Ticker

6/recent/ticker-posts

Kalubalen Neman Kudi Da Tanadin Hausawa a Duniyar Intanet

An ciro daga littafin:

BIƊA DA TANADI A DUNIYAR INTANET
(Sana’o’i, Kasuwanci, Ƙwadago)

Na

Abu-Ubaida SANI
Abdulrahman ALIYU

Bida Da Tanadi a Duniyar Intanet (Sana’o’i, Kasuwanci, Kwadago)
Manazartar Littafi: Sani, A-U. & Aliyu, A. (2026). Biɗa Da Tanadi a Duniyar Intanet (Sana'o'i, Kasuwanci, Ƙwadago). Amsoshi Academic Publishers. ISBN: 978-978-62480-1-1. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.21361768

Tuntuɓa Domin Samun Littafi: 
Dr. Abu-Ubaida Sani: Imel - abuubaidasani5@gmail.com | WhatsApp - 08133529736
Dr. Abdulrahman Aliyu: WhatsApp - 08036954354

6.3 Ƙalubalen Biɗa Da Tanadin Hausawa a Duniyar Intanet

Ƙalubalen biɗa da tanadi a nan yana nufin wasu al’amura ko yanaye-yanaye waɗanda suke haifar da naƙasu ko koma-baya dangane da harkokin biɗa da tanadin Hausawa a duniyar intanet. A matakin duniya, akwai nau’o’in ƙalubale daban-daban da suke kawo tasgaro ga harkokin biɗa a duniyar intanet. Duk da haka, za a mayar da hankali kan waɗanda suka shafi Hausawa kawai. A ƙasa an kawo wasu ƙalubalen da suke yi wa Hausawa tarnaƙi a ƙoƙarinsu na rungumar hanyoyin biɗa da tanadi a duniyar intanet.

6.3.1 Matsalar Wutar Lantarki

Dukkannin nau’o’in ƙwadagon kan intanet da na’urori ake gudanar da su. Amfani da na’urori kuwa abu ne da yake buƙatar wutar lantarki. Wannan ya kasance wani babban ƙalubale ga ‘yan ƙwadagon kan intanet da suke wuraren da ba su da dauwamammiyar wutar lantarki. Matsalar wutar lantarki ba baƙon al’amari ba ne a Nijeriya (ƙasar da take da yawan Hausawa sama da ko’ina a duniya). Ko bayan matsalar yawan ɗauke wuta, akan samu lalacewar wuta a matakin ƙasa baki ɗaya (national grid collapse). Ademola (2024) ya kawo rahoton cewa, a shekarar 2024 kaɗai, wutar ƙasar ta lalace har sau goma a tsakanin watan Janairu zuwa Nuwamba.

A jahohin arewacin Nijeriya kamar su Bauchi da Kano da Katsina da Sakkwato da Zamfara, Hausawa ‘yan ƙwadagon kan intanet da dama suna aiki ne cikin matuƙar takura. Hakan yana kawo musu naƙasu game da ayyukansu. Kammala aiki cikin lokaci yakan kasance ƙalubale babba. Sau da dama a bisa tilas sukan je gidajen sayar da mai ko kafe (cafe) domin samun caji kawai.[1]

6.3.2 Matsalar Sabis Ɗin Intanet

Kamar yadda sunan ya nuna ƙarara, a kan intanet ake gudanar da ƙwadagon kan intnet. Ko ma wane nau’in ƙwadagon kan intanet mutum yake gudanarwa, akwai gaɓar da dole sai ya buƙaci sabis. Za ta iya yiwuwa domin yaɗawa da tallata hajarsa, ko domin karɓar aiki ko gudanar da aikin ko kuma tura shi yayin da aka kammala.

Hausawa da suke gudanar da ƙwadagon kan intanet musamman mazauna Nijeriya suna fuskantar wannan ƙalubale. Akan samu lokutan da ayyuka suke wuce su ko su kasa tura aiki cikin lokaci, da dai sauran matsaloli makamantan waɗannan. Idan aka ɗauki ayyukan fassara a matsayin misali, sau da dama akan gudanar da su ne a kan injunan fassara (kamar yadda aka tattauna a ƙarƙashin 6.1.11 a sama). Yayin da babu sabis ɗin intanet mai ƙarfi, kai tsaye ba za a iya gudanar da ire-iren ayyukan ba.

