Citation: Dalha, I., & Sani, A.-U. (2026). Bitar tasirin Musulunci a kan tsarin sarautar Hausawa. ƊEGEL: Journal of the Faculty of Arts and Faculty of Arabic and Islamic Studies, 22(1), 103–113. https://doi.org/10.57233/djfafais.2026.v22i01.011
BITAR TASIRIN MUSULUNCI A KAN TSARIN SARAUTAR HAUSAWA
Daga
Ibrahim Dalha
Department of Nigerian Languages and Linguistics,
Sule Lamiɗo University Kafin-Hausa, Jigawa State
Email: ibrahimdalha1@gmail.com
Phone: 08060574254
Da
Abu-Ubaida SANI, Ph.D.
Department of Languages and Cultures,
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Email: abuubaidasani5@gmail.com | official@amsoshi.com
ORCID: https://orcid.org/0000-0001-6447-4334 |
WhatsApp: +2348133529736
Tsakure
Manufar wannan takarda ita ce fito da cigaban da addinin
Musulunci ya kawo dangane da abin da ya shafi siyasar mulkin Hausawa ta
gargajiya. Binciken ya samu zarafin bibiyar wasu daga cikin ayyukan da suka
danganci tsarin sarautar Hausawa da kuma waɗanda suka kalli wasu ɓangarori na Musulunci. Takardar ta fi bayar da ƙarfi a kan hira da
karance-karance da kuma sauraren fasahohin Hausawa da suka danganci adabi a
matsayin tushen bayanai. Wannan dalili ne ya sa aka yi garkuwa da wasu waƙoƙin baka musamman na fada a
matsayin wata kafa da ta haska hoton yanayin tsarin sarautar Bahaushe ta
gargajiya. An yi amfani da Ra’in Sassarƙuwar Al’adu (Cross-Cultural Theory) wanda
Edward Twitchell ya assasa a shekarar 1959 a matsayin jagora ga nazarin.
Takardar ta samu nasarar gano sakamakon bincike guda biyar waɗanda suka haɗa da: Tsarin sarautar Hausawa ya yi gwagwarmaya a matakai
daban-daban, inda ya fara daga lokacin jahiliyya zuwa zamanin da aka samu
wayewar kai ta addinin Musulunci. Hausawa sun daɗe suna zama a ƙarƙashin shugabanci, don haka suka yarda da
gabaci tun kafin su karɓi addinin Musulunci. Wannan
dalili ya sa lokacin da addinin Muslunci ya zo musu da tsarin shugabanci,
lamarin bai zamo baƙo a gare su ba.
Fitilun
Kalmomi: Musulunci,
Sarauta, Bahaushe, Shugabanci, Jagoranci
1.0
Gabatarwa
Tun tsawon zamani, Hausawa mutane ne da suka aminta da
bin tsarin shugabanci a zamantakewarsu. Wannan ne ya sanya lokacin da addinin
Muslunci ya zo musu da tsarin shuganaci, lamarin sai ya zamo abin da Bahaushe
yake cewa: “An tashi daga kan faƙo, an koma kan daɓe.” A wata fahimta da ta so cin karo da wannan, aikin
Mu’azu (2013 shf. 19-20) ya nuna cewa, a lokacin da Bahaushe yake Maguzanci ba
shi da wani tsari na mulki ko wata shari’a ko kuma wani hukunci tabbatacce. Ba
su da alƙalai
da dogarai da gidajen kurkuku. A lokacin abin da suke yi shi ne idan wani ya
zalunci wani ko ya kashe shi, to sai ‘yan’uwansa su taru su rama masa. Suna iya
rama masa da ƙarfi ko ta hanyar tsafi[1].
A fahimtar Abdulƙadir, (2011 shf. 478) kuwa, tun tuni Bahaushe
yake da tsarin shugabanci na ƙashin kansa. Tsarin ya kasance mai tafiya tare da
shugabannin sana’o’i da na bauta ba. Sarakuna a kowane gari sun bai wa
shugabannin sana’o’i da manyan bokaye da jarumai tare da dattijan gari matsayi
na musamman wajen gudanar da mulkinsu[2].
Duk da cewa, tunanin Hausawa da imaninsu a wancan lokacin yana takun-saƙa da na Musulunci, akwai
wasu abubuwa da dama da aka amfana da su. Sau da dama ana yi wa tsarin sarautar
gargajiyar Bahaushe ta jiya kallon yanayi na duhun kai da jahilci. An manta da
cewa, zama cikin duhun kai na jahiliyya ba sabon abu ba ne, musamman idan aka
waiwayi tarihin al’ummun Romawa da Girkawa da kuma Larabawa. Su ma sun tsinci
kansu cikin wannan yanayi. Duk da cewa Hausawa sun ce: “A daina tuna baya, wai
in ji gyartai da ya ci sarauta.”
1.1 Fashin Baƙin Fitilun Kalmomin Taken
Bincike
Ƙoƙarin wannan takarda na fayyace tasirin addininin Muslunci
a cikin tsarin sarautar Bahaushe ta gargajiya, yana buƙatar a bayyana muhimman
kalmomin da suka gina takenta. A wannan muhalli ne aka bayyana ma’anonin
kalmomin ‘tasiri’ da ‘Musulunci’ da ‘sarauta’ da kuma ‘Bahaushe.’
