Ticker

6/recent/ticker-posts

Abincin Hausawa a Mahadin Magani

Citation: Musa Alhaji Abdulrahaman (2017). Abincin Hausawa a Mahaɗin Magani. Yobe Journal of Language, Literature and Culture (YOJOLLAC), Vol. 5. Department of African Languages and Linguistics, Yobe State University, Damaturu, Nigeria. ISSN 2449-0660

ABINCIN HAUSAWA A MAHAƊIN MAGANI

By

Musa Alhaji Abdulrahaman

ABSTRACT

The issues of food and medicine in the life of Hausas is like any other society issue in this world each and every community in the world has their way for sourcing their cuisines, recipes and medicine. The benefit of food is not longer to fight against hunger but can also save as medicine. In any society living in this world has their kind of food and medicine that they use, and also it can proud with it. The essence of this paper is to bring the way that Hausas using food as an ingredient of medicine traditionally like a medicine for self-defense, for medication, for poisoning and so on. Any things that can substance which specifically promotes healing when drink or consumed in some way, that is call medicine.

TSAKURE

Al’amrin abinci da magani a rayuwar Hausawa harka ce da kowace al’umma da take rayuwa a doron ƙasa tana da nata irin abincin da magani da ta dogara da su kuma take amfani da su ko sarrafa su don buƙatun rayuwa ko kashe yunwarta ko kawar da cututtukan da suke tattare da su, babu wata al’umma da take rayuwa a doron ƙasa face tana da nata irin abincin da magani da take amfani da su, kuma take alfahari da su. Babban burin wannan maƙala ita ce bayyana hanyoyin da Bahaushe ke amfani da abinci a mahaɗin magani da ya danganci biyan buƙatun zuci ko cutarwa ko warkarwa ko kare kai.

1.0 GABATARWA

An yi rubuce-rubuce da dama kan abubuwan da Hausawa ke amfani da su a mahaɗin magani amma wannan maƙala tana magana ne kan abincin Hausawa a mahaɗin magani. Saboda batu ne da nake ganin cewar manazarta su ƙara zurfafa bincike a kansa. Wannan maƙala za ta yi dubi ne kan yadda ake amfani da abincin a fagen haɗa magungunan Hausawa na gargajiya a jiya har ma a yau, ire-iren waɗannan magunguna kuwa sun haɗa da; magungunan biyan buƙatun zuci da magungunan da ake amfani da su wajen cutarwa da magungunan warkarwa da magungunan kare kai. Hausawa sun jima suna amfani da abinci a mahaɗin magungunansu don gudanar da rayuwarsu ta yau da kullum.

2.0 MA’ANAR ABINCI

Hausawa ko ƙasar Hausa Allah ya albarkace ta da abinci iri ko nau’i daban-daban da suke amfani ko suke sarrafawa don kashe yunwa ko marmari ko kuma buƙatun rayuwarsu ta yau da kullum.Masana da manazarta sun bayyana ma’anar cimaka ko abinci, kamar haka, wani nau’i ne na abinci, wanda kowace irin al’umma ta zaɓi ta yi amfani da shi tun asali, kuma ta tashi da shi ya zama sananne a gare ta, ya ci gaba da cewe‚Cimakar Hausawa ita ce ire-iren abinci waɗanda Hausawa suke ci ya bi jiki, ya ƙara ƙarfi da lafiya, ya kuma kare jiki daga cutuka, sannan kuma suka jima suna amfani da su, musamman ma tun kafin su sadu da wasu baƙin al’ummu Gusau, (2008:4).

Abinci wanda kowace al’umma ta ɗauka shi ne hanyar ciyarwarta, shi ne cimakarta Hornby, (2000:459). Haka ma, a ‚Sabon Ƙamus Na Hausa Zuwa Turanci, na CNHN (1979), an bayyana maanar (Cima) da abinci na asali ko sananne ko na gargajiyar al’umma. Har aka ba da misalin ‚tuwo cimar Hausawa ce‛ (1979:20). Haka zalika, a cikin ƙamus mai suna ‚Ƙamusun Hausa na CNHN (2006), an nuna maanar kalmar cimaka tana nufin abinci ko abin yanka dawa ko moyi watau abincin da rai ya fi so (2006:76-347).Shi kuwa, Abraham, (1976:144) ya bayyan cewa: ana kuma amfani da kalmar cimaka ga kowanne abinci ko girki na gargajiyar kowace al’umma.Al’amrin abinci harka ce da kowace al’umma da take rayuwa a doron ƙasa tana da nata irin abincin da ta dogara da shi kuma take amfani da shi don buƙatun rayuwa ko kashe yunwarta.

