Ticker

6/recent/ticker-posts

Nakaltar Matakan Neman Kudi Da Tanadi a Kan Intanet

An ciro daga littafin:

BIƊA DA TANADI A DUNIYAR INTANET
(Sana’o’i, Kasuwanci, Ƙwadago)

Na

Abu-Ubaida SANI
Abdulrahman ALIYU

Bida Da Tanadi a Duniyar Intanet (Sana’o’i, Kasuwanci, Kwadago)
Manazartar Littafi: Sani, A-U. & Aliyu, A. (2026). Biɗa Da Tanadi a Duniyar Intanet (Sana'o'i, Kasuwanci, Ƙwadago). Amsoshi Academic Publishers. ISBN: 978-978-62480-1-1. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.21361768

Tuntuɓa Domin Samun Littafi: 
Dr. Abu-Ubaida Sani: Imel - abuubaidasani5@gmail.com | WhatsApp - 08133529736
Dr. Abdulrahman Aliyu: WhatsApp - 08036954354

Naƙaltar Biɗa Da Tanadi A Duniyar Intanet

6.0 Shimfiɗa

A babi na huɗu da na biyar an tattauna hanyoyi daban-daban na biɗa da tanadi a duniyar intanet waɗanda Hausawa suke iya amfana da su. Daga cikinsu akwai waɗanda suka kasance gama-gari tsakanin mutanen duniya (ayyukan da suka shafi kimiyya da fasaha da koyar da darussa da sauransu). Waɗansu daga cikinsu kuwa, ana sa ran su kasance keɓantattu ga Hausawa. Babban misali a nan shi ne, duk aikin ƙwadagon da ya shafi harshe ko al’ada, kai tsaye an fi son ɗan gado ya aiwatar da shi ba ɗan haye ba. Ma’ana a nan ita ce, an fi son wanda Hausa take matsayin harshen uwa a gare shi ya aiwatar da ire-iren ayyukan. Akan yi hakan ne don gudun abin da Bunza (2017) ya kira Grammatical Rift” (p. 5) da “Cultural Lacuna” (p. 11) wato “Giɓin Nahawu” da “Giɓin Al’ada.” Bayan haka, abubuwan da ake buƙata suna iya bambanta bisa bambance-bambancen da suke tsakanin nau’o’in biɗa da tanadin ko muhallan gudanar da su. Wannan ɓangare na aikin ya mayar da hankali ne a kan muhimman abubuwan da mai ƙoƙarin shiga harkar biɗa da tanadin duniyar intanet ya kamata ya sani. Sun haɗa da matakan naƙaltar harkokin da kuma ƙalubale da illolin da suke cikinsu.

6.1 Matakan Biɗa Da Tanadi a Duniyar Intanet

Harkokin biɗa da tanadi na duniyar intanet suna buƙatar karatun ta-natsu kafin fara gudanar da su. Faɗa musu ba tare da cikakken ilimi ba yawanci yakan kai ga hasara ko shan wahala. Ya yi daidai da abin da Bahaushe yake cewa: “Iya ruwa fid da kai.”

Da dama daga cikin hanyoyin biɗa a duniyar intanet sun shafi hulɗa da mutanen da ba Hausawa ba. Suna da al’adu da salailan mu’amalar zamantakewa waɗanda ba dole ne su zamo iri ɗaya da na Hausawa ba. Haka kuma, dokoki da ƙa’idojin nau’o’in hulɗoɗi da ake gudanarwa suna da matuƙar tsauri da buƙatar a bi su sau-da-ƙafa. Muhimman abubuwan da mai ƙoƙarin shiga wannan layin ya kamata ya fahimta sun haɗa da:

a. Ƙwarewa a fannin da aka ɗauka

b. Sanuwa a duniyar intanet (online visibility)