1.1.1Tasiri
A wannan bincike, kalmar tasiri tana nufin mamayar da
addinin Musulunci ya yi wa tsarin mulkin Bahaushe na gargajiya, inda sannu a
hankali ya sauya daga yadda aka san shi a baya. Wani abin armashi shi ne,
wannan ma’ana zaren tunaninta ya dace da wadda CNHN, (2006 shf. 431) ya bayar,
inda ya bayyana kalmar tasiri da ma’anar, “Muhimmanci ko dangantaka ko ƙarfi."
1.1.2 Musulunci
Kalmar Musulunci an samo ta ne daga harshen Larabci. Tana
da ma’anar aminci. Don haka idan an ce, addinin Musulunci, ana nufin addinin
zaman lafiya. CNHN (2006 shf. 353) da Bunza, (2022 shf. 2) sun yi ittifaƙi a kan cewa Musulunci shi
ne: “addinin da Musulmai suke bi na bauta wa Allah shi kaɗai, babu tarayya da shi, kuma Annabi Muhammadu Manzonsa
ne, d.s.”
Sani da wasu (2023 sh. 499) sun bayyana cewa: “Musulunci
na nufin sauƙaƙƙen addini da ya shafi
shika-shikan imani shida: Imani da Allah da manzanninsa da mala’ikunsa da
littattafansa da ranar ƙiyama da kuma ƙaddara mai kyau ko mummuna, wanda kuma ya
ginu a kan ginshiƙai guda biyar: Imani da Allah da salla da azumi da zakka
da aikin Haji ga wanda ya samu iko, tare da gudanar da bauta da zamantakewa da
hulɗa da tunani da duk sauran ayyuka bisa
koyarwar saukakken littafin ƙarshe (Alƙur’ani), da sunnar manzon ƙarshe (Muhammadu (tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shi)) da ijima’in malamai.”
1.1.3 Sarauta
Sarauta kalma ce da take ɗaukar matakai guda biyu a tsarin ginin kalmomi a mahangar
masana harshe. Farko, kalmar tana ɗaukar matsayin kumbura,
inda takan samar da jam’i da jinsi. Misali,
a. Sarki (namiji tilo)
b. Sarauniya (mace tilo)
c. Saraki/sarakuna (jam’i)
Haka kuma, tana komawa matsayin tsira, inda take samar da
kalmar aikatau daga suna. Misali, kalmar sarki mai ma’anar suna, takan tsira ta
koma “sarauta” wadda take nuna aikatau, wato gudanar da mulki. Fasihan mawaƙan Hausa sukan sarrafa
kalmar a cikin waƙoƙinsu. Makaɗa Musa Ɗanƙwairo yana cewa:
Jagora: Sarautar da babu
Alkali ba Yari,
: Babu
Majidaɗi ba Makama,
: Na
ji mutane suna ta cewa,
Yara: Wagga sarauta wacce iri
ta.
Gindi: Maisulken faɗa ba a kai ma wargi,
: Ɗanmadami Ali Baba.
(Musa Ɗanƙwairo: Waƙar Ɗanmadami Ali Baba)
Duk da
cewa Yahaya da wasu (1992 shf. 73) sun bayar da ma’anar sarauta, hakan bai hana
a laluɓi tushen kalmar ba. Ga
alama, kalmar sarki wadda ta kumbura ta zama sarauta tushenta ba Hausa ba ce.
Hausawa aro ta suka yi daga wani harshe. Bunza, (2023 shf. 12) ya tabbatar da
cewa, “Kalmar “sarki” Hausawa aro ta suka yi daga maƙwabtansu na bakin ruwan
Chadi ƙabilar
Buduma. Kodayake, maganar macijin da yake rijiyar Kusugu ta Daura mai suna
“Sarki” in ya inganta abin dubawa ne.” a game da haka Bunza (2014)[3]
ya bayyana cewa, kafin Hausawa su sami kalmar sarki suna amfani ne da kalmar
“Gogarma.” Shi ne ya sanya Makaɗa Narambaɗa yake cewa:
Jagora: Gogarman Tudu jikan Sanbo,
: Maza
su ji tsoron ɗan mai Hausa.
1.1.4
Bahaushe
Karɓuwa da buwayar da Bahaushe
ya yi a faɗin Afirka da ma duniya baki
ɗaya, ya sanya masana da manazarta duƙufa wajen fayyace shi a
ilmance. Misali, CNHN, (2006 shf. 29) ya bayyana Bahaushe a matsayin:
“Haifaffen mai magana da harshen Hausa da rayuwa irin ta Hausawa.” Bunza (2022
shf. 12 da 2023 shf. 12) yana daga cikin waɗanda suka yi amfani da ɓangarorin guda biyu, inda ya yi amfani da wasu matakai
guda biyar a tasa mahanga ta bayyana wane ne Bahaushe.
i. Dole ne ya kasance ba ya da harshen gado sai Hausa.
ii. Ba ya da wata ƙasa face ƙasar Hausa.
iii. Ya yarda shi Bahaushe ne ya yi tinƙaho da haka.
iv. A same shi baƙar fata tilin da suma dunƙulalliya baƙa ƙirin.
v. A same shi ba wata al’ada da yake tinƙaho da ita face al’adun
Hausawa da ya gada kaka da kakanni.
