Maƙalar da aka gabatar a taron ƙara wa juna sani na ƙasa da ƙasa na Biyu Kan ‘Heroes and Heroines of Hausaland da Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya da Ilimin Kimiyyar Harsunan, Jami’ar Jihar Kaduna ya shirya, a ranakun 3-5 ga watan Yuni, 2016.
1.0
Gabatarwa
Masana da manazarta da dama sun yi rubuce-rubuce da dama kan abin da ya shafi
rayuwar wasu muhimmai kuma mashahuran mutane waɗanda suka rayu a cikin wani
zamani, kuma rayuwarsu ta zamto abin alfahari ga al’umma. Ire-iren waɗannan
mutane akwai su da dama cikin al’umma, wasu akan san su har su yi fice a
duniyar ƙarninsu duk da cewa suna raye, wasu kuwa ba a gane muhimmancinsu a
cikin al’umma sai bayan sun bar gidan duniya. Ire-iren waɗannan mutane suna nan
birjik a cikin al’umma waɗanda ke ba da gudunmawa ta fuskoki mabanbanta ga ci
gaban rayuwar jama’a, ko dai da ƙarfinsu, ko da aljihunsu, ko kuma da irin
kowace baiwa da Allah ya huwace musu. Wanda wannan kan sa a riƙa tunawa da su
ko bayan rayuwarsu, sannan kuma ayyukansu sukan zamto ababen koyi ga ‘yan baya.
Malam Sa’adu Zungur na daga cikin irin waɗannan zaƙaƙuran mutanen da har abada
tarihi ba zai manta da su ba.
Kasancewarsa fitacce a fannoni daban-daban na rayuwa, wanda kuma ya taka
muhimmiyar rawa ga ginuwar ba ma Arewacin Nijeriya kaɗai ba har da sauran
yankunan ƙasar baki ɗaya. Kasancewar Malam Sa’adu Zungur ya yi fice a fannonin
da suka shafi siyasa da adabi da addini da zamantakewa da kuma ilimin zamani,
wanda har ake ganin cewa ko a zamaninsa samun irinsa sai an darje. Wannan ya sa
wannan takarda ta ƙuduri aniyar zaƙulo muhimman bayanai dangane da abin da ya
shafi rayuwar wannan ɗan tahaliki musamman kasancewarsa marubuci kuma ɗan
siyasa wanda ya sha gwagwarmaya, wanda kuma ya ɗauki alƙalaminsa a matsayin
makamin da yake shiga fagen daga da shi don kare kai da kuma kai suka da shi
duk da cewa rubuce-rubucensa sun fi karkata a ɓangaren siyasa amma dai baifi
bai wa siyasar jam’iyya fifiko ba, abin da kawai ya fi dubawa shi ne ƙasarsa,
wato shi mutum ne mai kishin ƙasa da son ci gabanta. Yawancin ayyukan da aka
gabatar kan rayuwar Malam Sa’adu Zungur sun shafi wani ɓangare ne, wato idan
wani ya kalli wani ɓangare, wani kuma sai ya dubi wani ɓangaren daban. Misali;
Gaya (1972) da Kano (1973) da Abduƙadir (1974) da malumfashi (2012) da Ingawa
(2014) duk sun yi ƙoƙarin bayyana wane ne Malam Sa’adu Zungur, sai da babu
wanda ya kawo bayanai filla-filla kan wannan gwarzo kan duk abin da ya shafi
rayuwarsa da ayyukansa baki ɗaya, sai dai Yakubu (1999) ya yi hoɓɓasa kwarai
wajen ganin haƙarsa ta cimma ruwa, tabbas aikinsa gagarumi ne kuma ya cancanci
jinjina. Sai dai kash! Marubucin bai yi nazarin yadda wannan zaƙaƙurin ɗan
kishin ƙasa ke sarrafa alƙalaminsa ba. Wannan ne ya sa wannan takarda ta ƙuduri
aniyar yin nazarin irin yadda kaifin alƙalamin Malam Sa’adu Zungur yake,
musamman a fagen siyasar Nijeriya. Amma kafin nan sai an kawo tarihinsa tun
daga haihuwarsa da neman iliminsa da ayyukansa da rubuce-rubucensa. Sannan daga
bisani za a yi nazarin rayuwar siyasarsa. Mu je zuwa!
2.0 Wane
ne Malam Sa’adu Zungur?
An haifi Malam Sa’adu Zungur yankin Ganjuwa a cikin garin Bauchi ranar
20/11/1914, cikakken sunansa shi ne Ahmad Mahmud Sa’adu Zungur. Tarihi ya nuna
cewa asalinsu mutanen ƙasar Borno ne, duk da cewa ba a fadi rana ko shekarar da
suka yi ƙaura daga ƙasar Borno zuwa Lardin Bauchi ba. Zamansu a Bauchi ya sa
suka ƙulla alaƙar auratayya tsakaninsu da ƙabilar Bankalawa waɗanda suke wani ɓangare
ne na ƙabilar Jarawa a Kudancin ƙasar Bauchi. Kodayake kafin haihuwarsa
iyayensa sun riga sun saje da al’ummar Hausa-Fulani a harshe da kuma al’adunsu.
Maimakon kasancewarsu Barebari daga asali zuwa ƙabilar Bankalawa, sai al’adu da
tsarin rayuwar Hausawa ya yi tasiri a kansu. Wanna ya sa Malam Sa’adu da kansa
ya kira kansa da Bahaushe(yakubu;1999)
An bayyana cewa asalin kakanninsa Malamai ne, wanda aka nuna cewa mahaifin
kakansa mai suna Malam Idris ya yi karatu a wajen Mujaddadi Shehu Usmanu ɗanfodiyo
a Degel, inda a nan ne suka haɗu da Malam Yakubu (sarkin Bauchi na farko da
Shehu ya bai wa tuta). Bayan dawowarsu daga Degel sun raka Malam Yakubu zuwa
Sokoto wajen karɓo tuta domin gudanar da jihadi. Malam Idris tare da
‘yan’uwansa Bankalawa sun zauna a wani wuri da ake kira Zungur Dutse, daga
bisani suka gangaro zuwa gaɓar kogi, inda suka kafa gari mai suna Zungur Kogi,
wanda ake ganin daga nan ne aka samu laƙabin Zungur a cikin sunan Malam Sa’adu
Zungur. Mahaifin kakansa Malam Idris da Kakansa Malam Ahmad dukkansu ba su yi
sarautar garin Zungur Kogi ba, maimakon haka sun fi mayar da hankali wajen
koyar da ilimi. Allah ya azurta kakan Malam Sa’adu Zungur da ‘ya’ya da yawa,
daga cikinsu akwai Malam Muhammad Bello mahaifin Sa’adu Zungur wanda yake
fitaccen malami ne, wanda kuma ya tashi cikin tarbiyya irin ta malanta.