c. Samun sabis ɗin intanet mai ƙarfi da rashin yankewa

d. Girmama lokaci

e. Gaskiya da riƙon amana

f. Naƙaltar harshe ko harsuna

g. Koyon dabarun ƙirƙira da saurin yanke hukunci

h. Tanadar na’urori masu sauri da inganci

i. Wuri mai sirri da rashin hayaniya

j. Naƙaltar injunan fassara

k. Ilimin kare kai daga damfara

6.1.1 Ƙwarewa a Fannin Da Aka Ɗauka

Aiki a kan intanet yana buƙatar matuƙar ƙwarewa irin wadda Hausawa suke yi wa kirari da “hannu ya iya jiki ya saba.” A mafi yawan lokuta, ba a faye damuwa da satifiket ko matakin karatu ba. Babban abin da ake mayar da hankali a kansa shi ne ‘ƙwarewa.’ An fi damuwa da abin da mutum ya aiwatar a baya da kuma abin da zai iya aiwatarwa a yanzu. Dangane da wannan, waɗanda suka fi samun aiki a kan intanet su ne waɗanda suke da kyakkyawan tarihin ayyuka a baya. Hakan yana nuni da cewa sun ƙware a fannin da suke.

Makamancin wannan ne yake faruwa a fannin abin da ya shafi hulɗayyar kasuwanci a kan intanet. Hausawa da sauran mutane waɗanda suka gudanar da hulɗoɗin kasuwanci masu yawa ba tare da matsala ba, yawanci kafar intanet ko manhajar takan ba su tambari ko baji (badge) na musamman. Wannan tambari ko baji zai yi nuni ga matsayinsu a cikin kasuwar. Bugu da ƙari, zai yi manyan ayyuka guda biyu:

1. Samun Kulawa Ta Musamman: Waɗanda suke da babban matsayi a ire-iren waɗannan kafafe da kasuwannin kan intanet, jami’an da suke kula da kasuwannin za su riƙa ba su kulawa ta musamman. A duk lokacin da suka tuntuɓi sashen taimako, to za a saurare su cikin gaggawa.[1]

2. Samun Abokan Hulɗa Masu Yawa: Duk wanda yake kasuwancin kan intanet da zuciya ɗaya, to burinsa shi ne haɗuwa da ‘yan kasuwa masu nagarta da sauƙin kai. Wanda yake da tambarin nagarta a akawun ɗinsa, lallai ‘yan kasuwa masu yawa za su riƙa ribibin ganin sun yi hulɗar kasuwanci da shi.

6.1.2 Sanuwa a Duniyar Intanet (Online Visibility)

Harƙallolin kan intanet sun dace da kirarin nan na Hausawa “a san mutum a san cinikinsa/sana’arsa.” Wani babban abu mai muhimmanci ga Bahaushe wanda yake neman ayyuka a kan intanet shi ne sanuwarsa a kan intanet ɗin. Dole ne ya sanu ta yadda da zarar an tura neman ‘yan ƙwadagon kan intanet da suke gudanar da irin aikin da yake yi, to zai fito cikin sakamakon da injin nema zai bayar. Misali, idan ana neman masu aikin fassara ne daga Hausa zuwa Ingilishi, to sanuwa a duniyar intanet ne zai ba wa ɗan ƙwadago a wannan fannin damar bayyana har a tuntuɓe shi.[2]

Dangane da wannan, dole ne Hausawa masu ƙoƙarin shiga harkar fassara a kan intanet su yi rajista da kamfanonin fassara daban-daban.[3] Bugu da ƙari, dole ne su buɗe akawun a kafafen baje hajar basira. Ire-iren kafofin da Hausawa ‘yan ƙwadagon kan intanet suke yin rajista domin baje kolin fasaharsu sun haɗa da:

a. Behance (www.behance.net)

b. Dribbble (www.dribbble.com)

c. Fiverr (www.fiverr.com)

d. Freelancer (www.freelancer.com)

e. Gengo (www.gengo.com)

f. Guru (www.guru.com)

g. LinkedIn (www.linkedin.com)

h. PeoplePerHour (www.peopleperhour.com)

i. ProZ (www.proz.com)

j. Smartcat (www.smartcat.com)

k. Toptal (www.toptal.com)

l. TranslatorsCafe (www.translatorscafe.com)

m. Upwork (www.upwork.com)[4]

Ko bayan yin rajista da ire-iren waɗannan kafafe, dole ne Hausawa ‘yan ƙwadagon kan intanet su riƙa sabunta bayanansu lokaci zuwa lokaci.