Idan aka dubi taliyon waɗannan bayanai da masana suka bayar, ana iya cewa,
Bahaushe shi ne wanda ba shi da wani harshe sai Hausa, sannan al’adunsa na
Hausawa ne kuma yana bugun gaba da kasancewarsa Bahaushe.
1.3 Hanyoyin Gudanar Da Bincike
Wannan bincike ya laluɓi bayanai ta muhimman fuskoki guda uku. A fuska ta farko,
an yi ƙoƙarin bin diddigin wasu
bayanan daga bakin ‘ya’yan sarauta da waɗanda suke da ruwa da tsaki da ita. Wannan haƙa ba ta samu cimma ruwa ba,
saboda mutum ba zai ɗau wuƙa ya daɓa a cikinsa ba.
Takardar ta yi ƙoƙarin tuntuɓar malaman Musulunci, saboda tunanin cewa, wa’azozin da
suke gudanarwa wata kafa ce da za a iya tsintar bayanan da suka danganci tsarin
sarautar Hausawa ta gargajiya da yadda addinin Muslunci ya yi mata gyara. Haka
kuma, an waiwayi wasu ɓangarori na adabin bakan
Bahaushe, saboda kasancewarsa wani fage da yake ɗauke da hoton rayuwarsa.
Bugu da ƙari, an tuntuɓi wasu daga cikin ayyukan al’ada da na addini da masana
da manazarta suka wallafa. Waƙoƙi kuwa sun tallafa wajen sake haska hoton wasu batutuwa
tare da fito da bayanansu fili.
1.4
Ra’in Bincike
Ra’i dai wata kafa ce ta ilimi da take jagorantar bincike
domin ya samu damar kaiwa ga nasara. Bisa wannan tunani, an ɗora wannan nazari a kan, Ra’in Sassarƙuwar Al’adu (Cross-Cultural
Theory). Ra’in ya samo asalinsa ne daga aikin Edward Twitchell mai taken: “The
Silent Language” a shekarar 1959 (Gusau 2015 shf. 45-46). Edward, ya yi
rayuwarsa a ƙasar
Amurka daga 1914-2009.
Ra’in ya samu karɓuwa a ayyukan mutane da dama a ƙasashen Amurka da Japan da
da sauran sassan duniya. Ɗaya daga cikin mabiya wannan ra’i mai suna Triger ya
rubuta wani littafi da ya gina tubalinsa a kan wanan ra’i mai suna, The
Analysis of Culture. Ado (2017 shf. 86) ya nuna masana irinsu Usman (2008)
da Gusau (2015) sun tabbatar da cewa, ana amfani da ra’in sassarƙuwar al’adu domin yin
nazarin al’adun rayuwar al’ummar duniya da suke iya canzawa a sanadiyyar sarƙuwar al’adar wata al’umma
da ta wasu a dalilin cuɗanya da juna.
Dalilan da suka kawo na cuɗanyar al’umma sun haɗa da, ƙaura da neman ilimi da ziyarar buɗe ido ko kuma ta addini. Wannan ra’i yana da alaƙa da wannan aiki musamman
idan aka yi la’akari da yadda takardar take ƙoƙarin fito da tsarin mulkin
Hausawa na gargajiya da irin sauyin da ya samu a dalilin tasirin addinin
Musulunci. Wani abin sha’awa shi ne, tunanin wannan ra’i ya dace da falsafar
Bahaushe da take cewa: “Zama da maɗaukin kanwa, shi yake kawo
farin kai.” Ke nan, maganar Makaɗa Sani Aliyu Ɗandawo tana da tushe:
Jagora: Wane shi ba ɗan sarki ba,
: Amma
ga kainai yai kora.
Yara: Zama da maɗaukin kanwa.
Gindi: Mai Yawuri sabon Sarki,
:
Sha’aibu maɗaukin fansa.
(Sani Aliyu Ɗandawo: Waƙar Sarkin Yawuri Alhaji Shu’aibu Abarshi)
2.0 Sarauta a Zamantakewar Hausawa
Tun asali, tsarin sarautar Bahaushe ta faro ne tun daga
gida. Ƙananan
yara a gida suna girmama na gaba da su tare da karɓar umarni daga gare su. Hausawan da suke zaune a nahiyar
yammacin ƙasar
Hausa suna kiran manya daga cikinsu yannai (yayu) ko “magaji.” Wato su ne a
matsayin magada iyayensu. Alhassan da wasu (1982) da Yahaya da wasu (1992) da
kuma Argungun (2017) duka sun nuna cewa, a gidan Bahaushe akwai tsarin
shugabanci, kuma shi ne ya yi tasiri ta yadda babba a gida yake jagorantar ɗaukacin al’ummar da take gidan, komai
yawansu. Haka abin ya ci gaba har aka kai lokacin da aka kafa tunga, har abin
ya kai ga ƙauye
da gunduma da kuma masarauta.
