𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaykum warahmatullah. Mun gode sosai da taimaka mana da kuke yi. Allah ya ƙara muku lafiya da basira. Don Allah ina da tambaya mutum yayi aure matar ta zo da ciki, cikin kuma nashi ne ta yi watanni biyar zuwa shida ta haihu. kowa yasan da haka yanzu ya mutu. Shin wannan ɗan zai yi gadon baban ko ba zai yi ba? na gode Allah ya ƙara wa malam ilmi da basira.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikis salam wa
rahmatullahi wa barakatuhu.
Mutukar dai an tabbatar da
cewa wannan Matar ta yi cikakkun watanni shida a gidan mijin kafin ta haihu,
Kuma shi mijjn nata bai fito fili ya nisanta kansa daga wannan abin da ta haifa
ba, to tabbas wannan yaron nasa ne. Kuma yana da gadonsa daidai da sauran
'ya'yansa.
Acikin Alƙur'ani Allah ya bayyana cewa
ؕ وَحَمۡلُهٗ
وَفِصٰلُهٗ ثَلٰـثُوۡنَ شَهۡرًا ؕ
"Ɗaukar
Cikinsa Da Rainonsa (Har Zuwa Yayewa) Watanni Talatin Ne" (Surah: Al-Ahƙaf, Ayat: 15).
Sannan acikin suratul baƙarah Allah ya bayyana cewa
وَالۡوَالِدٰتُ
يُرۡضِعۡنَ اَوۡلَادَهُنَّ حَوۡلَيۡنِ كَامِلَيۡنِ لِمَنۡ اَرَادَ اَنۡ يُّتِمَّ
الرَّضَاعَةَ ؕ
Uwaye su shayar da jariransu
shekaru biyu cikakku, ga wanda yake son ya cika shayarwar... (Surah: Al-Baƙara, Ayat: 233).
Wannan na nuna cewa shayarwa
har zuwa shekara biyu (Wato watanni ashirin da huɗu
kenan) haƙƙi ne na jariri da aka
kwadaitar akai domin samun cikakkiyar lafiya da girma.
To daga waɗannan
ayoyin ne manyan Malamai daga cikin sahabbai suka kafa hujjar cewa idan mace ta
yi wata shida a gidan miji to duk abin da ta haifa nasa ne.
Shi addinin musulunci yana
kiyaye nasaba ne da kuma tattalin kyakkyawar dangantaka atsakanin jama'a. Don
haka zargin da akeyi cewar watakil ta zo da cikin ne, zargi ne marar tushe.
Idan kuma an tambayi matar
ko kuma wasu shaidu nagartattu sun tabbatar da zargin da akeyi cewar ta zo
gidan ne da cikinsa, To lallai wannan yaron ba zaici gadon marigayin ba. Hasali
ma babu auren nan. Domin dukk auren da aka daurashi alhali matar tana ɗauke
da juna-biyu, to bai dauru ba. Ba aure bane.
Don haka wannan yaron ba zai
ci gadon marigayin ba. Kuma itama uwar tasa bata da gado tunda zaman nasu ba
aure bane.
WALLAHU A'ALAM.
Zauren Fatawoyi Bisa
Alkur'ani Da Sunnah.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.