Mahaifin Malam Sa’adu yana jin Hausa da Fillanci da kuma Larabci. Ya auri
mahaifiyar Malam Sa’adu a matsayin matarsa ta uku(Yakubu;1999).
Malam Sa’adu Zungur na ɗaya daga cikin ‘ya’ya uku kacal da Allah ya azurta
mahaifiyarsu da su. Shi ne kaɗai namiji, sauran ‘yan’uwansa biyun kuwa mata ne;
Aisha(Nana) da Hassan(Aji). Kodayake, yana da sauran ‘yan uwa maza uku da mata
uku. Kenan su tara ne a wajen mahaifinsu, maza huɗu mata biyar. Mahaifiyar
Malam Sa’adu ta rasu lokacin yana da shekaru shida kacal a duniya, a dalilin
haka sai yarsa Nana Aisha ta ɗauke shi domin ci gaba da riƙonsa, wadda ta girme
shi da shekaru goma sha huɗu, kuma a lokacin tana aure da almajirin mahaifinta
mai suna Malam Giɗaɗo.
3.0
Neman Iliminsa
Kasancewar Sa’adu ya fito daga gidan ilimi, sai ya tashi cikinsa, ya kuma
kasance yaro mai hazaƙa da ƙwazo ƙwarai. Ya fara karatun alƙur’ani mai girma
tun yana da ƙarancin shekaru, wannan ya sa ya sa haddace Alƙur’ani yana ɗan
shekara 15 (Abdulƙadir;1974). Sa’adu ya ci gaba da neman ilimi da karatu a
wajen mahaifinsa inda ya yi karatu mai zurfi a fannoni da dama kamar su;
Tafsiri da Fiƙihu da Tauhidi da Nahawu da sauransu, inda ya tsere wa dukkan
‘yan’uwansa. Kasancewarsa haziƙi a fagen karatu ya sanya mahaifinsa ya fi ƙaunarsa,
inda har yakan yi wa sauran ‘yan’uwansa gorin cewa sun kasa kamo ɗan ƙaramin ƙaninsu.
Tun yana ƙarami, Sa’adu ya kasance mai sha’awar karanta tatsuniyoyin Larabawa
da Indiyawa, wanda yakan samu daga karikitan mahaifinsa. Bayan ya fara tasawa
sai ya koma karatun rubuce-rubucen ƙarni na sha tara, lokacin jihadin Shehu ɗanfodiyo,
musamman rubuce-rubucen Malam Abddullahin Gwandu(Yakubu;1999).
Bayan ɓullowar ilimin boko, sai Sa’adu ya buɗe wani sabon shafi na fafutikar
neman ilimi, duk da cewa burin mahaifinsa shi ne ya zamto ya samu ilimin addini
mai zurfi ta yadda zai gaje shi a fagen malanta, wannan ya sa a farko mahaifin
nasa ya ƙyamaci karatun boko duba da irin yadda irin Wannan ilimi ya samo asali
da kuma waɗanda suka zo da shi wato Turawa ‘yan Mishan da ‘Yan mulkin mallaka.
Duk da kasancewar an dauki mahaifin Sa’adu Zungur aikin malanta a makarantar
firamare ta Yelwa a nan lardinsu na Bauchi, hakan bai hana shi ƙyamatar karatun
boko ba, a matsayinsa na malami mai koyar da ilimin Larabci da kuma addinin
Musulunci. A ra’ayin mahaifin Malam Sa’adu Zungur ya so ɗan nasa ya gaje shi
kamar yadda shi ma ya gaji mahaifinsa Malam Ahmad, Malam Ahmad kuma ya gaji
kakansa Malam Idris. Saboda haka Malam Bello wato mahaifin Sa’adu ya so ya gaje
shi a matsayin babban shaihin malami. Ashe Allah ya ƙaddari Malam Sa’adu Zungur
da samun fice a kan dukkan fannonin ilimin guda biyu, wato fannin ilimin
zamani(boko) da kuma na addinin Musulunci.
Sa’adu Zungur ya samu shiga makarantar firamare ta ta lardin Bauchi ƙarƙashin
kulawar mahaifinsa a shekarar 1920, lokacin yana ɗan shekara shida. Tun a
farkon kafa makarantun boko an riƙa amfani da sunayen garuruwan da ɗalibai suka
fito fito maimakon sunayen iyayensu. Hakan ya sa lokacin da aka sanya Sa’adu a
makarantar firamare sai aka riƙa kiransa ‘Sa’adu Bauchi’, haka ma sauran waɗanda
suka shiga makaranta a wannan zamanin dukkansu da sunayen garuruwan da suka
fito aka riƙa kiransu. Misali; Abubakar Tafawa ɓalewa da Ahmad Raɓah da Madugu
Zurmi da Abubakar Dogon Daji da Ibrahim Kajuru da Yahaya Gusau da Umaru Gwandu
da Dungus Borno da Umaru ɓaɓura da Abdullahi Okene da Jimada Pategi da Damale
Kaita da Fate Kafin Madaki da sauransu (Yakubu;1999). Sai bayan da ya ajiye
aikin gwamnati sannan ya mayar da sunansa ya koma ‘Sa’adu Zungur’.
Hazaƙa da ƙwazon Sa’adu Zungur ya sa a shekararsa ta farko a makaranta sai aka
nemi ya riƙa koyar da ɗalibai ‘yan aji uku darasin Larabci da ilimin addinin
Musulunci. Wannan ya sa ya kammala karatunsa cikin nasara a shekarar 1926.
Sa’adu bai samu tafiya makarantar midil ba domin a lokacin babu ita a duk faɗin
lardin Bauchi, inda sai a wuraren shekarar 1930 aka samar da ita a lardin na
Bauchi. Hakan ya sa a wuraren 1929 lokacin yana ɗan shekara 15 ya shiga cikin
ajin manya, inda ya yi nasarar lashe jarabawar shiga kwalejin Katsina, wadda
ita ce makaranta mafi girma a Arewacin Nijeriya. Kasancewar an samar da
kwalejin katsina ne a shekarar 1921 domin horar da malaman makarantun midil,
Sa’adu ya sami shiga kwalejin domin samun horo a matsayin malamin kimiyya. Inda
maimakon shekaru biyar da zai yi kafin ya kammala, sai aka amince masa ya
kammala a cikin shekaru uku saboda ƙwazonsa, wato daga shekarar 1929 zuwa 1932.
Daga nan ya ƙure matakin ilimin boko a Arewacin Nijeriya. A wanna lokacin kuma
sai ya ci gaba da neman ilimi mai zurfi na Fiƙihu daga manyan malan birnin
Katsina.