2.1 Tsarin Sarauta a Ƙasar Hausa Kafin Shigowar
Addinin Musulunci
Zamantakewar kowace al’ummma kafin ta sunsuni addinin
Musulunci takan bambanta da lokacin da ta karɓe shi. Yanayin al’umma a wancan lokaci rayuwarsu takan
kasance abin da Hausawa suke cewa: “Bakin gudunka bakin ladanka.” Wannan kuma
ba abin mamaki ba ne, Abdullahi (2008 shf. 36) ya nuna cewa, kowace al’umma
daga gargajiya ta fito kafin ta samu kaiwa ga tsayayyen addini. Har yanzu ana
samun Larabawan da ba Musulmi ba. Duka waɗannan bayanai suna ƙara tabbatar mana cewa, kowace al’umma ta ɗanɗani yanayi da zamantakewa irin ta jahiliyya. Wasu daga
cikin yanaye-yanayen tsarin sarauta a ƙasar Hausa kafin bayyanar addinin Musulunci
sun haɗa da:
2.1.1 Hanyar Zaɓen Sarki
Yana
daga cikin yanayin mulki a ƙasar Hausa, idan sarauta ta faɗi (sarki ya rasu) akan zaɓi shugaba ta hanyar jarumtarsa. Hakan ya sa wasu daga
cikin masarautun ƙasar Hausa suke zaɓen sarki ta hanyar wata bajinta da ya nuna a wurin yaƙi. Misali, a lokacin mulkin
Haɓe, masarautar Zazzau suna zaɓen sarki ne saboda bajintar da ya nuna a
fagen yaƙi
(Soba, 2017 shf. 68). Ƙasar Ƙatsina kuma suna zaɓen Sarki ne ta hanyar kokawa. Garba, (2020 sh. 20) ya
nuna duk shekara ake gudanar da kokawa da sarkin da yake kan gadon mulki. Wanda
duk ya kayar da shi, zai sa wuƙa ya yanka shi ya hau gadon Sarauta. A ruwayar Soba (2017
shf. 68-69), a Katsina, kafin a samu sarki a lokacin Haɓe sai an yi kokawa.[4]
Wanda ya fi ƙarfin
kowa shi ne zai zamanto sarki kuma akan ba shi wuƙa da tukunya da kuma
tambari. Wuƙa ita
ce wadda ake yanka wanda aka kayar, sai tukunya kuma ita ce wadda ake tare
jinin wanda aka yanka, tambari yana zama abin da ake bugawa don ba masu kokawa ƙaimi. Kodayake wannan
labari da ake bayarwa tamkar tarihihi ne idan aka kwatanta shi da bayanin Bunza
(2023 shf. 42-43).
A ɓangare ɗaya kuma, Ibrahim (1982 shf. 8) ya bayyana
cewa, a wancan lokaci babban aikin shugaba shi ne kula da gunkinsu[5]
da magana da shi da tsare dokokin farauta, da kuma tabbatar da biyayyar jama’a
ga gunkin da suke bauta wa. Don haka a tsarin sarautar Hausawa kafin zuwan
Muslunci, babu wanda zai shugabanci jama’a sai boka wanda yake da alaƙa da gunkin da jama’a suke
bauta wa ko kuma jarumi wanda ya nuna ya fi kowa sadaukantaka.
Kafin bayyanar addinin Musulunci a ƙasar Hausa, babban aikin
shugaba shi ne, kula da tsafin gari ko ƙasa, tare da tabbatar da cewa, al’umma ba su
kauce wa dokokin iskar da mutanen wannan ƙasa suke bauta wa ba. Misali, a Kano, baban
abin bautarsu ita ce Tsumburbura ta nan kan dutsen Dala. Haka lamarin yake ga
mutanen Katsina da Zamfara inda suke bauta wa tsafin Ɗantalle da na Magiro. A
takaice, babban ma’aunan da suke amfani da su wajen zaɓen Sarki su ne: Fice ta fuskar jarumta da kuma kusanci da
iskar ko abin tsafin da mutanen wannan ƙasa suke bauta wa.
2.1.2 Yanayin Majalisar Sarki
Ga al’adar majalisar sarakunan gargajiyar Bahaushe suna
da tsarin da ‘yan majalisa waɗanda suke zama tamkar
waziransu wajen jan ragamar jagorancin jama’a. Bayan fadawa da galibinsu suka
kasance bayi, akwai wasu keɓantattun muƙamai da ake ba da su a fada
domin tafiyar da mulki. Wannan dalili ne ya sa suke amfani da shugabannin
sana’o’i a matsayin wakilan sarki ta ɓangagorin da suke shugabanta. Bunza (2024)[6]
ya tabbatar wa da wannan bincike cewa, a wancan lokaci sarakuna suna naɗa muƙamai ne bisa matsayi na ƙwarewa (specialisation).
