Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Matar Da Take Daukar Kudin Mijinta Ba Tare Da Saninsa Ba

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓

Assalamualaikum Barka da safiya Malam Dan Allah 🙏 malam mijin ƙanwata ne yada rufin asiri Allah ya wadatashi Amma ita inta tambaye shi kuɗin kitso, kunshi da abin da ba arasa ba sai yahanata ita Kuma Babu. Yanda za ta yi inda ya ajje kuɗin shi sai ta dau Wanda zai ishe ta kunshi da kitso malam Hakan Babu lefi Allah ya ƙarawa malam lpia

HUKUNCIN MATAR DA TAKE ƊAUKAR KUƊIN MIJINTA BA TARE DA SANINSA BA

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumus salam warahmatullahi wabarakatuhu.

Idan mijin ya ba ta kuɗin kitso ko kwalliya da yardarsa, to babu laifi ta yi amfani da kuɗin wajen abin da aka ba ta domin shi. Amma idan ya ajiye kuɗinsa ne ba tare da ya ba ta izinin ɗauka ba, kuma tana ɗaukar kuɗin a ɓoye domin ta yi kitso ko kunshi, to bai halatta ba, domin dukiyar mijinta ce. Ko da yana hana ta ko yana wahalar da ita, ba za ta ɗauki kuɗinsa a ɓoye ba sai idan akwai wani hakki na wajibi da yake hana ta, kamar abinci domin shi hakkine na musamman kuma wannan yana da ƙa'idodi na musamman.

Matar da take ɗaukar kuɗin mijinta ta yi amfani da su saboda mijinta maƙeƙe ne ko mai ƙoro, ba ya ba su abincin da zai ishe su, to ya halasta ta teɓi kuɗinsa su ci abinci gwargwadon buƙatarsu ba tare da ɓarna da almubazzaranci da dukiyar ba, dalili a kan haka shi ne: Nana A'isha Allah ya ƙara mata yarda ta ruwaito hadisi cewa: Lallai Hindu ‘yar Utbata ta ce: Ya Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) lallai Abu Sufyana ya kasance mutum ne maƙeƙe, ba ya ba ni abin da zai ishe ni da ‘ya’yana, face sai abin da na ɗauka daga wurinsa bai sani ba, sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya ce: "Ki ɗauki abin da zai ishe ki da ‘ya’yanki tare da kyautatawa". Bukhariy 5364.

Wannan hukuncin ya keɓanta ne kaɗai ga matar da mijinta ba ya ciyar da su yadda ya dace saboda maƙo alhali yana da hali. Amma duk matar da mijinta ke ba su haƙƙoƙin ciyarwa gwargwadon hali, to idan ta ɗebi kuɗin mijinta bai sani ba ta yi amfani da su, tabbas ta ci haramun, sai ta biya shi gobe Alƙiyama, kuma abin da ta yi sunansa ha'inci, ko zamba cikin aminci.

Idan abin da yake ba ta shi bai ishe ta ba, hanya mafi kyau ita ce ta yi masa magana cikin ladabi, ta bayyana masa bukatarta, ko ta rage abin da za ta kashe gwargwadon abin da ya ba ta.

Allah Ya gyara tsakaninsu, Ya sa mijin ya riƙa kyautata mata, ita ma ta riƙa kiyaye amanarsa. آمين.

WALLAHU TA'ALA A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

 ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam   

Post a Comment

0 Comments