Ticker

6/recent/ticker-posts

Karin Magana Dake Ƙunshe Da Zamantakewa: Karin Magana Da Ke Ƙunshe DaZamantakewa

1. Ka so naka duniya ta Ƙi shi, ka Ƙi shi duniya ta so shi.
2. ďa na kowa ne.
3. Zama alƘarya sai da karkara
4. Zama cikin mutane daďi gare shi
5. Zama da arne shi ya kawo cin mushe
6. Zama da mai kora yana sa shafar kai
7. Zama da mugun babba, yaro sake dabara
8. Zama da mutum sai da dabara
9. Zama da wane sai ďan wane
10. Zama da ďan Adam sai da haƘuri
11. Zama in da babu mutane azaba ne
12. Zama inuwa yakan kawo daďin magana
13. Zama kishiyar tafiya
14. Zama kusa-da-kusa zaman gira da idanu
15. Zama lafiya ya fi zama ďan sarki.
16. Zama wuri ďaya tsotsayi inji kifi
17. Zama zamnewa ne
18. Zaman daji wauta ne
19. Zaman duniya cuďe-ni-in-cuďe-ka
20. Zaman duniya haƘura
21. Zaman duniya haƘuri, maƘiya sun fi masoya
22. Zaman duniya iyawa ne.
23. Zaman duniya tamkar rumbu ne miƘo mani in miƘo maka
24. Zaman gari akwai Ƙarya inji Ƃerar daji
25. Zaman kare a karofi, ba reni ba matsa
26. Zaman lafiya ya fi dukiya
27. Zaman lafiya ya fi gara.
28. Zamani ba ka jin magani.
29. Zamani riga ne.
30. Zo mu zamna, zo mu Ƃata

 www.amsoshi.com

Post a Comment

0 Comments