Ticker

6/recent/ticker-posts

Tubalan Bakar Addu'a A Cikin Rubutattun Wakokin Hausa

DANO BALARABE BUNZA
Sashen Koyar Da HarsunanNijeriya
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.
07035141980

Da

Abdullahi Sarkin Gulbi
Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato
08089949294

Tsakur


Waƙa na cikin hanyoyin da ake amfani da su don sadar da addu’a kamar yadda ayyukan Ainu (2007) da Usman (2008) suka tabbatar dangane da yadda mabuƙaci ke addu’a . Irin waɗannan addu’o’i munana ne ba na alheri ba. Wannan maƙala ta fuskanci bayanin irin waɗannan waƙoƙin da ke ƙunshe da baƙaƙen (munanan) addu’o’i da dalilan da ke sa tusgowar su a waƙa ko rubuta waƙa a kansu. An kawo dalilan da ke sa yin baƙar addu’a da misalan baitocin da ke ɗauke da munanan addu’o’in da suka tabbatar da wannan iƙirari.

1.0 Gabatarwa


Masana da manazarta sun yi bincike a fannoni masu yawa na rubutattun waƙoƙin Hausa musamman Ɓangaren binciken neman shedar karatun digiri na uku. Daga cikinsu akwai Hiskett (1975), da Muhammad (1977), da Ɗangambo (1980), da Yahya (1987), da Birniwa (1987), da Birnin Tudu (2001). Ainu (2007), ya yi aiki kan salon addu’a a cikin rubutattun waƙoƙin Hausa, sai dai ya dubi addu’o’i ne baki ɗaya ba tare da bambantawa tsakaninsu ba. Usman (2008), ya yi nazarin waƙoƙin Umaru Nassarawa Wazirin Gwandu waɗanda ba a rasa irin wannan addu’a da ake magana a kai musamman idan aka dubi rataye shafi na 562 zuwa 563da Idris (2013) da ya yi magana kan “Tubalin Baƙar Addu’a a Waƙoƙin Baka Na Hausa” da Bunza (2013) day a dubi “Tsettsefe Jigo Da Salon Baƙar Addu’a A Cikin Waƙar Audu Makaho Ta Mai Wa Amo Takkai” da sauran ayyuka da dama da aka gudanar a kan rubutacciyar waƙar Hausa.
Ganin ba a kalli baƙar addu’a a fagen nazarin rubutacciyar waƙa ba ya sa na ƙuduri yin haka, keƁance domin tabbatar da cewa akwai ta a cikin rubutattun waƙoƙin Hausa.

2.0 Mene ne Addu’a?


A ƙoƙarin bayyana ma’anar addu’a, ƙamusun Hausa na Jami’ar Bayero Kano ga abin da aka ce:- Addu’a na nufin roƙon Ubangiji. Haka kuma sun yi nuni da a dubi kalmar addu’a wadda ke nufin cewa, suna ne na mace kuma ɗaya tak, mai jam’in addu’o’i da ake gudanarwa bayan salloli biyar da ake yi a cikin wuni.
Bergery (1934: ), kalmar addu’a na nufin roƙon da ake yi bayan wanda ake yi a lokacin salloli biyar na wuni. Sai dai an ba da ma’anar ne a Turanci. Nicholas Awde (1996: cewa aka yi, Addu’a na nufin prayer, prayer kuma na nufin addu’a. A cikin littafin Hausa Metalanguage cewa, addu’a na nufin doxology (1990:56).
Ke nan roƙon Allah ake nufi da addu’a, duk da yake roƙo suna ya tara. Akwai roƙo na alheri da kuma mummuna. Roƙon kirki shi ne addu’ar alheri, wanda ba na kirki ba kuwa shi ne, baƙar addu’a ko mugun roƙo ko muguwar fata.

3. Mece ce Baƙar Addu’a?


Fahimtar da aka yi wa abin da ake nufi da addu’a, za a iya fahintar abin da bakar addu’a ke nufi da cewa, addu’a ce da ba ta alheri ba. Wani abin da ya kamata a sani shi ne mafi yawan baƙar addu’a wasu ake yi wa, domin da wuyar gaske mai hankali ya yi wa kansa baƙar addu’a sai in ya shiga halin taƁuwar hankali. Za a iya fahimtar baƙar addu’a da cewa addu’a ce maras kyau zuwa ga wani ko wasu a kan ɗaya daga cikin dalilan da ke sanya yin ta da za a kawo nan gaba kaɗan.
Ganin haka ya sa takardar ta ce, “Mummunar addu’a na nufin roƙon da ake yi ga Allah zuwa ga wani abu ko wani mutum ko mutane ko dabbobi da sauran halittu domin wani sharri ko illa ta same su, duk da yake ba su son a yi musu wannan addu’a. Idan aka yi musu za su ɗauki wanda ya yi musu baƙar addu’a maƙiyinsu ne. Duk da haka tilas na sa a yi baƙar addu’a a kan wasu dalilai.