2.1 IRE-IREN ABINCIN HAUSAWA

Hausawa suna da abinci iri daban-daban da suke sarrafawa ta hanyoyi da dama don gudanar da rayuwarsu ta yau da kullum, daga ire-iren kayan abincin da suke kewaye iri daban-daban. Da can Hausa suna amfani da rana wajen sarrafa wasu daga cikin abincin da suke amfani da su. Tun lokacin da Hauswa suka gano wuta sai ya kasance sun girka wato sun dafa ko gasa ko kuma ɗunɗuma (ɗumama) cimakar da za su ci, sannan su yi amfani da ita, in ban da abubuwan da suka shafi wasu daga cikin kayan marmari waɗanda suke ci kai tsaye daga tsinkowa wato a ɗanyinsu. Daga cikin waɗannan mabambantan cimaka akwai waɗanda ake sarrafawa ta hanyar tuƙawa ko talgawa ko kirɓawa ko turarawa ko nasawa ko toyawa ko kwaɗantawa ko damawa ko yayyankawa ko miya da dai sauran abubuwan ci. Gusau, (2008:119).

Ire-iren abincin Hausawa sun haɗa da:

a) Abincin da ake tuƙawa: Waɗannan nau’in abincin Hausawa kuma shi tuƙawa ake yi,wato sai an niƙa garin abincin zalla ko tsagwaransa kana kuma a tuƙa shi, su kuma sun haɗa da: tuwon gero, tuwon dawa, tuwon masara, tuwon alkama, tuwon rogo, tuwon, wake, tuwon aduwa, tuwon shinkafa, tuwon biski, tuwon tsari, tuwon acca da sauransu.

b) Abincin Turarawa: Su kuma ire-iren waɗannan abincin Hausawa, turara shi ake yi da wuta, wato a ɗan masa barazana da wuta, kafin a yi amfani shi, amma ba koda yaushe ba, ire-irensu ga su kamar haka: hoce, wasa-wasa, dambu, gyaɗa da sauransu.

c) Abincin Kirɓawa: Waɗannan nau’in abincin Hausawa kuwa su kuma ƙirɓawa ake kafin a yi amfani da su, kamar daƙuwa da fura/hura wasu lokuta ana haɗa su da nono wajen amfani da su wasu lokuta kuma haka ma ake cin su zalla, su ma ga su kamar haka:daƙuwa, yakuwa, rama, gyaɗa, fura ko dawo.

d) Abincin Nasawa (Nashi): Wannan nau’i na abincin Hausawa su kuma nasa su ake yi, ana nasawa ne a cikin tukunya da ruwa yana tafasa akan wuta, ire-irensu ga su kamar haka:ɗanwake, tubani, ɓula, ɗangauda, dawo da sauransu.

e) Abincin Kwaɗantawa: Abincin Hausawa da ake kwaɗantawa suna da dama, amma Hausawa sun fi kwanɗanta abincinsu da suka danganci ganyayyaki, kuma sun fi amfani da ƙuli/ƙarago wanjen kwaɗon abinci, ire-iren abincin da Hausawa suke kwaɗantawa sun haɗa da: rama, zogale, yaɗiya, tafasa, yakuwa, dankali, makani, gwaza, dundoji, ‘yar unguwa, ingidido, dambu da sauransu.

f) Abincin Damawa: Nau’in waɗannan abincin da Hausawa ke amfain da su, su kuma yawancin lokuta dama su ake kafin a yi amfani da su, wato da ruwan zafi ko ɗumi ko nono ko wani abu daban, suma ire-irensu na da damar gaske, ga su kamar haka: kunun kanwa, kunun tsamiya, kunun salala, kunun shinkafa, kunun gyaɗa, kunun dauro, fura da nono, gumba da nono, dambun hatsi da nono, koko/ kamu, tukuɗi, kunun zaranya gumba da ruwan tsamiya, hura/fura da ruwan tsamiya da sauransu.

g) Abincin Toyawa: Abincin da Hausawa suke toyawa na da yawan gaske, akasarin abubuwan da Hausawa suke toyawa a matsayin abincinsu da mai ake amfani wajen toyawa, su ma ga su kamar haka: waina/masa, ƙosai, kifi, kayan ciki, nama, dankali, gyaɗa, ‘yar tsala, fanke, wainar ƙwai, alkaki da sauransu.

h) Abincin Nama: Akwai nau’o’in nama da Bahaushe ke amfani da su a matsayin abinci, sun haɗa da dabbobi na gida da na daji da tsuntsaye su ma da na gida da na daji, kuma Bahaushe na amfani da hanyoyi da dama wajen sarrafa nama face tun daga dafawa da toyawa da gasawa da busarwa da sauransu, bugu-daƙari Bahaushe yana sarrafa nama ta waɗannan hanyoyi kamar haka: Tsire, Kilishi, Balangu, Dambu, Soye, Langaɓu Ragadada, Hanji/kayan ciki, Ganda, Jargi, Banda, Kifi, Ɗanbashino da sauransu.

i) Abincin Dafawa: Ire-iren waɗannan abinci dafa su ake kafin a yi amfani da su, wataran gayansu ake dafawa wani lokaci kuma a na haɗa wa da kayan miya ko wasu ganyaye, misali, ire-iren waɗannan abinci nsun haɗa da: wake-dafa-duka, langaɓu, dafaffen ƙwai, dafaffen rogo, dambun gaisuwa, dambun zogale, shinkafa warwara, shinkafa dafa-duka, shinkafa tuƙe, tuwon hatsi, dawa warwara da sauransu. Fatahiyya, (2009:57-62).

