Na


Dano Balarabe Bunza
Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya
Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.
Email: danobunza@yahoo.com
Phone: 070351419801.0 Gabatarwa


Hausawa sun ce ’’Abin aro ba ya Ƙawa’’. Idan aka yi la’akari da wannan, karin magana ne na habaici da ke faruwa tsakanin yara maza da mata. Akan yi wannan ne ko dai a Ƃangaren wasa ko kuma neman rigima. Sai dai kash! Ba wannan aro aka hanga cikin wannan takarda ba domin, na nuna fasahar da Allah ya yi wa wasu bayinsa ne. Hasali ma, kowane harshe na bugun gaba da irinsa. Haka kuma ba domin aron da harsuna ke yi tsakaninsu ba, da yanzu wani harshe ya mace baki ďaya. Za a ga gudummuwar da marubuta waƘoƘi suka bayar ga harshen Hausa da wadda suke kan bayarwa domin ciyar da adabi gaba. Ba mai musanta aron murya da marubuta waƘoƘin Hausa ke yi tsakaninsu. Za a tabbatar da haka idan aka yi la’akari da muryoyi da ake ji iri ďaya na marubuta daban-daban a lokacin rera rubutattun waƘoƘin Hausa, duk da yake akwai wannan a cikin waƘoƘin baka na Hausa. Wannan aron murya ba abin musu ba ne domin abu ne da yake a fili, kamar yadda Hausawa ke faďa, “Filin wuri dabon ďan kama”. Don haka wannan takarda za ta nazarci aron murya tsakanin wasu marubuta waƘoƘin Hausa. A iya bincikena, wannan takarda ce zakaran gwajin dafi domin ba a sami ganin wani binciken da aka yi kininsa ba. Za a dubi abubuwa cikin wannan takarda kamar haka:

2.0 Ma’anar Kalmar Aro


Kalmar na cikin kalmomi masu harshen damo idan aka yi la’akari da ma’anarta. Abin nufi shi ne, kalmar na ba da ma’ana fiye da ďaya aƘalla. An ba da ma’anarta cikin wani littafin ma’anar kalmomi da aka ce “KarƂar abu don a yi amfani da shi a mayar wa mai shi”. Wannan ne aro na al’ada da aka sani sai dai, aron murya da ake magana a kai ya bambanta da wannan ma’ana. Aron muryan da ake magana a nan shi ne abin da ya shafi rubutattun waƘoƘin Hausa. Kamar yadda aka san cewa marubuci na ganin waƘar da yake da ra’ayin yi wa Ƙarin layi ďaya ko biyu ko uku ko kuma huďu na yi ba da sanin marubucin farko ba, haka aron murya yake, ba sai an nemi izni ake yin sa ba, a wasu lokuta kuwa ana yi tare da masaniyar marubucin farko kamar yadda za a gani nan gaba. Yin la’akari da wannan zai tabbatar muna da cewa kalmar aro na da ma’ana fiye da ďaya. Don haka aron murya baiwa ce da Allah Ya yi wa wasu mutane daga cikin marubuta waƘoƘin Hausa. Haka kuma basira ce da aka ba wani aka hana wani domin kowa da abin da aka hore masa. An hore wa wasu baiwar aron magana da tafiya da sauransu. Ana kiran aron murya da aron kari a nazarin waƘoƘin Hausa (Na baka da rubutattu). Idan aka ce aron murya ko aron kari, duk abu ďaya ne a fannin nazarin waƘa. Wani dalilin da ya sa aka ce ba a aron murya da sanin mai ita shi ne, ba mallakarsa ba ce. An dai wayi gari ne kawai ya tsinci kansa da ita. Ai shi ya sa ake samun muryar mutum na canzawa a lokacin da yake da mura. Wannan canjin murya na faruwa ba tare da son mai muryar ba, domin al’amari ne na rashin lafiya. Ban sami wanda ya kai Ƙarar wani a kotu ba saboda an ari muryarsa domin rashin zuwa neman izni a wurinsa. Haka kuma ko ba maganar aro ba ana samun muryar wasu mutum biyu ta kasance iri ďaya ba tare da suna da alaƘar komi ba saboda mashi’a ta Allah, kamar yadda aka tabbatar da akwai kama ta halitta.