Kasancewarsa mai ƙarancin shekaru, wannan ya sa ake ganin ya yi ƙarami wajen
zurfafa ilimin Fiƙihu, hakan ya sa ya shafe shekara guda a matsayin malamin
kimiyya a Kastina. A cikin shekarar sai aka yanke shawarar tura shi sabuwar
kwalejin Yaba da ke Lagos, wadda ita ce kwaleji mafi girma a faɗin Nijeriya a
wancan lokacin. An fuskanci turjiya daga wurin mahaifinsa kasancewarsa wanda ya
ƙyamaci karatun boko, hakan ya sa aka nemi Sarkin Bauchi na wancan lokacin ya
sanya baki da yawun ɓangaren ilimi, inda aka bai wa Sa’adu damar ƙaro ilimi a
kwalejin Yaba da ke Lagos. Sa’adu ya kasance ɗan Arewa na farko wanda ya fara
halartar wannan kwalejin, wanda kuma Turawan mulkin mallaka suka ɗauki nauyinsa
zuwa ƙaro ilimi mai zurfi daga Arewa a lokacin yana ɗan shekara 19. Ko da ya
dawo hutun zangon karatu na farko sai ya ƙi komawa, bisa hujjar cewa duk
abubuwan da ake koyarwa a makarantar ya riga ya san su, domin shi ya je
kwalejin ne domin samun ilimi mai zurfi kan halittu masu rai(Biology) da kuma
ilimin harhaɗa magunguna(Chemistry), amma sai ya ga abin ba haka yake ba. Hakan
ya sa ya ƙi komawa, inda aka kaɗa aka raya amma ya ƙeƙasa ƙasa ya ce ba zai
koma ba. Daga ƙarshe dai dole aka haƙura aka bar shi.
Malam Sa’adu ya rasu a shekarar 1958 bayan doguwar jinya. Duk da cewa ɗaya
bayan ɗaya ya auri mata shida a lokuta mabambanta, don bai taɓa zama da mata
biyu lokaci guda ba. Ya rasu ya bar matar aure ɗaya, Allah bai azurta shi da
haihuwa ba. Allah ya gafarta masa(Yakubu;1999).
4.0
Ayyukansa
Tun bayan ɗauki ba ɗaɗin da aka yi ta yi da Malam Sa’adu Zungur kan ya koma
kwalejin Yaba amma abin ya ci tura, sai Turawa suka ga cewa barin mutane irin
su Malam Sa’adu ba tare cin moriyarsa basirarsu ba babbar hasara ce, sai suka
yanke shawarar tura shi makarantar koyon aikin tsafta, inda sashen kiwon lafiya
suka zaɓi Malam Sa’adu Zungur suka tura shi domin samun horo a matsayin malamin
tsafta mai daraja ta uku (Third Class Sanitary Inspector) a shekarar 1935. Duk
da cewa matakin iliminsa ya wuce a ɗauke shi a wannan matakin, amma sun yi masa
haka ne a matsayin horo kan bijirewa umarninsu da ya yi da kuma mayar musu da
martani da kalamai marasa daɗi da shi ɗin ya yi wa Turawan.
Wata guda bayan kama aiki, sai Malam Sa’adu ya tsere wa tsara a cikin dukkan
daliban, inda har babban Baturen ilimi ya buga waya ya bayar da umarnin ɗaukaka
darajarsa zuwa matakin malami a makarantar. Daga ɗalibta sai ya koma malanta,
amma duk da haka sai suka ƙi biyan sa albashin da ya kamata wanda ya kai
matakin ilimi irin nasa ya samu.
A shekarar 1938 ya samu nasarar kammala wani kwas na zama cikakken malamin
tsafta da sakamako mafi girma (Distinction).
An koma da shi sashen farfagandar kiwon lafiya (Health Propaganda Unit) a
shekarar 1938.
A shekarar 1939 kuma an bayyana shi a matsayin mafi ƙwazo a wurin aikinsa.
An yi wa Malam Sa’adu Zungur sauyin wurin aiki zuwa makarantar koyon aikin
tsafta da ke Zariya a matsayin malami a shekarar 1939.
An tura shi ƙauyen Anchau a matsayin jami’in yaƙi da ƙudar tsando, inda ya yi
aiki har zuwa shekarar 1943, inda ya ajiye aiki saboda matsalar rashin lafiya.
A lokacin albashinsa yana fam 104 a shekara.
Ya yi aiki a matsayin wakilin jaridar West African Pilot ta Azikiwe.
Ya riƙe muƙamin sakataren jam’iyyar N.C.N.C (Yakubu;1999).
5.0 Rubuce-Rubucensa
Kasancewar rayuwar Malam Sa’adu Zungur rayuwa ce da tun farkonta aka fara ta
bisa tarbiyya ta ilimi, hakan ya sa wannan gwarzo ya kasance ba shi da wani
abin taƙama wajen warware matsalolinsa na zamantakewa a kimiyyance ko a
siyasance da ya wuce alƙalaminsa. Malam Sa’adu ya ɗauki alƙalami tamkar takobi
musamman lokacin da ya tsinci kansa a fagen dagar siyasa, inda ya riƙa amfani
da shi wajen kare kansa da kai suka ga abokan hamayyar siyasa musamman domin
tabbatar da gaskiya da adalci, da kuma kore ƙarya da handama da babakere.
Malam Sa’adu Zungur ya yi rubuce-rubuce
da dama waɗansu na addini wasu na siyasa wasu kuwa na zamantakewa. Kasancewarsa
fitacce a fagen ilimin addini wannan ya sa duk inda ya ɗauki alƙalaminsa domin
kattaba wani abu, za a tarar tasirin addinin ya fito ƙarara a cikinsa. Tun daga
wasiƙu da jawabai, da waƙoƙin da ya rubuta duk sun fito da wannan tsarin.
Fitattu daga cikin rubuce-rubucen Malam Sa’adu Zungur su ne waƙoƙi, domin a
wancan lokacin waƙa ita ce hanya mafi sauƙi wajen isar da saƙo ko yaɗa manufa
ga al’umma. Daga cikin waƙoƙin da wannan gwarzo ya rubuta waɗanda kuma suka yi
tasiri ƙwarai ga rayuiwar al’umma sun haɗa da:
a- Waƙar Bidi’a
b- Waƙar Maraba da Soja
c- Waƙar ‘Yan Baka
d- Waƙar Arewa Jamhuriya ko Mulukiya
e- Waƙar Yaƙi da Shaiɗani
f- Waƙar Mulkin Nasara.
g- Waƙar Jihadin Neman Sawaba.
Baya ga waƙoƙi waɗanda su ne suka fi fice cikin rubuce-rubucensa, sannan kuma
akwai wasiƙu waɗanda ya riƙa aike wa hukumomi da sarakuna da shugabannin
siyasa, waɗansu na ƙorafi, waɗansu na martani, waɗansu na neman izinin gudanar
da tarurrukan siyasa, waɗansu kuma zuwa ga abokan siyasarsa da suke jam’iyya ɗaya.