2.1.1 ABINCIN KWARI/ RAFI/ RANI

Wannan shi ma wani rukuni ne da ya danganci kayan abincin da Huasawa kan samu da rafi ko kwari, akwai nau’i-nau’ na kayan abincin da ake sarrafawa wanda daga rafi suke fitowa, amma kuma a wannan lokaci akasarin abubuwan da ake samu lokacin rani a lokacin da mina ma ana samun wasun su, ire-iren waɗannan kayan abincin da ake samu daga rafi sun haɗa da:tumatur, tattasai, albasa, attaruhu, kabewa/kabushi, alayyahu, yakuwa/sure, kuɓewa/guro/yauƙi/yauɗi, karkashi, lalo, barkono, lansir, yalo da sauransu.

2.1.2 ABINCIN TUDU/ DAMINA

Ire-iren irin waɗannan nau’o’in abincin an fi samun su lokacin damuna, kuma a gonakan da suke tudu aka fi yinsu, Hausawa kan sarrafa abincin da ake samowa daga gona don amfanin gida wani lokaci kuma a kai kasuwsa a sayar don biyan buƙatun rayuwa. Nau’o’in wannan ireiren abincin sun haɗa da: hatsi, dawa, masara, maiwa, acca, gumi, wake, gyaɗa, gangala/gujjiya, riɗi da sauransu.

2.2 KAYAN MARMARI

Wannan wani rukuni ne na abincin Hausawa da suka danganci kayan marmari, wanda a zahiri an san su a ƙasar Hausa wanda Hausawa sun juma suna amfani da su a matsayin cimakar marmari, ire-iren abubuwan marmarin ƙasar Hausa suna nan da dama kaɗan daga cikin su sun haɗa da: yalo, gurji, goruba, furan kalgo, aduwa, kurna, magarya, dinya, kanya, ɗinya, zogale, tafasa, yaɗiya, rama, ‘yar anguwa,ingidido, lansir, mangwaro, gwaiba, gwanda, kankana, ceɗiya, bambus, taura, rake, takanɗa, zuma da sauransu.

3.0 MA’ANAR MAGANI

Masana da manazarta da ɗalibai da dama ciki da wajen Hausa sun bayyana ra’ayoyinsu dangane da ma’anar magani. A fagen kare-kai da buƙatun zuciya da cutarwa da warkarwa da camfi ko kiwon lafiya, kalmar magani sananniya ce ga kowane Bahaushe. Dangane da haka ga abin da masana da manazarta suke cewa: Magani shi ne yin amfani da itatuwa ko rubutu ko addu’a ko surkulle, don warkar da wata cuta, ko neman wani amfani, ko gusar da sharri, ko haddasa wani abu saboda biyan buƙata (Alhassan da wasu, 1982:66).

Magani shi ne duk wani abu da za a yi, ko wata hanya, ko kuma wata dabara da ake yi don gusar da wata cuta daga jikin mutum ɗungurungum, ko kuma kwantar da ita don kawo jin daɗi ga jiki ko zuciya da sawaƙa duk wahala da damuwa da sita cutar kan iya haifar (Ahmad, 1984:6). Magani hanya ce ta neman kawar da cuta ko wace iri, ko kuma neman kariya daga gareta ko kuma neman gwanewa da ƙwarewa kan wani abu (Ingawa, 1984;25).

Magani shi ne duk wani abu da ɗan’Adam kan yi don samun warkarwa da buƙata da ɗaukaka a rayuwarsa ta kullum. Don kuwa ɓangaren rayuwar ɗan’Adam duk tafiya take wajen fafitikar neman maganin warkewa daga cututtuka da kwantar da damuwar zuciya, in ya samu, sai kuma ya shiga neman maganin ɗaukaka da kariya wajen abokan hamayya. Haka kumarayuwar ɗan’Adam take tafiya kullum. Inya yi maganin wannan yana buƙatar maganin wancan (Tukur, 1988:14-15).

Magani wata hanya ce ta warkar da ko kwantar da ko rage wata cuta ta ciki ko ta waje ko wadda aka samu ta haɗari. Ko neman kariya ga cuta ko abokan hamanyya ko neman ɗaukaka ta daraja ko ta buwaya ta hanyar siddabaru da sihirce-sihirce na ban al’ajabi, Bunza, (1990:134). Bunza, (1995) ya yi ƙoƙarin fito da nasu ra’ayi a kan ma’anar magani.

