Ticker

6/recent/ticker-posts

Surkullen ‘Tsari’ a Rayuwar Bahaushe: Nazarin Sukullen Kariya a Yankin Guddiri

Citation: Baba Mohammed Shehu & Dahiru Yalwa Mohammed (2017). Surkullen ‘Tsari’ A Rayuwar Bahaushe: Nazarin Sukullen Kariya A Yankin Guddiri. Yobe Journal of Language, Literature and Culture (YOJOLLAC), Vol. 5. Department of African Languages and Linguistics, Yobe State University, Damaturu, Nigeria. ISSN 2449-0660

SURKULLEN ‘TSARI’ A RAYUWAR BAHAUSHE: NAZARIN SUKULLEN KARIYA A YANKIN GUDDIRI

Na

Baba Mohammed Shehu

Da

Ɗahiru Yalwa Mohammed

TSAKURE

Masana sun kalli Hausa ta fuska biyu wato Hausar Gabas da ta Yamma. Yankin Guddiri yana cikin rukunin Hausar Gabas. Shi kuma surkulle wasu tarin kalmomi ne da akan furta masu wuyar haddacewa, a inda akan yi hargitsa ballen kalmomi da ke da surkin harsuna daban – daban domin neman kariya ko magani ko wata biyan buƙata.Wannan takarda ta yi ƙoƙarin fito da ire-iren surkulle na neman kariya da Hausawan yankin Guddiri suke amfani da su. Takardar ta fito da ire-iren surkulle na neman tsari da suka haɗa da na mutuwa da na takaba da na zaman makoki da sauransu.

1.0. GABATARWA

Masana da manazarta na yi wa al’ada kallo ta fuska uku wato fuskar furuci ko ambato da baka (faɗar baki) ko aiwatarwa da gaɓoɓi da kuma fuskar ƙudurtawa a zuciya (Bunza 2006). Wannan takarda za ta yi ƙoƙarin fito da ire-iren surkulle waɗanda suka shafi mutuwa da takaba da tattalin lahira da zaman makoki da kuma al’amarin da ya shafi sha’anin fatalwa a yankin Guddiri na ƙasar Hausa.

1.1 MA’ANAR SURKULLE

Bunza (2006) ya yi fashin baƙin surkulle inda ya nuna cewa, asalin kalmar ta Hausa ce wadda take da tushe guda biyu ‘sur’ da ‘kulle’. Tushen ‘sur ya yi daidai da tushen surru, wanda a ganin wasu, surkulle kan ɗauki ma’anar surutu. Kuma gaɓoɓin ‘kulle’, wanda suka yi daidai da ƙulli na maganin gargajiya da ake yi don warkar da ciwo.

Haka kuma Adamu (1994) ya bayyana surkulle da cewa: ‘Surkulle wasu jerin maganganu ne a sassarƙe da ake ƙirƙirar su cikin Hausa da Larabci. Akan cukuɗa a furta da nufin bayyyana wasu abubuwan mamaki don cim ma biyan buƙata.

Shehu (2013:22) ya bayyana maganar kalmar surkulle da cewa:

‘Surkulle kitsa wasu kalmomi ne

ko maganganu (da fatar baki) da ake

surka kalmomin Larabci da Hausa

cikin kalami na yanki-faɗi domin

aiwatar da wata biyan buƙata’

Shi kuma Almajir (2009) ya kalli surkulle ta fuskar yanaye-yanayensa tare da nuna muhimmancinsa ga rayuwar Hausawa. Daga ciki, ya bayyana nau’o’in surkulle tare da fito da masu yinsa.

Binciken Shehu(2002: 14) ya bayyana cewa, asalin surkulle ya samu ne a sakamakon cuɗanyar Hausawa da Fulani a ƙasar Hausa. Wato a wannan ra’ayi, ana ganin kamar surkulle ya samo asali ne daga Fulani.

A dangane da bayanan da suka gabata, surkulle shi ne ire-iren lafuza da akan furta da fatar baki waɗanda sau tari ba su da wata ma’ana; akan surka harsuna daban-daban domin neman biyan wata bukata.

An gudanar da wannan bincike ne a wurare daban-daban na yankin Guddiri ta ƙasar Hausa da suka haɗa da : Garin Azare da Madara cikin Ƙaramar Hukumar Katagum. Sannan an ziyarci garuruwan Beli da Ganuwa da ke Ƙaramar Hukumar Shira. Har ila yau, an ziyarci garuruwan Dambam a ƙaramar Hukumar Dambam da Zadawa a ƙaramar hukumar Misau da kuma Ariri a ƙaramar hukumar Zaki dukkansu a cikin Jihar Bauci.