3.0 Kari


Idan aka ce kari, ana nufin wani rauji ko kiďan waƘa da ke haifar da reruwar ta. Abin nufi a nan shi ne muddin babu kari to kuwa abin da ake son a kira waƘa ba zai reru ba, ba zai kuma zamo waƘa ba.
A wani wuri kuma cewa aka yi ma’anar karin waƘa dai ita ce wanzuwar Ƙafafuwa masu bibbiyar juna cikin tsari a baitin waƘa ko da baitin mai layi nawa ne. Kuma Ƙafa ďaya tana iya maimaita kanta a baiti ko baitocin waƘa domin ta ba da karin waƘa. Haka kuma kari na nufin yadda mawaƘi ya tsara bugun sautin waƘarsa.

4.0 Murya


Murya na nufin yanayin sautin magana ko kuma yanayin amon ganga. A Larabci kari na nufin bahari. A nazarin waƘa da aron murya da aron kari duk abu ďaya ne. Dalili shi ne, murya ke tabbatar da karin waƘa. Shi kuma kari ba ya samuwa sai tare da murya. Idan aka dubi waďannan abubuwa biyu duk suna nufin abu ďaya a nazarin waƘa rubutatta da ta baka. Saboda haka, duk sunan da aka yi amfani da shi a cikin biyun, wato kari ko murya, abu ďaya ake nufi.

5.0 Dalilan Da Ke Sa Aron Kari/Murya


Akwai dalilan da ke sa marubuci ya ari muryar wani marubuci ďan uwansa a fagen rubuta waƘa., duk da yake an riga an faďi cewa akan yi aron ne ba tare da sanin mai muryar da aka ara ba. Haka kuma akan sami wanda aka ari muryarsa cike da farin cikin ganin wani ya ari muryarsa ya shirya waƘarsa da ita. Wani lokaci ma mai muryar farko bay a sanin an ari muryarsa gaba ďaya saboda nisan wuri ko kuma ya bar duniya kafin a ari muryarsa a yi wata waƘa, kamar yadda ta faru ga wasu marubuta na aron muryarsu da aka yi bayan sun bar duniya. Za a haďu da irin wannan bayani a cikn misalan da za a kawo a cikin waƘoƘin da aka ari muryoyin masu su. Daga cikin dalilan da ke sanya aron muryar wani marubuci akwai:

5.1 Ficen Marubuci da WaƘarsa


Idan marubuci ya yi ficen da aka san shi a ko’ina da wuya ba a sami wani ya ari muryarsa ya tsara waƘa ba. Haka abin yake ko a Ƃangaren waƘoƘin baka na Hausa don akan sami wani shahararren makaďin da wani ya ari muryarsa ya yi tasa waƘa. Misali a nan shi ne, Salihu ďan kama ya ari muryar Alhaji (Dr) Mamman Shata Katsina ya yi waƘarsa ta kamanci kuma ba wanda zai yi musun ficen Mamman Shata a fagen waƘar baka. Don haka, akwai marubuta waƘoƘin Hausa da suka yi fice kuma aka ari muryoyinsu aka rubuta waƘoƘi da su. Za a tarar da misalan haka a cikin bayanin aron murya da za a yi nan gaba.

5.2 Daďin Muryar WaƘa


Sau da yawa akan sami marubuta da ke rera waƘoƘinsu bayan sun rubuta su.Ta haka ake gano murya mai daďi da wadda ba ta da shi. Jama’a na buƘatar sauraren waƘar mai muryar da ke da daďi fiye da maras daďi. Akwai marubuta sanannu da suka rera waƘoƘinsu tare da muryoyin da jama’a ke jin daďin sauraro. Daga cikinsu akwai Abubakar Ladan Zariya da Garba Gwandu da wasu kamar yadda za a gani nan gaba.

5.3 SaƘon WaƘa


Idan marubuci ya tsara waƘar da jigonta ya yi tasiri ba shakka suna jin daďinta kuma ba su Ƙosawa da sauraren ta tsawon zamani. Haka abin yake a Ƃangaren rubutattun waƘoƘi da na baka. Da yawa gwannati ke sa marubuci ko makaďi ya waƘe wani lamari domin isar da saƘo ga jama’a. Idan aka ci nasarar abin, za a ji wannan waƘa a kafafen yaďa labarai masu yawa domin tabbatar da saƘon ya kai ga jama’a. Wannan na faruwa ne domin muhimmancin saƘon da waƘar ke ďauke da shi. Ba waďannan kaďai ne dalilan da ke sa a yi aron murya tsakanin marubuta waƘoƘin Hausa ba. Zai yiwu a same su da yawa bayan waďannan da aka kawo. Sai dai an kawo su ne domin a tabbatar da ba a aron murya ba tare da dalila ba. Haka kuma, duk marubucin da ya ari muryar wani marubuci ďan uwansa zai faďi dalili ko dalilan da suka sanya shi yin aron.