4.0 Dalilan Yin Baƙar Addu’a


Sanin Allah ya isa ya zama madogara ga kowa ya sa masu addu’a ke yin ta domin neman biyan buƙata a gare shi. Idan aka cuce su ko aka ƙware su ko aka fi ƙarfinsu ko aka yaudare su, addu’arsu za ta kasance ta neman agajin Allah da sakayyarsa bisa ga waɗannan dalilai. Daga cikinsu akwai:

4.1 Zalunci

A cikin ƙamusun Hausa (2006:488) an ba da ma’anar zalunci da cewa, ƙwaruwa ko tauye haƙƙi, ko yin ha’inci ga wani don a cuce shi.

4.2 Sata

Bunza A.M. 2015 ya kawo cewa, “Sata wata rashin gaskiya ce ta musamman daga cikin nau’ukan rashin gaskiya da ɗan Adam ke aikatawa. Rashin gaskiya nau’i-nau’i ne da ya haɗa dabarar raba mutum da abin da ya mallaka ta kowace fuska ita ce sata”. Ya ƙara da cewa “An yi bayanai daban-daban game da ma’anar sata ta fuskar addini da tsare-tsaren mulkin zamani don gudanar da hukunce-hukunce. Duk da haka Bahaushe ya kalli sata a matsayin wata dabara ko wayo ko yaudara ta musamman.
A fahimtata sata na nufin ɗaukar kayan wani da niyyar raba shi da shi gaba ɗaya ta hanyar laƁaƁe ba tare da saninsa ba. Ba a yi wa mutum sata yana kallo sai dai bayan idonsa. A fahimtata, abu biyu Ɓarawo ke amfani das u a wajen yi wa mutane sata wato, hankali da kayansa. Ɓarawo ba zai taƁa kaya ba matuƙar hankalin mai kaya na ga kayan, sai ya tabbatar da hankalinsa ya gushe.
Akwai marubuta waƙoƙi da Ɓarayi suka yi wa sata har suka mayar da raddi ga Ɓarayin da miyagun addu’o’i. Daga cikin marubutan akwai Aƙilu Aliyu, da Audu Makaho Birnin Kabi. Zan fara da waƙar da Aƙilu Aliyu ya yi ta gargaɗi ga jama’ar Nijeriya mai suna ‘Gaskiya Mai Ɗaci’. Ya yi baƙaƙen addu’o’i ga Ɓarayin da suka sace masa jaka a tashar jirgin ƙasa da ke Zariya. Akwai tarkace mai yawa a cikin jakarsa da aka sace. Jin zafin wannan sata ya sa Aƙilu Aliyu ya yi wa waɗanda suka yi masa satar baƙar addu’a. Ga abin da ya ce kafin ya biyo da miyagun addu’o’i.
Baitoci biyu da ke sama bayanin satar da aka yi wa sha’iri ne na abubuwan da ke cikin jakarsa. Haka kuma ya biyo da miyagun kalamai ga duk wanda ke da hannu ga satar. Ga misalai daga wasu baitoci:

22. Allah haɗa su da tashin hankali,
Dare da rana yamma da safiya.

23. Allah zuba musu cuta jahila,
Da babu warkewa nan duniya.

24. Ciwon idanu, kazwa, sanƙarau,
Allah haɗa wa miyagun duniya.

26. Ka ninka cutocinka daban-daban,
Ka tattaro wa miyagun duniya.

27. Allah haɗa su da kowace jarraba,
A rayuwa tasu ɗungum duniya.

28. Kaɗe su ya Allah taƁar da su,
Su kasa kowa ɗakin duniya.

29. Ya Ilahi gurguntar da su,
Su zam a baya da kowa duniya.

33. Fa duk buƙata kar ka biya musu,
Fa kar su sadu da hairi duniya.

A cikin baitocin da aka jero sama, marubucin ya yi wa Ɓarawon day a yi masa sata babbaƙun addu’o’i masu yawa saboda jin haushin tarkacensa da aka ɗauke. Kowace sata na da zafi sai dai, wata na gaban wata. Matafiyi ya komo daga tafiya kuma, ya sayo tsaraba domin iyalinsa da yaransa da sauran abokan arziki kuma ko isa gida bai yi ba, a sace su a raba shi das u, me zai hana ya yi baƙar addu’a? Ai sai addu’ar da ya manta kaɗa ice ba zai yi ba.
Audu makaho Birnin Kabi bai bar Ɓarawo hakanan ba da ya yi masa sata sai da ya yi masa baƙar addu’a a wani wuri duk da yake waƙar gargaɗi ce a kan a nisanci sata. Mamaki da haushin Ɓarawo ya kama Audu matuƙa ganin a duk unguwarsu mai jama’a masu ɗimbin yawa Ɓarawo bai ga wanda zai yi wa sata ba sai shi. Sai da ya fahinci don ba ya gani ne aka yi masa wannan sata ganin ta fi sauƙi. Ga baƙar addu’ar da ya yi wa Ɓarawon da ya yi masa sata:-
Rabbi Allahu na roƙe ka,
Don Muhamman da littaffanka,
Don waliyanka masu biyak ka,
Don sahabbai da adillanka,
Tankwahe wanda kai min sata.

Audu Makaho ya yi addu’a cewa, Allah ya tankwahe Ɓarawon da ya yi masa sata tare da yin tsani da wasu bayinsa nagartattu day a ambata a cikin baitocin da ya kawo. Ya yi haka ne domin ganin kusancin su da Allah fiye da shi. Tankwahewa a nan na nufin matsarwa. Ba shakka duk wanda ya sace maka abin da ka mallaka ya matsar da kai. Ganin matsuwar da aka sanya sha’iri a ciki ya sa ya roƙi Allah ya matsar da wanda ya yi masa sata.

4.3. Zaman Banza

Daga cikin abubuwan da ke cutar da al’umma da sanya su yi sata akwai zaman banza da wasu mutane suka runguma domin mutuwar zuciya da suka dogara a kai ba tare da hango illarsa gare su ba. Muhamamdu Sambo Wali Basakkwace ya yi wa zaman banza baƙar addu’a a cikin waƙarsa mai suna, “Waƙar Tarbiyya ta 1: Hayya Fa Jama’a ku Bar Zaman Banza da Roƙe-Roƙe da Barace-Barace” a baiti na goma sha shida da na hamsin da bakwai. Ga baƙar addu’ar da ya yi wa zaman banza:-
16. Zaman banza ba ni son ka ban son mai yin ka,
Zama kuma ab ba ni yi da duk wani mai yin ka,
Ga dubin kowammu mun ga dukkan aibinka,
Muna roƙon wanda a’Azizu ya mirɗe ka,
Ka faɗa rami ka daina cutar jama’armu.

A cikin wannan baiti da ke sama, a layuka biyu na ƙarshe, baƙar addu’a suke ɗauke da ita ba. Idan aka kula da ɗangon ƙarshe marubucin ya fito da cewa zaman banza abu ne mai cutar da jama’a.
Haka kuma a baiti na 57 na waƙar da ke sama ta Muhammadu Sambo Wali Basakkwace ya ƙara yi wa zaman banza baƙar addu’ar da yake cewa:-
57. Zaman banza kullu yaumi babban halakakka,
Kana iya lalata wanda duk yak kama ka,
Ka sa shi ya zamna cikin tsiya ba ya gudun ka,
Muna roƙon wanda a’Azizu ya mirɗe ka,
Ka koma daji ka daina cutar jama’armu.

A wannan baiti da ke sama akwai Kalmar mirɗe da ke nufin wulaƙantarwa da kuma maganar ka koma daji mai nufin ana buƙatar ya haukace ya koma daji kamar yadda mahaukata ke yi, wanda mutuntar da zaman banza sha’iri ya yi a wannan baiti. A taƙaice dai ta kowane hali baƙar addu’a ce aka yi wa zaman banza domin fahimtar da ake da ita ta cutarwar da yake yi wa jama’a.
Ganin cutar da yunwa ke ɗauke da ita ya sa wani mawallafi Malam Abubakar Maikaturu ya yi mata baƙar addu’a tun a baitin farko, wanda daga baya kuma ya tsaro matsalolin da yunwa ke haddasawa ga jama’a. Wani abin ban sha’awa kuma, sai marubucin ya mutantar da yunwa ya yi mata laƙabi da ‘Halima’ a matsayin sunan waƙar. Ga baitin da addu’ar ke ciki:-
1 Ya kamata ba shakka,
‘Yan’uwa mu yo barka,
Zama Halima ta ɗauka,
Wanda babu albarka,
Allah Shi kashe ta.