Yayin gudanar da binciken, an yi amfani da hanyar hira ta baki da baki a tsakanin mutane. A tattare da haka, an zanta da adadin mutane da yawansu ya kai goma sha biyar (15) maza goma (10) mata biyar (5) domin samun sahihan bayanai. Duk da cewa maza ne suka fi yawa, amma an fi samun cikakkun bayanai wurin mata. Wannan na nuna cewa, a yankin Guddiri mata sun fi yin surkulle a wannan fuska ta rayuwa.

1.2 MATSAYIN SURKULLE A YAU

Surkulle daɗaɗɗiyar al’ada ce wadda a da al’ummar Hausawa suke rungume da ita. Haka kuma Hausawa a mafi yawan lokaci suna tafiyar da al’amuran rayuwarsu ne ta hanyar amfani da surkulle. Idan aka dubi yadda Bahaushe yake tunkarar abin da ya shafi kariya da neman biyan bukatun rayuwa, sai a tarar da surkulle yake tinƙaho. Wato da surkulle ake warware matsaloli da suka shafi taɓin hankali ko daidaitawa tsakanin aljanu da marar lafiya ko maita ko kuma matsaloli da suka shafi sana’o’i irin su : Bokanci ko Wanzanci ko Tsibbu da sauransu Hausawa na tafiyar da su ne ta hanyar surkulle (Bunza 2006 :261).

Al’adar surkulle a yau abu ne da ke (kan gaba wajen) samun koma - baya a tsakanin al’ummar Hausawa. Wannan kuwa ya faru ne sakamakon haɗuwar Hausawa da baƙin al’ummomi. Saboda kasancewar Hausawa al’umma ce da take da matuƙar son jama’a, ya janyo takan rungumi duk wata al’ummar da ta yi alaƙa da ita tattare da al’adunta, yadda hakan ya janyo ita kuma take ƙoƙarin rasa wasu daga cikin muhimman aladunta. a sanadiyyar irin haka, ya sa a yau mafi yawan matasa a tsakanin al’ummar Hausawa ba su san wannan al’ada ta surkulle ba.

Wani dalili kuma da ya sa surkulle ke ci gaba da samun koma-baya musamman ɓangaren maza shi ne tasirin addini da kuma zuwan ilmin karatu da rubutu na boko. Waɗannan al’amura sun taimaka wajen daƙushewar al’adar surkulle.

1.3 TARIHIN ƘASAR GUDDIRI

Masan sun kawo ra’ayoyi dangane da tarihin ƙasar Guddiri. Hamma, (1981:9-10) a ƙoƙarin bayyana asalin kalmar Guddiri, ya yi nuni da cewa kalmar asalinta daga harshen Fulfulde aka samo ta, wato ‘Leddi ngudduri’ manufa ‘yar ƙaramar ƙasa ko ƙasa da aka yanke. A nan, ke nan daga wannan manufar ne aka samo sunan yankin ‘Guddiri’. Haka kuma Hamma (1981), ya ƙara bayyana da cewa lokacin da malam Ibrahim Zaki ya je karɓar tuta wurin Shehu Usman Ɗanfodiyo, domin a nuna masa iyakar masarautarsa sai Shehu ya ce masa duk da cewa dukkan yankunan nasa ne ( na Shehu) ya yanke masa iyaka, wato sai Shehun ya ce masa,’Ƙasarka ita ce ‘yar Gundur’ ko ‘Yahu Leddi ma ngunduri’ manufa, na ba ka ‘yar ƙaramar masarauta ko yankakkiyar ƙasa. Lokacin da mal Ibrahim Zaki ya ga an nuna iyaka ta masarautarsa sai kuma ya bukaci Shehu ya yi masa addo’a saboda ƙasarsa ta samu yawan al’ummar musukmi. Wannan shi ya haifar da samuwar ƙasar Guddiri.  

Ƙasar Guddiri ɗaya ce daga cikin yankunan ƙasar Hausa wadda take da daɗaɗɗen tarihi. Masana da dama sun bayyana ra’ayoyinsu dangane da kalmar Guddiri. Azare (2017: 26) da ya ambato Bello (1992) ya bayyana cewa ƙasar Guddiri ƙasa ce ta Hausa wadda take arewa maso gabashin Nijeriya da ake samun ta a tsakanin jihohin Bauchi ,Yobe da kuma Jigawa. A bisa ga wannan ra’ayi na Bello (1992), an bayyana cewa ƙasar Guddiri ta yi iyaka da ƙasar Bauchi .