6.1.3 Samun Sabis Ɗin Intanet Mai Ƙarfi Da Rashin Yankewa

Dukkannin hanyoyin biɗa da tanadin kan intanet suna da alaƙa da ‘sabis ɗin intanet.’ Kamfanonin ƙwadagon kan intanet masu yawa sukan tambayi yanayin ƙarfin sabis ɗin intanet na ɗan ƙwadago kafin su ba shi aiki. Akwai kafafen da ake iya auna ƙarfin intanet. Yayin da aka auna, za a ɗauki rahoton sannan a tura shi ga kamfanin da suka buƙata. Misalan kafafen auna ƙarfin intanet sun haɗa da:

a. AT&T Internet Speed Test (www.att.com/support/speedtest)

b. Fast.com (www.fast.com)

c. Google Fiber Speed Test (http://speed.googlefiber.net/)

d. Meteor by OpenSignal (https://www.opensignal.com/apps)

e. Spectrum Speed Test (www.spectrum.com/internet/speed-test)

f. Speedtest by Ookla (www.speedtest.net)

g. Xfinity Speed Test (https://speedtest.xfinity.com/

Yana da kyau Hausawa masu shirin shiga fagen su san da wannan ilimi. Yayin da suke auna ƙarfin sabis ɗin da suke amfani da, hakan zai taimaka musu wajen neman mafita idan akwai buƙatar hakan.

6.1.4 Girmama Lokaci

Dole ne Hausawa da suke son yin fice a wannan fannin su naƙalci girmama lokaci. Girmama lokaci a nan yana nufin cika duk waɗansu alƙawura da mutum ya ɗauka dangane da lokaci. Alƙawarin yana iya kasancewa a rubuce ko kuma na fatar baki. Mafi yawan ayyukan ƙwadagon kan intanet suna tafiya ne da lokaci. Saɓa lokaci a wurin ɗan ƙwadagon kan intanet babban naƙasu ne a gare shi.

Akwai kafafen intanet na ƙwadago da suke da tsarin da yake nuna adadin lokacin da ɗan ƙwadago ya taɓa saɓawa. Daga cikinsu har da kafafen da Hausawa suke aiki a kai. A duk lokacin da ɗanƙwadon ya saɓa alƙawarin lokaci, to za a tara mintuna ko awannin da ya ƙara a saman alƙawarin, a ɗora su a kan akawun ɗinsa. Misali, idan an yi alƙawri da shi zai tura wani saƙo ko ya kammala wani aiki ƙarfe goma (10:00) na safe, sai kuma bai tura ba har sai ƙarfe goma da minti biyar (10:05), to za a sanya mintuna biyar (5) ɗin a kan furofayil ɗinsa. Idan a gaba ya sake saɓa mintuna bakwai (7), to za a ƙara su a kan mintuna biyar (5) ɗin (sun zama goma sha biyu ke nan (2)). Ga misali a ƙasa:

Hoto Na 6.1: Misalin Mintunan Saɓa Alƙawarin Lokaci a Kafar BLEND

Nakaltar Bida Da Tanadi a Duniyar Intanet

Madogara: Akawun Ɗin BLEND Mai Lamba

A hoto na 6.1 da aka kawo a sama, za a lura da cewa mai akawun ɗin bai taɓa saɓa alƙawarin lokaci ba ko da na minti ɗaya ne. Bugu da ƙari, ya kammala ayyuka ɗari da tamanin da takwas (188) waɗanda suka kai adadin kalmomi dubu ɗari da casa’in da ɗari biyu da sittin da bakwai (190,267). Hakan zai ba wa akawun ɗinsa daraja sama da na wasu da ba su da tarihin waɗannan nasarori a kan kafar.