Wannan ma’ana da wannan shehin malami ya ba wa maganin gargajiyar Bahaushe ta fito da cikakkiyar ma’anar magani a sarari, don kuwa a kan ma’anar magani, an feɗe biri har jela.Hakan yana nuni ne cewa ‚Magani‛ kalma ce mai iya ɗaukar maana mai faɗi. Magani shi ne duk wata hanya da za a yi amfani da ita domin rage kaifin cuta ko rage raɗaɗinta ko kawar da ita gaba ɗaya ko walware wata matsalar rayuwa. Irin wannan hanyar tana iya zama ta kimiyar zamani ko gargajiyar Bahaushe, misali; Bori da jiƙo da tsafi da duba da tsubbu da siddabaru da bokanci da dai duk wata hanya da al’umma take bi don neman magani. Kalmar ‚magani‛ ba hatsin bara ba ce Hausa ce babu wani alamun aro a ƙirarta ko furucinta. A fagen nazari masana da manazarta da ɗaliban al’adun Hausawa sun kawo ra’ayoyi mabambanta dangane da ma’anar wannan kalma kamar haka:

Magani shi ne duk wani abu da za a yi, ko wata hanya, ko kuma wata dabara da ake yi don gusar da wata cuta daga jikin mutum ɗungurungum, ko kuma kwantar da ita don kawo jin daɗi ga jiki ko zuciya da sauwaƙa duk wahala da damuwa da ita cutar kan iya haifar Adamu, (1983).

Wannan ma’ana an yi ƙoƙari, amma ba ta shafi wasu magunguna da ake amfani da su wajen cutarwa ba, misali, kamar; karya tambaya, ko kurciya, ko sammu, ko haukatar da wani da dai sauransu. A ra’ayin mai nazari, magani na nufin duk wata hanya da za a bi a sami sauƙi ko waraka ga jiki ko zuciya muddin ba ta saɓawa addini ko al’ada ba, shi ne magani.

4.0 MASU BAYAR DA MAGUNGUNAN GARGAJIYA

Hausawa mutane ne da ba su da wata hanya ta rubutu da karatu sai da suka fara cuɗanya da al’ummomin duniya. Yahaya, (1988:8). Yadda Hausawa suka samarwa kan su hanyoyin rayuwa tun a jiya. Haka, suka samarwa kan su hanyoyi waɗanda suke amfani da su wajen warkar da cututtukan da ke tattare da su.Waɗannan cututtukan da ke addabar Hausawa su ne suka haifar da samuwar addinin gargajiya a wancan lokaci, Abubakar, (2006:19). A da idan wani yana fama da wata cuta da ta ƙi-ci-ta-ƙi cinyewa sai aka samu wani ya ba da shawara ko magana da ta gusar da wannan cutar, daga nan wannan mutumin ya zama abin tsoro da girmamawa. A ganin mutanan da wannan mutum yana da alaƙa da mutanan ɓoye, wato su ne suka samar da shi magungunan da yadda za a yi amfani da su. A ganin wasu Hausawa mutanen ɓoye ke sanya wa al’umma cututtuka, Abubakar, (2006:59-60).

Masu ba da magani a ƙasar Hausa sun haɗa: Bokaye da ‘Yan bori da Magori da ‘Yar mai ganye/ɗan mai ganye da Malam Tsibbu da masu sana’o’in gargajiya.

4.1 BOKA

Kowane Boka mai ba da maganin Iskoki ɗan Bori ne, amma ba kowa ne Bahaushe ne ɗan Bori ba, idan Bahaushe ya ƙira mutum ɗan Bori abin kan ɗauki fassarori da dama, daga cikinsu akwai ƙarancin hankali ko rashin natsuwa ko rawar kai ko bokanci da makamantansu (Bunza, 2005: 5).

Daga cikin masu magunguna a ƙasar Hausa waɗanda suka san cuta da magani akwai Boka, kuma shi ne likita a ƙasar Hausa. Kuma shi Boka an kasa su gida uku kamar haka:

Babban Boka: Shi ne babban masanin cututtuka da kuma magunguna iri-iri yana bayar da magunguna na cutar sarari da ta ɓoye, yana warkar da ciwo kowane iri, yana yin duba, yana magana da Aljanu da dai sauransu. Kuma ba ya yawo har gida ake zuwaana tarar da shi.

Boka Ci Kaji: Shi wannan darajarsa da kwarewarsa ba takai na farko ba, kuma ƙarfin ayyukansa da saninsa maganinsa bai kai na farko ba, don haka shi ya kan zaga daga wannan gari zuwa wancan, kwana biyu uku sai ya yi gaba. Kuma yana yawan ambaton a kawo kaza baƙa ko fara ko wake-wake da dai sauransu. Kuma a mafi yawan lokaci ya fi hulɗa da mata.

Boka Ba-Ni-Tsaki: Shi kuma shi ne ƙarami duk a cikinsu, kuma shi mai neman abinci ne, yana zaga gari ya kirari cewa ga Boka ya iso in da mai tambaya, ya kan bayar da maganin farin jini da mallaka da ɗan mannau ga mata, kuma ya bayar da kwarjinin da gagai da maganin basur ga maza. A mafi yawan lokaci maza sukan bayar da ɗan abin hasafi mata kuwa sukan ba shi nɗan tsaki ko goro (Adamu, 1998: 28-29).

4.2 ‘YAN BORI

‘Yan Bori su ma suna cikin masu warkar da marasa lafiya (Bunza, 1995, da Adamu, 1998). Sakamakon hulɗar da take gudana tsakaninsu da Aljanu musamman muyagun Aljanu da kan haddasa ciwon hauka.Sukan ba da magani ne ta hanya girka. Wato a kore shaiɗanun Aljannu a bar masu kyau kan mutum. A wajen ‘Yan Bori ne akan samu maganin farfaɗiya da daji da shan Inna da baƙon dare da rashin haihuwa da sauransu. Wushishi, (2011:52).