Sannan kuma akwai rubutattun jawabai na tarukan siyasa da sauransu.
6.0 Malam Sa’adu Zungur a Fagen Siyasa
Mafi yawancin waɗanda suka san ko suka ji labarin Malam Sa’adu Zungur yawanci
ba su san shi a kan wani gagarumin aiki da aiwatar a rayuwarsa ba. Mafi yawansu
sun san shi ne kawai a suna, watakila ma idan aka tambayi wasu wane ne Sa’adu
Zungur? Amsar da za su bayar bai wuce su ce, sunan wani ɗakin kwanan ɗalibai ne
a jami’ar Bayero, Kano ba. Wasu kuwa cewa za su yi sunan wani titi ne a Bauchi,
ga wasu kuwa sunan wata ƙungiyar mawaƙan Hausa ne da ke Kano.
Wane mutum! Malam Sa’adu Zungur ya wuce nan. Idan aka nemi sanin haƙiƙanin
amsar wanna tambaya da aka yi a sama, to za a iya amsa ta da cewa Malam Sa’adu
Zungur wani fitacce ne, gagarumi kuma mashahurin malami, gawurtaccen ɗan
siyasa, tsayayyen ɗan kishin ƙasa, fasihi a fagen rubutun adabi, gogagge a
fagen aikin jarida, sannan ɗa ne ɗaya daga cikin fitattun ‘ya’yan da Allah ya
huwace wa Arewacin Nijeriya. Shi ne mutumin da ya sadaukar da rayuwarsa ga ci
gaban ƙasa baki ɗaya.
A fagen siyasar Nijeriya Malam ya taka muhimmiyar rawa wajen ganin an samu
daidaito tsakanin masu mulki da waɗanda ake mulka, in kuwa daidaiton bai samu
ba to talaka ya sami sassauci daga irin ƙuncin rayuwar da yake ciki.
Kasancewar Malam Sa’adu zungur wanda ke adawa da tsarin da Turawan mulkin
mallaka ke kai, wannan ya sa a kodayaushe yake ƙoƙarin faɗakarwa da ƙoƙarin
wayar da kan al’umma wajen guje wa bauta da ƙoƙarin samun ‘yanci. A kodayaushe
babu kalmar da aka fi samu cikin bayanai da rubuce-rubucensa kamar ‘adalci’.
Tun bayan da ya ajiye aikin gwamnati, sai ya shiga harkar ƙungiyoyi, waɗanda
yawancinsu ƙungiyoyin siyasa ne domin ci gaban al’ummar Arewa. Malam Sa’adu ya
jagoranci kafa ƙungiyoyi kamar su; Zaria Friendly Society(ZFS), da Bauchi
Discussion Cicle(BDC) da Bauchi General Improɓement Union(BGIU) da sauransu. Waɗannnan
kungiyoyi kusan za a yi iya cewa su ne tsittsigen siyasar jam’iyyu wanda har
Malam Sa’adu Zungur ya bar duniya yake kai. Malam Sa’adu yana ɗaya daga cikin
waɗanda suka kafa jam’iyyar NPC, kai hasali ma, shi ne mutumin da ya yanka mata
ragon suna cikin harshen Ingilishi, daga sunanta na farko a matsayin ƙungiyar
siyasa, wato Jam’iyyar Mutanen Arewa zuwa ‘Northern People
Congress’(Yakubu;1999). Kasancewarsa mutum ne da kullum yake ƙoƙarin faɗa da
zalunci da mulkin danniya da babakere, sannan kuma yana fito-na-fito da
tsare-tsaren Turawa.Wannan dalilin na daga cikin dalilan da suka sa ya fice
daga jam’iyyar N.P.C, kasancewar ya lura cewa jam’iyyar ta kauce daga kan
manufar da aka kafa ta a kai na yaƙi da jahilci da lalaci da zalunci, da kuma
bai wa mata damar shiga majalisa da kuma shiga zaɓe, da yin gyaran fuskan ga
hukumar NA domin ta dace da zamani. Wannan ne ya sa da farko ake ganin cewa
jam’iyyar NPC ce jam’iyyar neman sauyi(Malumfashi;2016). Domin tun da farko
jam’iyyar an kafa ta ne don mutanen Arewa baki ɗaya, domin kuma ci gaban arewa
da al’ummarta, amma daga bisani sai sarakuna da masu faɗa a ji suka haɗa kai da
Turawa suka rungumi abin da Malam Sa’adu ya kira da mulkin danniya da babakere.
Daga nan sai suka kafa jam’iyyar NEPU wadda ta samo asali daga ƙungiyar NEPA
wadda ita ma ƙungiya ce ta siyasa amma ba ta zama jam’iyya ba duk da kasancewarta
ƙungiyar siyasa ta farko wadda kuma ta fi samun karɓuwa a Arewacin Nijeriya.
Kasancewar jam’iyyar NEPU an ɗauke ta jam’iyyar talakawa masu neman sauyi,
jam’iyyar NPC kuma jam’iyyar ‘yan jari hujja, wato sarakuna da Turawa, hakan ya
sa ya ƙaddamar da yaƙi da zalunci inda ya mayar da alƙalaminsa shi ne babban
makamin da yake amfani da shi a fagen dagan siyasa. Kamar yadda ya ce;
Daga yau mun ɗauki makamanmu
Na kisan zaluncin ma su gari,
Domin halshe shi ne kansakali
Mashi kuwa alƙalami na gari. (Waƙar Jihadin Neman Sawaba.)
7.0 Kaifin Alƙalamin Malam Sa’adu Zungur a Fagen Siyasa
Babban makamin da Malam Sa’adu Zungur ya yi amfani da shi a fagen siyasarsa shi
ne alƙalaminsa, wanda ya yi amfani da shi wajen yin rubuce-rubuce na waƙoƙi
domin jawo hankalin al’umma da faɗakar da su kan siyasa, da wayar musu da kai.
Kasancewarsa mutum ne da kullum ke kira kan a yi adalci wannan ya sa ba ya jin
tsoron faɗin gaskiya komai ɗacinta ga kowa. Wannan ya sa tun a farkon waƙarsa
ta Arewa, Jamhuriya ko Mulukiya ya buɗe da cewa;
In za ka faɗi, faɗi gaskiya,
Ko me taka ja maka ka biya.
Sannan ya dubi sarakunan yankin Arewa ya ce musu;
Sallama a gare ku sarakuna,
Mun yi niyyar bayyana gaskiya
.
Wannan ya nuna cewa Malam bai bar kowa ba in dai kan faɗin gaskiya ne, domin
har iƙirarin faɗin ta ya yi a ko’ina ba tare da shakka ko tsoron abin da hakan
zai haifar ba. Dubi abin da yake cewa;
Gaskiya dai mu kam za mu faɗa,
Ko ana ɗauri har kan zakari
Gaskiya launinta guda ɗaya ne,
Ko da a gaban Dujal mahari.
