Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Kiss Ta Hanyar Waya

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓

Assalam alaikum. Malam shin ya halatta mutun ya yi wa budurwarsa kiss yayin da suke waya?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam warahamtullahi Wabarkatuh

Bai halatta mutum ya yi wa budurwarsa kiss (sumbata) ko muryar sumbata ta waya ba, koda kuwa an riga an tsayar da maganar aure (baiko). yin hakan haramun ne.

Musulunci ya hana kowane irin abu da zai ja mutum zuwa ga zina ko kuma ya motsa masa sha'awa kafin a daura aure, kamar fadin kalaman batsa, nuna sha'awa, ko fitar da sautin sumba (kiss) a waya. Allah Ta'ala yana cewa

وَلَا تَقْرَبُوا الزِّنَا ۖ إِنَّهُ كَانَ فَاحِشَةً وَسَاءَ سَبِيلًا

 "Kuma kada ku kusanci zina. Lalle ne ita ta kasance alfãsha ce kuma tã mũnãna ga zama hanya." (Suratul-Isra'i: 32).

Bawai haka kawai Allah s.w.a ya ce kada akusanci zina ba sai dai kasancewar Ƙanƙanin abu zai iya kaiwa ga zinar, Kamar yadda nassi ya tabbatar akwai zinar ido akwai ta baki, ruwan Al'aurane ya gasgata ko akasin haka, dan haka bai halatta ba sai dai idan ma'auratane.

Wannan yana daga cikin ire iren abubuwan da fitsararrun samari da 'yan matan zamani suka jirkiro kuma yana daga cikin abubuwan da suke cire musu kunya, kuma yake afkar dasu acikin zina. Misali saurayi da budurwar da suka saba yi wa Junansu Kiss ta waya, da zarar sun Haɗu FACE TO FACE, babu abin da za suyi tunani illa su aiwatar da Kiss ɗin azahiri. Irin wadannan al'adun turawa ne, bai dace da dabi'unmu da addininmu ba. Mu a addininmu ba ayin kowanne irin Kiss sai bayan an ɗaura muku aure da juna.

Kunya tana daga cikin ginshikin imanin Musulmi. Saba wa wannan aiki yana cire wa saurayi da budurwa kunya a tsakaninsu, wanda hakan kan kai su ga aikata abin da ya fi haka azahiri idan sun haɗu. Annabi Sallallahu alaihi Wasallam yana cewa: ''Kunya tana daga Imani. Duk wanda bashi da kunya, to bashi da Imani.." kuma ya ce "duk wanda ya yi kama da wasu mutane, to tabbas yana cikinsu".

Malamai sun bayyana cewa duk wani abu da zai ja mutum zuwa ga saɓon Allah ko ya tura shi zuwa ga faduwa a cikin haramun, to shi ma an haramta shi.

Don haka duk wanda yake so ya haifi 'ya'ya masu albarka, to wajibi ne ya nuna dabi'u masu kyau irin na Musulunci tun alokacin neman auren mahaifiyarsu.

Wanda ya kiyaye dokokin Allah, tabbas Allah zai kiyaye shi, wanda ya bi son zuciyarsa, to Allah yana nan a madakata.

Allah ya shirye mu baki daya, Yasa masu yi su daina. Ameen

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

 ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam  

Post a Comment

0 Comments