𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum mallam muna neman shawara ne wato budurwa ce ta bi khudubar zuciya har takai ga ta aikata abin da bai kamata ba (wato zina) da wani saurayi yanzu ta yi nadamar abin da ta aikata, tana son ta yi aure ne yanzu. To mallam shawara da take nema shi ne, za ta iya fada ma saurayin da za ta aura abin da ta aikata a baya?
SHIN ZAN IYA SANAR DA
SAURAYINA CEWA NA TAƁA AIKATA ZINA?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikumussalam
warahmatullahi wabarakatuh.
A'a bai kamata ta
bayyana masa ba. Domin hakika Manzon (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya gaya wa
Sahabbansa watarana "Kuyi mun mubaya'ah akan cewa ba za ku yi shirka da
Allah ba. Ba za kuyi zina ba, ba za kuyi sata ba. Kuma ba za ku kashe wani rai
wanda Allah ya haramta ba, sai da hakki. "Wanda ya cika wannan alkawarin
daga cikinku to ladansa yana wajen Allah. Wanda kuma ya aikata wani abu daga
ciki kuma akayi masa Uƙuba akansa (anan duniya) to wannan kaffarah ce gareshi.
Wanda kuma ya aikata wani abu daga ciki kuma Allah ya suturceshi to lamarinsa
yana wajen Allah. Idan yaso ya yi masa rangwame, idan yaso kuma ya yi masa
azaba". Bukhariy da Muslim ne suka ruwaito ta hanyar Sayyiduna Ubbadah bn
Samit (RA).
To kinga a nan Annabi
(Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ba da shawara ga masu manyan zunubai daga cikin
al'ummarsa cewa in dai Allah ya rufa maka asiri bai kamata ke kuma ki tona ba.
Kuma a cikin wani hadisin wanda Imamul Bukhariy da Muslim suka ruwaito, Manzon
Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) Ya ce "Dukkan al'ummata za a gafarta
musu amma banda masu bayyanar da zunubi. Yana daga cikin bayyanar da zunubi
mutum ya aikata wani abu cikin dare, sai ya wayi gare alhali Allah ya riga ya
rufa masa , jiya na aikata kaza da kaza, alhali ya kwana Allah yana suturceshi,
amma ya wayi gari yana yaye suturar daga jikinsa".
Shawarata gareta shi
ne taji tsoron Allah ta tuba zuwa gareshi da irin cikakkiyar tubar da yake nema
daga bayinsa. Sannan kuma ta yi gum da bakinta kada ta gaya ma saurayin nata
kuma kada ta kuskura ta gaya ko wane mahaluƙi, Domin sanarwar za
ta iya zama dalilin rabuwarsu ko kuma zubewar Ƙimarta da mutuncinta
awajensa.
WALLAHU A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.