Gaskiya launinta guda ɗaya ne,
Ko a fadan Fir’aunan garari
ƙarya ce mai launi goma
Babu mai haske ko an wayi gari.
(Waƙar Jihadin Neman Sawaba).
A nan Malam yana nuni ne da muhimmancin gaskiya da kuma faɗin ta komai ɗaci,
inda ya nuna cewa duk yadda azzalumi ya kai ga zalunci, ba zai kai Fir’auna ba,
to ko a gabansa ne ka faɗi gaskiya ba tare da tsoronsa ba. An kawo wannan ne
duba da yadda a yau aka ɗauka cewa yana daga cikin ɗabi’un ‘yan siyasar wannan
zamani yadda suka ɗauki ƙarya tamkar wani ginshiƙi a cikin siyasa, ta yadda har
mutane sun ɗauka ƙarya hali ne na kowane ɗan siyasa, wanda ko kaɗan ba haka
abin yake ba domin idan aka yi nazarin rayuwar mutane irin su Malam Sa’adu
Zungur za a ga cewa gogaggun ‘yan siyasa ne waɗanda kusan ma in aka ce daga
wurinsu aka koyi siyasar zamani to ba za a ce an shara ta ba. Amma duk da haka
suka ɗauki aƙidar faɗin gaskiya da aiki da ita saɓanin ‘yan siyasar yanzu waɗanda
ba a san ko daga ina suka koyi tasu siyasar ba.
Haka kuma idan aka yi nazarin tarihin Malam Sa’adu Zungur za a ga cewa, mutum
ne wanda yake adawa da tsarin Turawa, a kodayaushe cikin sukar lamarinsu yake
domin bai yarda ya biye wani duk wani abin da suka zo da shi idonsa a rufe ba.
Wannan ne ma ya sa suka sha yin musayar yawu da Turawan, kuma kasancewar su ke
juya akalar komai a lokacin sai suka yi ta tsananta masa da horo ta duk hanyar
da suka samu dama. Misali yadda suka ɗauke shi aiki a ƙaramin matakin da bai
kai matakin karatunsa ba, da yadda suka riƙa biyansa albashin da bai kai abin
da ya kamata a biya shi ba, da yadda suka riƙa yi masa canjin wurin aiki domin
horo; dubi canjin da aka yi masa daga Zariya zuwa Anchau ya ishe ka misali.
Malam ya fito da irin wannan aƙidar tasa ta yin fito-na-fito da tsarin da ya saɓa
wa tsarin gargajiyar Bahaushe wanda aka gada tun can azal. Dubi abin da yake
cewa;
Kar ka bar arna su shige musu
Don su watsa dafin jamhuriya
………………………………
Duk misalan nan na Amirka ba
Mai kyau, na shirin jamhuriya.
(waƙar Arewa, Jamhuriya ko Mulukiya)
A nan Kalmar arna da ya yi amfani da ita na nufin ‘yan kudu waɗanda suka ɗauki
aƙidar Turawa. Za a fahimci haka ne kuwa idan aka dubi baitin da ya zo bayan
wannan inda ya ambaci Amirka kai tsaye inda ya nuna cewa duk tsarinsu babu mai
kyau, don haka kada a bi su. Haka kuma cikin waƙar ‘Jihadin Neman Sawaba’ ya
fito da yadda tsarin mulkin Turawa yake tare da nuna wa al’umma cewa fa kura da
shan bugu ne gardi da karɓe kuɗi. Inda ya nuna cewa tsarin Turawa ba bin
amincewa ne ba, domin kuwa sun mayar da mu saniyar tatsa ne kawai, kuma ragamar
mulkin namu ma su ne ke juya akalarta. Dubi yadda ya fasalta abin cikin
baitocin da ke biye;
Mun gane gizo na nasara bare
Na baransu Minista ‘yan garari
An ce ikon komai na gun
Sarki wai don shi ke da gari
Amma Razdan, Di’o da waninsu
Duk mashawarta ne ba na gari
ƙaryar banza ƙaryar wofi
Su ke da zare su ke waɗari
Ai sarakai kam hotanni ne
Na sarautar al’ada a gari
Razdan, Di’o da su ADO
Su ke da mabuɗin al’amari
Su ke da wuƙa su ke fiɗar
Mulkin jama’a bisa kan garari
Malamin yanka shi da wuya
Kai da fata sai su Abubakari
Ladar fiɗa kuma za a fitar
Don su Gwanto da Maina da ‘yan bidiri
Tarkacen hanta huhu hanji
Za a tatse don a raba a gari
Hasali dai duk nama na gun
Turawan mulki ‘yan garari.
(Waƙar Jihadin Neman Sawaba)
A nan idan aka yi nazarin baitocin nan da aka jero a sama za a ga cewa Malam
Sa’adu Zungur yana sukar salon mulkin nan ne na jeka-na-yi-ka (Indirect Rule),
inda yake nuna cewa, suna ne dai mu muna da sarakuna amma ba su da wani tasiri,
domin ba su iya aiwatar da komai sai yadda Turawa suka so domin kuwa duk
mashawartansu suna tare ne da Turawan, kasancewar ba a mugun sarki sai mugun
bafade. A ƙarshe dukkan wasu albarkatun ƙasa Turawan ne za su kwashe su bar mu
da ɗan abin da bai taka kara ya karya ba.
Malam ya ci gaba da sarrarfa alƙalaminsa wajen wayar da kan ‘yan Arewa inda ya
nuna musu cewa wajibi ne ‘yan Arewa su dawo cikin hankalinsu, su kuma nuna ƙyamar
su ga tsarin jamhuriya domin in suka amince da wannan tsarin to bai zai haifar
musu da ɗa mai ido ba, hasali ma cutar da su zai yi. Ya ce;
In kunka sake jama’ar Kudu
Suka hau mulkin Nijeriya
Daɗa ba sauran mai tambaya
Kowa ya san zai sha wuya. (waƙar Arewa, Jamhuriya ko Mulukiya)
Ya nuna cewa ‘yan Arewa su tashi kai da fata, su kuma tsaya tsayin daka don
ganin ba a yi musu sakiyar da ba ruwa ba. Domin idan suka yi sakaci har mulki
ya suɓuce musu to fa lallai za su ɗanɗana kuɗanrsu. Allahu akbar! Ka ji masu
hangen nesa. Tabbas batun Malam gaskiya ne, domin an yi wani lokaci da yankin
Arewa ya faɗa cikin halin-ƙaƙa-nika-yi, sakamakon sakacin ‘yan Arewa da suka
sakar wa ‘yan kudu ragamar jagoranci. Kai idan na ce har yanzu yankin Arewa bai
gama farfaɗowa daga halin jinyar da yake ciki ba ban yi ƙarya ba. Wanda ke da
tantama ya tambayi al’ummar Arewa maso Gabas!
