𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum malam mene ne salatus tasbihi? Kuma yaya ake sallatus tasbihi? Kuma Mene ne ingancin ta?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikumussalam
warahmatullahi wabarakatuh.
salatus tasbihi wata sallace
mai daraja, Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ne ya ba da falalarta
kamar yadda hadisinta ya zo a cikin (MUSNADUL IMAM AHMAD DA SUNANUL IBNUL ABU
DAWUD) Hadisine ingantacce babu shakka gameda ingancinshi, koda yake akwai wasu
malamai da suke ganin wasu ruwayoyi basu ingantaba, amma dai asalin hadisin ya
tabbata.
Malaman Hadisi irin su:
Al-Imam Muslim, da Al-Imam Abu-Dawud, da Al-Imam As-Subkiy da Al-Hafiz Ibn.
As-Salah, da Al-Hafiz Ibn. Hajr Al-Asƙalaniy,
da Al-Mujaddid Al-Albaaniy (Rahmatul Laahi Alaihim) duk sun kyautata wannan
hadisin saboda yawan hanyoyinsa. Kamar yadda aka samu wasu malaman irin su:
Al-Imam Al-Baihaƙiy
yana cewa: ‘Abdullah Bn Al-Mubarak ya kasance yana yin Salatut-Tasbihi, kuma
sashen malaman ƙwarai
(Sahihai) sun riƙa
koyonta daga sashensu.
Annabi sallallahu alaihi
wasallam ya cewa kawunshi, wan mahaifinshi (ABBAS) ya kawu ina sonka zan yi
maka wata kyauta, zan yi maka wani alkhairinda Allah zai gafarta maka
laifuffukanka baki ɗaya, kananan su da manyansu
yafadi falala masu yawa.
Ita sallar raka'a huɗu ce
(4) akeyinta kamar (AZAHAR KOH LA'ASAR KOH ISHA'A) duk yanda kayita daidaine
inkaso za ka yi karatunka a bayyane koh kayi asirrance koh kayi dukka raka'a huɗun a
bayyane koh kayi raka'a biyun farko a bayyane raka'a biyun karshe a sirrance
kamar (ISHA'A), ita ana karanta mata (FATIHA DA SURAH) dukka raka'a huɗun.
Idan ka gama karatun (FATIHA DA SURAH) ba ruku'u za ka yiba, sai ka karanta:
SUBUHANALLAH, WALHAMDULILLAHI, WALA'ILA HA'ILLALLAHU, WALLAHU AKBAR Sau goma sha
biyar (15) a tsaye bayan karatun FATIHA da SURAH kafin kayi ruku'u; sannan kayi
ruku'u kayi zikirorin da akeyi a ruku'u sannan ka karanta: SUBUHANALLAH,
WALHAMDULILLAHI, WALA'ILA HA'ILLALLAHU, WALLAHU AKBAR sau goma (10) sannan ka
dago daga ruku'u, bayan kayi Addu'an dagowa daga ruku'un sai kuma kamaimaita: SUBUHANALLAH,
WALHAMDULILLAHI, WALA'ILA HA'ILLALLAHU, WALLAHU AKBAR sau goma (10), sannan
kayi sujuda bayan Addu'an sujuda sai kamaimaita: SUBUHANALLAH, WALHAMDULILLAHI,
WALA'ILA HA'ILLALLAHU, WALLAHU AKBAR sau goma (10), sannan ka dago daga sujuda
kayi zikirin da akeyi a tsakanin sujuda guda biyu sannan kamaimaita:
SUBUHANALLAH, WALHAMDULILLAHI, WALA'ILA HA'ILLALLAHU, WALLAHU AKBAR sau goma
(10), sannan ka koma sujuda ta biyu bayan zikirin sujuda sai kamaimaita:
SUBUHANALLAH, WALHAMDULILLAHI, WALA'ILA HA'ILLALLAHU, WALLAHU AKBAR sau goma
(10), sanda ka ɗago daga sujuda ta biyu kada
ka mike tsaye kayi abun da ake kira (JALASATUL ISTIRAHA) shi ne dan zaman da
akeyi tsakanin rakaoi guda biyu sai kamaimaita: SUBUHANALLAH, WALHAMDULILLAHI,
WALA'ILA HA'ILLALLAHU, WALLAHU AKBAR sau goma (10) idan ka haɗasu
sun zama saba'in da biyar (75) ke nan a raka'a ɗaya,
haka za ka maimaita ta a raka'a ta biyu, data uku, data huɗu,
idan ka haɗasu dukka ya zama (300) ke nan a raka'a
huɗu.
Shari’ar Musulunci ta kwaɗaita
wa masu Imani yin wannan sallar. Tana jawo wa musulmi gafarar Zunubansa na
farko, da Zunubbansa na ƙarshe,
da Zunubbansa daɗaɗɗu,
da Zunubbansa sababbi, da Zunubbansa da ya yi cikin kuskure, da Zunubbansa da
ya yi da gangan, da Zunubansa ƙanana
da Zunubbansa manya, da Zunubbansa na ɓoye,
da Zunubbansa na bayyane.
Manzon Allah tsira da
Amincin Allah su tabbata agareshi ya ce; duk laifukanka za a gafarta maka In
sha Allah, za ka iyayinta da rana ko dare. Manzon Allah (Sallallahu Alaihi
Wasallam) ya ce idan za ka iya yi kullum kayi, idan ba za ka iyaba ka rinkayi
duk mako (Sati) idan ba za ka iya yiba karinkayi duk wata, idan ba za ka iya yiba
karinkayi duk shekara, Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce ko sau ɗaya
ne a rayuwarka kayi kafin Allah ya ɗauki
ranka, tanada lada. Wannan ita ce ake kira da salatus tasbihi.
WALLAHU A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.