An ciro daga littafin:
BIƊA DA TANADI A DUNIYAR INTANET
(Sana’o’i, Kasuwanci, Ƙwadago)
Na
Abu-Ubaida SANI
Abdulrahman ALIYU
6.2 Tagomashin Biɗa Da Tanadin Duniyar Intanet
Samuwar
hanyoyin biɗa da tanadi a kan intanet ya zo da alfanu mai yawa ga Hausawa da
harshen Hausan kansa. Ya kawo cigaba ta fuskoki daban-daban da suka shafi bunƙasar tattalin arzikin
Hausawa da kuma sauƙaƙa musu hanyoyin samun kuɗi da dogaro da kai. A ɓangare
ɗaya kuwa, ya taimaka wajen yayata harshe da al’adu da adabin Hausawa. A ƙasa an kawo wasu daga cikin
tagomashin biɗa da tanadin duniyar intanet.
6.2.1 Bunƙasar Tattalin Arzikin Hausawa
Samuwar
ayyukan yi wani muhimmin mataki ne na bunƙasa tattalin arzikin al’umma. Abin ya fi
armashi musamman idan aka ce aiki ne wanda ya shafi samun kuɗi daga ayyukan da
ake gudanarwa, saɓanin sayar da abubuwa. Ma’ana dai, idan aiki al’umma suke
gudanarwa ake biyan su, hakan ya fi riba sama da a ce wasu abubuwa suke
sayarwa. Hakan yana faruwa ne kasancewar mai sayar da wani abu dole ne ya kashe
kuɗaɗe kafin samar da shi.[1]
Nau’o’in
ƙwadagon
kan intanet da dama ba su buƙatar sayar da wani abin da ya shafi albarkatun ƙasa. A maimakon haka, ana
iya cewa basira da ƙwarewa da kuma lokaci ake sayarwa. Wannan yana iya
kasancewa dalilin da ya sa mafi yawan ayyukan kan intanet suke da tsarin biya
na awa-awa. Misalan hanyoyin samun kuɗi a kan intanet waɗanda Hausawa suke cin
gajiyarsu sun haɗa da ayyukan da suka shafi kimiyyar harshe[2] da
ayyukan da suka shafi intanet da na’urori da waɗanda suka shafi baje koli/haja,
da sauransu.
Duk
kafafen sada zumunta da aka duba a yau za a tarar da akawun-akawun na Hausawa.
Haka kuma, za a tarar da tallace-tallace da suke ɗorawa a kansu. Yayin da aka
duba wata fitacciyar kalmar Hausa (misali wadda ta shafi wani abin amfani na
yau da kullum ko wani al’amari mai jan hankali) a kan YouTube ko TikTok,
jerin sakamakon da yake bayyana yana da tsawo sosai.
6.2.2 Yaɗa Al’adu Da Harshe Da Adabin Hausawa
Ƙwadagon kan intanet daban-daban sun taimaka wajen yaɗuwar
al’adu da harshe da adabin Hausa a kan intanet. Kafafen intanet irin su Amsoshi
da Bakandamiya da Makarantar Hausa da WikiHausa suna ɗauke
da bayanai masu yawa gama da al’adun Hausawa.