4.3 MAGORI

Hausawa kan yi masa kirari da cewa, “Magori wasa kanka da kanka, magori jikan Ladi, ci kaji magani sai Allah, magani sai da gwaji, magani ɗari ɗaya babu, da sauransu. Magori na nufin Boka mai sayar da magunguna na gargajiya iri-iri kamar na sammu ko na rashin lafiya da sauransu, Ƙamusun Hausa, (2006:317). Magori ya san wasu da ga cikin cututtuka da magunguna kuma yawo yake yi yana tallar magungunansa kwararo-kwararo unguwa da ƙauyuka da kasuwanni da garuruwa yana tafe yana wasa ko koɗa kansa da kansayana kirari.

4.4 ‘YAR MAI GANYE

Asalin ‘yar mai ganye ɗiyar maguzawa ce masu ɗaura ganye a kwankwaso don rufe al’aura Bunza, (1995).Matan da suka yi gadon bayar da magani daga iyayensu su ne ake ƙira ‘yar mai ganye. ‘Yar mai ganye Bokar mata ce kuma takan nemo tsirraa ne da sassaƙe-sassaƙe da ganyaye ta zaga cikin gari tana tallar magunguna, Wushishi, (2011:53). Akwai kuma ɗan mai ganye shi kuma namiji ne mai tallar magani a kwando amma mafi yawa an fi samun su wuri ɗaya, musamman kasuwanni za a tarar ya baza magunguna kamar sassaƙe da saiwowi da ganyaye da kauci da sauransu, Adamu, (1998).

4.5 MALAMAN TSIBBU

Kalmar Tsibbu asalin ta daga Larabci aka aro ta, wato “ɗibbi” ma’ana magani, “ɗibib” kuma na nufin mai magani. Tsibbu wani nau’i ne na magani da Hausawa suka aminta da shi bayan saduwarsu da addanin Musulunci saboda haka kalmar tsibbu na nufin magani da ya keɓanta da malamai zuwa ga buƙata a lafazance ko a rubuce da za a sarrafa shi a al’adance ko a addinance domin biyan wata buƙata, Bunza, (2004). Tsibbu ko tsubbu na nufin magani ta yin rubutun sha ko duba ko surkulle, Ƙamusun Hausa, (2006:459).

4.6 MASU SANA’O’IN GARGAJIYA

Akwai rukunin al’umma da dama da suke aiwatar da sana’o’i daban-daban don biyan buƙatun kansu da al’ummar da suke tare da su, masu sana’o’in gargajiya na Hausawa da suke ba da magani ko magungunasun haɗa: Maƙera da Masunta da Wanzamai da Majema da Mafarauta da Mahauta da Maɗaura da Ungozoma da sauransu. Duk waɗannan da aka ambatoa sama suna ba da magani ga al’umma wani lokaci kuma ga kansu, misali, duk wanda ya tashi yiwa yaro kaciya da kuma son ta warke da wuri to Wanzami zai nema, in kuma ƙayar kifi ta maƙalewa wanzami shi kuma masunta zai nema, in kuma wuta ta ƙona masunci shi kuma maƙera zai nema, in kuma maƙeri ya taka ƙaya mafarauta zai nema, in kuma mafarauci matarsa haihuwa ta gabato ungozoma zai nema, in su dukkansu suka nemi ɗaukaka kan sana’o’insu da neman farin jini to malaman Tsibbu za su nema.

5.0 MA’ANAR CUTA

Masana da manazarta da ɗaliban al’ada sun yi bayanai mabambanta kan ma’anar cuta. “Cuta wani yanayi ko wani abu da zai matsa wa rai ko ya kawo rashin gamsuwa ga rayuwa” Hamza, (1977:3). A cikin ƙamus na Kirt, (1981:480) ya yi nuni da cewa cuta na nufin, “Jin yamutsar zuciya na buƙatar yin amai, ko rashin jin daɗin jiki na rashin lafiya ko ciwo shi.” Ahmad, (1984:5) ya bayyana cuta da cewa “Wata aba ce wadda ta shafi sha’ani wato yanayin raunana da kawo rashin jin daɗi.”

Shi ko Bunza, (1990:132) cewa ya yi “Cuta wata damuwa ce da ta shiga jikin Ɗan Adam domin raunana lafiyarsa ko kuma ta damu zuciyarsa ta fuskar buƙatunsa na jin daɗi ko ɗaukaka darajarsa da sauransu.”  

Dangane da wannan ma’anoni da masana da manazarta suka bayar dangane da ma’anar cuta, cuta na nufin cewa kasantuwar wani raɗaɗi ko rashin jin daɗin jiki ko gazawar aikin wata halittar wani sashi na jikin ko kuma damuwa a zuciyar Ɗan Adam.