Haka kuma masana sun bayyana cibiyar ƙasar Guddiri ita ce Katagum. Sauran garuruwan wannan ƙasar sun haɗa da: Azare da Misau da Shira da Gamawa da Yayu da Jama’are da Saɗe da Dambam da Lanzai, dukkansu suna arewacin jihar Bauchi ta yanzu suke. Sannan akwai garuruwan Kiyawa da Birnin Kudu da Gwaram , a jihar Jigawa, Azare (2017:7-8).

Ƙasar Guddiri, ƙasa ce mai rairayi, musamman ma ta arewacin yankin. Sannan, tana da koguna waɗanda suka ratsa ta ƙuryar arewamaso gabas ; waɗanda suka haɗu da tafkin Chadi ( Lake Chad). Ibinola,(2009 : 3) .

Bisa ga bayanai da suka gabata, za mu iya bayyana cewa ƙasar Guddiri ƙasa ce mai daɗaɗɗen wadda masana suka gudanar da bincike ta fuskoki daban-daban.

2.0. SURKULLEN TSARI A RAYUWAR SAURAN JAMA’A

Yanzu bari mu duba ire-iren surkulle da ba su dangaci magani ba. Wato waɗanda suka shafi al’umma baki ɗaya, ba lallai sai bokaye ko ‘yan bori ko matsibbata ba. Surkulle ne da kowa na iya yin su.

A ƙarƙashin wannan rukuni, za a yi nazarin surkulle, da suka shafi mutuwa da takaba da tattalin lahira da zaman makoki da kuma na fatalwa da kuma neman tsari daga ire-iren mutanen da ake ganin za su iya cutarwa.

Surkulle ya yi tasiri kan waɗannan al’amura da aka ambata a yankin Guddiri. Waɗannan surkulle suna nan da dama kuma kala- kala a yankin Guddiri sai dai ya danganta daga wuri zuwa wuri.

2.1. SURKULLE NA JIN LABARIN WANI YA MUTU

Subuhaaka wa innii mayyitu

In lookacii yaa arzama

Sarikatun wa sarikaatu mautu

Atiidu da Raƙiibu matambayaa

Ku yii masa tambaya da sauƙii

Baa da raazanarwaa ba.

Wannan surkulle ana yin sa ne a yayin da aka bayyana wa mutun cewa wani ya mutu wato in aka faɗa wa mutum ya zo jana’izar wani ya mutu, sai wanda aka gayyata ya yi wannan surkulle.

Fa'’idar da ke tattare da wannan surkulle ita ce, furta surkullen da aka ambata a sama yana hana mutum ɗimaucewa idan ya ji bayanin mutuwar.

Wani abin lura a wannan surkulle shi ne za a ga yana da tasirin harshen Larabci a cikinsa. A tattare da haka akwai subuhaaka da ‘wa’ da ‘innii’ da kuma ‘mayyitu’. An saƙala gaɓoɓi biyu a ƙarƙashin kalmar ‘subuhakaa’ don a kauce wa faɗin ‘subuhaanaka’ ne ‘wa’ na nufin ‘da’, ‘innii’ ‘ni’ ake nufi, sannan ‘mayyitu’ kuma an shafe baƙin ƙarshe na asalin kalmar mayyitun ta larabci amma dai duka mai mutuwa ko mamaci ake nufi. Haka a jimlar ‘in lookacii yaa arzama’ ana nufin idan lokacin mutuwa ya zo. Kalmar ‘sarikaatu’ tana nufin ɗanɗana zafin mutuwa. A dunƙule, amfanin surkullen shi ne yana nuna yi wa wanda aka ji labarin ya mutu addu’ a ne da cewa matambayan kabari su yi masa (ga shi mamaci) tambaya da sauƙi.

2.2. SURKULLE NA SHIGA GIDAN DA AKA YI MUTUWA

Ku shaa, ku shaa

ku shaa ruwanku,

wata raanaa naamu

zaa a shaa.

Cikin wannan surkulle, a jimlar farko ta ‘ku shaa, ku shaa’ a ganin masu binciken, jimlar tana nufin mamacin da ma sauran waɗanda suka mutu a wannan gida, su kasance cikin halin jin daɗi, ‘ruwaa’ da aka ambata ana nufin ruwan alkausara ko kuma zaman jin daɗi a kabari.

Haka kuma kamar yadda majiyarmu ta bayyana, ambaton ‘wata rana namu za a sha’ yana nufin shi ma wanda aka gayyata, wata rana shi ne zai mutu, mutane su yi gayyar tasa mutuwar.

2.3. SURKULLE NA WANKAN GAWA

Bismillaahi allaahumma

suturhu, wa rufauhuu

fii ƙabarin ƙabaraata

har abadaa, bari mu

wankee shi, kafin a wankee mu,

ba mu san ranar kauraa ba,

ba mu san wanda zai wankee mu ba.

