𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
As-Salamu Alaikum, Malam, mu biyu ne a wurin mijina. To, sai na yi tafiya a ranar da na fita girki, kuma na dawo ranar da ya kamata in karɓi girki. Amma saboda yana yin tafiya ban shigo gida da wuri har na iya ɗora girkin ba, don haka abokiyar zamana ce ta yi mana abinci a wannan daren. Shi kuma da ya zo sai kawai ya shige wurinta ya kwana! Tambayata a nan ita ce: Hakan da ya yi daidai ne?
NA DAWO TAFIYA… MIJINA YA
KWANA A ƊAKIN
KISHIYATA
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam Wa
Rahmatul Laah.
Da farko wajibi ne a Shari’a
kafin miji ya ƙara auren mace ta
biyu sai in ya san cewa zai iya yin adalci a tsakaninsu a cikin abubuwan da su
ke a fili a bayyane. Allaah (Subhaanahu Wa Ta’aala) ya ce:
ﻓَﺈِﻥۡ ﺧِﻔۡﺘُﻢۡ ﺃَﻟَّﺎ ﺗَﻌۡﺪِﻟُﻮﺍ۟ ﻓَﻮَ ٰﺣِﺪَﺓً ﺃَﻭۡ ﻣَﺎ ﻣَﻠَﻜَﺖۡ ﺃَﯾۡﻤَـٰﻨُﻜُﻢۡۚ
Idan kuma kuka ji tsoron
cewa ba za ku iya yin adalci ba, to sai ku auri guda ɗaya,
ko kuma abin da hannuwanku na dama suka mallaka. (Surah An-Nisaa’: 3)
Rabon-kwana yana daga cikin
abubuwan da dole miji ya yi adalci a tsakanin matan aurensa a cikinsa. Asali in
ji malamai, rabon kwana ɗai-ɗai
ne, watau dare ɗaya da yini ɗaya
ga kowace mace. Kuma ba zai iya wuce hakan zuwa kwanaki biyu-biyu ko uku-uku ko
sama da haka kamar mako-mako ko wata-wata ba, sai da amincewarsu kuma da
yardarsu.
Don haka, a lokacin da aka
gama kwanakin amarci, watau: Kwanaki bakwai ga budurwa ko kwanaki uku ga
bazawara sai mijin ya zaunar da uwargida da amarya domin a tsara rabon-kwanan
da sauran duk wasu sharuɗɗa ko yarjejeniyoyin da za a
gudana a kansu, don samun ɗorewar zaman lafiya a gidan.
Muhimmin abin da ya kamata a
fahimta dai shi ne: Abin da Shari’ar Musulunci ta damu da shi a nan shi ne:
Rabon-kwana kawai amma ba girki ko dahuwar abinci ba. Domin ba kowace mace ce
take iya yin girki ko dahuwar abinci a koyaushe ba, saboda larurori kamar
rashin lafiya ko jego ko komowa daga tafiya ko rashin abin girkawa da sauransu.
Wannan kuma ba zai hana a yi rabon-kwana da ita ba.
Sannan rabon-kwana a dare ne
kuma yini yana bin sa. Don haka, zai iya shiga wurin wacce ba kwananta ba da
rana, amma ba da dare ba, sai in da wata larura mai ƙarfi.
Kamar yadda muka ambata a
baya, ya halatta a wurin rabon-kwana ma’aurata su kawo duk wata yarjejeniya ko
sharaɗin
da suke ganin zai taimaka wurin samar da zaman lafiya mai ɗorewa
a tsakaninsu, matuƙar
dai bai saɓa wa Shari’a ba. Manzon Allaah (Sallal
Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:
« ﺍﻟْﻤُﺴْﻠِﻤُﻮﻥَ ﻋَﻠَﻰ ﺷُﺮُﻭﻃِﻬِﻢْ »
Musulmi suna nan a kan sharuɗɗansu.
A wani lafazi kuma ya ce:
« ﺍﻟﺼُّﻠْﺢُ ﺟَﺎﺋِﺰٌ ﺑَﻴْﻦَ ﺍﻟْﻤُﺴْﻠِﻤِﻴﻦَ »
Sulhu halal ne a tsakanin
musulmi.
(Abu-Daawud: 3596, kuma Al-Albaaniy ya ce:
Hasanun Sahihi ne).
A riwayar Ahmad ya ƙara da cewa:
« ﺇِﻻَّ ﺻُﻠْﺤًﺎ ﺃَﺣَﻞَّ ﺣَﺮَﺍﻣًﺎ ﺃَﻭْ ﺣَﺮَّﻡَ ﺣَﻼَﻻً »
Sai dai sulhun da ya halatta
haram, ko ya haramta halal.
Don haka, kodayake a asali
ba girki a ke kallo a wurin rabon-kwana ba, sai dai kuma suna iya yin sharaɗi ko
sulhu a kan cewa: Mai girki ita ce da miji, ko kuma ba ita ce da miji ba. Ko
kuma duk lokacin da mai tafiya ta dawo ita ce da miji ko ba ita ce da miji ba,
da sauransu.
A ƙarƙashin
wannan, mijin da ya shiga wurin wacce ta yi abinci a wannan yammacin bai yi
laifi ba matuƙar dai haka suka yi
yarjejeniya ko sharaɗi tun da farko. Amma idan ba
su yi wannan sharaɗin ko yarjejeniyar ba, kuma
al’adarsu ba ta gudana a kan hakan ba, to bai yi daidai ba. Domin a fili ya ke
cewa: Wacce ta dawo daga tafiya an rage mata kwananta ɗaya,
ita kuma waccan an ƙara
mata. Don haka, sai a biya ta, watau a rama mata, in dai ba ita ce ta yafe ba.
Duk matar da ta yi tafiya na
wasu kwanaki ko watanni, to ba sharaɗi ba
ne a ce idan ta dawo sai an rama mata waɗannan
kwanakin da ba ta nan, idan kuma aka ce sai an rama mata to an cutar da sauran
matayen ko ɗaya matar idan su biyu ne. Saboda haka
kuskure ne babba miji ya rama wa matar da ta yi tafiya kwanakin da ba ta nan,
lallai wannan ba dai-dai ba ne, duk matar da ta yi tafiya har zagayowar
kwananta ya shuɗe ba ta nan, to haƙƙin wannan kwana ko kwanaki
sun faɗi,
ba wata maganar ramuwa, wannan shi ne adalci.
Mu'amala ta aure da
zamantakewa abin da shari'a ke buƙata a
cikin su shi ne yin adalci, aduk yadda mai gida da iyalansa suka tsara yadda za
su zauna matukar an kiyaye ka'idar (Kada ayi cuta kuma kada a cutar) toh babu
laifi, don haka ba laifi don ya shiga dakin wadda ta yi tafiya duba ga an dade
ba a haduba.
WALLAHU A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.