Ra’ayin Manazarci, cuta na nufin duk wani abu da zai ƙuntatawa jiki ko zuciyar ɗan Adam ko dabba, ya hana su sakat ko walwala ita ce cuta.

5.1 IRE-IREN CUTUTTUKA

Akwai ire-iren cututtuka da dama a ƙasar Hausa waɗanda tun fil’azal Bahaushe ya san da su kuma yana ƙoƙarin magance su. Adamu, (1998:5-7) ya bayyana ire-iren cututtuka kamar haka:

(i) Cuta ta sarari (jiki) inda ya nuna cewa “Cutar sarari, ita ce kan samu sakamakon gazawa ko mutuwar wata halittar jiki har ta daina aikin da aka san ta da shi gaba ɗaya ko kuma samuwar wani rauni na hatsari wanda zai kawo fitar jini ko kumburi ko karaya ko makamantansu wanda hakan zai sa ruɗewar gangan jiki da raɗaɗi ko zogin da zai sa rashin lafiya”. Hakan yana nuna cewa ke nan cututtukan sarari su ne irin waɗanda ido yake iya gani har a taɓa kai tsaye kuma a magance shi.

(ii)Cuta ta ɓoye (zuciya)ita wannan cuta ita ce wadda take kawo halin damuwa da rashin kwanciyar hankali ga Ɗan Adam kan shiga sanadiyar wani tunani mai zurfi a zuci. Cutar ɓoye takan kama mutum ne yayin da halin zamantakewar rayuwarsa ta gamu da tsananin tunani kishi ko tsoro ko sha’awa ko soyayya ko ƙiyayya ko hassada. Dukkan ɗaya daga cikin waɗannan dalilai sukan sabbaba rashin jin daɗi a zuciya mai fama da irin waɗannan cututtukan har ya kai ga tashin hankali da zai hana shi ci ko sha da barci sai yawan zullumi. Mutum ya rame wani lokaci har abin ya yi sanadiyar salwantar rayuwarsa.

Abin lura a nan a iya cewa cuta dai iri biyu ce wato da ta sarari da ta ɓoye. Sakamakon hakan za a iya ba wa kowace cuta suna ko laƙabin da ya dace da ita dangane da raɗaɗi ko illa ko irin wurin da ta kama daga sassan jikin ɗan Adam. 

6.0 ABINCI A MAHAƊIN MAGANIN CUTARWA

Lokuta da damar gaske Hausawa kan haɗa magani ba don komai ba sai don cutarwa. Ireiren irin waɗannan magunguna ana aiwar da su domin cutar da mutum ko mutane don cimma wani buri na rayuwar yau da kullum, wasu kan ƙira shi da ‚Magungunan sharri‛. Sarkin Gulbi, (2013:747). Ire-iren irin waɗannan magungunan da ake haɗawa da abinci don cutarwa sun haɗa da; sammu da kashe azzakarin namiji da mallake miji ko wani abu daban da kurciya da kashe wani ko wasu mutane ko jama’a da sauransu. Yawancin lokaci ana neman irin waɗannan magunguna ne don sharri na karya abokan hamayya ko mallake miji, a yi amfani da abinci a mahaɗin magani don cutarwa. Yawanci lokaci guba da yadda ake haɗa ta amfi amfani da abinci.

Bahaushe ya yi imani akwai Sammu kuma yana ganin idana abinci aka sa shi za a sa shi ga abin da aka fi marmari kamar Goro, ko Taba, ko kayan marmari, da dai sauransu ire-iren su. Idan aka yi wa mutum sammu yan iya lalacewa ko in ma mai basira ne ya zama dolo, ko in jarumi ne ya zama raggo, ko in mai ladabi ne ya zama sakarai, ko in ɗan sarauta ne ya zama ɓarawo, ko in malami neya zama fajiri, ko in tajiri ne ya zama talaka da dai makamantansu, Bunza, (2006:49).

6.1 ABINCI A MAHAƊIN MAGANIN KARE KAI

Hausawa sun jima suna amfani da abinci matsayin mahaɗin magungunan kare kai daga wata cuta kafin ta wakana ko ta auku, shi ya sa ma suke da karin magana mai cewa ‚Riga kafi ya fi magani‛. Magungunan kare kai shi ne, duk wani magani da za a nema gabanin aukuwar wata cuta ko wani haɗari ko bala’in da ake zaton zai auku wanda hakan zai iya kawo wata illa ga rayuwar mutum ko dabbba ko dukiya ana kiransa kariya, Ahmed, (2011:27). Magungunan kariyar kai, magunguna ne da Hausawa suka tanada domin kariyar kowace irin cuta daga kan su. Irin waɗannan magunguna sun haɗa da na baduhu da sagau da na kariyar haɗarin mota, da magani gobara, da na cizon kunama, da na sarar maciji, da na ƙarfe, da kahin gida ko gona (hana sata) da ɗaurin baki da sauransu. Sarkin Gulbi, (2013:748). Misali, cizon kunama da sarar miji da riga kafin kamuwa da wata cuta da ƙarfe duk ana amfani da abinci a mahaɗin waɗannan magungunan ko a barbaɗa garin magani akan abinci ko kuma a haɗa da abinci a ci don magani. Yawancin magungunan Tauri ko Ƙarfe itatuwa ne da saiwowi da ganyayen magani da ke tsumawa ko a tafasa ko a jiƙa domin sha, ko wanka, ko shafawa, wasu lokuta kuma akan haɗa magungunan guri guda a daka ya zama gari a riƙa shan sa a ruwa ko nono ko kuma a salala.