A dai bisa yadda muka zanta da mutanen da muka yi hira da su, amfanin surkullen shi ne ana ƙoƙari ne a tsabtace gawar ne daga irin zunubin da ta ɗauka, a zamanta na duniya.

Harshen Larabci ya yi tasiri matuƙa a cikin wannan surkulle, musamman idan an yi la’akari da kalmomin ‘Bismillahi’ da ‘allahumma’ da ‘fii’ da kuma ‘kabari’. Waɗannan kalmomi an aro su ne daga harshen Larabci kai tsaye wanda bisa ma’ana suna nufin farawa da sunan Allah, da ‘ya Allah’ da ‘cikin’ da kuma ‘kabari.’ Sannan kalmomin: ‘suturhu da rufauhu’ kalmomi ne da aka baddala su ta hanyar yi musu ɗafin ƙeya na ‘hu’ a ƙarshensu. Kalmar ‘suturhu’ tana nufin a yi wa mamaci sutura, wato a sanya shi cikin likkafani. Ita kuma kalmar rufauhu a nan tana nufin a rufa masa (mamaci) asiri manufa idan an sanya masa likaffani a rufe tsiraicinsa ko kuma neman ya samu tsira a lahira da kuma a kwanciyar da zai yi a kabarinsa. Haka kuma a jimlar ‘ba mu san raanar ƙauraa ba’ an yi amfani da kalmar ƙaura wadda take nufin sake wurin zama, wato daga duniya zuwa lahira. Abin lura a nan dai shi ne wannan surkulle addu’a ce ake yi wa mamaci ya samu tsira da zaman jin daɗi a kabari bayan ya mutu. Abin da za a iya fahinta a wannan surkulle shi ne samuwar tasirin harshen Larabci. Kalmomin ‘Bismillaahi da Allahumma da kuma Suturhu’ duka kalmomi ne na larabci aka surka da harshen Hausa.

2.4. SURKULLE NA FITAR DA GAWA DAGA GIDA

Wani nau’i na surkulle da ake samu a yankin Guddiri shi ne na fita da gawa daga gida bayan an gama shirya ta. Surkullen da ake yi kuma shi ne :

Kai Duwa, kai Duwaa-Duwa,

Baa ni wuriina in wuce, wuceewaa,

Yaushe ka san ni, yau ne ka san ni

Ka san sunaana? Naas an ka nan

San ‘yaa’ yanka. Inaa su duwai,

Inaa su Musaa da Isa ya jabbakaari,

Yaa Rasuullahi shaafa kainaa

Shafaa’atii, yii masa ceetoo muu

Maa mu samuu’.

A wannan surkulle na fitar da gawa daga gida zuwa yi mata jana’iza (Sallah) zuwa a kai ta kabari, akwai wata hikima ko dabara mai kama da hira tsakanin mutum biyu. A matakin farko na surkullen ana magana ta hanyar ambaton suna ‘kai Duwa kai Duwa’. Duwa ana nufin wai suna ne na mala’ika. Ba ni wuriinaa in wuce’ wai da zarar an faɗi haka sai kuma mai yin surkulle ya sake cewa, wuceewaa, yaushe ka san ni, yau ne ka san ni ka san sunana?,’ sai kuma a sake cewa naa san ka naa san ‘ya’yanka, inaa su Duwai ina su Musa da Isa. Wato ana nuna an san Duwa da ‘ya’yansa da ma sauran manyan mutane annabawa. Daga ƙarshe sai a ƙarasa da ambaton ‘yaa Rasuulillahi shaafa kainaa shafaa’afii, yii masa ceetoo, muu maa mu samuu.

A wannan surkulle za a iya lura da cewa yana da tasirin Larabci a cikinsa; a inda aka yi amfani da kalmomin ‘yaa da ‘rasuulallahi’ da kuma shafaa’afii dukkansu na larabci ne. rasuulallahi na nufin manzon Allah. ‘shafaa’a fii n’ na nufin ceto a cikin – wato ana neman manzon Allah ya yi ceto, wanda shi ma mai addu’ar zai samu shiga ciki.

2.5. SURKULLE NA DUBA GAWA DON GUDUN KADA TA YI FATALWA

A yankin Guddiri da ma sauran yankuna na ƙasar Hausa, sun yi imani da cewa, idan mutum ya mutu zai iya yin fatalwa. Wato bayan an binne shi zai riƙa fitowa daga kabarinsa yana dawowa duniya wurin mutanen da suka san shi. Kuma Bahaushe yana tsoron irin wannan dawowar wato fatalwa. Don haka idan mutum ya mutu sai a riƙa yin wannan addu’ar.

A uuzu, A uuzu bil kamata.

Rubuuwata hai’aata bika,

Wa’alayya harmun harama.

