TAMBAYA❓
As-salamu alaykum Allah ya karɓa malan lafiya da nisan kwana dan Allah. Malam ina tambaya mene ne hukuncin wanda baya zuwa sallar asuba yake yi a gida tare da matarsa na gode
AMSA:‼️
Wa alaikumus salam wa
rahmatullahi wa barakatuhu.
Namiji wanda yake da lafiya
kuma bashi da wani uzuri na shari'a, bai kamata ya riƙa yin sallar Asuba a gida tare da
matarsa ba alhali yana da ikon zuwa masallaci. Malamai sun saɓa
dangane da hukuncin sallar jam'i a masallaci, inda wasu suka ce wajibi ne, wasu
kuma suka ce sunnah ce mai ƙarfi.
An ruwaito daga Abu Hurairah
رضي الله عنه cewa wani makaho ya zo wurin Annabi (SAW) ya ce: “Ya Manzon Allah,
bani da wanda zai riƙa
jagorantar ni zuwa masallaci. Sai ya nemi izinin yin sallah a gidansa, Annabi (SAW) ya bashi izini. Amma lokacin
da ya juya zai tafi, sai Annabi (SAW)
ya
kira shi ya ce masa:
هَلْ
تَسْمَعُ النِّدَاءَ بِالصَّلَاةِ؟ قَالَ نَعَمْ، قَالَ فَأَجِبْ
Ma'ana: Kana jin kiran
sallah? Ya ce: “Eh.” Sai Annabi (SAW)
ya
ce: “To, ka amsa kiran.” (Sahihul Muslim, hadisi na 653).
Wannan hadisi yana daga
cikin hujjojin malamai waɗanda suke ganin wajibi ne
namiji ya halarci sallar jam'i a masallaci idan zai iya, har ma da wanda yake
da nakasa idan yana iya zuwa ba tare da wahala ko cutarwa ba.
Haka kuma Annabi (SAW) ya ce: “Sallar jam'i tafi
sallar mutum shi kaɗai da darajoji ashirin da
bakwai.” (Sahihul Bukhari, hadisi na 645; Sahih Muslim, hadisi na 650).
Saboda haka, idan mutum yana
da lafiya kuma babu uzuri, ya riƙa
zuwa masallaci domin samun falalar sallar jam'i da kauce wa saɓawa
ga umarnin Annabi ﷺ. Idan kuma ya yi sallah tare da matarsa a
gida, sallarsu tana iya inganta idan sun cika sharuɗɗan
sallah, amma hakan baya kawar da laifin barin jam'i a masallaci bisa ra'ayin
malamai waɗanda suke ganin wajibi ne.
A ƙarshe, ina nasiha ga dukkanmu damu ji
tsoron Allah, mu kiyaye sallolinmu, musamman sallar Asuba, mu riƙa halartar masallaci idan mutun nada iko
haka. Kada mutum ya mayar da gida wurin yin sallolin farilla kawai saboda
kasala, alhali masallaci yana kusa kuma babu wani uzuri.
Allah Ya samu kasance cikin
waɗanda
suke kiyaye sallolinsu kuma suke bin Sunnah ta Annabi ﷺ.
WALLAHU TA'ALA A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.