𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Shin ko ya halatta mutumin da ya taɓa yin zina da wata mace kuma daga baya ya auri 'yarta??
ZAN IYA AUREN 'YAR MATAR DA
NA TAƁA
YIN ZINA DA ITA?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Alal-haƙiƙa
malamai sun yi saɓani dangane da wannan
mas'ala, mazhabin shafi'iyya da kuma wani sashe na malikiyya sun tafi ne a kan
cewa idan mutum ya yi zina da mace to ya halatta a gareshi ya iya auren ita
kanta matar, ko ya auri 'yarta, ko kuma ya auri uwarta, haka nan ya halatta ɗansa ya aure ta ko kuma babansa ya aure
ta, hakanan suka ce idan mutum ya je ya yi zina da uwar matarsa ko kuma ya yi
zina da 'yar matarsa, to aurensu da matarsa yana nan bai ɓaci
ba, sannan suka ce idan mutum ya yi zina da mace har ya yi mata ciki ta haifi
'ya mace to ya halatta ya auri wannan 'yar da aka halicce ta daga ruwan
maniyyinsa, suka ce zina ba ta haramta abin da aure yake iya haramtawa, daga
cikin dalilansu sun kafa hujja da faɗin Aʟʟαн(ﷻ)
... وَأُحِلَّ
لَكُم مَّا وَرَاءَ ذَٰلِكُمْ ...
An halatta muku (ku auri
mata waɗan
da suke) koma bayan waɗancan (da aka haramta muku)
(suratul Nisá'i Aya ta 24).
Sai dai kuma Mazhabin
Hanafiyya da Hanabila da kuma wani sashe na Malikiyya sun tafi ne a kan cewa
idan Mutum ya yi zina da Mace to ya haramta a gareshi ya auri Asali (Uwarta) da
kuma Reshe ('Yarta) na wannan Mata, danhaka ke nan haramun ne ya ce zai auri
'Yarta ko kuma Uwarta, haka nan shima haramun ne Ɗansa
ya aure ta ko kuma Babansa ya aure ta, daga cikin Dalilansu suka ce Mαnzon Aʟʟαн
(Sallallahu alaihi Wasallam) Ya faɗa
acikin wani Hadisi cewa
"ملعون
من نظر إلي فرج إمرأة وإبنتها"
An tsinewa duk wanda yakalli
farjin wata Mace (ta hanyar sha'awa) kuma yakalli farjin 'Yarta (ta hanyar
sha'awa).
Sannan suka kafa Hujja da Faɗin Aʟʟαн (ﷻ)
inda Yake cewa
وَلَا
تَنْكِحُوا مَا نَكَحَ آبَاؤُكُمْ مِنَ النِّسَاءِ
Kada ku auri (ku sadu da)
Matan da iyayenku Maza suka taɓa aura (suka taɓa
saduwa dasu) (suratul Nisá'i Aya ta 22)
Danhaka ke nan zina tana
haramta irin abin da aure yake haramtawa, suka ce babu wani bam-banci a
tsakani, kuma suka ce idan Mutum ya yi zina da Uwar Matarsa ko kuma ya yi Zina
da 'Yar Matarsa, to nan take aurensu da Matarsa ya ɓaci,
danhaka dole ne ya rabu da ita, Saɓanin
abin da Malikiyya suka tafi akansa ke nan na cewa aurensu bai ɓaci
ba.
Amma sai dai magana mafi
inganci a kan wannan Mas'ala ita ce, da yawa daga cikin Malamai sun rinjayar da
maganar cewa zina ba ta iya haramta abin da aure yake iya haramtawa ba, danhaka
ke nan ya halatta ya iya auren 'Yar Matar da ya taɓaa
yin Zina da Uwarta.
Amma dangane da hukuncin
cewa Mutum zai iya auren 'Yar da aka halitta daga ruwan Maniyyinsa sakamakon
Zina da ya yi da Uwarta, anan kam mafi yawan Malamai sun tafi ne a kan cewa
haramun ne ya aure ta, Suka ce ai dukkan Malamai sun yi Ijma'i a kan cewa
haramun ne Ɗan-Zina ya auri
Uwarsa da ta yi Zina ta haife shi, to ke nan meye bambanci tsakanin Uwar da
Uban da wasu za su ce ya halatta Uban ya aure ta? Danhaka ke nan Yadda yake
haramun ne Ɗan-Zina ya auri
Uwarsa, to haka yake haramun 'Yar-Zina ta auri Ubanta.
WALLAHU TA'ALA A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa
Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.