Ticker

6/recent/ticker-posts

Allah Ba Ya Yafe Hakkin Wani Mutum A Kan Wani Har Sai An Mayar Masa Da Hakkinsa

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓

Assalamu alaikum, Malam. Barka da warhaka. Ina fatan kana cikin ƙoshin lafiya.

To, Malam, don Allah ina neman shawara ne a kan wani abu da ya daɗe yana damuna. A lokacin da nake ƙarami, kafin in kai shekarun da zan iya fahimtar nauyin aikina, na taɓa cutar da mutane a wasu hanyoyi. An ɗauke ni a matsayin yaron shago, kuma a lokacin na kan ɗauki kuɗin maigidanmu ba tare da saninsa ba. Haka kuma, lokacin da aka kai ni gidan mai, na taɓa cutar da mutane ta hanyar zuba musu mai ƙasa da wanda suka biya, domin in samu kuɗi. Na aikata irin waɗannan abubuwa da dama a wancan lokacin.

Sai dai a yau, na ga wata fatawa da ka bayar dangane da bashin wata mata da aka yi mafarkin ta mutu, kuma tana cikin wahala saboda bashin da ke kanta. Wallahi, Malam, tun da na karanta wannan fatawa, hankalina ya tashi matuƙa. Na kasa samun sukuni, domin na fara tunanin yadda zan mayar wa mutanen da na cuta hakkokinsu, amma ban san inda zan same su ba.

Har na fara tunanin sayar da gidana ko kuma neman haya, domin in raba kuɗin ga waɗanda na zalunta a madadinsu. Amma gaskiya ban san adadin kuɗin da na karɓa ko na cuce su da shi ba.

Don Allah, Malam, ina neman shawararka. Wallahi, ina cikin tashin hankali sosai. Duk lokacin da na tuna abin da na aikata, sai in ji kamar mutuwa ta zo mini, kuma zan tafi da nauyin waɗannan hakkoki a kaina. Ina tsoron haɗuwata da Ubangijina, kuma ina jin kunyar tsayawa a gabansa da irin waɗannan laifuffuka.

Wallahi, Malam, wannan lamari yana matuƙar damuna. Ina fatan za ka ba ni shawarar abin da ya kamata in yi domin in gyara kuskuren da na aikata, in biya waɗannan hakkoki, kuma in samu kwanciyar hankali a duniya da lahira.

Allah ya saka maka da alheri.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumussalam warahmatullahi wabarakatuh.

Ka Kwantar da hankalinka, wannan nadama da tashin hankali da kake ji da kuma son gyara kuskurenka babbar alama ce ta rayuwar zuciyarka da kuma tsoron Allah, kuma wannan shine mataki na farko na samun gafarar Ubangiji. Kada ka bar Shaidan ya saka maka yanke tsammani daga rahamar Allah har kake jin gwamma mutuwa; kofofin tuba a buɗe suke, Allah yana karɓar tuban bawansa duk lokacin da ya tuba mutukar dai ransa bai kai gargara ba. Wato mutukar bai zo karshen numfashinsa ba. Allah maɗaukakin sarki Ya ce:

قُلْ يَا عِبَادِيَ الَّذِينَ أَسْرَفُوا عَلَىٰ أَنفُسِهِمْ لَا تَقْنَطُوا مِن رَّحْمَةِ اللَّهِ ۚ إِنَّ اللَّهَ يَغْفِرُ الذُّنُوبَ جَمِيعًا ۚ إِنَّهُ هُوَ الْغَفُورُ الرَّحِيمُ

"Ka ce: 'Ya bayina waɗanda suka yi wa kansu Ɓarna ta yawan zunubi, kada ku yanke ƙauna daga rahamar Allah. Lalle Allah yana gafarta zunubai gaba ɗaya. Lalle Shine Mai gafara, Mai jin ƙai, (Suratul-Zumar ayata 53).

Sau da yawa idan mutum ya shiga cikin tashin hankali na tunanin zunuban baya, yakan ji kamar duniyar ta yi masa kaɗan, har ya dinga jin alamun damuwa mai tsanani (depression) ko fargaba (anziety). Ka sani cewa ba kai kaɗai ka taɓa yin kuskure a lokacin kuruciya ba, kuma akwai mafita ta shari'ah da zata kawo maka nutsuwa ba tare da ka tarwatsa rayuwarka ta yanzu ba.

Kada ka hanzarta sayar da gidanka ko shiga kangin rayuwa ba tare da tsari ba. Haramun ne ka jefa kanka ko iyalanka cikin matsala ko rashin matsuguni muddin akwai sauran hanyoyi. Gidanka shine babban suturarka. Musulunci bai gina tuba akan halakar da kai ko jefa kanka cikin rashi mafi tsanani ba idan da sauran mafita. Shari'ar Musulunci tana da sauki a irin wannan yana yin:

Yadda Zaka Biya Kuɗaɗen Da Ba Ka San Adadinsu Ba; Tunda baka san ainihin nawa ka ɗauka ba, Ka zauna, ka natsu, kayi tunani, ka yi lissafin kusan shekaru nawa ka yi a shago da gidan mai. Ka kiyasta adadin kuɗin da kake tunanin ka taɓa ɗauka ko ka cuci mutane a kai. Misali, idan kana tunanin kuɗin ba zasu wuce ₦50,000 ko ₦100,000 ba, sai ka ɗauki mafi yawan adadin da ka fi kyautata zaton shi ne (domin ka fita cikin shakka).