Wannan nau’i na surkulle yana da amfani ta fuskar samun kariya daga gamuwa da fatalwa kowace iri, ba sai lallai ta ɗan’uwan mamaci ba. A wannan surkulle za a ga akwai tasirin Larabci sosai a cikinsa. Kalmomin Larabcin a cikinsa sun haɗa da: ‘A’ uuzu da ‘bil’ da ‘bika’ da ‘wa’ da kuma ‘alayya’. A’uuzu na nufin da, kalmar ‘alayya’ na nufin a gare ni. Sauran kalmomin : ‘rubuuwata’ da ‘haiaata’ da kuma ‘harmun’ ba su da wata cikakkiyar manufa da za a iya bayyana su da ita. An dai yi wani abu ne mai kama da hargitsi-ballen surka larabci da Hausa a cikinsu.

2.6 SURKULLE DON KADA MIJI KO MATA TA YI FATALWA

Tarnakin tarmaaka, dabalnalin

Dabaibayin bakin sa, taf ka ba ruwaa,

Ka yi kwance, kwanciyar barcin har abada

Ba da taasoowaa ba.

Wannan surkulle da ya gabata yana da amfani ga miji ne ko macen da mijinta ya rasu ya bar ta. Amfanin wannan surkullen shi ne a yayin da miji ko mata ta yi wannan surkulle, mijin ko matar ba za ta dinga ganin fatalwar mijin nata ba.

Haka kuma wani abin lura shi ne wannan surkulle ma yana da tasirin addini a cikinsa. Za a ga inda aka fara da yin ‘ bismillahi’ sannan akwai kalmomin ‘bi’ da ‘a’alaa’ wato ma’anar wannan shi ne farawa da sunnan maɗaukaki sarki Allah.

2.7. SURKULLE NA ZAMAN MAKOKI

Zaman makoki shi ne zaman karɓan gaisuwa da dangin mamaci ke yi na tsawon kwana uku. A bisa al’adar Bahaushe duk wanda ya mutu akan yi zama na wuni uku. Haka kuma abin yake a yankin Guddiri ma. Ana fara zaman daga ranar da aka yi jana’izar mamaci.

surkulle da ake yi shi ne:

Jingim maa jingim

Fankam kara fankam

Allah shi kaɗai yake

A gare shi ba wani

Sai shi.

Wannan surkulle ne da ake yi a daidai lokacin da aka fara zaman makoki (wato karɓar gaisuwa). A bisa ga bincikenmu, wannan surkulle ba shi da wata takamammiyar fa’ida da ake yi dominta.

Har wa yau, za a ga an maimaita ambaton kalmomin, ‘jingim’ da kuma ‘fankam’. Kalmar ‘jingim’ tana nufin yawa, wato taron yawan mutanen da ke zama a wurin karɓar gaisuwar mutuwa (ta’aziya) ne kalmar ‘fankam’ ita ma ta ƙunshi makusanciyar manufar da kalmar ‘jingim’ wato tana nufin taruwar yawan jama’a ne masu zaman gaisuwa a wurin zaman makoki.

3.0 IRE-IREN SURKULLE DA SUKA DANGANCI SHA’ANIN TAKABA

A ƙarƙashin wannan akwai ire-iren surkulle daban-daban kamar haka:

3.1 SURKULLEN SHIGA TAKABA

Takaba wani ko wasu ayyunannun kwanaki ne da matar da mijinta ya rasu ya bari ke ƙillace kanta ta hanyar zama a gida har tsawon wata huɗu da kwana goma. Akwai surkulle da mata ke yi na shiga ka fara takaba kamar haka:-

Bismillahi warkafun,

Bi a’al zugum

Taalikai zugum-zugum

Gidaa da shaiduu, a nan zaa mu faara takabaa.

Wannan surkulle, yana da amfani saboda yana yin nuni ne game da shiga takaba da mata ke yi. Haka kuma amfanin wannan surkulle shi ne neman kariya daga sharrin iskoki a lokacin da suke yin takaba. A wata fuskar kuma mazauna wannan yanki (na Guddiri) sun bayyana mana cewa, mai shiga takabar tana yin wannan surkulle ne saboda ta yi saurin samun mijin aure, bayan ta gama idda.

Wannan surkulle shi ma akwai aron kalmomin Larabci a cikinsa. Wato ana ayyana shiga takaba ne ta hanyar wannan surkulle. Jimlar ‘bi a’alaa zugum taalikai zugum-zugum’ na nuna halin juyayin mutuwa ko mutumin da ya mutu ne, ambaton ‘a naan za mu faara takaba’ yana nuna shiga takaba ne kai tsaye.