Salala, na nufin kunu ne da ake damagarin gero ko maiwa ko dawa da ruwan magani na sassaƙe ko saiwoyi. Ana dama shi yadda ba zai yi kauri ko kuma ya yi tsarara ba. Ana shan sa kamar kunu (Kura, 2011:111).  

6.2 ABINCI A MAHAƊIN MAGANIN BIYAN BUƘATUN ZUCIYA

Zuciya ita ce tsokar da ke wakiltar mutum kacokan ɗinsa, don haka duk wani adawa ko kishi ko ƙiyayya ko soyayya ya danganci abin da zuciya ta rayawa mutum ko ta karkata. Bahaushe yana amfani da abinci a matsayin mahaɗin magungunan biyan buƙatun zuciya. Ire-iren magungunan biyan buƙatun zuciya, waɗanda suka haɗa da; magungunan haɗa soyayya da raba ta, magungunan samun dukiya, ko mulki, ko aure ko cin nasarar wani abu, ko farin jin da sauransu. Ire-iren waɗannan buƙatu na ɗan Adam ba ciwo ne ya shafi zuciyar mutum ba, kuma ba wani zogi ko zafi yake ji ba, illa abubuwa suna cin zarafin tunaninsa har su taɓa birnin hankalinsa idan ba a tashi tsaye aka warkar da su ba, Bunza, (1995:102). Hausawa suna amfani da abinci a mahaɗin maganin biyan buƙatun zuciya musamman kamar haɗa soyayya da raba ta ko neman aure da raba shi, akwai wani magani da matan Hausawa suke amfani da shi wajen mallakar miji mai suna bi-ta-zaizai wanda a abinci ake zubawa miji ya ci, haka ma samari sukan karɓi magani su zubawa budurwa abinci don taso su.

Farin jinin jama’a ake nema ma’aska sukan ce a nemo sassaƙen itacen farin ɓaure a daka shi a shanya. In ya bushe a sake dakawa a samu gari. Sai a riƙa shan shi da nonon farar Bafillata (Wushishi, 2011:140).

6.3 ABINCI A MAHAƊIN MAGANIN WARKARWA

A wannan ɓangaran magungunan da suka shafi warkarwa sune magungunan da ake yi domin a kawar ko magance ciwo ko cuta da ake ji ko gani da ke jikin mara lafiya da kuma waɗanda ba a iya gani sai jin zogin su. Magungunan warkarwa su ne magungunan da ake yi a warkar da cututtukan da ake iya gani a jikin mutum dangin ƙurji ko gyambo, ko kumburi da kuma raunin da ake samu a jiki,…. da kuma waɗanda ba a iya gani sai dai a ji raɗaɗinsu ko a ga alamun kamuwarsu ta hanyar kumburi ko rama ko hana gudanar da al’amura, Sarkin Sudan, (2000). Hausawa suna amfani da abinci a mahaɗin magungunan warkarwa, misali; wanda mazakuntarsa ta samu rauni akan ba shi irin waɗannan magunguna ko ya sha a kunu ko ya ci da nama ko a abinci da waɗanda rana ko basir ko ɗankanoma ke damu duk ana ba su ire-iren waɗannan magunguna kuma yawancinsu mahaɗin su abinci ne. Ga abin da Mai Salati kan ce:

Mace da take samun ciki yana lalacewa sai ta nemi waɗannan abubuwa kamar haka: 1. Garin zogale gwangwani uku 2. Raiɗaure gwangwani uku 3. Garin habbattusauda shi ma haka, sai ta cakuɗa a guri ɗaya sai ta sha cokali ɗaya da safe cokali ɗaya da rana cokali ɗaya da daddare a Kunu ko Koko (Mai Salati, 2012:12).

Maganin farin jinni ba baƙon abu ba ne ga Hausawa, don kuwa lokuta da damar gaske za a ji Magora suna yawo kwararo-kwararo da lungu-lungu suna ba da maganin farin jinni ga ‘yanmata da samari da ma sauran mabuƙata.

7.0 KAMMALAWA

An yi tsokaci kan abinci da ire-irensa da ma’anar magani da amfani da abinci a matsayin kayanhaɗin magani ga Bahaushe. Hausawa sun jima suna amfani da abinci a matsayin mahaɗin magungunansu na gargajiya, wanda har ya zuwa yau ba su saki al’adarsu na amfani da abinci a mahaɗin magani ba sai dai ma abi ya ci gaba, duk da sauye-sauyen zamani da ya yi tasiri a rayuwarsu ta yau da kullum ba nau’in abincin da Hausawa ba sa amfani da shi a matsayin mahaɗin magungunansu da suke tattare da don cutarwa ko warkarwa ko kare kai biyan buƙatun zuciya da ba a haɗa shi da abinci a matsayin mahaɗi don biyan buƙatar rayuwa, ire-iren abincin da Hausawa su ka fi amfani da a mahaɗin magungunansu sun haɗa da; kunu da nama dakifi da fura/hura da miya ko abincin kansa da kayan marmari duk ana amfani da su a mahaɗin magani a ƙasar Hausa.