Tunda abokan ciniki da dama ka cuce su wajen zuba musu mai kuma ba shi yiwuwa a san ko su wanene ko a nemo su ɗaya bayan ɗaya, shari'a ta ba da dama kayi sadaka da kuɗin a madadin kowannensu. Ka fitar da kuɗin da ka kiyasta na gidan mai, ka yi sadaka da shi ga gajiyayu, marayu, ko ginin masallaci/ruwan sha da niyyar ladan ya je ga mutanen da ka cuta. Idan ka yi haka, nauyin ya sauka daga kanka da yardar Allah. Ranar gobe kiyama idan Allah ya ba su wannan ladan sadakar, za su yafe maka hakkinsu da kake kansa tun a duniya.

Idan ba zaka iya biyan kuɗin lokaci guda ba, kada Ka tsananta wa kanka, ba sai ka sayar da gidanka ba. Zaka iya raba kuɗin gida-gida kana fitarwa Kaɗan-Kaɗan duk wata (misali ₦5,000 ko ₦10,000) har sai adadin da ka kiyasta ya cika. Sannan ka rubuta Wasiyya: Ka rubuta a takarda cewa ga adadin kuɗin mutane da ke kanka, kuma idan mutuwa ta ɗauke ka, a cire a dukiyar da ka bari a biya musu. Idan ka yi haka, Allah zai yafe maka tunda ka nuna niyya da kokari na zahiri.

Idan tsohon ogan naka yana raye kuma kana iya samun sa, zaka iya tura masa kuɗin ta hanyar da ba zai san daga wajen wa yake ba (kamar ta asusun banki ko ta hannun wani). Idan kana jin kunyar fada masa don gudun ɓacin suna ko barazanar tsaro. Zaka iya tura kudin ta POS asusun bankinsa, ko ka sanya a ambulan ka bai wa wani amintaccen mutum ya ce "Wani ne ya ce a ba ka kuɗin sa da yake kanka da can baya." Idan ya mutu, zaka iya ba wa magadansa, ko kuma kayi sadaka a madadinsa idan ba a san su ba.

Malaman Musulunci sun bayyana cewa Allah ba ya yafe hakkin wani mutum a kan wani har sai wanda aka zaluntar ya yafe da kansa, ko kuma a mayar masa da hakkinsa a duniya kafin a je Lahira. Idan lafin tsakaninka da Allah ne (kamar tauye hakkokin Allah), Allah yana yafe wa mai tuba gaba ɗaya. Amma idan hakkin ne da ya shafi wani mutum (kamar zalunci, cin hanci, cin mutuncin, zagin mutum, ko ɗaukar dukiyarsa) toh ko ka tuba Allah ba zai yafe maka ba. Dole ne a mayar wa mai shi dukiyarsa ko a nemi afuwarsa idan ta kasance ta baki ko ta jiki. Idan mutum ya tuba ga Allah amma bai biya hakkin wani ba ko kuma bai nemi afuwarsa ba kafin ya mutu, to a ranar Lahira za a karbi ladan wanda ya yi zaluncin a ba wanda aka zalunta. Tunda babu duniya da za a biya haƙƙin. Wanda ya zalunci wani zai biya shi da ayyukansa na kwarai. Idan ya shiga hakkin mutane, za'a rika ɗaukar lada daga cikin ayyukan wannan azzalumi ana baiwa wanda aka zalunta. Idan ladan mutumin ya kare kafin a gama biyan hakkokin mutanen da ya zalunta, za'a ɗauki zunubai da laifukan waɗanda ya zalunta a ɗora masa, sannan a jefa shi a wuta.

Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya yi bayani awani hadisi cewa akwai wanda zaizo da lada mai yawa aranar Alƙiyamah. Alhali ya zalunci wancan, ya zagi wancan, ya rike dukiyar wancan. To sai Allah ya sanya Mala'iku su rika kwashe ladansa suna biyan mutanen chan da ya zalunta. Idan ladansa ya Ƙare kuma ba a gama biyan mutane hakkokinsu ba, sai Allah ya cewa Mala'ikunsa ku rika kwasowa daga zunubansu kuna zuba masa. Daga karshe sai a jefa shi awuta. Imamu Muslim ne ya ruwaito hadisin da shigen irin wadannan kalmomin.

Na gaya maka wannan ne domin in fahimtar dakai girman laifin da ka aikata. Amma dai Ka kwantar da hankalinka, matakin da ka ɗauka na son gyarawa shi ne babban mataki na samun tsira. Wannan fargaba da kake ji ita ce zata tseratar da kai, amma kada ka barta ta koma yanke tsammani. Fara ɗaukar mataki yanzu na kiyasta kuɗin, sannan ka dage da yawan istigfari.

WALLAHU TA'ALA A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.  

Wallāhu Taʿālā Aʿlam — And Allah knows best.

Zauren Fatawoyi Bisa Alƙur’ani da Sunnah.

  ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam  

Post a Comment

0 Comments