Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Zuwa Wajen Mai Ba Da Maganin Mayu

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓

Assalamu alaikum. Malam wani mai ba da maganin mayu ne da ya taɓa hannun mutum yana gane mayu ne ko maleria, shin ya halatta a je wajansa ko a'a?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumussalam warahmatullahi wabarakatuh.

Wannan kowane ne sunansa na yanka da Allah da manzansa (SAW) suka bashi shi ne: BOKA, MUSHIRIKI, TANTAGARYAR KAFIRI. Bai halatta yin kara wajan sakaya ko ɓoye wannan sunan nasaba, Boka ne, mushiriki, kafiri ne kuma zindiƙi.

Sannan Abun da yakamata musani (maita) Bafa dabi'ah ce ko halitta ce da Allah yake halittar mutum da ita ba ne, a'a bokanci ne tsafi ne kowama in ya kafirce wa Allah ya zama kafiri mushiriki matsafi zai zama (maye) surkullene kawai da tsafi mutum yake yana iskancin da yake da sunan (maita) kuma kafircine tsantsa.

Sannan duk babu mai ba da maganin maita ko sihiri ko Aljanu yadda Allah da manzansa (SAW) suka koyar suka yarda sai Ahlus SUNNAH maibin tafarkin magabata na ƙwarai.

Sannan sai wanda ya san aƙida kuma ya fahimceta, komai tauhidin mutum inba yasha aƙida sosai ba in ya jefa kansa yakan fada cikin kura-kurai masu yawa. Domin ba duk mai tauhidi ba ne ya san aƙida, amma duk wanda ya san aƙida ya san tauhidi. To mas'alar ta aiƙdace dan haka yakamata asanya lura sosai akanta.

Hadisai dayawa sun tabbata da suke nuna haramcin zuwa wajan boka da matsafi damai bugun kasa, Daka cikinsu akwai hadisin safiyyah Allah ya kara mata yarda Annabi Sallallahu Alaihi wasallam ya ce: (Duk wanda ya je wajan ɗan duba ko boka ko matsafi ya tambaye shi kuma ya gaskata shi ba za a karbi sallar sa ta kwana Arba'in ba) Muslim.

Da hadisin Mu'awiyyah bin hakam Allah ya kara masa yarda wanda Muslim yaruwaito Daka Abu huraira Allah ya kara masa yarda ya ce: Manzan Allah Sallallahu Alaihi wasallam ya ce: (Wanda ya je wajan boka ko ɗan tsubbu, ko ya sadu da mace ta duburarta, Hakika ya yi bara'a (Karyata) Abun da Aka saukarwa Annabi muhammad (Sallallahu Alaihi wasallam.)

Abu dauda. Malamai suka ce: Haramun ne yin tsafi ko canji ko bokanci ko bori ko zuwa inda ake yin su, ko gaskata masu yin su, haramun ne bayar da kuɗi ko dukiya da na aiwa mutum su, duk wanda Allah ya jarabce shi da ɗaya dake cikinsa wajib ne ya gaggauta tuba. Fatawa Imamun Nawawi (230) Allah ya jikansa.

Saboda haka haramun ne zuwa wajan wannan mutumin domin boka ne, kafiri ne, mushiriki ne wanda yai baram-baram da Allah maɗaukakin Sarki, wajibine a yake shi a kore shi daka gari dan kange mutane daka fadawa kafirci bayan sun yi Imani.

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

 ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam   

Post a Comment

0 Comments