Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Sallah A Bayan Limamin Da Yake Kuskure A Cikin Karatun Fatiha

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓

Assalamu alaikum malam Khamis mene ne hukuncin sallah a bayan limaminda yake kuskure a cikin karatun fatiha, kuskurenda ke canja ma'ana yana cewa {ahadina} maimakon [ihdina]?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumussalam warahmatullahi wabarakatuh.

Wanda yake kus-kure a cikin karatun fatiha kus-kurenda yake canja ma'anar aya liman ne ko mamu sallarsa ta lalace, domin fatiha rukuni ce daka cikin rukunan sallah, wajibine iya karatunta sosai, yakoyi yanda akeyinta ya iya, sai in ya kasa iyawa bayan ya yi iya kokarinsa ya je makaranta yazauna gaban malamai amma yakasa iyawa saboda haka Allah ya yishi, Allah baya dorawa rai wani abu sai wanda za ta iyayinsa, Amma idan liman ne ba za ka yi sallah a bayansa ba sai inkaima irinsane ko bakama kaishiba wajan iya karanta fatiha ɗin.

Imamun Nawawi Allah ya jikansa da rahama Ya ce: Limancin wanda yake kus-kure akaratunsa makaruhine, saika lura idan kuskuren baya canja ma'ana kamar ya ce (ALHIMDI LILLAHI) maimakon (ALHAMDULILLAHI) Sallarsa ta yi wanda yabishi shi ma sallarsa ta yi, amma idan kus-kuren yana canja ma'ana kamar (AN'AMTU KO AN'AMTI) mai-makon (AN'AMTA) sallarsa ta ɓaci kamar (SIRADUL MUSTAƘEEM KO SIRADIL MUSTAƘEEM) sallarsa ta ɓaci idan ba harshensa ba ne haka to wajibine ya je yakoya, idan ba zai iya gyarawa ko lokaci ya yi karanci zai yi sallar haka sai yarama idan ya je yakoyo, Bai halatta abishi limanci ba.

Idan harshensa ba zai iya gyara kus-kuren ba, ko ba zai iya zuwa inda zai koyo ba, idan a fatiha ne yake wannan kuskuren sallar mutum irinsa da shi kansa ta inganta, sallar wanda yake da lafiyayyen harshe a bayansa ba ta inganta ba Amma idan ba a fatiha ba ne yake kus-kuren sallarsa ta yi da wanda ya yi sallah a bayansa. Rauzatul dhalibeen (1/350).

Ibnu ƙudama Allah ya jikansa ya ce: Idan wanda bai iya karatu ba ya limanci wani irinsa da wanda yake ya iya karatu to (Wanda ya iya karatu zai sake sallar shi kaɗai) domin sallarsa ba ta yi ba, amma idan irinsa ya limanta sallarsu ta yi. Sannan sai ya ce: Wanda yake barin wani harafi cikin karatun fatiha saboda ba zai iya fadinsa ba ko yake canjashi dawani, kamar mai in'inar da yake maida RA'UN (ر ) tazama GAINUN (غ ) komai saurin bakinda yake shigarda wani harafi cikin wani, koyake kus-kurenda yake ba ta ma'ana kuma bashida ikon gyara wannan kus-kuren, hukuncinsa shi ne kamar wanda bai iya karatu da rubutu ba ne wanda ya iya karatu dai-dai bai halatta yabishi sallah ba, Amma in ya samu wani irinsa yahalatta koya yabi kowa sallah atsakaninsu, idan kuma yana da ikonda zai iya gyara wannan kus-kuren amma yaki yagyara koya je yakoyo sallarsa ba ta yi ba haka sallar wanda yabishi.

Ibnu ƙudama Allah ya jikansa Ya sake cewa: Makaruhine limancin wanda yake kus-kuren karatu wanda baya ba ta ma'ana, kamar yanda Ahmad yafada, wanda ya iya karatu idan yabishi sallarsa ta yi, domin ya zoda wajibi, idan kuma yana ba ta ma'ana amma ba a fatiha ba ne, sallarsa ta yi haka wanda yabishi shi ma tasa ta yi, sai dai idan dagan-gan yake kuskuren sallarsa ta lalace.

Idan baya kus-kure wanda yake ba ta ma'anar ayoyi yahalatta a yi sallah a bayansa tareda wajabcin zuwa koyan karatun a kansa, idan kus-kuren ba a fatiha ba ne yana tauye sallah ne baya ba tata, sallah a bayan wanda ya iya kyautata karatu shi ne yafi babu kokwanto, Bai halatta ga shugabanni su dora irin waɗannan jahilai ba suna limantar mutane, in shugabanni da waɗanda hakkin sanya limami yake akansu basa tsayawa tsayin daka wajan sanya wanda yadace alimanci to sun yi tarayya dasu wajan zunubinsu. Almugniy (3/32-39) Kamar yanda ya zo afatawa lajnatul da'imah (2/527)da Majmu'u fatawa bin baaz (12/98-99)

Saboda haka bai halatta limaminda yake canja ma'anar aya karatun fatiha, cewa (AHDINA) maimakon (IHDINA) canja ma'anane, shikansa sallarsa ba ta yi ba in ya yita indai zai iya gyara kus-kuren ko yana da da inda zaije akoya masa ya iya, ba harshen sane hakaba. Wajibine acanjashi dawanda ya iya kyautata karatu, in hakan zai iyu ba tareda wata fitinaba, ai masa nasiha yagyara inko duk ba zai iyu ba, saiku watse kudena binsa sallah kusanya wanda ya iya karatu yadunga janku sallah, shikuma ku kaurace masa harsai ya je yakoyo koya gyara.

Wanda yafi chanchanta da ya yi limanci ga jama'a shi ne wanda yafi su sanin littafin Allah, watau yafisu aiki da abin da Alkur'ani ya kunsa koda bai haddace dukka ba, ya kuma kassance mai nisantar abin da Zai zubar masa da mutuncinsa ya kuma kassance yana wa mutane limanci ne da yardarsu ba a kan dole ba (Sun amince da shi) dadai sauran abubuwan da akeso mutum ya cika su ko kuma ya kassance yana da su kafin ya zama liman kamar yadda hadisai za su nuna mana su.

Daga Abdullah Ɗan Mas'ud (RA) Ya ce Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) Ya ce wanda yafi mutane karatun Alkur'ani shi ne zai jagoranci Mutane sallah, idan sun kassance a cikin karatun(Alkur'ani daidai suke to sai wanda yafi su sanin Sunnah (watau yafisu sanin Hadisan Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya jagorance su, idan sun kassance a cikin sanin sunnah dai dai suke to, sai wanda ya rigasu yin hijra, ya jagorancesu, idan a cikin hijrah Dai dai suke sai wanda yafisu Yawan shekaru ya jagorancesu.

A cikin hadis mai na'ana kamar haka,ku sanya al'amurran addininku a hannu masu ilminku, limamanku sune makarantunku, amma in agarinku Ko anguwarku akwai masallaci Da aka zaɓi liman Ratibi watau wanda jama'a suka zabeshi idan wani ya yi wa, wani izini da ya jagorancin mutane, to ba laifi Sai a kula da kyau, ba kawai idan an kira sallah ba, liman ba zai zo, sai ace wane Zo kayi mana sallah, wannan wannan ya saɓa wa koyarwa addini.

WALLAHU A'ALAMU.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

 ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam   

Post a Comment

0 Comments