Ticker

6/recent/ticker-posts

Takaitaccen Tarihin Samuwar Zogale a Kasar Hausa

An Ciro Daga: Bakura, A.R., & Sani, A-U. (2026). Zogale a ƙasar Hausa: Magani, abinci, tattalin arziki. SAS Publishers. ISBN: 978-978-63958-1-4. https://doi.org/10.5281/zenodo.22682300

 Na

Adamu Rabi’u Bakura

Da

Abu-Ubaida Sani

Zogale a Kasar Hausa: Magani, Abinci, Tattalin Arziki
1.2 Ƙasar Hausa

Ƙasar Hausa tana cikin nahiyar Afirka ta Yamma, a farfajiyar da yake tsakanin dazuzzukan da suke kusa da gaɓar Tekun Atilantika daga Kudu cikin Nijeriya zuwa hamadar Sahara a Arewa cikin ƙasar Nijar, kamar yadda Alhasan da wasu (1988 sh. 1) da Adamu (2017 sh. 36) da Gusau (2024) suka bayyana. A wani ra’ayin an nuna ƙasar Hausa tana tsakanin tafkin Kogin Chadi daga gabas, zuwa guiwar Kogin Kwara a can Yamma. Wannan ne ya sa ake kiran ta da suna “Sudan ta Yamma”. Ƙasar ta asali ta faro ne daga Lalle da Asodu da ke Arewa Maso Gabas da Agadas a cikin Jamhuriyar Nijar. Daga can ne Gobirawa suka taso sannu a hankali har suka iso mazauninsu na yanzu a Nijeriya.

A tasawirar Afirika kuwa, ƙasar tana tsakanin layi na goma sha biyar (15N) zuwa na goma sha takwas (18N) a Arewa da Ikwaito. A Gabas da layin Greenwhich kuwa tana tsakanin layi na takwas (8E) zuwa na goma sha biyu (12E).

Bisa la’akari da waɗannan bayanai, ana iya cewa ƙasar tana shimfiɗe a farfajiyar Afirka ta yamma, a Arewacin Nijeriya. Ta kwarara har cikin ƙasar Nijar, wajen Maraɗi da wasu garuruwa. A Gabas ta yi iyaka da ƙasar Barno, kan iyaka da Haɗeja. Yamma kuwa ta yi iyaka da wani sashe na Dahome, wato Benin a gaɓar Kogin Kwara. A Kudu ta yi iyaka da ƙabilaun Gwari, da na kudanci Zariya da Yawuri da na kudanci Bauchi, (Alhassa, 1988 sh. 1) da (Adamu, 2017 sh. 36).

Ƙasashen Hausa kuwa sun haɗa da: Kano da Katsina da Daura da Zariya da Zamfara da kuma Arewacin Jahar Bauchi. A ƙasar Nijar kuwa, akwai: Ƙwanni da Damagaran da Maraɗi da sauransu (Alhassan, 1988: 1).

1.2.1 Sunayen Zogale a Yankunan Ƙasar Hausa

A faɗin ƙasar Hausa, itaciyar Zogale tana da sunaye iri-iri da suke nuna bambancin karin harshe da al'adun kowane yanki. Waɗannan sunaye suna ɗauke da tarihin tafiyar da wannan itaciya ta yi tun daga Asiya har zuwa cikin gidajen Hausawa. Daga cikin sunayen akwai:

1. Zogale, Zogala-gandi, Tamakka: Waɗannan su ne sunayen da suka fi yaɗuwa a mafi yawan sassan ƙasar Hausa, musamman a jihohin Kano, Kaduna, Katsina, da Sakkwato. A wasu yankunan kuma ana kiran ta da zogala-gandi wato "zogale babba" don nuna girman itaciyar idan ta girma sosai, ko kuma don bambanta ta da wasu nau'ukan da ba su da girma. Har ma akan yi mata kirari kamar haka:

Zogale-gandi mataimaki,

Ana saran ka kana fure.