A irin wannan addu’a kamata ya yi a karƁa da amin, domin ta shafi kowa, idan aka yi la’akari da aibin da yunwa ke yi wa jama’a. Irin wannan ne ya faru ga matar Audu Makaho Birnin Kabi mai suna Amina, almajira ce da ke zuwa gidaje tana neman sadaka. Daga baya aka sa mata waƙa (musamman mata) wadda ba mai kyau ba. Da abin ya dame ta sai ta gaya wa mijinta. Ga abin da ya ce a baiti na 12:-
Tac ce “Maigida ka san abu ya Ɓaci,
Ga yau hal lugude akai ana ta yi min waƙa”.

Za a iya fahimtar cewa, lafuzzan waƙar ba masu kyau ba ne zuwa ga Amina don ƙara ce ta kawo da neman agaji kan damuwar da abin ke yi mata. Ganin haka ya sa Audu Makaho ya yi tambayar cewa, wane ne ya sa ma Amina waƙa? Audu bai sami wanda ya fara yi wa matarsa waƙa ba shi kuma, sai ya yi addu’a ga duk wanda ya sa wa matarsa waƙa, da wanda ya ji waƙar kuma ya taya wanda ya yi waƙar har ma da wanda ya ji daɗin da aka yi waƙar. Ko da yake addu’ar ba mai kyau ba ce, mummuna ce. Da za a dubi addu’ar da Audu ya yi wa wanda ya yi wa matarsa waƙa, za a fahimci cewa baƙar addu’a ce ɗari bisa ɗari. Ga baiti uku a matsayin misali:-
14 Har maza har matansu Rabbana duk ya san su,
Allah ka wahal da masu wa Amina waƙa.

15 Wanda yaw wa Amo tosku Allahu kai kas san shi,
Ka sa shi wurin nan da za ka sawan maƙiyanka.

16 Wanda yay yi mata da wanda yaj jiya yat tanye shi,
Da mai murnar an yi mata kwaƁe musu jin ƙanka.

Idan aka yi la’akari da baitocin da ke sama, ba sai an ƙara nanata cewa suna ɗauke da munanan addu’o’i ba. Idan aka ce wahal da ana nufin a sanya mutum cikin matsala a cire shi daga cikin halin yalwa da hutawar da yake ciki. Faɗar ka sa shi wurin nan da za ka sawan maƙiyanka na nufin a sanya shi cikin wuta a ranar lahira. Ko shakka babu wannan baƙar addu’a ce idan aka yi la’akari da magangannun da abin da suke ɗauke da shi. Addu’ar da ke cikin baitin ƙarshe wurin da aka ce kwaƁe musu jin ƙanka na nufin kar Allah ya tausaya musu a ranar ƙiyama dangane da hisabin da za a yi musu. Marubucin na sane da ayar nan da ke cikin suratul Fatiha (sura ta 1, aya ta 2), kuma ya fahimci cewa Allah na iya yi wa kowa baiwa a duniya musulmi da kafiri baki ɗaya. Jin ƙai a lahira kuwa ya keƁanta ga mutanen kirki kaɗai. A ganin sha’iri duk wanda ya yi wa Amo waƙa bai kamata a yi masa ahuwa ba saboda ya yi abin da bai dace ba na zalunci.

4.4 ƙiyayya
.

Gurin wani ya rasa ni’imar da yake da ake nufi da hassada ko ta dawo gare shi ko kuma ga wani ko kuma kowa ya rasa.
A ƙamusaun Hausa (2006:282) cewa aka yi ƙiyayya na nufin tsananin rashin son wani wanda yakan kai ga yin illa. Idan akwai ƙiyayya tsakanin mutane, tana iya kasancewa dalilin da ke sanya a yi wa juna baƙar addu’a sai dai, a san cewa wanda ke ƙiyayyar na iya yin baƙar addu’ar kamar yadda wanda ake ƙin ke iya yi, idan ya fahimci hakan. Za mu fara da dalilin ƙiyayya kafin na hassada da ke sanya a yi baƙar addu’a. A cikin waƙar Abdullahi Bayero Yahya mai suna ‘Du’a’i’, akwai baƙar addu’ar da ya yi wa wanda ya nuna masa ƙiyayya. A daidai baiti na 27 ga abin da ya ce.
27.Anta Kafi ka isam min,
Murje bawan da ka ƙi na.