6.3.3 Rashin Koyar Da Zamanantattun Darussa

A manyan da ƙananan makarantu a Nijeriya, an fi mayar da hankali kan ra’o’i da tsurar karatu a maimakon aiwatar da ilimi a aikace. Bugu da ƙari, sau da dama akan koyar da abubuwa ne waɗanda an riga da an wuce su a duniyar kimiyya da fasaha. Idan aka ɗauki fannin fassara a matsayin misali, har yau an fi mayar da hankali wajen koyar da ra’o’inta kawai. Wannan ya shafi ma’anar fassara da ire-irenta da barun gudanar da ita a gargajiyance. Duk da bayanan za su iya kasancewa masu muhimmanci, ba su da wani tasiri mai yawa a duniyar fassarar yau.

A ɓangaren intanet da na’urori ma akan ci karo da irin wannan ƙalubale. Intanet wani al’amari ne mai sarƙaƙiya tare da cakwakiya. Yana buƙatar ilimi na musamman. Yana tafiya da harsuna na daban. Yayin gudanar da al’amuran intanet, akwai buƙatar samun ilimin waɗannan yaruka ko harsunan intanet.[2]

Rashin samun ilimin waɗannan harsunan intanet koma baya ne ga gudanar da harkokin kafafen intanet. Sun kasance tamkar tubalan ginin kafafen. Idan babu su, kafafen intanet ba za su iya wanzuwa ba kamar yadda ake kallon su. Akwai dalilai da suke sa Hausawa ƙasa a guiwa a wannan ɓangare na koyon harsunan intanet. Sun haɗa da:

i. Babu wadatattun masu ilimin da za su koyar da harsunan intanet da kwamfuta.

ii. Babu wadatattun santoci da makarantun koyar da harsunan intanet da kwamfuta.

iii. Yawancin Hausawa ba su da ra’ayi a wannan ɓangaren ilimi.

iv. Koyon harsunan kwamfuta da intanet yana buƙatar biyan kuɗin horaswa. Yawancin waɗanda suke da ra’ayin koyon ba su da damar biyan kuɗin horaswar da ake buƙata.

A ɓangare guda kuwa, harkar gudanar da kafafen intanet abu ne mai buƙatar lokaci. Da farko akwai buƙatar lokacin koyon harsunan kamar yadda aka ambata a sama. Samun wannan lokaci ba ƙaramin ƙalubale ne ba. Da a ce akwai tallafi ga masu wannan hoɓɓasawar, da haƙiƙa gudanar da kafafen zai zo da sauƙi. Dalili shi ne, tallafin zai ishe su biyan buƙatun rayuwar yau da kullum. Haka na nufin kenan za su duƙufa ka’in da na’in wajen aiki ba kama hannun yaro, tun da ba su tunanin rashin ruwan ciki wanda da shi ne ake jan na rijiya.

A shekarar 2022, Hukumar Kula Da Jami’o’i Ta Ƙasa (National Universities Commission (NUC)) ta yi wani hoɓɓasa na sanya tsarin koyar da zamanantattun darussa a jami’o’i. Hakan zai ƙara samar da hanyoyin dogaro da kai ga waɗanda suka kammala karatun jami’a, saɓanin yanzu da aka fi mayar da hankali kan ayyukan gwamnati kawai.[3] Kamar yadda NUC (2022 sh. 1) ta nuna, an saka kwasakwasai masu alaƙa da intanet da kwamfuta domin ɗalibai su sami ilimin zamani. Hakan ne zai ba su damar iya yin gwagwarmaya a duniyar yau.