6.0 Aron Murya A Cikin Rubutattun WaƘoƘin Hausa Tsakanin Wasu Marubuta


Ba shakka masana da manazarta sun sha ƘoƘarin kai kawo na tattauna wasu batutuwa masu yawa da suka shafi rubutattun waƘoƘin Hausa sai dai, ina ganin cewa wannan batu sabo ne domin ban sami ganin wanda ya gabace shi ba a lokacin da ake gudanar da wannan bincike. Idan kuma an sami gabatar da wani irinsa a gabaninsa, hannuna bai sami kai gare shi ba kuma, kunne bai taƂa jin labari ba. Haka kuma ba shakka marubuta waƘoƘin Hausa na aron murya a tsakaninsu domin su samar da nasu waƘoƘi. Abin da wannan takarda ta saka a gaba shi ne fitowa da misalai gwargwado na marubutan da suka yi aro da waďanda aka yi aron a wurinsu tare kuma da misalan baitocin waƘoƘin da suka yi da kuma waďanda suka ari muryoyinsu suka samar da nasu. Ba manufar wannan takarda ce a kawo waƘoƘi da yawa ba sai dai, a kawo misalan da za su sa a gamsu da wannan maganar cewa tabbas ne akwai aron murya a cikin rubutattun waƘoƘin Hausa da ya gudana tsakanin wasu marubuta waƘoƘin Hausa kamar yadda yake kan gudana. Ga wasu daga cikin marubuta da suka ari murya daga wasu da kuma waďanda aka yi aron daga gare su:

6.1 Muhammad Ahmad Shinkafi da Abubakar Ladan Zariya


Alhaji Abubakar Ladan Zariya sanannen marubuci waƘoƘin Hausa ne da kuma rera su. Haka kuma waƘoƘinsa sun yi fice musamman a Nijeriya ta Arewa. Alhaji Abubakar Ladan Zariya ya wallafa waƘoƘinsa a cikin littafi mai suna ‘WaƘar Haďa Kan Al’ummar Afirka’ tun a shekarar 1975 bayan shirya shi da ya yi a 1973. A taƘaice wannan waƘar Abubakar Ladan Zariya sananna ce a Nijeriya. Saboda ficen wannan waƘa da marubucinta, ya sa Muhammad Ahmad Shinkafi ya ari muryar Abubakar Ladan ta ‘Haďa Kan Afirka’, ya rubuta tasa mai suna “WaƘar Haďa Kan Musulmi” a shekarar 2014 kuma ya rera. Za a kawo misalin waƘar wanda aka ari muryarsa daga bisani a zo da misalin na wanda ya yi aro. Ga wani baiti daga waƘar Abubakar Ladan Zariya a cikin “WaƘar Haďa Kan Al’ummar Afirka”:
Allah ya Allah ya Allah,
Haďa kanmu Afirka mu so juna

Turawa sun ga Afirkanmu,
A mafara har suka neme mu,
A yaƘini yau suka same mu,
Domin himma da yawan ilmu,
Suka sadu da sababbin Ƙaumu.

Shi kuma Muhammad Ahmad Shinkafi na Ma’aikatar Lamurran Addini ta Jihar Zamfara ga abin da ya ce a cikin nasa baitoci kamar haka, duk da yake shi da bakinsa ya furta cewa ya ari karin waƘar Abubakar Ladan Zariya ne ya samar da tasa waƘar. Ga baitocin kamar haka:

Allah ya Allah ya Allah,
Haďa kai na musulmin duniya.

Zan fara faďar sunan Allah,
Na daďa da biďar buďin Allah.