A cikin wannan baiti akwai baƙar addu’a da kuma dalilin yin ta, cikin kowane layi. Idan mai yin addu’a ya ce Allah ya isam masa, yana nufin a fitar masa da haƙƙensa da aka ci. Murjewa kuwa da ke layi na biyu a wannan baiti na nufin halakarwa zuwa ga mutumin da ke ƙin sa, musamman ya fito da maganar ƙi a fili, mai nufin buƙatar da yake da a rayuwarsa ga duk mai adawa da shi , mai nufin sa da sharri.
A waƙar Alƙali Haliru Wurno mai suna ‘Tura ta kai Bango’ akwai baƙar addu’ar da ke nuna akwai ƙiyayya tsakanin marubucin da wasu mutane. Ya kawo wannan addu’ar ne a baiti na 7 inda ya ce:-
7. Ga ni Jalla ka san ilgazi,
Rabbana ka ban nan dai hamzi,
Kunyata shi mai yo min hamzi,
Shi da wanga mai yo min lamzi,
Kar ka ba su filin darawa.

Hamzi na nufin zunɗe, lamzi kuma na nufin raɗa. Masoyi ba ya yi wa masoyinsa su sai dai wanda ke ƙiyayya da shi. Haka kuma ba ya yuwa wani ya nemi kunyatar masoyinsa sai dai maƙiyi. A layin ƙarshe ma ya fito da tabbacin ƙiyayya ce ke akwai tunda ya faɗi cewa kar Allah ya ba maƙiyan filin darawa, wato kar ya biya musu buƙatunsu.
4.5 Hassada
A ƙamusun Hausa (2006:197) an ce kalmar hassada ko hasada na nufin ganin ƙyashi. Akwai marubutan da suka yi baƙar addu’a ga masu hasadar su. A waƙar Mallam Mahe ƙaura Namoda mai suna ‘Gora’ akwai baƙar addu’a sosai. Shi kuma ya yi la’akari da masu yi da shi, ya yi addu’ar cewa, Allah ya isam masa ga duk mai yi da shi. A nan ma akwai bayanin dalilin hassada musamman a baiti na 30. Ga abin da ya ce:-
30. Ja’iri, azzalumi mai hassada,
Kumyatas sad da duk yay yi da ni.

A nan za a iya fahimtar cewa, mai wannan waƙa na addu’a ne ga wani bawan Allah mai ƙulla wa mutanen kirki sharri. A taƙaice yana addu’a ga wannan mutum saboda ba mutumin kirki ba ne. Abin da ya tabbatar da rashin kirkinsa su ne, miyagun halayen da aka jero a ɗango na farko. A kan haka marubucin ya yi addu’ar cewa Allah ya sa a gano abin da yake faɗi ƙarya ne ba gaskiya ba, domin ko da ya faɗi wani abu dangane da wani a gano ƙarya yake yi ba gaskiya ba ne. A taƙaice dai a gano duk abin da ya faɗa, akasinsa ke tabbata.
Bayan waɗannan baitoci da ke sama akwai wata baƙar addu’a a cikin waƙar Malam (Dr). Umaru Nassarawa Wazirin Gwandu mai suna ‘Godiya da Neman Shiriya’ da murubucin da ya yi a shafi na 562-563 cikin kundin digirin Bello Bala Usman cikin ratayen waƙoƙin dad a ya yi. Za a sami baƙar addu’a a baiti na 34 da na 37. Ga baitocin tafe kamar haka:-
34. Mai saurara
Da ji shi tsara,
Shi zo shi ƙara,
Ka kurumta shi.