6.3.4 Talauci

Talaucin[4] da ake fama da shi a yankunan ƙasar Hausa wani ƙalubale ne ga ‘yan ƙwadagon kan intanet. Da dama daga cikin hanyoyin samun kuɗi a kan intanet sun dogara ne ga al’ummar da ake gudanar da aiki dominta ko kuma ake yi mata talla. Ana iya tabbatar da hakan yayin da aka yi la’akari da cewa:

a. Wanda ya buɗe kafar intanet ta Hausa sannan ya sanya masa tsarin yin rajista, lallai ba zai samu kwastomomi.

b. Wanda ya buɗe kafar intanet ta Hausa sannan ya dogara a kan tallace-tallace domin samun kuɗin shiga, lallai ba zai samu wata riba ba. Hakan yana faruwa ne kasancewar ƙasar Hausa ba ta ɗaya daga cikin wuraren da ɗora tallace-tallace yake kawo kuɗi. Wannan ma yana da alaƙa kai tsaye da talaucin yankin da kuma rashin bunƙasarsa a fannin sayayyan kayayyaki a kan intanet.

c. Wanda ya ƙware a wani fannin ƙwadagon kan intanet da ya shafi intanet da na’urori, yawanci sai dai ya riƙa neman ayyuka daga ƙasashen ƙetare. Hakan yana faruwa ne kasancewar a yankunan ƙasar Hausa babu cigaban yawaitar buƙatun ire-iren ayyukan (kamar bayar da tsaro a kafar intanet da makamantansu).

Waɗannan matsaloli da sauran makamantansu sun kasance ƙalubalen da suke da alaƙa da tattalin arzikin Hausawa. Ko a duniyar zahiri, mutuwar al’adar sayen littattafai ba ta taƙaita ba ga rashin son karatu ba kawai. Tana da alaƙa da matsalolin kuɗi da suke damun ɗalibai da manazarta. Haka abin yake a duniyar intanet. Mafi yawan Hausawa ba su iya saya ko zama silar samun kuɗi ga ‘yan ƙwadagon kan intanet.[5]

6.4.5 Rashin Karɓar Sauyi

Ɗan’adam yana da ɗabi’ar ƙin karɓar sauye-sauye a rayuwa. Wannan ne ma ya sa ake da ra’o’in “resistance to change” da “cultural lag” (ƙin karɓar sauyi da liƙe wa al’ada).[6] Waɗannan ra’o’i suna nuna cewa, ɗan’adam yana jin shakku da waswasi game da duk wani sauyi da aka gabato masa da shi a rayuwa. Zuciyarsa za ta raya masa cewa, tsohuwar hanyar da yake bi ita ce daidai. Zai kuma ji cewa, sabuwar hanyar tana iya kasancewa cike da ƙalubale da wahalhalu, sannan ba za ta ɓulle ba.

Mutum yana karɓar sauyi a rayuwa yayin da ya yi amfani da abin da ake kira “overcoming resistance to change” (yaƙar ɗabi’ar ƙin karɓar sauyi). Sau da dama yayin da mutum ya karɓi sabon al’amari, zai yi mamakin kasancewar har ya fi tafarkin da yake bi a baya sauƙi da aminci. Bayan haka, zai yi mamakin yadda sannu a hankali zai saba da sabon sauyin da ya runguma. Sau da dama sauyi yakan zo wa mutum cikin sauƙi, ba kamar yadda a da yake tunanin ba zai iya sabo da shi ba.[7] Masu ƙoƙarin samar da kafafen intanet na Hausa da sauran Hausawa ‘yan ƙwadagon kan intanet suna fuskantar wannan ƙalubale mai alaƙa da ƙin karɓar sauyi a tsakanin Hausawa. Binciken ya gano cewa:

i. Ba su samun goyon bayan da ya kamata yayin da suka tinkari cibiyoyi ko sashe-sashen nazarin Hausa.[8]

ii. Ba su samun goyon bayan da ya kamata yayin da suka tuntuɓi masana harshen Hausa.[9]

iii. Ba a samun goyon baya daga ɗaliban Hausa kamar yadda ya kamata.[10]

Cikin sauƙi, abin da ya kamata shi ne a bi maganar Bahaushe inda yake cewa: “Zamani riga.” Ya jaddada wannan batu a wurin da ya ce: “Zamani abokin tafiya.” Ta hanyar karɓar sauyi ne kawai za a iya amfana da damarmakin da zamani ya zo da su.

6.4.6 Dokokin Gwamnati

A haƙiƙanin gaskiya, sau da dama gwamnatocin ƙasashe sukan yi takun saƙa da mutanen da suka kawo wani sabon sauyin rayuwa. An samu irin wannan har a manyan ƙasashe irin Amurka a lokacin da aka fara yunƙurin farko na ƙirƙiro da kuɗin intanet. Ko a shekarar 2023, BBC sun kawo rahoton yadda Amurka take yaƙar harkar hadahadar kuɗaɗen intanet. Rahoton Sherman (2023 SL. 4-11) ya kawo yadda gwamnatin Amurka take ƙoƙarin daƙile ayyukan wasu kamfanonin hadahadar kuɗaɗen intanet.