Hakan ya sa wanda ya fi kowa ƙwarewa wajen iya bori shi ake naɗawa sarkin bori. Haka abin yake ga manoma da maƙera da sauransu. Sulaiman
da Sani (2025 sh. 246) sun bayyana jarumta da buwaya da ƙwarewa a cikin mizanan da ake
la'akari da su wajen bayar da sarautun sana'o'in gargajiya a da.
A ɓangare ɗaya kuma, ga al’adar sarakunan ƙasar Hausa kafin bayyanar
addinin Muslunci, a duk lokacin da za a yi zaman fada akan buɗe da wasu surkulle na ambaton tsafi waɗanda suka same su daga bautar iskoki. Suna
yin haka ne saboda kariya daga wasu abubuwa da suke tsoro[7].
Bugu da ƙari, a
wancan lokaci, ba a yin sallama idan an shiga fada. Akan yi dai wasu surkulle
ne da suke da saƙonnin jinjina da kuma gaisuwa ga sarki.[8]
2.1.3 Yanayin Tsarin Mulki a Bahaushiyar Al’ada
Ga al’adar ɗan’adam, yanayin abin da
yake bauta wa yana tasiri a kowane lamari na rayuwarsa. Kafin Hausawa su karɓi addinin Musulunci dokokin da Iskokinsu suka
shimfiɗa musu ne suke zama
tafarkin da sukan tafiyar da rayuwarsu a kai. Wasu daga cikin abubuwan da suka
yi amo a tsarin tafiyar da mulki na wancan lokaci sun haɗa da:
2.1.3.1 Zalunci
Zalunci kalma ce da take da ma’anar ƙwara ko tauye haƙƙi ko yin ha’inci ga wani
don a cuce shi (CNHN, 2006 shf. 488). Garba, (2020 shf. 84) ya lissafo wasu
daga cikin zaluncin sarakuna waɗanda suka haɗa da: Kisan kai da son kai da yanke hukunci
ba bincike da da sauransu.
2.1.3.2 Tsafi Wajen Neman Mulki
Bunza (2006 shf. 35) da Sarkin Gulbi (2014 shf. 33) sun
sake fito da ma’anar tsafi a matsayin: “Wasu hanyoyi na gargajiya musamman yi
wa iskoki hidima da yanka da bauta domin biyan wata buƙata ko kuma samun wani
amfani ko tunkuɗe wata cuta.” Wannan ya
nuna tsafi wata tsohuwar hanyar bauta ce ta gargajiya, wadda ake amfani da ita
da nufin neman wata kariya daga cuta ko kuma neman wata ɗaukaka. Idan aka dubi yadda Makaɗa Musa Ɗanƙwairo ya kawo hoton wannan ɗabi’a akwai abin dubawa:
Jagora: Ai ga wani ɗan Sarkin Keffi,
: Can
nig ganai cikin daji inda tsamiya,
: Yana
ta rawa yana baya-baya ba ta gani,
Yara: Da ɗan ƙulƙinai gun Magiro.
Gindi: Muhammadu Cindo bi da
maza,
:
Mammman ɗan Mamman bajimi
(Musa Ɗanƙwairo: Waƙar sarkin Keffi).
2.1.3.3 Yaƙi da Hanƙoron Faɗaɗa Ƙasa
A lokacin da Hausawa ba su karɓi addinin Muslunci ba, sarakuna sun yi ta yaƙe-yaƙe da juna saboda hanƙoron faɗaɗa ƙasa da sauran biyan buƙatu na tara dukiya da kuma
mallakar bayi da dangoginsu. Irin wanan ya kawo yaƙe-yaƙe tsakanin daulolin ƙasar Hausa, kamar Gobir da
Zamfara da Gobir da Katsina. Haka ta faru tsakanin Kano da Zazzau da dai
sauransu da dama. Ƙwarewar yaƙi da samun jarumai wani mizani ne na ƙarfin ikon da daula ko
masarauta take da shi a lokacin.
2.1.3.4 Yawan Karɓar Haraji a Wurin Talakawa
Karɓar haraji ba tare da
sassautawa ba, yana daga cikin abubuwan da tsarin sarautar Hausawa ta gargajiya
yake a kai[9].
A wancan lokaci, hatta binne mutum a maƙabarta, sai an biya sarakuna kuɗin haraji. Sarakunan sukan bautar da mutane
ta hanyar sanya su ayyukan ƙarfi kamar noman gonar sarki da sauran hidimomi da suka
dangance su.
2.2
Yanayin Sarautar Hausawa Bayan Shigowar Musulunci
Masana tarihi sun bayyana cewa, addinin Musulunci ya
shigo ƙasar
Hausa tun zamanin Sayyadina Mu’awiya ɗan Safiyanu wanda ya turo Uƙuba ibn Nafi’u. Wasu kuwa
sun ganin zamanin Halifa Umaru ɗan Kaɗɗafi (634-644) ne Musulunci ya shigo ƙasar Hausa (Yahaya, 2012
shf. 9). An ce ya shigo ta Borno a zamnin mulkin Maidunama (1098-1150). Bunza
(1995 shf. 162) ya tabbatar da cewa, Musulunci ya zo Katsina a zamanin
Muhammadu Korau (1320-1350). Kano kuma ya shigo a zamanin Sarkin Kano Aliyu
Yaji ɗan Tsamiya (1349-1359).