Wasu kuma sukan ce:

Zogala-gandi mataimaki,

Ana yagar ka kana tsaye,

Kana kallon jama’ar gari.

2. Ɗanhaki (a yankin Zamfara - Bunguɗu da Maru): A yankunan Bunguɗu da Maru na jihar Zamfara, ana yi mata laƙabi da ɗanhaki.

3. Dakable a yammacin Gummi

4. 'Yarmakka (a Ruwan Ɗoruwa): A yankin Ruwan Ɗoruwa da kewayenta, ana kiran Zogale da 'yarmakka. Wannan suna yana nuna alaƙa da Makka (ɗiyar Makka), wanda yake ƙarfafa hasashen cewa, itaciyar ta zo ne ta hannun mahajjata da suka dawo daga aikin Hajji.

5. Bagaruwar Makka (a Ƙasar Nijar): A maƙwabciyar ƙasar Nijar, ana kiran Zogale da bagaruwar Makka. Wannan suna ya yi daidai da na 'yarmakka da ake kira a Ruwan Ɗoruwa, wanda yake nuna cewa a ƙalla a tunanin al'ummar yankin, zogale tana da alaƙa da ƙasar Makka ko kuma ta zo ne ta hannun matafiya da suka fito daga can.

1.2.2 Hasashen Hanyoyin Zuwan Zogale Ƙasar Hausa

Akwai manyan hasashe guda biyu da masana tarihi da al'adu suka yi game da yadda itaciyar zogale ta shigo ƙasar Hausa:

a) Ta Hannun Mahajjata (Daga Makka)

Hasashen da ya fi yaɗuwa shi ne, zogale ta zo ƙasar Hausa ne ta hannun mahajjatan da suke tafiya aikin Hajji zuwa Makka. Sunayen da ake kiran ta a yankuna daban-daban kamar 'yarmakka (Ruwan Ɗoruwa) da bagaruwar Makka (Nijar) suna nuna ƙarfin wannan hasashe. Mahajjata a ƙarni na 19 da na 20 sun saba dawowa da tsaraba ta 'ya'yan itatuwa daga ƙasashen Larabawa da Masar, musamman waɗanda suke da darajar da ake amfani da su wajen magani da abinci. Zogale tana ɗaya daga cikin waɗannan tsirran da suka fi dacewa, domin tana da sauƙin ɗauka kuma ba ta buƙatar ruwa mai yawa don shuka.

Bugu da ƙari, al'ummar Hausawa suna da tarihin tafiya Hajji tun ƙarnuka da yawa da suka gabata, kuma hanyoyinsu na tafiya sun ratsa ƙasar Sudan da Masar da kuma lardin Larabawa. A tsawon lokutan tafiye-tafiyen, suna cin karo da zogale a waɗannan ƙasashe, kuma suna ɗaukar 'ya'yanta don su shuka a gida.

b) Daga Masar ta Hanyar Ciniki da Hijira

Hasashe na biyu shi ne, itaciyar zogale ta zo ƙasar Hausa kai tsaye daga Masar. Tarihi ya nuna cewa Masar tana ɗaya daga cikin ƙasashen da aka fara shigo da zogale daga Indiya tun ƙarnuka da yawa da suka gabata. Misirawa sun daɗe suna amfani da zogale a magungunansu na gargajiya, musamman mai da ake samu daga 'ya'yan zogale. Wannan mai, Misirawa suna shafa shi a fatar jiki don kariya daga ƙazantar da iskar hamada take samarwa, da kuma maganin kumburi da ƙuraje. A dalilin wannan daraja, Misirawa suna girmama zogale sosai, kuma suna noma ta a kusa da gidajensu.