Da nufar Alwahidu zan fara,
Ya Allah ka daďe ni basira,
Da fasaha domin in tsara,
WaƘar haďa kai ciki in yi kira,
Ga musulmin faďin duniya.
Wani abin ban sha’awa kan marubutan biyu shi ne, dukkansu sun rubuta kuma sun rera a kafafen yaďa labarai har ma idan aka saurare su da wuyar gaske a iya rabewa a tsakaninsu musammam idan ana farkon sauraren su.
6.2 Bawa Sha’iri da Yusuf Kantu Isa
An gudanar da gasar “Wa Ya Fi Iya WaƘa” tun lokaci mai tsawo da ya gabata tsakanin waďannan sha’irai. An gudanar da gasar a Kano, shekarar 1958. Sanadiyar wannan kuwa shi ne zuwan da Bawa Sha’iri ya yi a Kano. Bawa makaho ne. Da saukarsa sai ya haďu da wani mutum kuma ya tambaye shi ko nan ne garin Kano? Mutumin ya amsa wa Bawa da ‘I’. Bawa bai tsaya a nan ba sai ya Ƙara yi wa mutumin tambaya da cewa, “Shi ne ake cewa ko da me mutum ya zo an fi shi”? Mutumin ya mayar wa Bawa da amsar cewa “Haka ne”. Da jin haka sai Bawa ya kayar da baki ya ce “To ni da waƘa na zo kuma, ni na fi”. Da mutane suka ji wannan magana ta Bawa sai aka shirya gwagwarmayar mawaƘa a gidan Silima na ‘Plaza’ domin a gani tsakaninsa da sauran mawaƘan Kano wa ya fi iya waƘa.
Da aka fara karawa tsakanin Bawa da mawaƘan Kano sai aka sami Bawa ya cinye su baki ďaya. Wanda kawai ya rage shi ne Yusuf Kantu Isa. Da shigowar Yusuf fili sai ya saka wa Bawa wasu Ƙa’idojin gasar da za su yi a tsakaninsu. Daga cikin Ƙa’idojin da Yusuf ya gitta wa Bawa akwai:
1. Kowace kalmar Ƙarshen baiti ta Ƙare da ‘ye’ a matsayin amsa-amon waje (Babban amsa-amo).
2. Gasar ta nan take ce, ba sai an je an shiryo ba.
3. WaƘar ta kasance tare da tsarin rubutacciyar waƘa
4. Kuma Yusuf Kantu ne zai buďa wannan gasa da tambaya.
5. Bawa ne zai karƂa kowace tambaya da irin muryar da aka tamabaye shi.
Ga yadda gasar ta kasance tsakanin Yusuf Kantu da Bawa sha’iri kamar haka:
Yusuf: Kai Bawa Assha’ir inai maka tambaya,
Don na gane ka aboki kanka a waye.

Bawa na jin haka tare da yin l’akari da Ƙa’idojin gasar da aka gindaya masa, sai ya buďa baki ya amsa wa na Isa (Yusuf Kantu) da cewa:
Bawa: To ga ni na tsayu tambayan ni abin da duk,
Kaka yin nufi don ga ni yanzu a shirye.

Da jin Bawa ya ba da amsa daidai, sai Yusuf Kantu ya jefa wa Bawa wata tambaya kamar haka:
Yusuf Kantu: Ko ka faďa mini dagga nan barnin Kano,
Shin mil nawa ne zuwa Ƙaraye?

Bawa: Mil ďin zuwa Ƙaraye ni ban san su ba,
Bisa wagga amsa sai na ce na janye.

Haka gasar ta ci gaba da gudana Yusuf na tambaya Bawa na ba da amsa har sai da aka kai ga tambayar Ƙarshe a inda Yusuf ya yi wa Bawa sha’iri wata tambayar da ya kasa cewa uffan sai da ya ďauki kimanin minti biyu na agogo, wanda ya sa ‘yan kallo suka ďauki shewa da ihu cewa Yusuf ya yi kaye. Abin da wannan takarda ke nema shi ne wurin da wasu mawaƘa biyu suka yi amfani da murya iri ďaya a lokacin da wani ya ari muryar wani. A nan kuwa za mu fahimci cewa, Bawa Sha’iri ne ya ari muryar Yusuf Kantu, kuma waƘar a kan murya iri ďaya ta tafi.