3.2. SURKULLEN WANKAN MAI TAKABA MAKO-MAKO

Wannan binciken ya fahimci cewa, idan mace ta shiga takaba a yankin Guddiri sau ɗaya kawai za ta yi wanka a mako, wato ranar Juma’a. Don haka, yayin da aka zo yi mata wankan ana yin wannan surkulle:

Allaahumma innii waraa ta janii

Bi ismika tirkaamaa tirkaa.

Da farko,amfanin wannan surkulle dai shi ne mai takaba za ta samu kariyar isaka. Haka kuma kamar yadda muka zanta da wani a garin Azare (da ke yankin Guddiri) , an bayyana mana cewa, a yayin da mace take yin takaba, akwai wani hamami da ke jikinta wanda ke jawo hankalin iska. Ana ganin karanta wannan surkulle, zai kawar mata da wannan hamami.

Haka kuma wannan surkulle ya ƙunshi kalmomin Larabci a cikinsa. Sai dai kuma kalmar, ‘wara’a’ ta yi kama da ta filatanci mai ma’anar zuwa. ‘Allahumma’ na nufin ya Allah ‘Bi’ na nufin da, ‘ismika’ kuma shi ne ‘sunanka’. Wato da sunan Allah. Kalmar ‘tirkaa’ ta yi kama da kalma mai ma’ anar dukiyar gado da aka bari kafin a yi rabon gadon, amma a nan tana nufin hoɓɓasan yin kwanaki bakwai na wancan, ma’ana dukan kwanakin ake nufi cewa an yi musu niya guda.

Yayin da aka fara wankan kuma sai a ce :

Ilaahii zunubi algaya

Akalahuu wal lawaaya

A cikin wannan surkulle za a iya ganin tasirin harshen Larabci. Misali kalmar ‘ilaahi’ na nufin Ubangijina, ‘zunubi’ na nufin laifuka da aka aikata na haramci ‘akalahuu’ aka cinye, ‘wal’ da, ‘ lawaaya’ kalmomi ne marasa ma’ana cikin wannan surkulle. A nan, a wannan surkulle ana neman gafara ne da kuɓuta daga aikata kuskure yayin wancan.

3.3. SURKULLEN GAMA WANKA

Yayin da aka gama wanka kuma sai a ce:

Alluhudun hudun

Tafi dum

Wannan surkulle ne da ake yi bayan an gama wancan takaba. Surkullen ba shi da wata ma’ana. Sai dai kamar yadda muka zanta da wani malami ya bayyana cewa ana yin surkullen be don kariya daga sharrin iskoki ka da su yi wa mutum wata illa. Sai dai kalmar ‘dum’ ana nufin kada mai wanka ta ji bugu ‘dum’ na dundu a bayanta. Wato kada aljani ya buge ta kafin fita daga ban-dakin.

3.4. SURKULLEN RUFE KOFA DA DARE

Ana yin surkullen kamar haka:-

Sama lu’un aala lu’un

A’uuzubillahi lu’un

Urtun addaashimii

Mace addaashimaa

A cikin wannan surkulle ma kamar sauran, za a iya ganin da tasirin Larabci a cikinsa. Misali Kalmar ‘aala’ daga’ala’ take wadda take nufin kan ko ‘bisa’ haka kuma kalmar ‘a’uuzubillaahi’ a nan tana nuna neman tsarin Allah. Sauran kalmomin kuwa za a ga babu wata ma’ana keɓaɓɓiya za a dangantata da su.

Har ila yau, wani abin lura kuma shi ne akwai maimaicin kalmar lu’un sau biyu. A cikin wannan ma akwai nashewar ƙwayar sauti ta wasalin ‘ii’ta kalmar ‘addashimii’ ta Koma ‘aa’ a kalmar ‘addaashimaa’. Kalmar da ta kare da ‘ii’ tana nuna jinsin namiji, wadda ta ƙare da dogon wasali ‘aa’ tana nuna jinsin mace wato an yi amfani da hanyar ƙirar kalma ta kumburi na kalma a wannan surkulle.

3.5. SURKULLEN SHIGA ƊAKI GA MAI TAKABA

Daga cikin abubuwan da ya shafi takaba a yankin Guddiri sun haɗa da karatun shiga ɗaki na farko lokacin da takaba ta kama mace, yadda take ambaton wannan surkullen.

Saahuuna maa ‘uuna

Kaucee daga nan

Zan wuce

Abin sha’awa dangane da wannan surkulle shi ne yadda ya kasance Hausa tsantsa babu surkin Larabci a cikinsa ko kaɗan kalmomin surkullen yawancinsu ba su da wata tabbatacciyar ma’ana idan ban da kaɗan daga cikinsu. Misali a kalmar ‘kaucee’ ana nufin sanar da iskokin wannan gida da za a shiga da su ba da wuri ana so a shiga gidan. Ana ambaton hakan ne domin kada a yi wa iskokin da ke gidan laifi bisa tsarinsu na zaman gidan.

