Ticker

6/recent/ticker-posts

Azkar Da Addu'o'i Kafin Kwanciya Barci

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓

Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu, Malam Khamis.

Don Allah, ina so a ba ni wasu azkar ko addu'o'i da ya kamata mutum ya riƙa karantawa kafin ya kwanta barci domin samun kariyar Allah da kwanciyar hankali.

Abin da nake lura da shi shi ne, wani lokaci idan ban yi addu'a ba kafin barci, nakan yi barci lafiya lau. Amma a duk ranar da na yi addu'a kafin in kwanta, sai in riƙa yin mafarkai iri-iri marasa daɗi.

Don Allah, Malam, me ya kamata in riƙa karantawa kafin barci? Kuma mene ne ya dace in yi idan na lura cewa mafarkai marasa daɗi suna yawaita a duk lokacin da na yi addu'o'in kafin barci?

Allah ya saka maka da alheri.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

A koyarwar addini, shaiɗan baya son mutum ya kusanci Ubangijinsa ko ya nemi kariya. Saboda haka, idan kayi addu'a, sai ya yi amfani da mafarkai masu ban tsoro domin ya firgita ka, da nufin tsorata ka har ka daina yin addu'ar ko ka cire rai daga amfaninta. Wasu malaman suna ganin cewa addu'a tana zama kamar garkuwa da ke bayyana abubuwan da ke ɓoye . Mafarkin yana iya zama alamar cewa addu'arka tana yakar wasu miyagun abubuwa da suke kewaye da kai wadanda da can ba ka sani ba.

Kada ka daina yin azkar saboda ka lura cewa wani lokaci bayan kayi addu'a kana yin mafarki mara kyau. Azkar kariya ce da Annabi ﷺ ya koyar damu, kuma mafarki baya zama hujjar cewa addu'ar ta jawo wani abu.

Ina baka shawarar ka riƙa yin azkar na Sunnah kafin ka kwanta barci. Ka fara da yin alwala kamar yadda kake yin ta don sallah, sannan ka kwanta a gefen damanka, ka karanta Ayatul Kursiyyu Annabi ﷺ ya bayyana cewa wanda ya karanta ta kafin ya kwanta, Allah zai sanya masa mai tsaro, kuma Shaidan ba zai kusance shi ba har zuwa safiya (Sahihul Bukhari).

Haka kuma ka haɗa tafukan hannayenka, kayi tofi mai sauƙi a cikinsu, sannan ka karanta Suratul Ikhlas, Falaq da Nas, ka shafi jikinka da hannayenka gwargwadon iyawarka, ka fara daga kai da fuskarka zuwa sauran sassan jikinka. Ka maimaita hakan sau uku, kamar yadda Annabi ﷺ ya kasance yana yi kafin kwanciya barci (Bukhari da Muslim).

Sannan ka karanta ayoyi biyu na ƙarshe na Suratul Baqarah, (wato Amana Rasulu) Annabi ﷺ ya ce wanda ya karanta ayoyi biyu na ƙarshe na Suratul Baqarah da dare, za su isar masa (Bukhari da Muslim).

Haka kuma ka riƙa karanta wannan addu'ar:

بِاسْمِكَ اللَّهُمَّ أَمُوتُ وَأَحْيَا

Ma'ana: Da sunanka Ya Allah nake mutuwa, kuma da sunanka nake rayuwa.

Sannan akwai addu'ar neman kariya:

أَعُوذُ بِكَلِمَاتِ اللَّهِ التَّامَّاتِ مِنْ شَرِّ مَا خَلَقَ

Ma'ana: Ina neman tsarin Allah da cikakkun kalmominsa daga sharrin dukkan abin da Ya halitta.

بِاسْمِكَ رَبِّي وَضَعْتُ جَنْبِي، وَبِكَ أَرْفَعُهُ، فَإِن أَمْسَكْتَ نَفْسِي فارْحَمْهَا، وَإِنْ أَرْسَلْتَهَا فَاحْفَظْهَا، بِمَا تَحْفَظُ بِهِ عِبَادَكَ الصَّالِحِينَ.

Da Sunanka ya Ubangijina na kwanta, kuma da Izininka ne nake tashi. In Ka riƙe raina (da mutuwa), to Ka ji ƙanta, in Ka sake ta kuwa, Ka kiyaye ta da abin da Kake kiyaye bayinka salihai da shi.

اللَّهُمَّ إِنَّكَ خَلَقْتَ نَفْسِي وَأَنْتَ تَوَفَّاهَا، لَكَ مَمَاتُهَا وَمَحْيَاهَا، إِن أَحْيَيْتَهَا فَاحْفَظْهَا، وَإِنْ أَمَتَّهَا فَاغْفِرْ لَهَا، اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ العَافِيَةَ.

Ya Allah! Kai ne Ka halicci raina, kuma Kai ne Kake karɓan sa. Gare Ka Kaɗai mutuwarsa da rayuwarsa suke. In Ka rayar da shi, to Ka kiyaye shi; in Ka dauƙe shi, to Ka gafarta masa. Ya Allah! Ina roƙonka aminci daga dukkan mummuna.

اللَّهُمَّ أَسْلَمْتُ نَفْسِي إِلَيْكَ، وَفَوَّضْتُ أَمْرِي إِلَيْكَ، وَوَجَّهْتُ وَجْهِي إِلَيْكَ، وَأَلْجَأْتُ ظَهْرِي إِلَيْكَ، رَغْبَةً وَرَهْبَةً إِلَيْكَ، لَا مَلْجَأَ وَلَا مَنْجَا مِنْكَ إِلَّا إِلَيْكَ، آمَنْتُ بِكِتَابِكَ الَّذِي أَنْزَلْتَ، وَبِنَبِيِّكَ الَّذِي أَرْسَلْتَ.

Ya Allah! Na sallama raina gare Ka, na mai da al’amarina gare Ka, na fuskantar da nufina gare Ka, na dogara da Kai (a cikin dukkan al’amurana) saboda Kwaɗayin abin da ke gare Ka, da tsoron Ka. Babu mafaka, babu matsira daga gare Ka sai zuwa gare Ka. Na yi imani da Littafinka da Ka saukar, da kuma Annabinka da Ka aiko.

Idan kayi mafarki mara daɗi, Annabi ﷺ ya koyar damu cewa mutum ya nemi tsarin Allah daga Shaidan, ya yi tofi mai sauƙi ta gefen hagunsa sau uku, ya sauya gefen da yake kwance, kuma kada ya riƙa ba mutane labarin mafarkin (Sahihul Bukhari da Muslim).

WALLAHU TA'ALA A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

      ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam  

Post a Comment

0 Comments