A
ɓangaren harshe kuwa, ko bayan rubuce-rubuce game da fannonin nahawun Hausa, a
yau an samu ƙamusoshin
Hausa a kan intanet. Ƙamusu matattara ce ta kalmomi da ma’anoninsu. Yana da
matuƙar
amfani ga bunƙasar harshe. Tuni Hausa ta yi wa sauran harsuna sa’o’inta
zarra a wannan ɓangare. A rumbun manhajojin wayoyi na PlayStore, akwai
manhajojin ƙamusoshin
Hausa masu yawa. Suna kasancewa cikin tsari na musamman, daga cikinsu akwai:
a. Ƙamusun kalmomin Hausa da bayanan Ingilishi
b. Ƙamusun kalmomin Hausa da bayanan Hausa
c. Ƙamusun kalmomin Hausa zuwa kalmomin Ingilishi
d. Ƙamusun kalmomin Ingilishi zuwa kalmomin Hausa
Daga
cikinsu akwai waɗanda ba a iya amfani da su sai da data. Hakan yana nufin ko da
an sauke su a kan waya ko kwamfuta, to dole sai an kunna data kafin a iya
amfani da su. Wasu daga cikinsu kuwa, da zarar an sauke su a kan kwamfuta ko
waya, to ana iya amfani da su ko da babu data. Kaso na uku su ne waɗanda ba a
sauke su a kan kwamfuta ko waya. A maimakon haka, ana yin amfani da data ne
kawai a duba su a kan intanet. An kawo misali a ƙasa cikin hoto:
Hoto
Na 6.2: Ƙamusun
Hausa Na Kan Intanet
Madogara:
Shafin Farko Na Hausa
Dictionary: http://hausadictionary.com/Main_Page
A
hoto na 6.2 da yake sama, za a ga ƙamusu ne na Hausa wanda ake amfani da shi a kan intanet.
Kamar yadda ake gani a cikin hoton, an ba da damar bincika kalma kai tsaye a
gurbin da aka rubuta “Bincika <> Search.” Da zarar mutum ya
rubuta kalma a wannan wuri, to ƙamusun zai gabato da bayananta nan take. Bayan haka, an
yi wani tsari na abajada. Yayin da mai nema ya latsa ɗaya daga cikin abajadan, ƙamusun zai gabato masa da
dukkanin kalmomi da suka fara da wannan harafi. A shekarar 2024 ma WikiHausa
sun kafa harsashen samar da ƙamusun kan intanet. A duba hoto na 6.3 da yake ƙasa.
Hoto Na 6.3: Yunƙurin WikiHausa Domin Samar
Da Ƙamusu
Madogara: Kafar WhatsApp Ɗin WikiHausa
Waɗansu
daga cikin nau’o’in kasuwanci suna da sauƙin gudanarwa. Misali, kasuwancin sayar da
data da katin waya da na wutar lantarki da talabijin duk saita su kawai ake yi
a bar su a kan intanet. Ɗan kasuwa ba ya buƙatar wata wahalar ciniki ko miƙa kaya. A maimakon haka,
kwastomomi su ne za su biya kuɗi kawai su ɗauki kaya. Hausawa masu irin wannan
kasuwanci, suna kwance sai dai su ji shigar kuɗi a akawun ɗinsu.[3] Ga
misali daga wani shagon sayar da data na kan intanet na Hausawa:
Hoto Na 6.4 Shagon Kan Intanet Na AMLAS Data
Madogara: https://app.amlasdata.com.ng
A
hoto na 6.4 da yake sama, za a iya ganin cewa wannan shagon an saita shi domin
kwastomomi su sayi abubuwa da kansu. Duk abin da suka saya, za su biya kuɗin ta
kan intanet ba tare da buƙatar yin magana da mai shago ba. Hakan ya nuna yadda
Hausawa masu ire-iren waɗannan kasuwancin kan intanet suke samun hutun jiki.
6.2.4 Ƙarancin Jin Rauni Sakamakon Aiki
Akan
samu raunuka daban-daban a wuraren ayyuka a duniyar zahiri. Raunukan sukan samu
a sakamakon haɗurra na tuntuɓe ko faɗowar kayan aiki ko gobara ko fashewar
abubuwa, da dai sauransu. Ayyukan da Hausawa suke yi a duniyar zahiri masu
haɗurra sun haɗa da kafintanci da walda da gini da tonon rijiya da sauransu.
Ana kuma iya samun haɗari a hanyar zuwa wurin aiki. Duk waɗannan sun danganta
da yanayin aikin da ma’aikaci yake gudanarwa da kuma wurin aikin.[4]
Hausawa
masu ƙwadago
a kan intanet suna da ƙarancin fargabar aukuwar ire-iren waɗannan haɗurra.
Dalili kuwa shi ne, aikinsu ba ya buƙatar tafiye-tafiye (misali zuwa wurin aiki da
dawowa a kullum). Idan a cikin gidansu suke gudanar da ayyukan, hakan yana
nufin suna iya kasancewa a wuri ɗaya. Gidansu kuwa wuri ne wanda suka saba da
shi.[5]
6.2.5 Cikakken ‘Yanci Da Walwala
Hausawan
da suke gudanar da kasuwanci ko ƙwadago a kan intanet suna da cikakken ‘yanci da walwala.