Ƙasar Masar kuma ta kasance cibiyar ciniki tsakanin Afirka ta Arewa da Afirka ta Yamma tun ƙarni na farko. 'Yan kasuwa daga Masar da Sudan suna ratsa hamadar sahara zuwa cikin ƙasar Hausa da sauran yankunan Afirka ta Yamma, suna sayar da kayayyaki kamar gishiri, fata, da tsaba da 'ya'yan itatuwa. A wannan hanyar, Zogale ta iya shiga ƙasar Hausa.

c. Ra'ayin Hambali Junju da Alaƙar Hausawa da Masar

Wani ra'ayi mai ban sha'awa wanda Hambali Junju ya gabatar shi ne, Hausa ta samo asali ne daga Masar. Wannan ra'ayi ya dogara ne a kan kamanceceniyar harshe da al'adu tsakanin Hausawa da wasu al'ummomin Masarawa, da kuma tarihin ƙaura da hijira da aka yi a baya. In kuwa wannan ra'ayi daidai ne, to za mu iya cewa, tun lokacin da kakannin Hausawa suka fara ƙaura daga Masar zuwa yankin da muke kira ƙasar Hausa a yau, sun zo ne da zogale a matsayin ɗaya daga cikin dukiyoyinsu na al'ada da magani.

Bayan haka, kamar yadda ake cewa "masara" ta zo ƙasar Hausa ne daga Masar (wanda wasu masana suka tabbatar da hakan), to ba abin mamaki ba ne idan itaciyar zogale ma ta bi wannan hanya. Masara da zogale duk suna daga cikin tsirran da ake amfani da su wajen abinci da magani a Masar tun da, kuma dukansu sun sami kyakkyawar karɓuwa a ƙasar Hausa. Wannan yana nuna cewa alaƙar ciniki da hijira tsakanin Masar da ƙasar Hausa ta daɗe sosai, kuma tana ɗaya daga cikin manyan hanyoyin shigo da tsirrai masu amfani.

1.2.3 Ƙayyadadden Lokacin Zuwan Zogale

Duk da waɗannan hasashe masu ƙarfi, babu wani mahaluƙi da zai iya fitowa fili ya faɗi ainihin lokacin da zogale ta fara shigowa ƙasar Hausa, ko kuma wane mutum ne na farko ya kawo ta. Wasu masana tarihi sun yi zaton cewa wataƙila ta zo ne a ƙarni na 15 zuwa na 18, lokacin da ƙarfin ciniki tsakanin Masar da Afirka ta Yamma ya ƙaru sosai, sannan kuma a lokacin da ayyukan hajji suka zama ruwan dare tsakanin al'ummar Hausawa. Babu wata shaida ta rubuce-rubuce wadda ta tabbatar da wannan hasashe.

Sanin ainihin lokacin da Zogale ta fara zama sananniya a ƙasar Hausa, da kuma wanda ya fara shigo da ita, gaibu ne (ilm al-ghayb) wanda babu wanda ya sani sai Allah. Abin da muka sani shi ne, itaciyar zogale ta zama ɗaya daga cikin shahararrun tsirrai a al'adun Hausawa, kuma ta sami daraja sosai a fannin abinci, magani, da kuma ƙwalama. Wannan darajar ita ce ta sa Hausawa suka kiyaye itaciyar, suka yaɗa ta a gidaje da ƙauyuka , har ta zama kusan kowane yanki na ƙasar Hausa suna da itaciyar zogale.

Zuwan Zogale ƙasar Hausa misali ne na yadda hulɗar al'adu da ciniki tsakanin Afirka ta Arewa da Afirka ta Yamma ta ba da gudummawa wajen wadatar da al'adun Hausawa da sabbin tsirrai masu amfani. Ko ta hanyar mahajjata ne, ko kuma ta wurin 'yan kasuwa daga Masar, abin da yake tabbata shi ne, itaciyar zogale ta samu karɓuwa mai ban mamaki a tsakanin Hausawa, har ta zama wani ɓangare na rayuwarsu ta yau da kullum. 

Post a Comment

0 Comments