𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum da fatan Malam yana lafiya tare da dukkan jama'arsa baki daya. Malam tambayata Ita ce mene ne hukuncin matar da mijinta ya tafi bai dawo ba har sai da aka Shekara 20 sannan ya dawo, bayan ita kuma ta auri wani mijin?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikumus salam wa
rahmatullah.
A bisa tsarin Shari'ar
Musulunci (musamman a Mazhabin Malikiyyah), hukuncin matar da mijinta ya tafi
kuma ta sake aure ya danganta da yadda ta bi matakan rabuwa da shi kafin ta yi
auren.
Bisa Mazhabin Malikiyyah
idan mace mijinta ya tafi ya barta, kuma babu wani labari daga gareshi, to tana
da damar takai maganarta wajen Alkali. Shi Alkalin zai bayar da izini ga
waliyyan mijin nata suje su nemoshi aduk wuraren da ake tsammanin samunsa.
Idan har aka shekara huɗu ba
a samoshi ba, kuma babu labarinsa, to Alkali zai ba ta damar yin takaba
(iddatul wafat) tsawon wata huɗu da kwana goma. Daga nan
kuma idan ta kammala to tana da damar sake yin wani sabon aure idan ta samu
wani mijin.
Idan irin waɗannan
matakan aka bi har aka kaiga yin sabon auren, to shi tsohon miji bashi da
hujjah a karkashin shari'ar addinin Musulunci.
Idan ba ta kai maganar ga
Alkali ba, ta yanke hukunci da kanta ko ta auri wani ba tare da an raba auren
ta na farko ba ta hanyar shari'a ba, to auren da ta yi na biyu ba tacce ne (ba
ya inganta), kuma dole ne a raba tsakaninsu. Mijinta na farko yana da damar ya
dawo da ita idan ya ga dama
Wannan ita ce fatawar
Mazhabin Malikiyyah da Hanbaliyyah. Amma su Mazhabar Habafiyyah sun tafi a kan wani
ra'ayin saɓanin wannan. Su suna ganin cewa matarsa
ba za ta yi sabon aure ba, har sai bayan Ƙarewar
sa'anninsa. Misali kamar bayan sa'anninsa sun cika shekaru tamanin ko fiye da
haka aduniya.
WALLAHU A'ALAM.
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.