Idan aka ɗauki ayyukan ƙwadagon kan intanet a matsayin misalai, hakan a bayyane
yake ƙarara.
Hausawa ‘yan ƙwadagon kan intanet sukan karɓi ayyuka ne a lokacin da
suka ga dama kawai. Bugu da ƙari, sukan zaɓi ayyukan da suka ga dama sannan su yi
watsi da waɗanda ba su kwanta musu a rai ba.[6] A
duk lokacin da wani kamfani zai turo aiki ta kan intanet, to dole sai ya
bincika idan ɗan ƙwadagon yana da lokaci sannan yana da sha’awar karɓar
aikin.[7] A
duba misali a ƙasa:
Hoto Na 6.5: Misalin tambayar ɗan ƙwadago idan yana da damar
karɓar aikin Hausa (availability check)
Madogara:
Saƙon imel daga kamfanin
fassara na GoTransparent
A
ɓangare ɗaya kuwa, Hausawa masu ƙwadago a kan intanet sun kauce wa takunkumin zuwa wurin
aiki kullum. Saɓanin ma’aikatan duniyar zahiri da suke buƙatar tafiya wurin aiki,
‘yan ƙwadagon
kan intanet suna iya zama a gidajensu domin gudanar da ayyukansu. Wani ƙarin ‘yanci shi ne, mutum
ɗaya yana da damar yin ayyuka a kamfanoni ko ɗaiɗaikun mutane daban-daban. Abin
ya yi daidai da maganar Hausawa ta “in laila ta ƙiya a koma basha” ko kuma
“gida biyu maganin gobara.”
Su
ma nau’o’in kasuwancin da ake saita su domin su gudanar da kansu a kan intanet
(automation), suna bayar da damar samun ‘yanci da walwala ga Hausawa ‘yan
kasuwa. Wannan ƙarin tagomashi ne a kan hutun jiki (kamar yadda aka
tattauna a ƙarƙashin 6.2.3 a sama). Babban
misali a nan shi ne, wanda yake da shagon sayar da katin waya da data a duniyar
zahiri, to lallai dole ya rufe shagonsa ko kuma ya nemi yaron shago idan yana
son tafiya wani wuri. Bahaushe wanda yake da shagon kan intanet da yake sarrafa
kansa kuwa, zai je wurin da ya ga dama a lokacin da ya ga dama ba tare da
hadahadar kasuwancin shagonsa ya fuskanci wani ƙalubale ba.
Yayin
da wani Bahaushe zai fara gudanar da wata sana’a ko kasuwanci a duniyar zahiri,
to yana buƙatar
jari. Jarin da zai nema ya danganci nau’in sana’a ko kasuwancin da zai gudanar.
Idan shago zai buɗe, to yana buƙatar sayen fili da kuɗin gini, ko kuma karɓar haya. Haka
kuma, akwai kashe kuɗin gyaran shago da biyan kuɗin wuta da na haraji.
Makamancin haka ne yake faruwa ga masu sana’o’i kamar kafintan ƙasa (kafintan mata) da mai
shagon kwamfuta ko kafe (cafe) da makamantansu.
Wani
muhimmin abin burgewa tattare da hanyoyin samun kuɗi a duniyar intanet shi ne
yadda ba su buƙatar wani jari mai yawa. Jarin da ake buƙata bai taka kara ya karya
ba, duk da ya danganta da nau’in kasuwanci ko sana’ar da aka saka a gaba. Ana
iya ɗaukar mai koyarwa a kan intanet a matsayin misali. Abin da yake buƙata kawai shi ne na’ura da
sabis ɗin intanet da kuma wutar lantarki. Hakan ya sha bamban da yadda abin
yake a duniyar zahiri a inda aƙalla sai an tanadi aji ko azuzuwa.[8]
6.2.7 Rage Cunkoson Ababan Hawa Da Rage
Cutar Da Muhalli
Wani
alfanun da yake tattare da biɗa da tanadin duniyar intanet shi ne rage cunkoson
ababan hawa a kan tituna. Hakan yana faruwa ne sakamakon ire-iren ayyukan nan
ba su buƙatar
tafiya ofishi na musamman a wata ma’aikata ko kuma wurin aiki na musamman. Rage
cunkoson ababan hawa kuwa, yana taimakawa wajen rage cutar da muhalli.