Da ya karkato kan sarakuna sai ya yi musu gargadin cewa idan ka ga gemun ɗan’uwanka
ya kama da wuta to ka shafa wa naka ruwa. Inda ya buga musu misalai da wasu ƙasashen
duniya waɗanda suka karɓi tsarin jamhuriya suka kwan ciki. Sai ya ba da misali
da ƙasashe irin su; India da Burma da Indonesia duk sun tsinci kansu cikin
matsala sakamakon shigo-shigo ba zurfi da Turawa suka yi musu ta hanyar
tsunduma su cikin tsarin jamhuriya.
To sarakai sai ku yi tattali
Na adala ban da haramiya
Sai ku hango gemun ɗan’uwa
Da ya kama wuta da gaganiya
Sai ku nemi ruwa ku yi yayyafi
Kada ku ma naku ya sha wuya
(Waƙar Arewa, Jamhuriya ko Mulukiya).
Domin ganin haƙar Turawa ta cimma ruwa sai suka yi tunanin cewa idan suka bar
‘yan ƙasa suka ci gaba da zama kan su a haɗe to ba za su samu gudanar da mulkin
mallaka yadda suke so ba, hakan ya sa suka yi amfani da tsarin nan na ‘A raba
kansu a mulke su’ (Diɓide and Rule system), inda suka riƙa zagayowa suna faɗa
wa ‘yan Arewa cewa kada su kuskura su yarda da ‘yan Kudu. Dubi wannan baitin;
‘Yan fince da su da nasararsu
Sun ƙulla abotar masu gari.
‘Yan fince anan yana nufin masu fada aji, kamar su Razdan da Di’o da alƙalai da
sauran masu riƙe da madafun iko, nasara kuwa su ne Turawan mulkin mallaka waɗanda
suka haɗa kai da sarakai wancan lokacin. Sai suka riƙa zuga masu faɗa a ji da
masu mulki don su raba kan ‘yan ƙasa kada su kasance tsintsiya maɗaurinki ɗaya.
Hakan zai ba su damar miƙe ƙafa su yi yadda suke so. Kamar yadda Malam Sa’adu
ya bayyana waɗannan baitocin;
“Mu Turawa ba mu burin
Dauwama a Arewa ƙasa ta gari”
………………………………….
“Kar ku yarda da ‘yan kudu arna ne
Za su gaje ƙasarku da al’amari”
“Za su gaje ayyuka masu yawa
Siniya sabis da na masu gari”
A nan yana ƙoƙarin bayyana wa ‘yan Arewa ne irin makircin da kutunguilar da
Turawa suke shiryawa, ta hanyar yaudara da raba kan al’umma da nuna musu cewa
ai so suke su mamaye ko’ina su mayar da su tamkar bayi domin za su mamaye
manyan ayyukan gwamnati. Bayan wannan kuma sai su Turawan suka ci gaba da yi
musu romon baka don dai su sami haɗin kansu, inda suka yi musu alƙawarin cewa
za su tabbatar cewa NPC ce ta ci zaɓe don dai su tabbatar tsarin da suka dasa
ya ci gaba. Haka kuma, za su yi ƙoƙarin hana jam’iyyar adawa tasiri da duk
mabiyanta. Dubi yadda marubucin ya hakaito zancen;
“Za mu daddage bisa zaɓenku
Mu da NA daular masu gari”
“Za mu dankwafe NEPU da RSS
Da dukkan jam’iyya mai haɗari”
Hakan ko aka yi, Turawa sun murɗe zaɓen da aka gudanar inda suka bai wa
jam’iyyar NPC rahotanni ta yadda za a ci dunun NEPU, aka kuma shiga ba ‘yan
doka da alƙalai damar da za su kame su ɗaure ba mai cewa ahir. Aka dinga nuna
wa NPC dokokin da za su yi amfani da su su tamke ‘yan Nepu ba tare da wani
ka-ce-na-ce ba (Malumfashi,2016).
Alal haƙiƙa, Malam Sa’adu Zungur ya yi gwagwarmaya a fagen dagar siyasa inda
shi da kansa fa yake nuna cewa tura fa ta kai bango don haka lokaci ya yi da ya
kamata su ɗauki makamansu su shiga fagen daga don a fafata, kamar yadda yake
cewa;
Daga yau mun ɗauki makamanmu
Na kisan zaluncin ma su gari,
Domin halshe shi ne kansakali
Mashi kuwa alƙalami na gari.
(Waƙar JIhadin Neman Sawaba)
Ya nuna cewa yaƙi ba sai lallai da takobi ko mashi ko bindiga ake yi ba, inda
ya nuna cewa harshensa shi ne takobinsa, mashinsa kuwa shi ne alƙalaminsa,
wanda da su yake sara da sukar duk wani abokin hamayyarsa a siyasa. Haka kuma, tsakaninsa
da abokan adawar siyasa nan ma an ja daga, duk da cewa bai kama suna ba, amma
ya yi musu gugar zana gami da yin jirwaye da kamar wanka, domin dai masu
hikimar magana sun ce; “Kowa ya yi zagi a kasuwa ya san da wanda yake yi”. Ya
yi amfani da kausasan kalamai domin huce haushinsa, ta hanyar yi wa ‘yan adawa
tonon silili. Ga abin da fasihin marubucin ke cewa;
Kai baƙi aniyarka baƙa
ɗanduna gabanka akwai haɗari
………………………………..
Wani ya yi gajarta yai tumbi
Yai taiɓa yai gurun kuturi
Wani ya yi tsawonsa tsawon banza
Sai gulma da dogon azzakari
ɗan Dada Ajuji maras kunya
A wala hakkilo a kan lamari
Ya girma da kaka sai fitina
Da dabarar warware alkawari
Ya sha mamanta na zalunci
Da rashin kunya da rashin nazari
Ai Dada Ajuji fatalwa ce
Da bazarta take yawo a gari.
…………………………….
Waɗannan kausasan kalamai sun yi wa ‘yan NPC ciwo. Kasancewar waƙar cike take
da maganganu masu sosa rai ga abokan hamayya a wancan lokaci, hakan ya sa aka
sanya dokar fito da waƙar a rubuce a bainar jama’a. Watakila wannan ne ma ya sa
yawancin waɗanda suka rubuta wani abu dangane da rayuwar Malam Sa’adu Zungur ba
su kawo waƙar ba.
