ga ‘yan hujjojin da suka sa muke ganin baya ta haihu:
    i)                   YaÆ™in da aka jibge a yankunanmu ba a sa ranar tsakaita wuta ba. Haslai ma, a kasafin kuÉ—in shekarar 2014 makamai aka keÉ“e wa kaso mafi tsoka.
    ii)                Cikin dabara an gayyato UN Æ™asashen duniya sun karÉ“a mata kira bisa ga sunan da ‘yan Æ™asarmu suka Æ™irÆ™iro muna, an halastar da jininmu saki ba Æ™aidi.
    iii)             In da yawa muke taÆ™ama, akwai raÉ—e-raÉ—in cewa, a yankunanmu da ake yana ba za a yi zaÉ“e ba. Masu karatun jaridu sun san biri ya yi kama da mutum.
    iv)              Wai! Yanzu Æ™asarmu ta binciko akwai ‘yan Nijeriya fiye da miliyan arba’in da biyu a Æ™asashen duniya. ZaÉ“en da za a yi na (2015) ana son a ba su damar jefa Æ™ur’a daga Æ™asashen da suke zaune. Kun dai gane.
    v)                Matsalolin da ke tattare ga tantancen adadin masu zaÉ“e ga abin da jaridu ke sunsunowa ya yi yawa. Ka da ku yi mamaki a haramta wa duk É—an Æ™asa da ba ya da takardar I.D ta zama É—an Æ™asa ba jefa Æ™ur’a. Idan aka zo da wannan salo za a sa mu tagumi. Don haka, kura gare ku masu awaki.
    vi)              Taron tarayya na Æ™asa da ake so a yi da lauje cikin naÉ—i. Wasu maÆ™iya wannan Æ™asa da sun ka gaji da zama da mu buÆ™atarsu a samu kafar raba Æ™asa ko yaÆ™i ya É“arke a yi tamiÆ™en dole. Mu tabbata ka da a yi komai duÆ™unce a yi shi ta-da-ta wankin É—an kanoma mashaya. Ba mu ce ka da a raba Æ™asa ba, amma in rabo za a yi a hura wuta kowa ya ga rabonsa.
    NaÉ—ewa:
    Tilasta zama Æ™asa É—aya dole ga mutanen da hankalinsu ya riga ya tashi ga juna wata babbar matsala ce. Da zama ana zubar da jini koyaushe gara a raba gari kowa ya yi tuwonsa. Samun shugaba adili da zai daidaici kowa cikin irin wannan tsari mawuyaci ne. Ganin laifin juna a koyaushe dole ne domin kowa takaicin É—an uwansa yake yi. Sake baki a bi Æ™ungiyoyi ko jam’iyyun siyasa ido rufe ba ya yi muna cefanen da za mu more romonsa. Da an yi kuren addini ga shugabanci an yi fargar Jaji. A shiga a gyara mun yi mun fi mai kora shafawa. A tsaya gefe a Æ™i shiga mun yi, an yi ba da mu ba. Mun sa hannu mu gyara an yaÆ™e mu. Mun sa baki mu gyara an É—aure mu. Mun Æ™i abin a zuci an yi saniyar ware da mu. Wace dama muke da ita wadda ta rage? Ina sauraren ku.
    Na gode.
    Visit the Authors Site...

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.