An Ciro Daga: Bakura, A.R., & Sani, A-U. (2026). Zogale a ƙasar Hausa: Magani, abinci, tattalin arziki. SAS Publishers. ISBN: 978-978-63958-1-4. https://doi.org/10.5281/zenodo.22682300
1.3 Zogale a Idon Duniya
Itaciyar zogale
ta shahara a ƙasashen Afirika, musamman
ma a ƙauyuka. Masana ilimin
kimiyyar tsirrai sun kira zogale da suna moringa. A ƙasashe da dama, da wannan sunan aka san ta.
Masu magungunan
gargajiya sun jima suna sarrafa ta wajen warkar da cututtuka da kuma matsayin
abinci mai gina jiki. Bayyanar nazarin ilimin kimiyya da bunƙasarsa ya wanzar da bincike game da zogale a
sassa daban-daban na duniya ciki kuwa har da Nijeriya. Sakamakon binciken ne ya
haifar da gano kimar ta, a matsayin magani da abinci da kuma abin sarrafawa a
masana’antu. A halin da ake ciki ana nomanta a nahiyoyi daban-daban kamar
Afirika da Amerika ta Kudu da Amerika Ta Tsakiya da kuma ƙasashen Sirilanka da Indiya da Mexico da Malesiya da
Filipin. Zogale tana da saurin girma da jure wa fari. Tana yi a wurare masu
yalwatattun ruwan sama da kuma ƙarancinsu,
kazalika kuma da yankuna masu zafi har ma da wuraren da babu
ingantacciyar ƙasar noma. Tana ɗaya daga cikin itatuwa da aka fi sanin ta da yawan amfani a duk faɗin duniya. Kusan komai na jikinta yana da amfani. Babu wani abun
yasarwa a jikinta.
Ƙasar Indiya ta zarce
kowace ƙasa a duniya a fagen noman
zogale. Ana noma kadada 38, 000, inda ake samar da ɗanyen kwanson zogale mai nauyin ton miliyan ɗaya da dubu ɗari ɗaya zuwa ɗari uku (1, 100, 000 – 1,
300, 000) a duk shekara.
An kafa babbar cibiyar ƙasa da ƙasa da ke gudanar da
nazarin kayan lambuna, domin rage talauci da ƙarancin rashin isasshen abinci mai gina jiki
a ƙasashe masu tasowa ta
hanyar inganta hanyoyin samar da kayan lambu tare da sahihiyar hanyar amfani da
su. Daga cikin ayyukkan wannan cibiya sun haɗa da binciken itaciyar
zogale.
Ana cin ganyen
zogale da kwansonta da aka ɗebo tun yana da taushi.
A ƙasar Indiya kuwa ana haɗa kwanson (ɓawon ‘ya’yan zogale) da
wasu kayan lambu a yi salad da su. Ana cin ɗanyen kwanson ko kuma
bayan an dafa shi.
A ƙasashe daban-daban ana magani da ganyen
zogale da ɓawonta da saiwarta da furenta da kuma
‘ya’yanta. Amfaninta bai taƙaita
ga ci da yin maganin gargajiya kawai ba. Sakamakon muhimmin sinadarin
da yake ƙunshe
cikinta, ana safarar ta zuwa ƙasashen ƙetare domin sayarwa. Kwansonta yana ƙunshe da sinadari kamar
PENICILLIN masu kashe ƙwayoyin
cuta waɗanda ake kira ANTIBIOTICS. Wannan ne ya sa ƙasashe kamar Ingila da Japan da Kanada da
wasu ƙasashen Gabas ta
Tsakiya suke buƙatar ta sosai. Tun fiye da
shekara goma da suka shuɗe, wani kamfanin ƙasar Indiya da ake kira da suna: “DRUM STICK
INDIA’ yake safarar kayan da aka sarrafa da zogale. Kamfanin ya shahara da yin
hulɗa da kamfanoni da hukumomin aikin gona da na kayan abinci da na
magunguna da kuma kamfunnan kayan kwalliya (ado).
Fiye da shekara
arba’in (40) da suka shuɗe, Hukumar Lafiya Ta
Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi amfani
da itaciyar zogale wajen kyautata lafiyar al’umma a ƙasashen da talauci ya yi wa katutu. Masana
sun tabbatar da cewa an ɓoye itaciyar zogale ne,
domin ɗimbin ribar da ake samu daga gare ta, ta
hanyar sarrafa ta ta fuskar magunguna da kayayyakin kyautata lafiya dangin
bitamin (vitamins) da gishirin ma’adanai mai kare lafiyar jiki (mineral
salts). Wannan ne ya sa manyan kamfanonin magunguna ba kasafai suke son bayyana
sinadarin da suke yin magunguna da shi ba, da kuma nau’o’in tsirran da suke tatso
sinadiran.