39. Sa annamimi,
Shi zama adimi,
Ba shi da komi,
Ka kumyata shi.

Idan aka yi la’akari da ɗangayen ƙarshe na waɗannan baitoci da ke sama, akwai baƙar addu’a a cikinsu sosai. Addu’ar Allah ya kurumta mai sauraren magana, ya ji ya je ya faɗi tare da ƙarawa baƙar addu’a ce ba kaɗan ba. Neman a kurumta mai jin magana ya ƙara na nufin a hana shi jin maganar balle ma har ya ƙara. A baiti na talatin da tara kuwa, marubucin ya yi addu’ar Allah ya kumyata mai ɗaukar maganar ƙarya ya je ya kai gaba domin neman haɗa mutane. Adduar a raba mutum da falalar da Allah ya ba shi baƙar addu’a ce kuma, idan addu’ar ta ci an kumyata bawa. A taƙaice ana buƙatar annamimi ya shiga halin ƙaƙa-nika-yi a rayuwarsa ta duniya a ƙarshe gobe lahira ya shiga matsalar da ta fi ta kowa..
Akwai baƙar addu’a a cikin rubutattar waƙar ‘Yan Santsi Sun Ji Kunya’ ta Yakubu Labaran a daidai baiti na 21 wurin da ya ce:-
21. Laifinai za mu auna,
Jatau sarkin hiyana,
Kare maciyin amana,
Allah tsine wa gwamnan,
Da ke yin fasiƙanci.

A nan, marubucin ya yi baƙar addu’a ga mutumin a dalilin cin amanar da yake yi ta jama’a ta hanyar wani aikin laifi da yake yi da ya haɗa da taƁin haƙƙen jama’a, ba na Allah kaɗai ba. Sanadiyar haka sai aka yi masa addu’ar cewa, Allah ya tsine masa, ashe ma gwamna ne. Ba shi kaɗai ba, duk wanda ke cin amanar jama’a za su rinƙa bin sa da addu’o’i marasa kyau kuma a ƙarshe su yi tasiri domin addu’ar wanda aka zalunta ba ta da shamaki zuwa ga Allah ma’ana, karƁaƁƁiya ce. Tsinewa na nufin nisantar rahamar Allah da kusantar azabarsa. Fatar sha’iri ita ce a sanya mai waɗannan halaye cikin azaba tare da nisantar da shi daga rahama. Duk mai aikata saƁo yana tara zunubi ba sai an yi masa addu’a ba shi ke halaka kansa da kansa domin aikata saƁo kusantar azaba ne kuma, nisantar rahama ne.
Akwai irin addu’ar da ke sama ta tsinuwa a cikin waƙar Aƙilu Aliyu mai suna ‘Jiya daYau’ a baiti na 35. ga abin da ya ce:
34. Allah tsine mayaudaranmu,
Wanda sun ci da taimakonmu,
Don su je gaba don su ƙi mu,
Rabbana maishe su baya.

Mutum na ƙiyayya da duk abin da ke yi wa cigabansa barazana kuma, ba zai aminta da shi ba har koyaushe idan ya gan shi ko dabba ne balle mutum. Yaudara da mayaudara maƙiya ne ga wanda ake shugabanta. Duk abin da aka yi masa sai dai ya raka shi da baƙar addu’a idan ba alheri ba ne domin an fi ƙarfinsa. Cutar da aka yi wa mutane ce ke sanya su yin baƙar addu’a. Idan aka yi tsinuwa ba shakka an ci amanar wanda ya yi ta. Faɗar Rabbana maishe su baya baƙar addu’a ce mai nufin Allah ya sa gammo ya juye da kaya, gaba ta koma baya, mulki ya fita hannunsu, su koma baya a wayi gari su ake mulka. Wannan na ba da hoton shugabancin zamanin da muke ciki a yau. A taƙaice ana nufin shugabancin da suke yi, ana buƙatar a sauke su, su komo ƙasa a aza wasu su shugabance su, su ɗanɗani abin da suka kasance suna yi wa jama’arsu lokacin da suke kan mulki.
Baƙaƙen addu’o’i na da yawa a cikin rubutattun waƙoƙin Hausa, sai dai misalai ne kaɗai aka bayar na wasu da ke ɗauke da su (baƙaƙen addu’o’i). Sai dai har yanzu a cikin waƙar Aƙilu Aliyu ta ‘Buƙatar Bayanin Halayen Jama’a, akwai baƙar addu’a a baiti na 20. sunan waƙar ‘Yaƙin Ojukwu (1967). Ga addu’ar nan tafe a cikin wannan baiti:-

20. Na roƙi Allah shi ka bayarwa duka,
Nasara shi ba mu a kan minafikai duka,
Inyamurai da irinsu sa musu hallaka,
Sa ɗaukakarka gare mu tare da tsarkaka,
Ka tsare mu sherin kafirin ga Ojukwu.

