Ticker

6/recent/ticker-posts

Nazarin littattafan zube: Alwashi Da Macijiya Da Duniya Ina Za Ki Da Mu

Abbas Musa
2017

Gabatarwa


A nan zan fara da gabatar da Littafi na farko mai suna Alwashi , Littafi ne da Kabiru Yusuf Anka ya Rubuta. Babu shekarar Bugu ,Amma mawallafin ya ce :Dalilin rubuta littafin shi ne wani Abu ƙuduri da ke zaune a cikin zuciyarsa .
Jigon Littafin shi ne Faɗakar da mutane a kan yawan Faɗuwar gaba da tsoro wanda sune ke sa a ii tsoron abinda bai kamata a ji tsoronsa ba ;A taɗaice dai littafin yana da jigon JARUMTA


Salon Sarrafa Harshe


A Littafin an samu salailai da dama kamar haka :
A shafi na ɗaya an samu salon kwalliya "Mutanen garin na matuƙar jin Daɗin zaman garin fiye da zaton zatura sarkin zato". Da kuma inda marubucin ke cewa "Babu Hanyar mota a garin balle ita kuma kanta uwar gidan (Mota).
Sannan akwai salon bada labari "Koda yake labarin Antaru ɗan Shaddad labari ne mai matuƙar daɗi da jan hankali musamman ga wanda ya san labarin ".
Akwai salon Karin magana mai labari "Yaron ya dage yana ba su labarin ƙanzon kurege".
A shafi na bakwai an samu salon Kambamar zulaƙe"Gudun da Ilu ya ke yi cikin tashin hankali da kaɗuwa ,ba Aljani ba ina tsammanin ko guguwa sai dai ta rufa masa asiri ,sai dai kuma mutuwa wadda ita dama ba a guje mata ".
A shafi na Takwas an samu salon kamance na Daidaito "Ilu ya yi kamar zai yi kuka ".
A shafi na sha ɗaya an samu salon Zayyana "Tsugunnawarsa ita ta bayar da damar fisgar ƙafaarsa ,sai ƙarashe fitsarin ya yi a inda aka fisgeshi haɗe da fitar da makararren Ihu! Wanda take ya firgita mutanen gari ya kuma tarwatsa su ,kowa ya yi Nasa wuri".
Sannan an samu salon Kambamar zulaƙe "Na kan Jakai suka dire suka baiwa wanduna iska masu ɗan rashin tsoro Irinsu Liman sune suka bar wurin cikin sauri,amma Addu'ar da suka yi ta cika Mangala ɗari biyu domin liman sai da ya karance Litattafan Addini Irinsu Iziyya ƙawa'idi Risala Ahallari har sau shida kafin ya ƙarasa gida ".
A shafi na sha biyu an samu Salon Gamin bauta "Abokansa guda biyu Manu da Taƙiri Suma dai sun yi ta macen ƙoƙarin zama kamar yadda suka saba don yin hira".
A shafi na sha uku an samu Salon kamancen Daidaito "Furta kalaman Aljannu da Salele ya yi ya zo dai-dai da Bugawar Zuciyoyin Su Manu da Taƙiri Kamar yadda ake buga guduma a kan bishiya ".
An samu salon karin Magana "Ganin abin da ya turewa buzu naɗi ". Da kuma "Aka yi ta tsuga Ruwa kamar da bakin ƙwarya ".
A shafi na sha tara an samu salon kamancen Daidaito 'Take ya ji kansa ya yi Dum ! Kamar an zuba masa ruwa ƙoƙo guda a cikin kunnuwa "Jikinsa ya yi Yar !kamar an watsa masa wuta".

A shafi na Ashirin da biyar An samu salon Zayyana kamar haka "Take ya miƙe daga Ƃoyen da yake yi ya doshi arnan dajin nan kafin su ankara ya kaftawa ɗaya daga cikinsu Adda a gadon baya ya kuma laftawa ɗaya a fuska suka zube ɗaka cikin Ihu! Irin na su Ragowar suka yo kansa da Lafta-Laftan ƙasusuwa wasu riƙe da mashi ,Kamar yadda daman bai yi zato ba haka kuma basu Ƃace ɗin ba ,ko kuma su rikiɗe Kamanninsu na tsoro na Aljannu ba".

A shafi na Ashirin da bakawai an samu Salon gamin bauta "TaƂɗijam! Nesa ta zo kusa ,Kunkuru ya hau Giginya ".