Ashe ba banza ba idan ka ga wani mawaƙin siyasa a yau yana kwarzanta
jam’iyyarsa, domin kuwa ya samo asali tun daga iyayen siyasar. Kasancewar
wannan gwarzo cikakken ɗan NEPU ne wannan ya sa bai ajiye alƙalaminsa ba sai da
ya tabbatar ya kwarzanta jam’iyyarsa domin fito da ita tare da tallata ta ga
jama’a. ya ce;
Jam’iyyar NEPU da RSS
Ansaruddini mutan zikiri
A nan yana nuna wa duniya cewa su fa jam’iyyarsu ta mutanen kirki ce masu burin
gina ƙasa da taimakon addini. Ya ci gaba da ƙarfafa wa ‘yan NEPU guiwa kan su
dage kada kuma su karaya, kada su ji wani rauni a zuciyarsu. Ya kuma ja
hankalinsu inda yake cewa kada su ji tsoron duka ko ɗauri ko ma kisa, domin ba
farau ne ba a wajensu, don haka su dage har sai sun yi nasara. Kamar yadda ya
ce;
Mu ba za mu toge ba bare mu bari
Za mu dage har sai mun ci gari
Ba farau ne ba a ɗaure mutum
A duhun zaluncin masu gari
……………………………..
In don ɗauri an ɗauri wasu
Bisa zamba da zalumcin masu
……………………………
A cikin daular birnin Bauchi
An ɗaure mutane sun fi ɗari
Wannan ƙarfafa guiwa ce da Malam yake yi wa ‘yan jam’iyyarsa ta NEPU domin a
gudu tare a tsira tare. Domin kuma kada ‘yan NPC su ɗauka cewa sun sallama musu
ne. Duk da haka ya ƙalubalanci mawaƙan NPC cewa in suna da mawaƙa kuma sun isa,
to su fito su mayar da martani. Ko kuma su fito da bayanai na gaskiya su yi
musu tonon silili kamar yadda suka yi idan har suna da abin faɗa.
Ya yi amfani da mashinsa ya yi suka ga jam’iyyar NPC, inda ya nuna cewa taken
jam’iyyar ma bai dace da ita ba, ya ce maimakon takensu na ‘Salama’ ai ‘Zalama’
ya kamata su ce. Kai ba ma wannan ba, cewa ya yi ai bai ma kamata a kira su da
NPC ba sai dai ‘yan fitina. Dubi abin da ya ce;
Su suke kasa ‘SA’ a mazaunin ‘ZA’
Sun furta Salama ba ahuri
……………………………….
NPC ne ko ‘yan fitina
Sai gulma da warware alƙawari
Ire-iren waɗannan kausasan kalamai da Malam Sa’adu Zungur ya yi amfani da su
sun kasance tamkar suka ne da mashi, ko sara da takobi ga ‘yan hamayya,
kasancewar ba shi da wata hanyar da zai isar da saƙonsa ga masu mulki da
al’umma cikin sauki in ba ta wannan hanyar ba. Kuma alƙaminsa shi ne babban
makamin da ya riƙe domin tunkarar abokan hamayya.
Wasiƙu/ Jawabai
Kasancewarsa fitacce kuma mashahuri sannan jagora a siyasar jam’iyyu na wancan
zamani, Malam Sa’adu Zungur ya yi amfani da alƙalaminsa wajen kare haƙƙin ‘yan
jamiyyarsa ta NEPU, ta hanyar kai ƙorafin wani abu da ba su gamsu da shi ba, ko
neman izinin yin tarurrukan siyasa, inda a yawancin lokuta akan yi fatali da buƙatunsu
don kasancewarsu ‘yan adawa. A wasu lokutan akan yi musu cin mutunci da zagi,
kai har akan yi amfani da ƙarfin iko a ɗaure su ba tare da wani ƙwaƙƙwaran
dalili ba.
Baya ga waƙoƙi, akwai waɗansu rubuce-rubuce da Malam Sa’adu Zungur ya yi waɗanda
suke da alaƙa da wannan nazari, amma za mu ɗauki wasiƙa guda ɗaya wadda ya
rubuta wa Sarkin Bauchi mu ga yadda fasalinta yake. Wasiƙa ce da Malam Sa’adu
Zungur ya rubuta wa sarkin Bauchi ranar 22 ga Mayu,1956 domin isar da ƙorafinsu
gare shi kan abin da suka kira shi da rashin adalci da wani alƙali ya yi musu
don kawai su ‘yan NEPU ne, inda ya zazzage su ya ci mutuncinsu kuma ya kori ƙarar
ba tare da bin bahasi don gane mai gaskiya ba. Inda a cewarsa ya saɓa
sananniyar ƙa’idar nan da aka san alƙalai da ita ta ‘Ba sani ba sabo’ wanda har
ya sa ake yi musu kirari da ‘ƙuliya manta sabo’. Dubi abin da ya ce;
Domin alƙali ba ya son NEPU, wannan ba zai zama waranti a gare shi, tun bai
binciki shari’ar da take gabansa na game da NEPU ba, sa’annan ya wanke hannu ya
faɗa NEPU da ‘yan NEPU da zagi da la’ana da wofintar da jam’iyyar tun bai
binciki komai na game da abin da ake tuhumarsu da shi ba. Ta yaya waɗannan
mutane za su tsammaci adalci ga wannan shugaba mai shari’a wanda ya cika ransa
da mummunan zato kuma ya cika bakinsa da zagi da la’ana tun bai bi bahasi ba?
(Yakubu,1999).
A nan Malam Sa’adu Zungur ya nuna irin kai ƙololuwar tsanar da ake nuna wa ‘yan
adawa ne. Sanna ba tare da tsoro ba ya rubuta wa sarki wasiƙa ya tsage wa sarki
gaskiya duk da cewa shi ma sarkin duk bakinsu ɗaya, ba kuma zai tsammaci wani
adalci ko goyon baya daga gare shi ba, amma dai ko banza takardar za ta kasance
kandagarki ne ga masu mulkin danniya, wato irin abin nan da ake cewa ‘Kifi na
ganin ka mai jar koma’.
Har ila yau, a cikin wannan takardar akwai inda ya yi ƙorafin cewa an kame ‘yan
jam’iyyar NEPU an garƙame su a caji ofis har sun kwana. Inda suka buƙaci a bar
su su yi sallar asubahi amma aka ƙi, amma aka fitar da wasu Sayawa waɗanda ba
su sallah aka ba su ruwa suka wanke ido. Amma ‘yan NEPU suna kulle suna roƙo a
bar su su yi sallah an hana su. A cikin takardar ya bayyana cewa babu wani ƙwaƙƙwaran
dalili da ya sa aka yi musu haka sai don sun kasance ‘yan jam’iyyar adawa,
wanda kuma shi adalci ga kowa dole ne ba sai wanda ke bin ra’ayinka ba. Dubi
abin da yake cewa;
Mun yi wannan kuka ne a gaban alƙali kuma muka shaida masa cewa, babu wani
dalili da aka ba mu na hana mu yin sallar safiya a “gadirum” wai sai don mu
‘yan NEPU ne!!! Ashe ba mu sani ba, shi alƙali ma yana nufin ƙin bin bahasin
wannan ƙara. Ko don mu ‘yan NEPU ne??!