Ga al’ada, duk lokacin da kiɗa ya sauya ita ma rawa takan sauya. Hakan ya sanya tsarin
mulkin Bahaushe ya sauya daga yadda aka san shi kafin ya karɓi addinin Musulunci. Wasu daga cikin sauyin
da addinin Musulunci ya kawo wa siyasar mulkin Bahaushe ta sarauta sun haɗa da:
2.2.1 Samar da Masana
Addini a Fada
Musulunci ya mayar da malamai da masana shari’a kan gaba
wajen taimaka wa sarki a lamuran tafiyar da harkokin mulki. Wannan dalili ne ya
jawo aka samu muƙaman limamin sarki da alƙali da marubucin sarki. Har
wa yau, an samu ci gaba inda aka kafa majalisar shura, wadda alhakin naɗa sarki da taimaka masa wajen tafiyar da
mulki ya rataya a wuyanta. Wannan majalisa ta shafi ƙwararru a kan fannonin
sana’a da ilimi da shari’a waɗanda suke gudanar da kowane
abu bisa haƙiƙanin yadda ya kamata.
2.2.2 Yanayin Girmama Sarakuna
Hanyoyin girmama sarki ya sauya daga yadda aka san shi a
baya, sai sarakuna suka koma yin musafaha da mutane maimakon sujada da ake yi
musu. Malam Abdullahi Fodiyo ya haska wa al’umma wanan al’ada ta girmamawa ga
sarakuna a lokacin jahiliyya a cikin waƙarsa ta Tsarin Mulki inda yake cewa:
Ga
al’adunsu kowaz zo shi duƙa,
Waɗansu suna afi ku ji wane daina.
(Abdullahi
Fodiyo: Waƙar
Tsarin Mulki na Islama).
2.2.3 Shigo da Addinin Musulunci Cikin Bukuwan Sarauta
An samu sauyawar bukuwan tsafi na shekara da sarakuna
sukan jagoranta zuwa na ranakun sallar idi, tare da jawaban da suka dace da
koyarwar addinin Musulunci maimakon yi wa iskoki kirari[10].
Bayan da Hausawa suka karɓi Musulunci, sai sarakuna
suka sauya wannan al’ada, ta koma idan an dawo daga sallar idi sarki yakan
tsaya ya yi jawabi a ƙofar gidansa maimakon wancan kirari da akan yi a baya.
3.0 Tankaɗe da Rairaya
Wasu daga cikin abubuwan da aka rairayo waɗanda suka shafi tasirin da addinin Musulunci
ya yi ga tsarin tafiyar da sarautar Bahaushe ta gargajiya sun haɗa da:
i. Mayar da majalisar sarki hannun malamai da masana da
kuma alƙalai,
ta yadda ya zamanto suna bin koyarwar Alƙur’ani da Hadisai maimakon biyayya ga bokaye
da matsafa da ake yi a baya, inda ake tambayar su abin da zai faru a shekara.
ii. An daidaita dokokin shugabantar jama’a bisa koyarwar
addini, inda sarakunan sukan zama alƙalai, da limamai ta yadda suke kasancewa
jagororin ibada, maimakon a baya da suke zama jagororin tsafi da bautar iskoki.
iii. Amon tasirin addini ya kawo buɗe zaman majalisar sarakuna (zaman fada) da addu’a, saɓanin lokacin jahiliyya da ake buɗewa da wani surkulle ko kuma tsafi.
iv. Ya tabbatar da haɗin kai a tsakanin daulolin Hausawa, wanda a baya suke yaƙar junansu.
v. An samu sauyawar yanayin suturun sarakuna zuwa na
kamala, inda suke naɗa rawani da sanya alkyabba,
maimakon warki da suke ratayawa a lokacin baya.
vi. An samu hulɗa da waɗanda ake mulka cikin
mutuntawa da sanin kimar ɗan’adam, saɓanin a baya da ake bautar da su.
vii. An samu wasu muƙamai da suke taimaka wa
sarki wajen tabbatar da tsarin shugbanci na addinin Muslunci. Misali:
a. Muƙamin Sa’i da yake kula da karɓar zakka.
b. Muƙamin Alƙali da yake kula da shari’a
c. Samar da muƙamin Sarkin Malamai da yake lura da harkokin
malamai a masarauta.
d. Muƙamin Shantali da yake kula da butar da Sarki yake alwala
da ita, da kuma riƙa masa ita idan zai shiga bayi kama ruwa da sauransu.