Addu’ar Allah Ya hallaka wani ko wasu baƙa ce. Layi na uku, wato ɗangon tsakiya na baitin da ke sama na ɗauke da bakar addu’a ga Inyamurai da irinsu ta neman Allah ya kashe su. Hallakar da marubucin ke nufi a nan, ita ce mutuwa ko kuma a rinjaye su cikin yaƙin da ake yi.
Ba wannan kaɗai ba, akwai baƙar addu’ar da Kyaftin Umaru Ɗa Suru ya yi zuwa ga duk mai ƙiyayya da garinsu ta hanyar zagin garinsu (Suru) inda yake zargin garin Suru da yawan sauro. Wannan ya fusata Kyaftin Suru sosai har ya kai wurin yin baƙar addu’a ga duk maijifar garin Suru da abubuwan da ba su da kyau. Mutumin day a tsargi garin Suru cewa ya yi:
Suru da yunwa tay yi kanta,
Sannan kuma ga mugun sauro,
Da yara da manya sun yi lauɗi,
Mutum bai gane ɗan uwanai.

Lokacin da Kyaftin ya tashi mayar da martani ga mutumin da ya tsargi garin Suru da yawan sauro, ga baƙar addu’ar da ya yi gare shida duk wanda ke baya gare shi cikin “Waƙar Suru Ta Biyu” a baiti na hamsin da biyu da na hamsin da uku:
52. An ce can dauri Suru ta yi yawan sauro,
Ba mai kwana cikinta sai da gidan sauro,
Sai ko mai son maleriya ciwon sauro,
Sauro yau babu ko guda a cikin Suru.

53. Kowac ce Suru a yanzu akwai sauro,
Jalla ka sa mai ciwon ƙusumbi shi yi doro,
Matar ta yi ƙazzuwa ɗiyan baƙon dauro,
Sauro yau babu ko guda a cikin Suru.
Idan aka kula da baitocin biyu, za a fahimci Kyaftin shimfiɗa ce ya yi a baiti na hamsin da biyu sannan ya bijiro da baƙar addu’a a baiti na hamsin da uku. Babu shakka addu’ar da Kyaftin ya yi ta karƁI sunanta na mummunadomin ba ta tsaya ga wanda ya jab a, ta haɗa da iyalinsa baki ɗaya.
Ba a ce waɗannan dalilan da aka kawo kaɗai ke sa a yi baƙar addu’a ba, a’a, suna dai cikin dalilan da ke sanya a yi baƙar addu’a. Haka kuma, an kawo misalai ƙarƙashin kowane dalili na baitoci daga wasu rubutattun waƙoƙin Hausa.

5.0 Kammalawa


Takardar ta fito da nau’in baƙar addu’a daga marubuta daban-daban. TaƁa haƙƙen jama’a na sanya a yi baƙar addu’a kamar yadda ba su haƙƙensu ke sanadiyar yin addu’a mai kyau. An kawo gabatarwa a ma’anar addu’a da tab aƙar addu’a da dalilan da ke sanya yin baƙar addu’a da suka haɗa da zalunci da sata da zaman banza da ƙiyayya da kuma hassada. Takardar ta fito da cewa ba a yi wa mai taimaka wa al’umma baƙar addu’a kamar yadda mai cutar da su bai samun ta ƙwarai. Yadda ake yi wa wanda ya taimaki al’umma addu’ar kirki, haka ake aika baƙar addu’a ga wanda ya cuce su. Duk wanda aka ƙulla wa sharri ko aka zalunta aka cuce shi ta hanyar sace masa dukiya da sauran kayayyaki ko aka yi masa fashi da makami ba zai ce Allah ya sa wanda ya yi masa ya gama lafiya ba, sai dai Allah ya hana shi gamawa lafiya. Haka abin yake kuma, ko yaushe haka zai kasance. Wanda aka taimaka ya yi addu’ar kirki, shi kuma wanda aka zalunta ya yi baƙa. Da wuyar gaske a sami mai ɗaga hannu ya ce bai taƁa yin baƙar addu’a ba, ko da sau ɗaya a rayuwarsa ta duniya ga wanda ya cutar da shi ba. Wannan na ƙara tabbatar da cewa addu’a makamin ce ga wanda aka zalunta.