6.3 Aliyu Muhammad Bunza da Kyaftin Umaru Ɗa Suru


Aliyu Muhammad Bunza sanannen marubuci waƘa ne kuma, fitacce a zamaninsa. Ya rubuta waƘoƘi masu yawa na ilimi da wasu da ba su ba. Daga cikin waƘoƘin da ya rubuta akwai waďanda ya ari muryar wani marubuci. Wasu kuma ba na aro ba ne, muryarsa ce asalan. Daga cikin waƘoƘin da ya ari muryarsu akwai waƘoƘin Captain Umaru Ɗa Suru da ba su kasa uku ba. A nan dai za a kawo misalin waƘar da Aliyu Muhammad Bunza ya rubuta mai suna ‘Ta’aziyyar Captain Umaru Ɗa Suru. Kaftin Suru sanannen marubuci waƘoƘin Hausa ne tun wajen shekarar 1960s kuma, ya rasu a shekarar 2012, bayan ‘yan kwanuka sai Aliyu ya rubuta waƘar ta’aziyyarsa. Ya ari muryar wata waƘar da Kyaftin ya yi mai suna ‘Sata Kyauta’. Ga misalin baitocin waƘar “Sata Kyauta” ta Kyaftin Umaru Ɗa Suru kamar haka:
1. Salama alaikum ‘yan uwana,
Mutanen Suru ku dakata.

2. Akwai ni da sharhi ‘yan uwana,
Ku zo ku ji mi zan ambata.

3.Bayani zan yi da gargaďi,
Don ku lura ku gane mazambata.

4. Batun ga da zan yi ‘yan uwana,
Mutanen Suru ku gaskata.

5. Akwai wasu na ga suna ta ruďin ku,
Sun maishe ku mahaukata.

Aliyu Muhammad Bunza ya ari muryar waƘar Kyaftin Suru da aka kawo a sama, ya rubuta waƘar ta’aziyyar shi Kyafyin ďin bayan Allah Ya yi masa rasuwa. WaƘar da Aliyu Bunza ya rubuta na ďauke da layi biyar ne a matsayin baiti. Ga misalin baiti biyu na waƘar ta’aziyyar Umaru Ɗa Suru da Aliyu Muhammad ya ari muryar ya rubuta:
1. Mu ce Ƙalu lillahi wa inna ilaihi ruji’i dole na,
Dukkan mai rai Ƙarshensa kwancin kushewa ce haka ko’ina,
Idan aka sonce rai jiki daďa ya zama gawa sai gina,
A wanke jiki a suturce gawa a kai ramensa a jingina,
A bar mu muna ‘yan koke-koken rashi daga nan kuma sai ina?

2. Mu ruďu cikin kewar da ba ta gushewa rai baƘonmu na,
Ziyara anka izo mu nan duniya mu gama ta mu dangana,
Da tsufa ko yarantaka lokacin kowa an ayyana,
Da ya cika al’amarin zaman duniya ya Ƙare ko’ina,
Ina a gida ArƘilla waya ta ishe mini saƘon girshi na.

3. Haruna na Maikwari ke gaya min abin nan sai da na jingina,
Ya ce saƘo yaz zo garai da’ Abuja rashin babanmu na,
Fasihi baban Hafsa dogo na Kulwa abin Ƙaunammu na,
Imamin Kulwa wajen siyasa na ji Fulani sun ce “Gonga na”,
Gwanin fara’a wasa da yin dariya an san haka ko’ina.
Allah Sarki! Da mai karanta wannan bayani na tare da kaset na waďannan waƘoƘin yana saurare da ya tabbatar da aron murya a cikin rubutattun waƘoƘin Hausa gaskiya ne. Ko ba haka ba idan aka rera waƘoƘin nan biyu a rubuce ma za a ji sautinsu iri ďaya ne. Ganin haka ya sa aka yi tunanin rubuta wannan takarda da kuma ganin kasncewar binciken sabo.
6.3.1 Aliyu Muhammad Bunza Da Kyaftin Umaru Ɗa Suru
Ba aron da aka yi bayani a sama kaďai Aliyu ya ari muryar kyaftin a cikin waƘoƘinsa ba. Akwai muryar waƘar Pakistani da Aliyu ya ara ta Kyaftin ya rubuta ta’aziyyar Malam Awwal Ibrahim Albani. Ko shakka babu duk wanda ya san muryar waƘar Pakistani ta Umaru Ɗa Suru zai tabbatar da aron murya ya kai aro. Lokacin da na fara jin wannan waƘar ta’aziyyar Albani kai tsaye na ce muryar waƘar Pakistani ce aka yi amfani da ita aka rera ta. Bayan na binciki wanda ya rera ta da wanda ya rubuta ta, sai suka tabbatar min da cewa, muryar waƘar Pakistani ce aka yi amfani da ita aka rera wannan waƘa. Ma’ana, ba Aliyu Muhammad ya rera waƘar da kansa ba. Sunan ya rera waƘar, Malami JaƂƂI Bunza. Saboda haka Hausawa ma cewa suka yi “WaƘa a bakin mai ita ta fi daďi”
Kyaftin Suru ne ya rubuta waƘar Pakistan da farko, shi kuma Aliyu Muhammad Bunza ya ari muryar waƘar ya rubuta ta ta’aziyyar Albani Zariya. Ga baitoci kaďan daga cikin waƘar Pakistan da Umaru Ɗa Suru ya rubuta:
1. Ya Assalamu Mujibun Muminun ga ni,
Ya Alimul gaibi Arrahamani dubo ni,
Hukumullazi Alwakilun ga ni ban izni,
Ka yi min basirar da zan waƘar Pakistani.