4.0
Sakamakon Bincike
Sakamakon
da wannan takarda ta kai ga ganowa su ne:
i. Tsarin sarautar Hausawa na gargajiya ya yi gwagwarmaya
a matakai daban-daban. Ya fara daga matakin jahiliyya zuwa lokacin da aka samu
wayewar kai ta addininn Musulunci. Hasali ma sarautun sun taimaka wajen yaɗuwar addinin Muslunci a ƙasar Hausa.
ii. Hausawa sun daɗe suna zama a ƙarƙashin shugabanci, don haka suka yarda da
gabaci tun kafin su karɓi addinin Musulunci.
iii. Addinin Musulunci ya kawo sauyi a tsarin shugabancin
Hausawa, inda zaman lafiya da adalci suka samu gindin zama a tsarin sarautarsu
musamman idan aka kwatanta yadda ta faro.
iv. Hulɗar Hausawa da wasu al’umomi
kamar Larabawa da mutanen Borno da Misra da sauransu ta taimaka musu wajen
sabunta harkokin sarautunsu, inda suka dace da na addinin Musulunci.
5.0 Naɗewa
Daga ƙarshe, siyasar mulki ta sarauta wata aba ce da ta daɗe Hausawa suna gudanar da ita. Tsarin
sarautar Hausawa yana da matakai guda uku fitattu. Mataki na farko shi ne,
kafin Hausawa su karɓi addinin Musulunci. Mataki
na biyu kuma, ya shafi yanayin yadda tafiyar da sarauta yake bayan Hausawa sun
sami sauyi na shiga addinin Muslunci. Mataki na uku kuma, ya karkata a kan
dubin yadda ake gudanar da mulkin ta hanyar cuɗanya al’adun gargajiya da kuma koyarwar addinin
Musulunci.
Manazarta
Abdulƙadir, Ɗ. (2011). Gyara kayanka:
Tasirin al’adun Hausawa ga cigaban ƙasa. Cikin Yalwa, L. Ɗ da Wasu (editoci). Studies
in Hausa language, literature and culture sixth Hausa international conference,
Pp. 474-482. Ahmadu Bello University Press.
Abdullahi, I.S.S. (2008). Jiya
ba yau ba: Waiwaye a kan al’adun matakan rayuwar maguzawa na aure da haihuwa da
mutuwa. [Kundin
digiri na uku da ba a buga ba]. Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Ado, A. (2017). Ra’o’in
bincike kan al’adun Hausawa. Kanki Classical Media Enterprises.
Ahmad,
S. A. (2021). Waiwayen sarautun mata na daular Gobir da yadda za a farfaɗo da su. Cikin Maishanu, I. M. et al (eds) transformation
in Gobir kingdom past and present, Pp. 369-377. Amal Printing Press.
Alhassan, H., Musa, U.I.
da Zarruƙ, R. M. (1982). Zaman
Hausawa bugu na biyu. Islamic Publication Bureau.
Argungu, A. I. (2017). Sarauta
a daular Kabi jiya da yau. Usmanu Danfodiyo University Press.
Bunza, A. M. (1995). Magungunan
Hausa a rubuce: Nazarin ayyukan malaman tsibbu. [Kundin digiri na uku da ba a buga ba]. Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.
Bunza, A. M. (2006).
Gadon feɗe al’ada. Tiwal Nigeria Limited.
Bunza, A. M. (2014). Hirar
da aka gudanar a gidan talabijin na Wisal.
Bunza,
A. M. (2023). Sarauta a tsarin ikon ƙasar Hausa (yadda take da yadda ake gudnar da
ita). Maƙalar
da aka gabatar a Jami’ar Bayero.
Cibiyar
Nazarin Harsunan Nijeriya (2006). Ƙamusun Hausa na Jami’ar Bayero. Ahmadu Bello University
Press.
Garba,
S. (2020). Karimci da zaluncin sarauta a al’adar Bahaushe: Nazari daga wasu
labaran gasa ta farko. [Kundin digiri na biyu da ba a buga ba]. Sashen
Koyar da Harsunan Afirka da Al’adu, jami’ar Ahmadu Bello.
Gusau, S. M. (2015), Mazhabobin
ra’i da tarke a adabi da al’adu na Hausa. Century Research and Publishing
Limited.
Gobir, A. Y. (2012). Tasirin
iskoki ga cutuka da magungunan Hausawa. [Kundin digiri na uku]. Sashen Koyar da Harsunan Nijeria, Jami’ar Usmanu
Ɗanfodiyo.
Ibrahim,
M. S. (1982). Dangantakar al’ada da addini: Tasirin musulunci kan rayuwar
Hausawa. [Kundin digiri na biyu da ba a buga ba]. Sashen Koyar da Harsunan
Nijeriya, Jami’ar Bayero.
Kotorkoshi,
A. M. (2023). Critical assessiment of Hausa traditional religious practices
in the light of Sokoto jihad literature. [Unpublish Ph.D. thesis].
Department of Islamic Studies and Shari’a, Bayero University.
Mu’azu,
A. (2013). Baƙin al’adu a ƙagaggun littattafan soyayya
na Hausa.
Ahmadu Bello University.
Sani,
A-U, Shehu, M. & Rambo, R.A. (2023). Bitar tasirin Musulunci a kan al’adun
Hausawa na mutuwa. Scholars International Journal of Linguistics and
Literature, 6(12), 498-502. www.doi.org/10.36348/sijll.2023.v06i12.007.
