𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum, Malam, ina da tambaya, da gaske ana ganin Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) a zahiri (ido da ido) ko ba a ganinsa sai a mafarki?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikumussalam
warahmatullahi wabarakatuh.
Malamai sun kasu
kashi biyu akan maganar ganin Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam) a
zahiri (ido da ido) bayan komawarsa ga Ubangiji:
1. Mahangan Mafi
Yawan Malaman Sunnah (Jamhur): Mafi yawan malamai (kamar su Ahlus Sunnah wal
Jama'ah) suna ganin cewa ba zai yiwu a ga Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) a
zahiri (ido da ido) a duniyar nan ba bayan rasuwarsa. Hujjojinsu sun haɗa da: Annabi
(Sallallahu Alaihi Wasallam) ya rasu kuma yana rayuwar Barzahu, kuma babu wani
matattu da yake dawowa duniya ko fitowa daga kabarinsa kafin Ranar Alkiyama.
Sahabbai (kamar su Sayyidina Ali, Nana Aisha, da sauran su) sun fuskanci manyan
fitintinu da matsaloli bayan rasuwarsa, amma babu wani daga cikinsu da ya taɓa cewa ya ga Annabi
(Sallallahu Alaihi Wasallam) a zahiri domin ya tambaye shi mafita.
2. Mahangan Malaman
Sufaye (Musamman Dariku): Wasu masana da malamai na ɓangaren Sufaye (kamar
su Tijjaniyya) suna ganin cewa zai yiwu a ga Annabi (Sallallahu Alaihi
Wasallam) a zahiri (ido da ido) a farke. Suna dogara da: Fassarar hadisin nan
dake cewa: "Wanda ya ganni a mafarki, zai ganni a farke..." (ko kuma
a wata sifar: kamar ya ganni a farke). Suna fassara "farke" a nan da
cewa mutum zai iya ganinsa a zahiri a nan duniya. (A ya yin da sauran malamai
kuma suka fassara "farke" da cewa ma'anarsa mutum zai ganshi ne a
ranar Alkiyama).
Ganin Annabi
(Sallallahu Alaihi Wasallam) a mafarki tabbataccen abu ne a fadin Manzon Allah
(Sallallahu Alaihi Wasallam) da kansa. Amma ganinsa a zahiri (ido da ido) a
farke bayan rasuwarsa, abu ne da malamai suka yi saɓani akai, inda mafi
yawan malamai suka ce hakan ba zai yiwu ba.
A takaice: ba a ganin
Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ido da ido, amma ana iya ganinsa amafarki,
nankuma sai wanda yake da ilmin sanin siffarsa "ka karanta shama'ilil
muhammadiyya, in sha Allahu, idan ka ganshi zaka gane shi"
Qarya ne mutum ko
waye shi yazo yace wai ya haɗu da Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ido da ido,
yabashi wata ibada wadda bai baiwa sahabbansa ita ba, Wannan kam qarya ne komai
girman mutum munce qarya yakeyi tinda har rikici yafaru tsakanin sahabbai (Radiyallahu
anhum) Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ko sau ɗaya be taɓa bayyana yace wane
shine akan daidai ba, wane ba akan gaskiya yake ba, to damme wasu zasuce wai
har sun gashi a zahiri. shin kun taɓa ji Aisha (Ra) da aka bunne Annabi
(Sallallahu alaihi wasallam) a ɗakinta tace yataso ya gayamata wani abun?
Shin meya sa Annabi
(Sallallahu alaihi wasallam) bai bayyana ya warware matsalar data faru tsakanin
Mu'awiya (Ra) Da Imamu Ali (Ra) ba, meya sa bai bayyana ba?? Kenan Masu qaryan
cewa sunga Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) a zahiri qarya suke ba Annabi
(Sallallahu Alaihi Wasallam) suka ganiba.
Kwanakin nan naga
wata wai Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) yazo ɗakinta cikin dare
harma yabata Alqur'ani kuma wai mijinta bai ganshi ba sai ita kaɗai ce ta ganshi.
Abunda muke tambaya
wai meya sa baya zuwa da rana se daddare?? Kunga Wannan ai Iskancine da raina
hankulan jahilai saboda haka ba a ganin Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) a
Fili ido da ido Amma ana iya ganinsa a mafarki. Ganin Annabi (Sallallahu Alaihi
Wasallam) na gaskiya a bayyane yana nan sai a ranar Alkiyama da kuma cikin
Aljanah.
WALLAHU TA'ALA A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa
Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
Wallāhu Taʿālā Aʿlam — And Allah knows best.
Zauren Fatawoyi Bisa Alƙur’ani da Sunnah.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.