6.1.5 Tsara Lokaci

Tsara lokaci wani mataki ne na tabbatar da girmama lokaci. Duk da haka, yana iya cin gashin kansa. Kai tsaye ya shafi daidaita lokaci domin amsa saƙonnin kwastomomi daga ɓangarorin duniya daban-daban. Yana da muhimmanci a tuna cewa, garuruwa kamar su Auckland na ƙasar New Zealand suna da ƙarin awanni goma sha biyu zuwa goma sha uku (12-13) daga Nijeriya. Garuruwa irin su Honolulu da Hawaii na Amurka kuwa, suna bayan Nijeriya da awanni goma zuwa goma sha ɗaya (10-11).[5] Hausawa mazauna Nijeriya dole ne su yi la’akari da wannan domin tsara lokutansu.

Ya zama dole ga Hausawa ‘yan ƙwadagon kan intanet su yi la’akari da kwastomominsu, da wuraren da suka fito. Wannan ne zai ba su damar daidaita lokacinsu ta yadda za su iya bayar da amsar saƙonnin da aka turo daga ƙasashe daban-daban ba tare da ɓata lokaci ba. Yana da kyau Hausawa su riƙe cewa, bayar da amsar saƙonni cikin lokaci abu ne mai matuƙar muhimmanci a harkar ƙwadagon kan intanet.

Akwai kamfanonin da suke tura sanarwar aiki ga ‘yan ƙwadago mabambanta a lokaci ɗaya. Waɗanda suke iya ba da amsa da wuri, da su ne za a tattauna har a samu wanda zai ɗauki aikin a cikinsu. A wasu lokutan kuwa, na’ura ce za ta tura aiki ga ɗan ƙwadago (system assignment). Da zarar ba ya kusa, za ta soke aikin sannan ta tura wa wani na daban.

6.1.6 Gaskiya Da Riƙon Amana

Kafin mutum ya shahara a wani fannin ƙwadago ko kasuwancin kan intanet, dole ne ya kasance mai gaskiya da riƙon amana. A duniyar zahiri ana da ɓarayi da ‘yan zamba da sauran miyagun mutane. Haka abin yake a duniyar intanet inda ake da ‘yan damfara iri-iri. Wannan ya sa kafafen intanet da dama (musamman waɗanda suka shafi kasuwanci ko hulɗoɗin kuɗi) suke da tsauraran matakan tsaro. Aikata rashin gaskiya ko cin amana laifi ne da zai sa a rufe akawun ɗin mutum nan take. Ko da ma dai, waɗannan miyagun ɗabi’u ne a al’adar Hausawa.

A ɓangaren ayyukan da suka shafi kimiyyar harshe, kafafe da dama sukan jero sunayen waɗanda suka aikata rashin gaskiya. Kafafe irin su Translation Directory (https://www.translationdirectory.com/) suna da abin da suke kira Black List. Ya kasance tamkar Baƙin Littafi a kan intanet inda suke sanya jerin waɗanda aka kama ko ake tuhuma da rashin gaskiya a fannonin ƙwadagon da suka shafi kimiyyar harshe. Hakan zai sa kamfanoni da ɗaiɗaikun ‘yan ƙwadago su guji mu’amala da su. Yana da kyau Hausawan da suke shirin shiga fannin su san da wannan sannan su yi bakin ƙoƙarinsu wajen riƙo da gaskiya da amana.

6.1.7 Naƙaltar Harshe Ko Harsuna

A baya an bayyana cewa, ɗan ƙwadagon kan intanet dole ne ya ƙware a fannin da ya ɗauka. Naƙaltar harshe wani abu ne da ya shafi ƙwarewa, amma mai cin gashin kansa. Ga Hausawa waɗanda suke ayyukan da suka shafi kimiyyar harshe, naƙaltar harshe wajibi ne a gare su, “farilla tusar mai bacci.”

Dangane da sauran fannonin ƙwadagon kan intanet kuwa, naƙaltar harshe yana taimakawa wajen tattaunawa da kwastomomi. Iya tsara zance da bayar da amsa yadda ya kamata abu ne mai muhimmanci a wannan fannin. Ya haɗa da zaɓen kalmomin da suka dace dangane da fannin da ake magana a kai.