Manazarta

Abraham, R.C (1976). Dictionary of the Hausa Language, Second Edition. London. Hodder and Stoughton.

Abubakar, R.U. (2006). “Camfi Surkullen Masu Bayar Da Magunguna A Ƙasar Hausa” Kundin Digirin Farko Jami’ar Bayaro Kano.

Adamu, M.T. (1983). Asalin Tsubbu Yaɗuwarsa Da Tasirinsa a Ƙasar Hausa B.A Dissertation B.U.K.

Adamu, M.T. (1998). Asalin Magungunan Hausawa Da Ire-irensu. Kano: Ɗan Sarkin Kura Publishers Ltd.

Ahmad, A. (1984) ‚Cututtukan Ciki Da Magungunansu‛. Kundin Digirin Farko. Kano: Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

Ahmad, S. A. (2011)‚ Gurbi Kwari a Magungunan Gargajiya na Hausa‛ Kundin M.A

Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.

Alhasan, H. Da Wasu, (1988). Zaman Hausawa 2. Lagos: Islamic Publishers Bureau.

Bunza, A. M. (1995)‚ Magungunan Hausa A Rubuce: (Nazarin Ayyukan Malaman Tsubbu)‛. Kundin Digiri Na Uku, Kano: Sashen Koyar Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

Bunza, A. M. (1999). Hayaƙi Fid da Na Kogo Nazarin Siddabaru Da Sihirin Hausawa‛. Kundin Digiri Na Biyu, Sashen Harsunan Nijeriya, Kano: Jami’ar Bayero.

Bunza, A.M. (2004). “Mahaɗin Magungunan Gargajiya” Maƙala, Sashen koyar Da Harsunan

Nigeriya Jami’ar Bayaro Kano.

Bunza, A.M. (2006). Gadon Feɗe Al’ada. Lagos: Tiwal Nigeria LTD.

CNHN (1979). Sabon Ƙamusun na Hausa Zuwa Turanci, Ibadan University Press, Limited.

CNHN (2006). Ƙamusun Hausa, Zariya: Ahmadu Bello University Press, Limited

Fatahiyya, I. A. (2009)‚ Cimakar Hausawa Ta Gargajiya Yanaye-Yayaneta Da Amfaninta A Rayuwar Hausawa‛. Kundin Digiri Na Biyu, Sashen Harsunan Nijeriya, Kano: Jamiar Bayero.

Gusau, S.M. (2008). ‚Jirwayn Cimakar Hausawa A Waƙoƙin Baka Na Hausa‛. Maƙalar da aka gabatar a taron ƙara wa juna sani tsakanin Jami’ar Bayero, Kano da Jami’ar Warsaw Ta Ƙasar Poland.

Hamza, M.W. (1986). “Kamancin Cuta Ko Buƙata Da Yanayin Mahaɗin Maganinta A

Magungunan Hausa”. Maƙala da aka gabatar a Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya, Jamiar Bayero, Kano.

Ingawa, Z.S. (1984). Magungunan Hausa Don Mata‛, Kundin Digiri Na Farko. Kono: Sashen

Koyar Da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano.

Kirk, P. (1981). Chambers Dictionary, Edinburgh.

Kura, G.Y.M. (2011). Dalilin Samuwar Waɗansu Cututtuka Da Maganinsu A Bahaushiyar

Al’ada‛.Kundin Digiri Na Biyu. Kono: Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya, Jamiar Bayero, Kano.

Mai Salati, A. (2012) Ciwon Sukari. Kano: Nuru Computer Graphics.

Sarkin Gulbi, A. (2013). Hanyoyin Tsafe-Tsafe Domin Magani A Al’ummar Hausawa, in Studies Hausa Language, Literature and Culture, 1ST National Conference, Held At Mambayya House, Bayero University, Kano, Between 14TH-16THJanuary, 2013.

Sarkin Sudan, I.A. (2000). Tasirin Magani Da Warkarwa A Cikin Rubutattun Ƙagaggun

Labarun Hausa‛. Kundin digiri na biyu Jamiar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.

Tukur, A. (1988). Nazarin Cututtukan Da Suka Shafi Fatar Jiki Da Magungunansu A

Bahaushiyar Al’ada‛. Kundin Digirin Farko. Kano: Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano.

Wushishi, S.S. (2011). Dangantakar Magani Da Wasu Sana’o’in Gargajiya Na Hausa‛ Kundin Digiri Na Biyu Sashen Harsunan Nijeriya, Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

Yahaya, I.Y. (1988) Hausa A Rubuce: Tarihin Rubuce-Rubuce Cikin Hausa. NNPC, Zaria.

Yobe Journal - Volume 5

Post a Comment

0 Comments