Sarkin Gulbi, A. (2014). Magani a ma'aunin karin magana. [Kundin digiri na uku da ba a buga ba]. Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami'ar Usmanu
Danfodiyo.
Shuni, M. D. & Dagimum,
M. U. (20210. A religious and political significance of the five fundamental
demands of Shaykh Uthman bn Foduye from Bawa Jan-gwarzo. In Maishanu, I. M. et
al (eds) Transformation in Gobir Kingdom Past and Present, Pp. 204-213.
Amal Printing Press.
Soba, A. S. (2017). Tanadin
tsaron gargajiya a ƙasar Zazzau: (Waiwaye cikin zamunnan
sarakunan Haɓe 1435-1804). [Kundin digiri na uku da ba
a buga ba]. Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar
Usmanu Ɗanfodiyo.
Suleiman, M. & Sani, A-U. (2025). From heritage to modern
influence: Changing criteria in the conferment of occupational titles in Kano.
Global Academic Journal of Humanities and Social Sciences. Global Academic
Journal of Humanities and Social Sciences, 7(6), 242-248. https://doi.org/10.36348/gajhss.2025.v07i06.001.
Talata
Mafara, M. I. (Babu Shekarar Bugu). Siyasa a mahangar musulunci. Nadabo
Print Production. ISBN: 978-978-48801-3.
Yahaya,
I. Y. (2012). Hausa a rubuce: Tarihin rubuce-rubuce cikin Hausa. Nothern
Nigerian Publishing Company.
Yahaya,
I. Y. da Wasu (1992). Darussan Hausa don manyan makarantun sakandare juzu’i
na III. University Press Limited.
[1] A hangen wannan takarda, kafin bayyanar addini, a
zamantakewar Hausawa ta Maguzanci bautar iskoki da tsafi da camfi su ne suke yi
musu jagora. Yanayin tsafinsu ya ƙyamaci sata da zina da sauran abubuwa na cin amana.
Wannan ne ya sa suka kiyaye su, suke bin abin da tanade-tanden dokokinsu suka
tsara musu sau-da-ƙafa.
[2] An yi lokacin da Sarkin
Kano ya zaɓi wani dattijo a matsayin
Sarkin Dattawa saboda babu wanda ya kai shi shekaru a masarautar (Bunza, 2024).
[3] Hirar da aka gudanar da
Farfesa Aliyu Muhammad Bunza a Wisal Telvission a shekrar 2014.
[4] Maganar kokuwa a lamarin zaɓen sarauta ya samu shiga a bakin mawaƙan baka na Sarauta. A
kowane lokaci aka zaɓi sarki suna fito da
maganar kokawa a cikin ɗiyan waƙoƙinsu. Misali, Makaɗa Narambaɗa yana cewa:
Jagora : Wawan kokawa kodayaushe
J/Yara : Shi aka shammata bai iya ba,
: Ga wata kokowwa an wuce da shi,
Yara :
Karsanai kakkaɓe mishi ƙasa
Gindi :
Ibrahimu na Guraguri
: Maishinkahi bajinin zagi
: Mu dai Allah ya bar muna kaya.
(Narambaɗa: Waƙar Ibrahimu na Guraguri).
Haka shi ma Makaɗa Musa Ɗanƙwairo Maradun yana cewa:
Jagora : Ya kada raƙumin daji,
Yara : Kuma ya taushe bushiya mai doron gado,
Gindi : Ba maza kashi tilas su bi ka,
:
Malam ɗan Idirisu.
(Muasa
Ɗanƙwairo: Waƙar Sarkin Zazzau).
[5] Gunki a nan ana magana ne a
kan nau’in iskar da Hausawa suke bauta wa, ba gunki da ake sassaƙawa da ita ce ba. Masana al’ada sun yi amannar cewa, Hausawa ba su bauta
wa gunki na ita ce ba. A wancan lokacin iskokinsu da dodonninsu da kuma
tsafe-tsafensu suke bauta wa. Misali, a Kano a wancan lokaci suna bauta wa
Tsumburbura ne. Wannan abin bauta nasu shi ne aljanin da ‘yan bori suke kira da Danko ɗan Musa (Ibrahim, 1982 shf. 9).
[6] Hira da Farfesa Aliyu
Muhammad Bunza ta wayar hannu ranar 08/10/2024.
[7] Hira da Farfesa Lawal
Abdulkarim a ofishinsa da yake Sashen Nazarin Addinin Muslunci, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato ranar
O2/10/2024
[8] Hira da Malam Adamu Ibrahim
Argungu ta wayar hannu, Malami a Sashen Hausa Kwalejin Adamu Augie, Argungu,
Jihar Kebbi, ranar 07-08/10/2024.
[9] Don neman ƙarin bayani, a dubi Shuni
da Dagimun (2021 shf. 207).
[10] Daga cikin irin kirarin da
yake mata akwai:
Jamuna
a kasa mun gama,
Ni
Magajin Dala,
Da
kun ƙi da
kun so,
Ku bi ni ba raɗi ba.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.