 

Karanta wata muk'ala

https://www.amsoshi.com/2017/07/21/aron-murya-tsakanin-wasu-marubuta-wakokin-hausa/

Manazarta


Ainu, H.A (2007) Rubutattun Waƙoƙin Addu’a Na Hausa: Nazarin Jigoginsu da Salonsu. Kundin Digirin Ph.D. Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.
Awde, N. (1996) ƙamusun Hausa da Turanci da Turanci da Hausa
Hippocrene Books, INC 17 Madson Avenue New York, NY10061

Birniwa, H.A (1981) The Imfuraji of Aliyu Namangi M.A. S.O.A.S. University of London.

Birniwa, H.A. (1987) Conservatism And Discent: A Comparative Study of NPC/NPN and NEPU/PRP Hausa Political Verse from CA 1946-1988, PhD Thesis Usmanu Danfodiyo University, Skoto.

Birnin Tudu, S.Y. (2001) ‘Jigo Da Salon Rubutattun Waƙoƙin Furu’a Na ƙarni Na Ashirin. Kundin Ph.D Sashen Koyar da Harsunnan Nijeriya Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.

Bunza, A. M. (1994) ‘Yaƙi Da Rashin Tarbiya, Lalaci, Cin Hanci Da KarƁar Rashawa Cikin Waƙoƙin Alhaji Muhammadu Sambo Wali Basakkwace’ Ibrash Lagos.
Bunza, A.M. (2014) “In Ba Ka San Gari Ba Saurari Daka: Muryar Nazari Cikin Tafashen Gambo”, Elkods Printing House, Cairo.

Bunza, D. B. (2014) Tsettsefe Jigo da Salon Baƙar Addu’a a Cikin Waƙar Audu Makaho ta “Mai wa Amo Takkai”, Ɗunɗaye Journal of Hausa Studies Vol.1 No.6. Department of Nigerian Languages, Usmanu Ɗanfodiyo University, Sokoto.

Ɗangambo, A. (1980) “Hausa Wa’azi Verse from Ca 1800-1970: A Critical Study of Form Language And Style” PhD Thesis S.O.A.S University of London.

Ɗangambo A. (2007) Daurayar Gaɗon Faɗe Waƙa (Sabon tsari) Amana Publishers ltd, Zaria, Kaduna.

Dunfawa, A.A (2003) ‘Waƙa A Tunanin Yara’ Ph D Thesis Usmanu Ɗanfodiyo University, Sokoto.

Giɗaɗawa, M.B. ( ) “Baje Kolin Hajar Tunani’.

JaƁƁI, B.M (1999) ‘Audu Makaho Da Waƙoƙinsa, Kundin B.A. Sashen Koyar da Harsunnan Nijeriya Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo Sakkwato.

Jami’ar Bayero Kano, (2006) ‘ƙamusun Hausa’, Cibiyar Nazarin Harsunnan Nijeriya, B.U.K.

Junaidu, 1. (1981) (Abokin Hira 1) Ciza Ka Busa, Longman Nigeria Plc.

Kaset: Waƙoƙin Audu Maƙaho.

Maikaturu, A. ( ) Waƙa (Halima).

Muhammadu, D. (1977) “Individual Talent in The Hausa Poetic Tradition: A study of Aƙilu Aliyu and His Art”. Ph.D Thesis, S.O.A.S, University of London.

Muhammad, D (ed 1990), Hausa Metalanguage Vol. 1. Ibadan, University Press Limited.
NNPC, (1976) Fasaha Aƙiliya, Zaria.

NNPC (1977), Waƙa A Bakin Mai Ita, Zaria.

Sanusi, A. (1985) “Umaru Ɗa Suru da Waƙoƙinsa”, Sakamakon Bincike na Digirin Farko, Takarda ta 308, Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Sakkwato.

Usman, B.B. (2008) “Hikimar Magabata: Nazari A Kan Rayuwar Malam (Dr) Umaru Nassarawa Wazirin Gwandu (1916-2000), Da Waƙoƙinsa”, Kundin Digirin Ph.D Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.

Yahya, A.B. (1982) Jigon Nazarin Waƙa, Fisbas Media Service, Kaduna.

Yahya, A.B. (2001) “Salo Asirin Waƙa”. Fisbas Media Service, Kaduna.

Yahya, A.B. (1989) “The Verse Category of Madahu with Special Reference to Theme, Style and Background of Islamic Source and Belief”. Kundin Ph.D Usmanu Ɗanfodiyo University, Sokoto.

Post a Comment

1 Comments

ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.