A nahiyar
Afirika kuwa, hukumomi da cibiyoyin nazari da bincike sun duƙufa haiƙan
wajen nazarin itaciyar zogale (moringa). Dr. Nworo A. Ozumsa da ke Sashen
Nazarin Ƙwayoyin Cututtuka Na
Jami’ar Nmandi Azikiwe, Akwa, ya gudanar da wani bincike a kan zogale, ga abin
da ya ce: “Haƙiƙa, a ƙididdigar baya-bayan nan da na aiwatar, na fahimci zogale yana
maganin cututtuka kimanin tamanin da ɗaya (81). Tana ma iya
warkar da kusan dukkan cututtukan da suke addabar jikin ɗan’adam. A can baya, mu masana kimiyyar zamani mun sha faman sukar
masu magungunan gargajiya da suke cewa, magani ɗaya yana warkar da
cututtuka ashirin (20). Yanzu kuwa, a ilmance mun gano
gaskiyar lamarin, domin an fahimci ganyen zogale yana iya warkar da cututtuka
masu yawan gaske. Ganyen zogale yana maganin ciwon suga da
zazzaɓin cizon sauro da rashin isasshen barci da dai sauran su.
Shi kuwa Dr.
Ozumba, wanda ya shekara goma sha ɗaya (11) yana nazarin
itaciyar zogale. Ya bayyana cewa: “Tun da na gane sirrin da yake ƙunshe cikin wannan itaciyar ban sake amfani
da maganin ƙarin gishirin ma’adanai da
jiki ke buƙata (miniral salts) irin
wanda kamfanonin magunguna suke sarrafawa ba. Sakamakon aikinsa bai kai ingancin wanda yake ƙunshe a cikin zogale ba. Masanin ya ƙara da cewa: A matsayinmu na masana masu
bincike, nauyin da ya rataya a wuyanmu shi ne, mu yi azamar bunƙasa itaciyar zogale domin sarrafawa a
masana’antu. Kuma mu yi ƙoƙarin ƙara mata kima.
Dr. I. M.
Bugaje cewa ya yi: “Amfanin zogale bai taƙaita
ga fannin abinci ba, domin tana tace ruwa. Idan aka fitar da mai da sauran
sinadaran da ake buƙata, tunkuzar ‘ya’yan
zogale tana iya tace ruwan sha da kawar da ƙwayoyin halitta (bacteria) masu haifar da
cututtuka.” Ya ƙara jaddada cewa: “Muna
iya tace ruwa ta amfani da ‘ya’yan zogale a maimakon alam (alib ko alimu) wanda
Nijeriya take kashe biliyoyin daloli domin sayo shi daga ƙasashen waje. Bugu da ƙari, zogale ba ta da wata illa a jikin
bil-Adam, don haka tana nan bisa yanayinta na ɗabi’a, alhali kuwa an san cewa alam na haifar da cututtuka da dama
wanda ya haɗa har da gurɓacewar jini.
Babban Daraktan
Kamfanin AVUCO Nigeria Limited Yohanna Dami cewa ya yi: “Zogale tana maganin
hawan jini da zazzaɓin cizon sauro da ciwon suga tare
da sauƙaƙe zafin zazzaɓin da masu ciwon ƙanjamau suke fama da shi. Su ma ‘ya’yan
zogale suna da mai (oil) mai daraja da ake sayarwa a kan dalar Amirka
goma ($10) kowace lita ɗaya a kasuwar duniya,”
kamar yadda Bakura da wasu (2019 sh. 52) suka kawo bayanin.
Shi ma Babban
Daraktan Cibiyar Bincike da Bunƙasa
Kayan Sarrafawa A Masana’antu (Raw Materials Research and Development Council
RMRDC), Farfesa Peter A. Onuwalu cewa ya yi: “Itaciyar zogale za ta taimaka
wajen samar da man abinci tare da sauran tsirrai masu samar da mai. A
lokaci ɗaya noman zogale da sarrafa ta zai kawo
mafita ga matsalar bayar da guraben aikin yi da kuɗaɗen shiga tare da kyautata lafiyar al’umma ta
hanyar samar da tsabtataccen ruwan sha”.
Yayin da
Farfesa Charles Wambede yake nasa bayani cewa ya yi: “Itaciyar zogale
tana ƙunshe da wasu fa’idoji
kamar haka:
a. Ganyen
zogale yana ƙara ƙarfin garkuwar jiki.
b. Tana ƙara kuzari.
c. Tana
taimakawa wajen zagayawar jini da bugawarsa.
d. Tana
taimaka wa aikin ƙoda
da hanta.
e. Tana
maganin gyambon ciki da sauransu
Masanin
ya ƙara da cewa, ganyen zogale
yana ƙunshe da nau’o’in sinadarai masu yawa kamar haka:
a. Ninki
bakwai (7) na bitamin SI (c) fiye da wanda yake cikin lemo.
b. Ninki
huɗu (4) na sinadarin kalsiyam, fiye da wanda yake
cikin madara.
c. Ninki
huɗu (4) na bitamin E (A) fiye da wanda yake cikin karas.
d. Ninki
biyu (2) na furatanin fiye da wanda yake cikin madara.
e. Ninki
uku (3) na sinadarin potassium fiye da wanda yake
cikin ayaba.
Ya kuma nuna cewa ‘ya’yan zogale suna ƙunshe da mai (oil) wanda yawansa ya kai kimanin kashi 38 zuwa 40 bisa ɗari (38-40%). Wannan man yana ɗauke da sifofi irin na man zaitun wanda ya shahara wajen daraja. Zogale za ta taimaka wajen magance ƙarancin abinci mai gina jiki. Nomanta zai samar da aikin yi da hajar sarrafawa a masana’antu, wanda zai taimaka matuƙa wajen bunƙasa tattalin arziki da rage talauci a ƙasashe masu tasowa.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.