Makamancin wannan yana faruwa a Nijeriya. Hasali ma, abin da yake faruwa a Nijeriya ya fi muni. Gwamnati tana fakewa da cewa hadahadar kuɗaɗen intanet shi ne ummul haba’isin faɗuwar darajar naira. Bugu da ƙari, takan ce ta hanyar kuɗaɗen intanet ne ake biyan masu ayyukan ta’addanci a Nijeriya. A ɓangare ɗaya kuwa, Hausawa ‘yan Nijeriya da suke wannan hulɗar kasuwanci sun tafi kan cewa zunzurutun rashin amana da rashin adalci ne suke saka gwamnati fito da waɗannan takunkumai.[11]

Gwamnatin Nijeriya ta saka takunkumai game da nau’o’in kasuwanci daban-daban na duniyar intanet. Abin ya faro tun daga kan taƙaita adadin kuɗin da za a iya turawa ƙasashen waje zuwa dala hamsin ($50) kacal a wata. Sannu a hankali ma ya kasance ba za a iya tura ko sisi ba. Hakan ya yi mummunan tasiri ga Hausawan da suke ƙananan kasuwanci a duniyar intanet.

A lokacin da Hausawa da sauran ‘yan Nijeriya suka rungumi kasuwancin kuɗaɗen intanet ka’in da na’in, sai kuma ga sababbin takunkumai da gwamnati ta gindaya. Sun shafi hana saye da sayar da kuɗaɗen intanet kwatakwata! An rufe asusun bankunan Hausawa masu yawa a dalilin wannan. Ta kai ga duk wanda ya tura kuɗi tare da bayani (transaction statement) wanda yake da alaƙa da kasuwancin kuɗin intanet (ko kuma shi aka turo masa kuɗin), to nan take za a kulle akawun ɗinsa na bankin.

Abin ya wuce nan inda har aka samu jami’an gwamnati[12] suna buɗe akawun a kasuwannin hadahadar kuɗaɗen intanet. Za su shiga a matsayin ‘yan basaja, tamkar dai ‘yan kasuwa na haƙiƙa. Da zarar wani ɗan Nijeriya ya tura musu kuɗi da nufin kasuwanci, nan take za su kulle akawun ɗinsa na banki.[13] Jaridar The African Report (Rahoton Afirka) sun kawo bayanin yadda gwamnatin Nijeriya har ta kai ga kama jami’an kasuwar hadahadar kuɗaɗen intanet mafi girma a duniya, wato Binance. Hakan ya sake jefa Hausawa da sauran ‘yan Nijeriya da suke hadahadar kasuwanci a wannan kasuwa cikin babban ƙalubale (Asu, 2024).

6.4.7 Harshen Kasuwanci

Harshen da ya fi karɓuwa a duniya game da hadahadar kasuwancin duniyar intanet shi ne Ingilishi. Mafi yawan manyan kasuwannin duniyar intanet cikin harshen Ingilishi suke hulɗa. Da dama daga cikin waɗanda suke cikin wasu harsuna na daban sukan fassara kafofinsu zuwa Ingilishi. A ƙasa an kawo misalin manyan kamfanonin duniya da suke da alaƙa da biɗa da tanadin duniyar intanet. Za a iya lura da cewa, dukkanninsu suna cikin harshen Ingilishi ne (ko da kuwa akan samu fassararsu cikin wasu harsunan).

