Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Tufafin Da Kare Ya Taba

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓

Assalamu alaikum malam mene ne hukunci shafar kare? Kuma mene ne hukuncin tufafinda kare ya taba, shin za su yi sallah?

HUKUNCIN TUFAFIN DA KARE YA TAƁA

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumussalam warahmatullahi wabarakatuh.

Yawun kare najasa ne, wajibi ne awanke abunda ya taɓa na kwano ko tufafi ko jiki, saboda fadin Annabi Sallallahu Alaihi wasallam (Ku tsarkake kwananku Idan kare yasha ko yaci abu a cikinsa sau bakwai, wanki ukun farko da turbaya).

Idan ya taɓa tufafi, idan aka sanya tufafin a cikin ruwa mai tsarki aka wankeshi har alamar najasar yawun nasa yagushe, tufafin ya tsarkaku gaba ɗaya daka najasar kare dama waninta, Amma wanki ukun farko da turbaya, ko abunda zai zama amadadin turbaya wajan gusar da datti, kamar sabulu, ko omo. Fatawa Lajnatul Da'imah (4/196).'

Bai halatta mutum ya dunga runguma ko chakuduwa da kare ba, saifa a cikin Al'amuranda shari'a ta yi rangwame akansu, kamar mafarauci ko ɗaukar karen gadi agida ko tsaron dabbobi. Domin duk wanda ya'aje kare koyake chakuda da shi yake shafarsa in dai ba karen farauta ko gadi bane, kowacce rana za a rage masa (Ƙiradi) ɗaya na ladansa ko (Ƙiradi biyu).

Daga Ibnu Umar Allah yakara da shi ya ce: Na ji manzan Allah Sallallahu Alaihi wasallam yana cewa: (Wanda duk yariki kare, inba wanda ake korawa dan farauta ba ko gadin kayan gona ko dukiya ba, kowacce rana ladansa yana raguwa da (ƙiradaini)). Bukhari (5059) da Muslim (2941).

Ƙiradi, Sayen magana ne na lada maiyawa daza a dinga yankewa mutum kullum.

Najasar kare tana cikin mafi girman najasar dabbobi, domin najasar kare ba ta tsarkakuwa saida wankewa sau bakwai ukun farko da turbaya, har alade da Allah ya fada cewa haramunne gaba dayansa, kuma kazanta ne najasane najasar sa ba takai wannan haddin wankewa sau bakwai ba, kare najasane mummuna .

Sai dai Abun bakin ciki da takaici za ka samu wasu mutanen sun rudu da koyi da kafirai wadanda suke amfani da ababe masu kazanta da najasa, suma sai suka zama suna daukar ko ajiyar kare dakiwansa ba tare da wata bukataba, suna tsaftaceshi tare da cewa har abada ba zai tsarkaku ba, ko da za a tsaftaceshi da ruwan kogi, domin najasarsa ayyananniya ce.

Nasiha ga irin waɗannan mutane ita ce, Su tuba zuwaga Allah su fitar da karnuka daka gidajensu. Amma wanda aka bukata, takama kamar nafarauta ko gadin dukiya ko gida, babu laifi a kan hakan, saboda izinin da Annabi Sallallahu Alaihi wasallam ya ba wa ta aje kare.

Shafar kare ba tare da hannunka yana jikeba ko tufarka tana jike da ruwaba ko jikinka, to wannan shafar ba ta sanya hannun ko rigar ko jikinka ya zama mai najasa.

Idan kuma akwai danshin ruwa to wannan tufar tazama mai najasa ko hannun Abisa ra'ayin mafi yawan malamai, wajibine wanke tufar ko hannun bayan karen ya taɓa sau bakwai ukun farko da turbaya, haka idan yaci ko yasha a cikin kwanon dakake amfani da shi wajibine wankeshi sau bakwai. Kamar yadda ya tabba ta a cikin Bukhari da Muslim daka hadisin Abu Hurayrah, Allah yakara masa yarda, daka Annabi Sallallahu Alaihi wasallam ya ce: (Idan kare yasha a cikin kwananku kuwankeshi sau bakwai ukun farko da kasa. Majmu'u fatawa Ibnu Usaimeen (11/246). da Fatawa Islamiyyah (4/44).

Dan haka idan akwai danshi ko ruwa kare ya taɓa tufafin dole ne saika wanke tufar sau bakwai wanki Ukun farko da kasa, sannan kayi Sallah da ita.

WALLAHU A'ALAMU.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam   

Post a Comment

0 Comments