Ticker

6/recent/ticker-posts

Allah Ba Ya Karbar Aikin Da Ba Ikhlasi A Ciki

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓

Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu, Malam.

Don Allah, Malam, ina da wata tambaya da ta shafi niyyata wajen aikata ayyukan alheri.

Na kasance mai son aikata ayyukan alheri, amma duk lokacin da na tashi yin wani aikin alheri, sai zuciyata ta riƙa kawo mini tunanin cewa wai don riya nake yin aikin. Misali, idan na yi niyyar bayar da sadaka, amma akwai mutane a wurin, sai in fasa bayarwar saboda ina tunanin za su ce ina yin hakan ne domin su yaba mini ko su sani.

Haka ma, idan ina karatun Alƙur'ani, wani lokaci idan mutane suka shigo gidanmu, sai in ji muryata ta sauya. Da zarar na lura da hakan, sai in daina karatun saboda ba na son in aikata wani abu domin wanin Allah.

Malam, gaskiya wannan hali yana damuna sosai. Duk lokacin da na yi niyyar aikata wani aikin alheri, idan akwai wani mutum a wurin, sai in ji irin wannan tunanin ya zo mini, daga nan kuma sai in fasa aikin.

Don Allah, Malam, ina neman shawara. Shin akwai wata addu'a da zan riƙa yi domin Allah Ya taimake ni wajen kawar da wannan tunani da kuma nisantar riya? Ina son in riƙa aikata ayyukan alheri saboda Allah kaɗai, ba domin mutane su yaba mini ba.

Na gode sosai. Allah Ya saka maka da alheri, Ya sa mu kasance cikin waɗanda suke aikata ayyukan alheri da ikhlasi, kuma mu amfana da ilimin da muke samu.

ALLAH BA YA KARƁAR AIKIN DA BABU IKHLASI A CIKI

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salamu, Tabbas Allah ba ya karɓar duk wani aiki da aka yi shi ba tsarkin ninya (ikhlasi), dole ne kowane musulmi ya yi iya qoqarinsa wajen ganin ya riqa yin duk wani aiki don Allah, ba don mutane su gani su yaba masa ba, matuqar ba a sami wannan a cikin ayyukan bawa ba, to waɗannan ayyukan Allah ba zai karɓe su ba, kamar yadda ayoyi da hadisai da dama suka yi gargaɗi, daga ciki, Allah hadisul Qudusiy yana cewa: "Ni na wadatu daga mushirikai game da shirka, duk wanda ya aikata kowane irin aiki ya haɗa ni da wani na a cikinsa, to na bar shi da shirkarsa". Sahihu Muslim 2985 .

Wannan na nufin duk wanda ya aikata wani aikin Allah don mutane su gani su yaba masa, to Allah ya bar shi da wannan aikin da ya yi, ba zai karɓa masa ba. A wani hadisin da Abuhurairata ya ruwaito, Annabi ﷺ ya ce: "Duk wanda ya jiyar da aiki Allah zai jiyar masa da shi, haka duk wanda ya nunar Allah zai nunar masa da shi".  Bukhariy 6499, Muslim 2986.

Wannan na nufin duk wanda ya yi wani aikin lada don mutane su ji su yaba masa Allah zai sa mutane su ji aikin, haka nan wanda ya yi aiki don mutane su gani su ce ya iya, to Allah zai nuna wa mutane su gani su yaba masa, amma ba shi da sakamako na lada a lahira, har ma zai sami zunubi na haɗa Allah da wani a cikin aikinsa, saboda mai yin riya yana yi ne don mutane su yaba masa, sannan ta wani ɓangaren kuma yana son Allah ya ba shi lada, don haka wannan shirka ce qarama in ji wasu malaman. Allah ya tsare mu da yin riya a cikin dukkan ayyukanmu.

Game da addu'a da kike nema wanda za ki riqa yi don Allah ya raba ki da riya, to ni a gaskiya ban san wata addu'a keɓantacciya da ake yi don Allah ya raba mutum da riya ba, amma dai qofar addu'a a buɗe take, matuqar ba ta saɓa wa Shari'a ba, wato kenan za ki iya yin addu'a a kan Allah ya raba ki da aikata riya, ki nace a kan hakan a duk lokacin da kika yi sujjada, kuma ki riqa tashi cikin dare kina roqon Allah ya raba ki da riya, in Allah ya so Allah zai taimaka maki a kan hakan. Kuma za ki iya haɗawa da wannan addu'ar ta Manzon Allah ﷺ:

يَا مُقَلِّبَ القُلُوبِ ثَبِّتْ قَلْبِي عَلَى دِينِكَ.

"Ya Allah, Mai jujjuya zukata, Ka tabbatar da zuciyata a kan addininka."

Shahru bin Haushab ya tambayi Ummu Salamata cewa wace addu'a ce Manzon Allah ﷺ ya fi yawan yi idan yana wurinki? Sai ta ce: "Addu'ar da ya fi yi ita ce:

 “يَا مُقَلِّبَ القُلُوبِ ثَبِّتْ قَلْبِي عَلَى دِينِكَ".

Sai ta ci gaba da cewa: "Na tambayi Manzon Allah ﷺ cewa; mene ya sa mafi yawan addu'arka ita ce wannan? Sai ya ce: "Lallai babu wani ɗan'adam face zuciyarsa tana tsakanin yatsu biyu daga cikin yatsun Allah"". Sunanut Tirmizhiy 3522.

Allah ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

      ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam   

Post a Comment

0 Comments