2. Ka yi min basira Tabaraka Jalla kama min,
Bisa nau nufi ‘yar fasahata ka Ƙara min,
Wani kuskure nau Ilahil Arshi gyara min,
Ka yi min ijaba, karama taka miƘo min,
Bisa gaskiya zan yi labarin Pakistani.

Aliyu Muhammad Bunza ya ari muryar wannan waƘa ya rubuta ta’aziyyar marigayi Ibrahim Awwal Albani Zariya a shekarar 2014. Ga wasu baitoci daga cikin waƘar ta’aziyyar Albani da Aliyu ya rubuta mai ďauke da muryar waƘar Pakistani:
1. Shukura ga Allah guda masanin halin bayi,
Mai Ƙaddarowa ta tabbata babu mai tsawa,
Ya mai hukuncin da ba makara da gaggawa,
Masani da ilminSa yaw wuce hankalin kowa,
Subhana lillahi tsalki na ga Rabbani.

2. Na yo salati ga manzo shugaban bayi,
Ahalinsa dukkan sahabbai ƘoƘari sun yi,
Na riƘo ga sunna ta sadu da mu ruwan sanyi,
MariƘa amana shahada kun riƘa kun yi,
Matsayin shahidi ga nafsi babu saƂani.

3. Mai rai a ce ya mace ba al’ajab ne ba,
Mutuwar shahada buki ne ba na wasa ba,
Ita ce ma’aunin aƘida ba ta yi Ƙura ba,
Ita fassara ce mutum bai tafka shirme ba,
Shedarmu ke nan ga Awwalu namu Albani.
6.4 Aliyu Muhammad Bunza Da Garba Gwandu
Garba Gwandu sanannen marubuci waƘa ne kuma waƘoƘinsa sun yi fice sosai musamman a Ƃangaren ilimi. Ya rubuta “WaƘar Makaranta” har da rera ta a kafofin yaďa labarai. Shi kuma Aliyu Muhammad ya ari muryar wannan waƘar Garba Gwandu ya rubuta waƘar ta’aziyyar Muhammadu Hambali Jinju a wani bukin karrama Marigayin da aka yi a jamhuriyar Nijar a garin Niamey. Duk wanda ya san waƘoƘin Garba Gwandu kuma ya ji muryar da Aliyu ya yi amfani da ita, zai tabbatar da muryar Garba Gwandu ce da ya yi ta “WaƘar Makaranta”. Ni kuma na yi magana da shi baki da baki ya tabbatar min da cewa muryar marigayi Garba Gwandu ce ya ara ya yi wannan waƘa. Ko bai faďa ba , duk wanda ya san muryar Garba Gwandu, ba sai an faďa masa ce ita ba. Ga wasu baitoci biyu na waƘar makaranta da Garba Gwandu ya rubuta kuma ya rera:
1. Bismil Ilahi na kirai sarkina,
Wannan da ya zan shi ka jin kukana,
Na yo salati ga Musďafa manzona
Allah Shi sa mu gane shi don makaranta.

2. Can dauri in na je gidan kakata,
Cewa takai ita kan tana Ƙyama ta,
Wai kafiri nike babu mai Ƙauna ta,
Girman kwabo nai tunda ban makaranta.

Aliyu kuma, da ya ari wannan murya ya rubuta waƘar ta’aziyyar Muhammadu Hambali Jinju, ga wasu baitoci da abin da ya ce a cikinsu:
1.Shege ba zai ga wuri na yin ďanga ba,
Domin ganin asalinsa ba na Ƙwarai ba.