A shafi na Talatin da ɗaya an samu Salon Kambamar Zulaƙe "Haƙiƙa taurin kanka yana kai ka inda ya kamata ,Ya dace ace ya zuwa yanzu ka mutu ,Amma saboda Mutuwar na Tausayinka shi ya sa ta ƙyaleka ,amma ka ci gaba da halin naka Yau ba za ka kai Labari,ko da kuwa Mutuwar ba ta ɗauke ka ba yau sai ka Mutu".

An samun salon bada labari a shafi na Talatin da ɗaya "In baka sani ba ,bari in sanar da kai Asalin garin nan ya sami Sunansa ne daga Kakan-Kakanka wanda ake ganin shi ne Barde a duk fadin garin , to Ni na kawar da shi daga Doron ƙasa ,kuma na yi ƙokarin na Shuɗar da duk Danginsa ,Ashe Tsinanniyar Kakarku tana doron ƙasa ban farga ba sai tsawon wani lokaci".
Halayyar waɗanda suka fito a Littafin
A littafin an bayyana Halayen mutane irinsu Sarki da Liman da Sauran Jama'ar gari da kuma Abokan Salele Wato Taƙiri da Abu a matsayin Matsorata ;Yayin da a gefe guda kuma aka bayyan Salele a matsayin Jarumin da ya yi amfani da Jarumtarsa ya ceto Rayukan Jama'ar garinsu na Tsaunin Barde daga Barazanar arnan Daji da ake tsammanin Aljannu ne saboda tsabar tsoro
Kuma Labarin ya faru da gaske kamar yadda Marubucin ya Faɗa.

Littafi na biyu da zan yi sharhi shi ne "Duniya ina za ki da mu ".
Wannan Littafi da Rilwanu Umar Birnin kebbi ya rubuta ,Littafi ne da aka Rubuta domin ya faɗakar da jama'a a kan abinda yake faruwa a yau da gobe na Halayen mutane ta yadda suke saurin Amuncewa da mutanen da Ba su waye da Halayensu ba, a taƙaice littafin yana da JIGON faɗakarwa ne a kan Saurin Amincewa da jama'a.
Halayen jama'ar da suka fito sune kamar haka :
1.Fadila :Ita ce Tauraruwar labarin mai ɗabi'ar saurin amincewa da jama'a .
2.Alhaji Sadiƙ:Wanda ya kasance mutun mai alamar Mutanen kirki a zahiri amma a baɗini shi ne jagoran ƙungiyar asiri masu watanda da Sassan jikin Mutane.
3.Abba :shi ne mahaifin Fadila Mutun ne mai Haƙuri
4.Likita Bashir: Likita ne mai Sauraren Koken Marasa lafiya kuma ya taimake su bakin gwargwadonsa .

Zubi da tsarin Littafin


Littafin zube ne mai labari irin na zamanin Amfani da ababen more Rayuwa.

Salon sarrafa Harshe
A Littafin an samu salailai da dama kamar haka :
Salon Aron harshe "Ta fito cikin wani banki mai suna (Oceanic Bank)".
Hakama a shafi na shida "Tana tsaye tana jiran (Taɗi)" .

A shafi na bakwai an samu salon karin magana "Da ɗyar da shuɗin goshi".
Sai kuma salon zayyana a shafi na takwas "Sa'annan kuma akwai wasu manyan samari zagaye da gidan ".
Da kuma "Ban ankara ba na ga sai ganin kanun mutane nake ga jini Male-Male a cikin ɗakin , can gefe kuma wasu mutane ne da ke kwance rai a hannun Allah kafin a yanka su".
A shafi na tara an samu salon kamancen Daidaito "Ina mai Matsanancin kuka kamar Raina zai fita".
Sai kuma salon Tarihi a shafi na goma sha huɗu "Mahaifiyar Alhaji Kabiru (Abba) Hajiya Bilkisu ɗiya uku ke gare ta ,Kabiru shi ne ɗanta na fari sai Aisha sai kuma shafa'atu".

A shafi na Ashirin da biyar an samu salon labari "Likita Bashir Lafiya ta ƙalau ba abinda ke Damuna dalilin da ya sa na ce ba na da lafiya shi ne na kwashe Labarin abinda ke faruwa tun daga farko har zuwa yanzu na gaya masa".

A shafi na talatin da tara an samu salon kamancen Daidaito "Sarkin na tsaye sai ga Abba da Alhaji Altine kowannensu rigarsa ta yage kamar waɗanda suka fito wurin farauta".

