Ticker

6/recent/ticker-posts

Ya Matsayin Sallar Mai Matse Bahaya Da Bawali

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓

Assalamu alaikum malam, ina tambaya ce, kamar yanzu na yi sallar Magrib sannan na rike alwala zuwa sallar Isha'i, to sai na ji fitsari Amma ba sosai ba sai na yi sallar a haka, ya matsayin sallar take ta yi ko kuwa sai na sake alwala saboda wannan fitsarin?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus salam, Yin sallah alhali mutum yana jin bahaya ko bawali abin kyama (makaruhi) ne a wurin mafi yawan malamai, saboda hadisi ya tabbata daga Nana A'isha Allah ya ƙara mata yarda ta ce ta ji Manzon Allah (SAW) yana cewa: "Babu sallah idan aka halarto da abinci, kuma babu sallah ga wanda ke jin bawali da bahaya". Sahihu Muslim (560).

Mafi yawan malaman Musulunci sun bayyana ma'anar hadisin da cewa babu sallah cikakkiya ake nufi, wato ba wai babu sallar gaba ɗayanta ba. Wato wannan na nufin babu kamalar sallah a lokacin da aka zo da abinci, sannan babu kamalar sallah ga wanda yake cikin matsuwa da bahaya ko bawali, duk kuma wanda ya yi sallah a alhali an zo da abinci za a ci, ko a lokacin da yake cikin matsuwa da bahaya ko bawali ko tusa, to sallarsa naƙasasshiya ce, amma ta yi kamar yadda akasarin malamai suka bayyana, sai dai an so ya sake sallar amma ba wajibi ba ne sakewar.

Amma wasu daga cikin malamai da suka haɗa da malaman Zahiriyya an naƙalto cewa sun ce duk wanda ya yi sallah a irin wannan hali sallarsa ɓatacciya ce. Saboda haka ƴar uwa mustahabbi ne ki sake sallar amma ba wajibi ba ne a bisa fahimtar Jumhur na malamai. Dubi Alminhaaj na Nawawiy (5/46).

Allah S.W.T ne mafi sani.

WALLAHU TA'ALA A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. 

 ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam  

Post a Comment

0 Comments