Haka kuma, yayin da aka samu bambancin ra’ayi tsakanin ma’aikaci da mai duba ingancin aiki, naƙaltar harshe yana taka rawa wajen fito da gaskiya game da jayayyar da ake yi (rebuttal). Hausawa sun yi gaskiya da suka ce “dokin mai baki ya fi gudu.” Sau da dama waɗanda suka ba da aiki (clients) sukan yaudaru da zaƙin baki da sanin kalmomin fannu da wani ɗan ƙwadago ya yi, musamman idan abokin jayayyarsa bai naƙalci harshe ba. M.A. Umar (keɓantacciyar tattaunawa, 23 ga watan Octoba, 2023).

6.1.8 Koyon Dabarun Ƙirƙira Da Saurin Yanke Hukunci

Ilimi da basira baiwa ce da Allah yake ba wa ɗan’adam. Duk da haka, ɗan’adam yakan koyi dabarun da za su bunƙasa masa kaifin basira da iya warware abubuwan da suka shiga duhu (Khilchenko & Perevoznikova, 2019 sh. 174). Duniyar intanet da na’urori fage ne mai matuƙar faɗi. Duk yadda mutum ya ƙware, akwai ranakun da zai ci karo da matsalolin da bai taɓa ganin su ko jin labarinsu ba. A irin wannan lokaci, dole ne ya yi amfani da hikimomi domin gano bakin zaren. Wannan ya haɗa da bincike cikin ƙwarewa a kan intanet game da matsalar ko makamanciyarta.

Yawan ƙorafi dangane da matsalolin da suka shafi intanet ko na’urori (da makamantansu) abu ne da yake janyo faɗuwar darajar ma’aikaci. Hakan ne ya sa daga cikin abubuwan da ake yawan bincikawa yayin ɗaukar ɗan ƙwadagon kan intanet akwai (i) yadda yake tunkarar matsaloli, da kuma (ii) yadda ya iya aiki a cikin yanayin takura ko ujila. Yana da kyau Hausawan da suke aiki a wannan fannin su naƙalci matakai da dabarun yanke hukunci cikin hikima da hanzari.

6.1.9 Tanadar Na’urori Masu Sauri Da Inganci

Na’urori masu sauri da inganci sun kasance ƙashin gadon bayan ayyukan ƙwadagon kan intanet. Jarin farko da Bahaushe ɗan ƙwadago zai samu shi ne na’ura mai inganci da biyan buƙata. Inganci ya haɗa da sauri da ƙarfin sabis ɗin intanet da kuma rashin ɗaukar zafi.

Dole ne Hausawa su naƙalci ɗabi’ar karɓar sauyi. Sauye-sauye a wannan bagiren sun haɗa da koyon aiki da sababbin na’urori da manhajoji. Bincike daban-daban sun nuna yadda na’urori masu kyau da sabis ɗin intanet mai ƙarfi suke taimakawa ga ayyukan kan intanet. Daga cikinsu akwai Cobo-Rendon & Maldonado-Trapp (2021) da Limniou (2021) da Hartley et al. (2023).

Ko ma wane irin nau’in harƙallar kasuwanci mutum yake yi a kan intanet, za a tarar yana buɗe kafafen intanet mabambanta a lokaci ɗaya a kan burawuzarsa. A wasu lokutan ma, yakan zama dole a yi amfani da burawuzozi daban-daban a lokaci ɗaya. Bugu da ƙari, ana iya buɗe manhajoji masu yawa a lokaci ɗaya. Duk waɗannan suna buƙatar na’ura mai inganci wadda ba za ta riƙa bayar da matsala ko tsaiko ba.