Binciken
Güven (2024) ya tabbatar da cewa, ƙwadagon kan intanet da kuma ayyuka daga gida ta kan
intanet[9]
suna matuƙar
taimakawa wajen rage cunkoson ababan hawa. Suna kuma taimakawa wurin taƙaita wasu illolin da
ayyukan ‘yan’adam suke yi wa muhalli. Hasan & Habib (2023) suna ganin, riƙo da dabarun gudanar da
ayyuka ta kan intanet za su iya taimakawa har a ɓangaren rage ɓarnata filaye.
Hakan zai faru ne yayin da aka taƙaita amfani da filaye wurin gina ofisoshin ma’aikatu. A
maimakon hakan, ma’aikata za su kasance suna gudanar da ayyuka daga gidajensu.
Ababen
hawa da ake amfani da su, suna fitar da sinadarin kabon dai’ozayid (carbon
dioxide (CO2)). Wannan sinadari kuwa yana matuƙar illata muhalli, musamman
abin da ake kira Ozon Leya (Ozone Layer).[10] A
ɓangare ɗaya kuwa, cunkoson da ya yi yawa yana iya yin mummunan tasiri a ƙwaƙwalwar mutum. Hakan ya
shafi saka masa damuwa da ƙagara (psychological stress). Wata mummunan illar da
cunkoson ababen hawa yaka haifarwa ita ce yiwuwar ƙaruwar saurin fushi da faɗa
a tsakanin mutanen da abin ya shafa.
A
taƙaice
ke nan, rage cunkoson ababan hawa a kan tituna zai taimaka wa muhalli. Wannan
kuwa alfanu ne ga al’ummomin duniya baki ɗaya, ciki har da Hausawa. Bugu da ƙari, zai taimaka wa mutane
ta fuskokin da suka shafi lafiyar jiki da na ƙwaƙwalwa da kuma kyautata
zamantakewa.
[1] Misali manomi sai ya kashe
kuɗi da lokaci wurin noma. Haka abin yake ga masu sauran sana’o’in da suka
shafi samar da wasu abubuwa.
[2] A kan Translation
Directory kaɗai, akwai Hausawa sama da ɗari biyar (500) da suka yi rajista
a matsayin ‘yan ƙwadagon kan intanet. Ana iya duba https://www.translationdirectory.com/translators/find_translators.php.
[3] Duk da haka akwai abubuwan
da ake buƙata
daga gare shi kamar ƙara kuɗi a lalitoci da duba daidaiton lamura da kuma
sauraren koken kwastomomi.
[4] Nordin (2014) ya tattauna
wasu daga cikin haɗurran da suke aukuwa a dalilin zuwa aiki.
[5] Duk da haka akan iya samun
rauni lokaci zuwa lokaci musamman idan ba a bi ƙa’idojin aiki ba. Misali,
ana iya samun ciwon baya ko ciwon wuya sakamakon daɗewa ana zaune ko zama yadda
bai kamata ba, da dai sauransu.
[6] Yawanci ‘yan ƙwadago sukan ƙi karɓar aiki idan lokacin
kammala shi (deadline) bai yi musu dadai ba, ko saboda farashin bai gamshe su
ba, da dai makamantan hakan.
[7] Wannan shi ake kira availability
check a harshen Ingilishi.
[8] Domin samun ƙarin bayani game da ‘buƙatar ƙaramin jari’ a matsayin
tagomashin biɗar kuɗi a duniyar intanet, ana iya duba Al-Jarf (2020) da Ren
& Raghupathi (2023).
[9] Work From Home (WFH)
[10] Don ƙarin bayani ana iya duba East et al. (2024).
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.