A kalmomi biyu na farko a surkullen suna da tsarin gaɓobi iri ɗaya ne na buɗaɗɗun gaɓoɓi masu dogayen wasula a gaɓoɓi biyu na farkon kowace kalma (daga cikinsu). Kalmomin ‘saahuuna’ da ‘maa’uununa’ kalmomi ne na yabo da girmama iskokin da ke gidan da aka yi mutuwar

3.6. SURKULLE DA MAI TAKABA TAKE YI KAFIN TA KWANTA A GADO DA DARE

Wannan surkulle ana yin sa na kamar haka:

Allaahu yaa Allah, yaa ubangijin

Saamuuna da gaskiyaa laa isimuka,

Da suunansa yaa ta zanni agafirrunaa

Allah kwantar ha’an arina in kaa kai

Numfaashiinaa, ka kai ni muuminaa,

Ka taashee ni saa ilaa.

Wannan surkulle na da tasirin harshen Larabci shi ma. Wato an yi amfani da aron kalmomin Larabci da dama a cikin wannan surkulle da ya gabata. Kalmomi ne da yawancinsu suke nuni da mahalicci da kuma tuba a wajen mahalicci Allah. Manufar kalmomin wannan surkulle suna da alaƙa da abin da surkulle ke nuni da shi sosai da sosai. Za a ga kalmar ‘yaa’ da Allahi’ da ‘Ubangiji’ da ‘samuuna’ suna nuna yabon Ubangiji Allah ne. Wani abin kula ko lura kuma shi ne wato sammai (jam’in kalmar sama). Sannan kalmar ‘agafirrunaa’ na nufin gafara ko yafewar Ubangiji ne. sai dai an yi nannagen baƙin ‘r’ domin a kauce wa kalmar agfirnaa ta asalin harshen larabci.

Wannan surkulle har wa yau nuna al’adar nan ta Musulmi mumini da in ya zo kwanciya da dare, irin yadda yake addu’a da komawa tare da sallamawa zuwa ga Allah. A nan ken an addu’ar surkullen ta kunshi al’ada da addini ne.

3.7. SURKULLE NA SHIGA BANDAKI

Wannan surkulle ana yin sa kamar haka:

Wa auli Rabbuka hattaa

Yaa tattakimu, yaa kai

Baawaa, raanar sakankan

Ceewar; it ace kaala, yaa

Fadaa annabi Muusa yaa

Fadda laabudda baa makwaa.

A wannan surkullen ma kamar a sauran ne, za a ga an yi aron kalmomin larabci da yawa a cikinsa.Wannan nau’i na surkulle ana yin sa ne domin neman tsari daga gamuwa da aljani a bandaki.

Kamar yadda ya gabata a wasu surkullen da aka ambata a baya, wannan surkulle yana da tasirin Larabci. An yi aron kalmomi Larabci da dama a wannan surkulle. A jimlar ‘wa auli Rabbuka’ ana nufin alkiyama cewa babu tababa ranar za ta zo.

Mafi yawan waɗanda aka zanta da su a wannan kasha mata ne. Don haka yawan-yawan surkulle da aka tattara suka kasance na sha’anin mata. Wannan ya faru ne saboda wannan ɓangare ya fi mayar da hankali ne kan sha’anin mutuwa musamman kuma an fi mayar da hankali kan ɓangaren takaba.

3.8. SURKULLE NA NEMAN TSARI DAGA MUTUMIN DA AKE SHAKKA KAN WANI LAMARI

Wannan karatu na surkulle kuma ana yin sa kamar haka:

Kutkulan dukulaini karaa

Wa kaalahuu, laulaini karaa

Wa huwabuu bushu’aini karaa

Wa buruuta kasbaini kara

Ayyuu kaana buruuji kasbaini karaa

Innallaaha kaana aliiman hakiimaa

Suururu kundi sharri, wahya subuhaana aaya tamat

A wannan surkulle da ya gabata, za a ga bisa manufa da fa’ida, yana da alaƙa da dalilin da ya sa ake yin sa. Wato akwai kalmomin da ke nuni da hakan da suka haɗa da: ‘dukulaini’ karaa, wa huwabuu, kasbaini da kuma sharri’. Kasancewar surkullen ya ƙunshi aron kalmomi da dama daga harshen larabci kusan a dukansa, za a ga waɗannan kalmomi, kalmar dukulaini na nufin shiga. A kalmar an sarƙafa‘duku’da ‘laini’ sai suka bada ma’anar shiga tsakanin abu biyu. Kara kuma kalma ce ta Hausa wanda ake nufin karan ya shiga tsakanin mai surkulle da wanda ake neman tsari daga gare shi. Kalmomin wada huwabu suna sanar da shi mutum da ba ayarda da shi ba. Sannan kasbaini na nuna tsakanin, an yi wa wannan ɗafin goshi ne na ƙasa domin a kauce ambaton ‘baini’ kai tsaye. Kalmar sharri kuma ma’anata a fili yake ana nufin sharrin mutumin da ba a yarda da shi ba.