6.1.10 Wuri Mai Sirri Da Rashin Hayaniya

Wani abu da ya kamata Hausawa su riƙe shi ne, mafi yawan kamfanonin fassara sukan tura takardar yarjejeniyar riƙe sirri. Ana kiran ta da suna NDA (Non-Disclosure Agreement). Takardar yarjejeniya ce wadda a cikinta ɗan ƙwadagon kan intanet zai yi alƙawarin riƙe sirrin duk waɗansu takardu ko bidiyoyi ko odiyo da aka turo masa a lokacin aiki. Zai kuma saka hannu kan amincewa da hukunce-hukuncen da doka ta tanadar idan ya saɓa wannan alƙawari.[6]

A bisa haka, dole ne Hausawa ‘yan ƙwadago su naƙalci riƙe sirri tare da tanadar keɓantaccen wuri sirratacce domin gudanar da ayyukansu. Bugu da ƙari, yawancin ƙwadagon kan intanet suna buƙatar nitsuwa. Surutu yana iya haifar da kurakurai a ayyukan da ake gudanarwa sakamakon ɗauke hankalin ma’aikacin.

6.1.11 Naƙaltar Injunan Fassara

Naƙaltar injunan fassara kai tsaye ya shafi ayyuka ne waɗanda suke da alaƙa da ƙwadagon fannin kimiyyar harshe. Kafin bunƙasar na’urori da intanet, Hausawa da sauran al’ummomi suna gudanar da fassara ne kawai ta hanyar rubutu. A yanzu an samu cigaban zamani sosai wanda ya haɗa da amfani da injunan fassara.

Injunan fassara (waɗanda ake kira translation tools a Ingilishi) fasahohin zamani ne da suka kasance cikin fasaloli daban-daban waɗanda suke taimaka wa ayyukan da suka shafi kimiyyar harshe.[7] Misalan injunan fassara da ake gudanar da ayyukan Hausa a kansu sun haɗa da:

1. SDL Trados Studio - Wanda kamfanin SDL suka samar (yanzu ɓangare ne na RWS Group)

2. MemoQ - Wanda kamfanin MemoQ Translation Technologies suka samar

3. Wordfast - Wanda kamfanin Wordfast LLC suka samar

4. Across Language Server - Wanda kamfanin Across Systems GmbH suka samar

5. Déjà Vu - Wanda kamfanin ATRIL Solutions suka samar

6. XTM Cloud - Wanda kamfanin XTM International suka samar

7. Memsource (an sauya masa suna zuwa Phrase) - Wanda kamfanin Memsource suka samar

8. Smartcat - Wanda kamfanin Smartcat suka samar

9. MateCat - Wanda kamfanin MateCat suka samar

10. OmegaT - Wanda kamfanin OmegaT Project suka samar

11. CafeTran Espresso - Wanda kamfanin CafeTran suka samar

12. Transifex - Wanda kamfanin Transifex suka samar

13. Crowdin - Wanda kamfanin Crowdin LLC suka samar

Naƙaltar injunan fassara dole ne ga Hausawa masu son shiga a dama da su a wannan fannin. Rashin iya aiki da su naƙasu ne wanda yake haifar da rasa aiki daga kamfanoni.

6.1.12 Ilimin Kare Kai Daga Damfara

Akwai kalmomi guda biyu a Hausa da ake rubuta su cikin abajadin “damfara.” Sa’id et al. (2006 sh. 93) sun yi ƙoƙarin fayyace su kamar haka: (1) damfara (damfàraa, i,e,o,u, fi.) (i) jibga, ko danƙara, ko maka kaya ko wani abu, d-d danna ko daddala. (ii) harhaɗa kaya wuri guda. (2) damfara (dàmfaràa, sn., mc.) (i) yaudara ko zamba da ake yi wa wani mutum da yake zaton zai sami wata ƙaruwa (ii) wala-wala. A wannan bincike, ana magana ne game da kalma ta biyu, wato wadda take ɗaukar ma’anar yaudara ko zamba.

Daga cikin ayyukan masana da manazarta da suka tattauna batun damfara akwai Bunza (1994 sh. 2) da Maiyama (2008 sh. 27) waɗanda suka yi tarayya a kan wasu muhimman kalmomi a matsayin tubalan gina ma’anar damfara (ƙarya da kwaɗayi da wayo da cuta ko zalunci). A taƙaice ana iya cewa, damfara hanya ce ta amfani da dabarun yaudara don kwaɗaitar da wani samun wani abin alfanu dangin kuɗi ko wani abu mai daraja domin karɓar wani abu daga gare shi na dindindin.