2.Yaro ga manya zai laƂe ya yi kuri,
Yau Hausa ta rasa ginshiƘi mai kauri,
Ta ďauro himma an rage mata sauri,
Ta yada zango ba da shiryawa ba

7. Kammalawa


Aron kari ko murya ba baƘon abu ba ne ga masana da manazarta sai dai, ba a cika gudanar da bincike a kansa ba. Ganin haka ya sanya aka hangi muhimmancin da ke tattare a cikinsa har aka tsakuro wani abu a kansa. Haka kuma an yi binciken ko an yi aiki irinsa, da aka gudanar da dogon bincike sai aka gano a iya binciken da aka yi, babu ko ďaya da aka yi na aron murya ko kari tsakanin marubuta waƘoƘin Hausa. Ita ma dai wannan takarda ta tsaya ne kusa domin yin tuni ga magabata da su zurfafa bincike a kan wannan lamarin aron murya ko kari a tsakanin marubuta waƘoƘin Hausa, duk da yake an taƂa gabatar da irinsa a waƘoƘin bakan Hausa shi ma, a cikin harshen Turanci. Duk da haka wannan aron murya ba abu ne da ya yawaita a tsakanin marubuta waƘoƘin Hausa ba. Ganin haka ne ya ba da Ƙwarin guiwan kalato wani abu a kansa, da fatar abin da aka nazarto zai amfani sauran ďalibai irina.

Ka/kin taba karanta wannan?

https://www.amsoshi.com/2017/07/18/isa-rasco-dangoma-ayyukansa-duniyar-adabin-hausa/

Manazarta


Ainu H.A (2007), Rubutattun WaƘoƘin Addu’a Na Hausa: Nazarin Jigoginsu da Salonsu. Kundin Digirin Ph.D. Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.
Birnin Tudu S.Y. (2001), ‘Jigo Da Salon Rubutattun WaƘoƘin Furu’a Na Ƙarni Na Ashirin. Kundin Ph.D Sashen Koyar da Harsunnan Nijeriya Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.
Bunza A. M. (1994), ‘YaƘi Da Rashin Tarbiya, Lalaci, Cin Hanci Da KarƂar Rashawa Cikin WaƘoƘin Alhaji Muhammadu Sambo Wali Basakkwace’ Ibrash Lagos.
Ɗangambo A. (1980) “Hausa Wa’azi Verse from Ca 1800-1970: A Critical Study of Form Language And Style” PhD Thesis S.O.A.S University of London.
Ɗangambo, A. (2007) Daurayar Gaďon Faďe WaƘa (Sabon tsari) Amana Publishers ltd, Zaria, Kaduna.
JaƂƂo B.M (1999), ‘Audu Makaho Da WaƘoƘinsa, Kundin B.A. Sashen Koyar da Harsunnan Nijeriya Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo Sakkwato.
Jami’ar Bayero Kano (2007), ‘Kamusun Hausa’, Cibiyar Nazarin Harsunnan Nijeriya, B.U.K..
Kaset: WaƘoƘin Audu MaƘaho.
Kaset: WaƘoƘin Kaftin Umaru Ɗa Suru
WaƘoƘin Aliyu Muhammad Bunza
WaƘar Garba Gwandu Ta Makaranta (Ilimi)
WaƘar Haďa Kan Musulmi Ta Muhammad Ahmad Shinkafi 2014.
Zariya A. L. (1975), WaƘar Haďa Kan Al’ummar Afirka
WaƘar Gasa Ta “Wa Ya Fi Iya WaƘa?”, Tsakanin Bawa Sha’iri da Yusuf Kantu Isa 1906.
Muhammadu, D. (1977), “Individual Talent in The Hausa Poetic Tradition: A study of AƘilu Aliyu and His Art”. Ph.D Thesis, S.O.A.S, University of London.
NNPC (1976), Fasaha AƘiliya, Zaria.
Usman, B.B. (2008), “Hikimar Magabata: Nazari A Kan Rayuwar Malam (Dr) Umaru Nassarawa Wazirin Gwandu (1916-2000), Da WaƘoƘinsa”, Kundin Digirin Ph.D Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.
Yahya, A.B. (1982), Jigon Nazarin WaƘa, Fisbas Media Service, Kaduna.
Yahya, A.B. (2001) “Salo Asirin WaƘa”. Fisbas Media Service, Kaduna.
Yahya, A.B. (1989) “The Verse Category of Madahu with Special Reference to Theme, Style and Background of Islamic Source and Belief”. Kundin Ph.D Usmanu Ɗanfodiyo University, Sokoto.