A wannan surkulle za mu ga ya yi surkin ko ya ƙunshi kalomomin Hausa da na Larabci waɗanda ke yi nuni da neman kauce wa sharrin mutumin da ake shakka a kansa ka da ya cutar.  

Wannan binciken ya yi ƙoƙarin fito da ire-iren surkullen da suka shafi mutuwa a yankin Guddiri na ƙasar Hausa. A inda aka gano cewa,mazauna wannan yanki na ƙasar Guddiri, suna amfani da surkulle a lokuta daban-daban a ta fuskar abubuwan da suka shafi mutuwa.A tattare da haka, takardar ta gano cewa masu amfani da surkullen, sukan yi ƙoƙarin danganta mafi yawan surkullen da harshen Larabci.A hannu guda kuma sukan jingina da hakan, su nemi kariya ta tsarin guje wa shiga wata larura. Wanda a ra’ayin wannan takarda suna son a sama wa surkullen gurbi ta fuskar addini.

MANAZARTA

Abubakar R. U. (2006). Camfi da Surkullen masu Bayar da Magunguna a Ƙasar Hausa. Kundin digiri na ɗaya, Shashen Harsunan Nigeria, Jami’ar Bayero Kano

Adamu, M. T. (1985). Tarihin Samuwar Ilmin Tsibbu ga Al-ummar Hausawa. Illmi Cikin Mujallar Nazarin Harshen adabi da Al’adu na Hausa kundi na Uku wanda cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero Kano ta tsara.

Adamu, M. T. (1998). Asalin Magungunan Hausawa da ire-irensu, Kano Ɗan Sarkin Kura publishers ltd.

Adamu, M. T (1990). Siddabaru A Ƙasar Hausa. Kundin Digiri na Biyu Sashen Harsunan Nijeriya Jami’ar Bayero, Kano.

Abdulƙadir, U. F ( 2009). Tarihin Kafuwar Masarautar Katagum (1807 – 2009) : Kano, Triumph Publishing Company, Nigeria.

Almajir, T. S. (2009).. Surkulle: Yanaye-Yanayensa da Muhimmacinsa ga rayuwar Hausawa. Cikin Himma Journal of Contemporary Hausa Studies Vol I No. 1 Department of Nigerian Languages, Umaru Musa ‘Yar’aduwa University, Kastina.

A’ishatu, B .M (2005). Ruƙiyya A Ƙasar Hausa: Hanyar Warkar da CiwonAljanu.Kundin Digiri na Farko Sashen Harsunan Nijeriya Jami’ar Bayero, Kano.

Azare, S. A (2O17). Canje-Canje A Karin Harshen Guddiranci: Nazari A Kan Tsarin Sauti da Tasarifi. Kundin Digiri na biyu. Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano.

Bagari, D.M ( 1979). Some Aspects of Guddiranci. The Guddiri Dialects of Hausa. A paper presented at Symposium on Chadic Languages.

Bunza, A. M. (2006). Gadon Feɗe Al’ada Lagos, Tiwal Nigeria ltd.

 C. (1990). Hayaki Fidda na Kogo (Nazarin Siddabaru da Sihirin Hausawa) Kundin binkice don Digiri na Biyu a Hausa Shashen Nazarin Harsunan Nigeria, Jami’ar Bayero Kano.

Doguwa, M.S (2002). Surkulle Karatun Mata: Gudummawarsa ga Adabin Hausa. Kundin Digiri na Biyu, Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya Jami’ar Usumanu Dan Fidiyo, Sokoto.

Hamma,A.S (1981). The Hausa Spoken in Harɗawa A Compartiɓe Study. A research project. Department of Languages and Lingujstics. University of Maiduguri.

Shehu, B.M (2002). Surkullen Mata Kundin Digirin Farko da aka gabatar a Sashen Nazarin Harsuna da Kimiyyarsu, Jami’ar Maiduguri.

Shehu, B. M. (2013). Surkulle cikin Magungunan Gargajiya na Hausawa Kundin Digiri na Biyu Shashen Nazarin Harsuna da Kimiyyarsu, Jami’ar Maiduguri.

Yobe Journal - Volume 5

Post a Comment

0 Comments