A ƙarshen wannan wasiƙa mai ɗauke da ƙorafi guda uku, Malamin ya kawo ƙorafi na
ƙarshe yadda wani ɗan NPC ya shiga cikin taron ‘yan NEPU ya aikata wani
ta’addanci amma babu wani mataki da aka ɗauka na hukunci a kansa. Inda ya yi
nuni da cewa da wani ne daga cikin ‘yan NEPU ne ya yi da tuni an yi masa
hukuncin ɗauri ko tara mai tsanani. Inda ya roƙi cewa a ba shi izini ya mayar
da martani kan wannan cin kashin da ake wa ‘yan NEPU. Dubi abin da ya ce;
Muna roƙon izinin Sarki kan mu mayar da mattani tare da ladabi da biyayya. Mun
gaya wa mai girma sarki tun da farko cewa laifin da wani ɗan NPC ya yi a wajen
taron NEPU da irin ta’addar da ya yi gaba gaɗi, idan da ‘yan NEPU ne suka yi da
tun da daɗewa an yi muusu hukuncin ɗauri ko tara mai tsanani, da yake ɗan NPC
ne ai ‘yan doka sun nuna kamar sun yi watsi da maganar duka duka, alhali kuwa a
gaban sarki aka ambata cewa wannan maganar tana hannun ‘yan doka za su kai
gaban shari’a.
Daga baya Ke nan, wai an yi sadaka da bazawara! Ai martanin ke nan Sa’adu
Zungur ya mayar amma domin nuna ladabi ga fada da kuma kasancewarsa mutum mai
hikima, sai ya nuna cewa bai riga ya yi martanin ba, domin dukkan bayanan nan
da ya fito cikin wannan wasiƙar duk yana nuna cewa ba komai ke cikin jam’iyya
NPC ba illa zalunci da danniya. Wanda kuma ba kowa ne ke cikin wannan jam’iyya
ba illa shafaffu da mai, waɗanda suka haɗa da sarakuna da alƙalai da malamai,
da Razdan da Di’o da sauransu.
8.0
Kammalawa
Kaifin alƙalamin
Malam Sa’adu Zungur ya wuce a kwatanta, domin kuwa zafin sara da sukar da
abokan hamayyarsa suka sha ba ya misaltuwa, musamman a ɗan guntun nazari kamar wannan. Kasantuwar irin
zafin sara da sukan da alƙalaminsa ke yi musu ya sa a dalilin waƙar “‘Yan Addakari” kaɗai an sha ɗaure ‘yan NEPU, inda har ta
kai ga duk wanda aka kama shi waƙar sai an ɗaure
shi. Wataƙila
wannan dalilin ne ma ya sa waƙar ta kusa salwanta, in ba don zaƙulo ta
da binciken Yakubu (2009) ya yi ba. Tun da farko, wannan takarda ta ƙuduri
aniyar yin nazari ne kan kaifin da alƙalamin Malam Sa’adu Zungur ke da shi a
fagen dagar siyasar Nijeriya. Inda aka kawo tarihinsa tun daga haihuwarsa da
neman iliminsa da ayyukansa da kuma rubuce-rubucensa. Daga bisani kuma sai aka
tsunduma cikin nazarin ka’in da na’in inda aka dubi yadda ya Malamin ya ja daga
da abokan hamayyarsa na siyasa, inda alƙalaminsa ya zame masa makamin kai hari da
kare kai, ta hanyar nazarin waƙoƙinsa, da wasu sauran rubuce-rubucensa.
Manazarta
Abdulƙadir, Ɗ. (1974) The Poetry, Life and Opinion of Sa’adu Zungur. NNPC,
Zaria.
Birniwa, H.A (1987) “Conservatism
and Dissent: A Comparative Study
of
N.P.C/N.P.N and NEPU/P.R.P Hausa Polical ɓerse From Circa 1946-1983”. Kundin
Digiri na Uku. Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sokoto.
Funtua
A.I. (2003) “Waƙoƙin Siyasa na Hausa A Jamhuriya ta Uku: Yanaye-Yanayensu da
Sigoginsu” Kundin Digiri na Biyu, Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero,
Kano.
Gaya, A.
S. (1972) “Comparison Between Mu’azu haɗeja and Sa’adu Zungur”. Kundin digiri
na ɗaya, Jami’ar A.B.U/B.U.K.
Ingawa, S.
Y. (2014) “Concluding Marɓyn Hiskett’s Thesis on Sa’adu Zungur’s Waƙar ‘Yanci”.
Muƙalar da aka samu a shafin Sa’adu Zungur na yanar gizo.
Kano, A.
(1973) Rayuwar Ahmad Mahmud Sa’adu Zungur. Zaria.
Malumfashi, I. A. M. (2012) “Who was Sa’adu Zungur? A Literary Historian’s
Glimpse”. Takardar da aka gabatar a taron ƙara wa juna ilimi karo na bakwai kan
matsayin adabi a Arewacin Nijeriya, wanda jami’ar Bayero, Kano tare da haɗin
guiwar jami’ar jihar Kwara, Malete suka shirya.
Malumfashi,
I. A. (2016) “Rarara da Yankan Kunkurun Bala” maƙalar da aka samu a shafinsa na
facebook mai suna ‘Malumfashi Ibrahim’.
Malumfashi,
I. A. da Kuna, M. J. (2014) “The Politics of Abuse and poetic of Violence in Northern Nigeria, 1946-1966”. A cikin Garkuwar
Adabin Hausa: A Festchrift in Tribute to Abdulƙadir Dangambo. Shafi na 181-198.
Malumfashi,
A. I. (2009) “Yankan Kunkurun Bala: Nazarin Tashin-Tashina da Samuwar Ayyukan
Adabi a Arewacin Nijeriya”. Muƙalar da aka Gabatar a taron ƙara wa juna sani, a
Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Umaru Musa Yar’aduwa, Katsina.
Usman,
B. B. (2015) Darasin Aji, Hausa Political Verse. Ajin masu neman digiri na biyu. Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo,
Sokoto.
Yakubu,
A.M. (1999) Sa’adu Zungur: An Anthology of the Social and Political Writings of
a Nigerian Nationalist. Nigerian Defence Academy Press, Kaduna.
Zungur,
S. (1968) Waƙoƙin Sa’adu Zungur. N.N.P.C Zaria.
5 Comments
[…] karanta wani […]
ReplyDelete[…] AlƘalami Ya Fi Takobi: Nazarin Kaifin AlƘalamin Malam Sa’adu Zungur a Fagen Dagar Siyasar Nijeri… […]
ReplyDelete[…] AlƘalami Ya Fi Takobi: Nazarin Kaifin AlƘalamin Malam Sa’adu Zungur a Fagen Dagar Siyasar Nijeri… […]
ReplyDelete[…] Wannan zai burge ku […]
ReplyDelete[…] Duba wata makala […]
ReplyDeleteENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.