Sai kuma Littafi na uku da zan yi sharhi mai suna Micijiya wanda Albeent G.Umar ta Rubuta .
Littafin yana bada labarin wani saurayi ne mai suna Safwan da Abokansa waɗanda suka haɗu da da fushin wata Macijiya da suka kashewa Miji Ita kuma ta sha ɗauki Alwashin ganin bayansu ɗaya-bayan-ɗaya kuma ta yi Nasarar haka domin duk ta kashe Abokan Safwan ɗaya-bayan-ɗaya ,Sai na ƙarshe a yayin da take ɗauki-ba-daɗi da Safwan domin ganin bayansa ta gamu da Ajalinta.

JIGO


Jigon Littafin shi ne faɗakarwa a kan yadda ake Amfani da Mata Kyawawa domin Samun Nasara a kan Samari Masu jini a jika

SALAILAI


A Ƃangaren salailai kuma an same su daban-daban kamar haka :
Salon Tatsuniya "Wasu sun ce wai bayan shekaru ɗari Majici ya kan rikiɗe zuwa kowace irin Sura".
Akwai salon hasashe a shafi na biyar "Kafin Maciji ya Mutu yana ganin wanda ya kashe shi ta cikin ɗwayar idonsa ".
An samu salon LulluƂi a shafi na bakwai "Macijiyar ta bayyana a siffarta ta kyakkywar Mace kamar yadda ta saba rikiɗa".

A shafi na sha biyar an samu salon Mutuntarwa "Ta hanyar kashe wannan hatsabibin Maciji ,yana nufin kamar kun gayyatowa kanku mutuwa ne".

A shafi na Ashirin an samu Salon karin Magana "Safwan ya ce Sa'arka ɗaya kana sanye da wannan layar,abinda ya hanata kenan ta afka maka kai tsaye ka tsallake rijiya da baya".

Sannan an samu salon kamance na daidaito a shafi na Ashirin da bakwai "Yana cikin gudu kamar na Fanfalaƙe".

A shafi na talatin da uku an samu salon habaici "Ai ka san akwai waɗanda ake haifarsu wawaye da kuma waɗanda ake wawantar da su ,ta ƙaraso tana cewa "Shi wannan yaron Malamin yana daga cikin wawaye ajin farko kai kuma kana cikin na biyu".

Sannan akwai Salon siffantawa a shafi na talatin da shida "Sihirtacciyar Layar da Malamin nan ya ba su".
Akwai kuma salon Dibilwa a shafi na talatin da bakwai "Cewa suka yi Kyakkyawar Mace kamarki ace wai tana yi mini fatan tsawon rai kamar tana yi mini Fatan mutuwa ne ".
A shafi na arba'in da uku an samu salon Alamci "Kuma bana son ki shiga sahun matan da mazajensu suka rigamu gidan gaskiya".
da shafi na Arba'in "Haka suka yi ta ɗauki-ba-baɗi da macijiyar.

ZUBI DA TSARI


Duka Litattafan suna da zubi irin na litattafan zube a Littafin Alwashi gaba ɗaya labari ne irin na zamanin Da kuma kamar yadda Marubucin ya faɗa Tarihin wasu Al'umma ce kuma labarin ya faru da gaske .

A Littafin Duniya ina za ki da Mu yana da zubin Labari irin na yau da gobe wanda ke faruwa cikin Al'ummarmu. A taƙaice labarin ƙirƙira ce ta Marubucin domin ya faɗakar da Mutanen lokacinsa.

A Littafin Macijiya kuwa Ya ƙunshi Labarin Da da kuma na Yanzu Kuma kamar yadda na fahimci labarin Tatsuniya ce aka wanka aka mayar Labarin Zube domin faɗakarwa .

KAMMALAWA


A taƙaice kamar yadda Malam ya Nema Da inyi Nazari da Sharhin Litattafan Zube uku a ƙarƙashin Inuwar Kwas mai Taken ALH 406 a sashen Nazarin Harsunan Nijeriya a Jami'ar Usmanu ɗanfodiyo Sokoto.Na yi abin da na ke iyawa dacewa ga Allah take.

MANAZARTA


Atuwo ,A.A(2017) Laccar Aii da aka gabatar a sashen Harsunan Nijeriya ,Jami'ar Usmanu ɗafodiyo sokoto.

Anka, K.Y(Ba shekara) Alwashi.

Birnin Kebbi,R.U(2009) Duniya ina za ki da Mu.

Mrs.Alkhamees,A.G.U(Ba shekara) Micijiya.

www.amsoshi.com

Post a Comment

0 Comments