Duk da ana damfara a duniyar zahiri, a yanzu ta fi yawa a duniyar intanet. Ayyukan Cross & Layt (2021) da Shang et al. (2023) sun kawo wasu nau’o’in damfara da ake yi a kan intanet tare da tattauna munin lamarin. A kullum wanɗanda adireshin imel ɗinsu ya yaɗu a kan intanet sukan samu saƙonnin imel na damfara masu tarin yawa.[8] Ta lambobin waya ma ‘yan damfara suna yawan ƙoƙarin gwada sa’arsu a kan mutane.

Dole ne Hausawa ‘yan ƙwadagon kan intanet su naƙalci hanyoyi da dabarun da ake bi domin kare kai daga ‘yan damfaran kan intanet. Wasu daga cikinsu su ne:

a. Ilimin iya tantance kafafen intanet na kasuwancin haƙiƙa da waɗanda aka ƙirƙira domin damfara[9]

b. Ilimin tantance liƙau ɗin da suke da tsaro da aminci da kuma waɗanda suke da rauni da alamun tambaya

c. Ilimin matakan binciko bayanan duk wanda ya turo saƙo

d. Ilimin tantance bayanan haƙiƙa da na ‘yan damfara

e. Nisantar zalama da saurin yanke hukunci game da al’amuran da suke da alamun rashin gaskiya a tattare da su




[1] Babban misali a nan shi ne baji na musamman wanda ake bayarwa a kan manhajar PalmPay, wato Premium. Baji ne wanda ake ba wa waɗanda suka cika wasu ƙa’idoji. Ƙa’idojin sun shafi gudanar da a ƙalla taransifa talatin (30) a wata da ajiye a ƙalla dubu goma (₦10,000) a cikin asusun, da dai sauransu. A duba Chidi (2024) ko manhajar PalmPay. Jami’an PalmPay suna bayar da kulawa ta musamman ga masu wannan matsayi.

[2] Rashin sanuwa a duniyar intanet ne ya sa Hausawa da suka ƙware a fassara da sauran ayyuka ba sa samun aiki. A maimakon haka, sai ake ba waɗanda ba ƙwararru ba sakamakon sun kasance sanannu ne a intanet.

[3] An kawo misalan kamfanonin fassara goma sha uku (13) waɗanda suke da sashen Hausa a ƙarƙashin 4.1.1 a babi na huɗu.

[4] Domin ƙarin bayani, ana iya duba Rai et al. (2019) da Duggan et al. (2020).

[5] Akan samu bambancin awa ɗaya ne kasancewar a yankunan can ana samun sauyin lokaci wanda yake bayar da tazara (ƙaruwa ko raguwar) ta awa guda.

[6] Kamfanin Translit Pro sun bayyana cewa “The purpose of an NDA is to set out who and how a party can access and use the information in question, and to establish penalties for disclosing confidential information by accident or on purpose”(O’Farrell & Leschen, 2023 SL. 6). Ma’anar a nan ita ce, amfanin NDA shi ne samar da ƙa’idoji game da waɗanda za su iya samun bayanai da kuma ta yadda za su same su har ma da yadda za su yi amfani da su. Ya kuma shafi samar da hukuncin da zai faɗa kan waɗanda suka fitar da waɗannan bayanan sirri bisa kuskure ko ganganci.

[7] Domin ƙarin bayani game da injunan fassara da amfaninsu, ana iya duba O’Brien et al. (2013) da Almanna & Gu (2020).

[8] Daɗinta ma shi ne, kamfanonin da ake buɗe akawun ɗin imel da su, suna da tsarin da yake tura saƙonnin imel masu alamar damfara zuwa sashen tarkace “spam folder.”

[9] Abubuwan da ake lura da su sun haɗa da daɗewar kafar intanet da tsarinta da sauransu.

Post a Comment

0 Comments