Jadawali Na 13: Manyan Kafafen Intanet Masu Alaƙa Da Biɗa Da Tanadi a Intanet

Sunan Kafa

Kamfani

Babban Shafin Intanet

Babban Ofishi

1

Kasuwannin Kan Intanet

Amazon

Amazon.com, Inc.

www.amazon.com

Seattle, Amurka

eBay

eBay Inc.

www.ebay.com

San Jose, Amurka

Alibaba

Alibaba Group Holding Limited

www.alibaba.com

Hangzhou, China

2

Kasuwannin Hadahadar Kuɗaɗen Intanet

Binance

Binance Holdings Ltd.

www.binance.com

George Town, Cayman Islands

Coinbase

Coinbase Global, Inc.

www.coinbase.com

San Francisco, Amurka

Kraken

Payward, Inc.

www.kraken.com

San Francisco, Amurka

3

Kafafen Sada Zumunta

Facebook

Meta Platforms, Inc.

www.facebook.com

Menlo Park, Amurka

YouTube

YouTube, LLC

www.youtube.com

San Bruno, Amurka

TikTok

ByteDance Ltd.

www.tiktok.com

Los Angeles, Amurka/Beijing, China

4

Manhajoji

Apple

Apple Inc.

www.apple.com

Cupertino, Amurka

Microsoft

Microsoft Corporation

www.microsoft.com

Redmond, Amurka

Google

Alphabet Inc.

www.google.com

Mountain View, Amurka

5

Kuɗaɗen Intanet

Bitcoin

Bitcoin

www.bitcoin.org

Ba shi da wuri taƙamaimai

Ethereum

Ethereum Foundation

www.ethereum.org

Ba shi da wuri taƙamaimai (yana ƙarƙashin jagorancin Ethereum Foundation in Zug, Switzerland)

Tether

Tether Operations Limited

www.tether.to

Road Town, Tortola, British Virgin Islands

Madogara: An tantance waɗannan bayanai daga kafafen intanet na kamfanonin

Wannan ƙalubale ne ga Hausawa, musamman waɗanda ba su naƙalci harshen Ingilishi ba. Dalili kuwa shi ne, karanta bayanai musamman dokoki da ƙa’idojin harƙalla a kan ire-iren waɗannan kasuwanni yakan zama abu mai wahala. Haka kuma, sashen taimako (help center) da na sasantawa sukan kasance cikin Ingilishi ne. A taƙaice, harshen kasuwanci babban tarnaƙi ne ga Hausawa masu biɗa ko tanadi a duniyar intanet.

6.4.8 Samuwar Sauƙaƙan Na’urantattun Hanyoyin Gudanar Da Ayyuka

A baya-bayan nan ana ci gaba da samun sababbin hanyoyin zamani na gudanar da ayyukan da suka shafi kwamfuta da na’urori. Idan aka ɗauki ayyukan da suka shafi gyara hotuna da bidiyoyi da zane-zane a matsayin misali, za a tarar wannan kasuwa tana samun sauye-sauye. A yau akwai kafafen intanet da manhajoji da dama da suke aiwatar da waɗannan ayyuka cikin sauƙi. Ma’ana dai, an tsara su ta yadda duk mai so zai iya yi wa kansa ire-iren waɗannan ayyukan ba tare da ya biya kuɗi ga wani ɗan ƙwadago don ya yi masa ba. A ƙasa an kawo misalansu:

a. Adobe Express - (https://www.adobe.com/express)

b. Canva - (https://www.canva.com

c. Clipchamp - (https://www.clipchamp.com)

d. Fotor - (https://www.fotor.com)

e. InShot - (https://inshot.com)

f. iPiccy - (https://ipiccy.com)

g. Kapwing - (https://www.kapwing.com)

h. Photopea - (https://www.photopea.com)

i. Pixlr - (https://pixlr.com)

j. VEED.io - (https://www.veed.io)

Samuwar ire-iren waɗannan kafafen intanet da manhajoji ƙalubale ne ga Hausawa da sauran al’ummomi masu irin wannan sana’ar kasancewar a har kullum suna ƙara rasa kwastomomi.

A ɓangaren ayyukan da suka shafi kimiyyar harshe ma akan samu ƙalubale makamantan wannan. Samuwar injunan fassara yana barazanar maye gurbin ma’aikatan fassara masu yawa a duniya. Yanzu da ake ci gaba da samun ingancin injunan fassarar harshen Hausa, hakan yana zama ƙalubale ga Hausawa masu ayyukan fassara a kan intanet. Samuwar ƙirƙirarriyar basira kuwa, barazana ce ga ayyukan da suka shafi ƙirƙirar rubutu.




[1] A.M. Umar (keɓantacciyar tattaunawa, 18 ga watan Agusta 2023) da M.S. Wali (keɓantacciyar tattaunawa, 18 ga watan Agusta 2023) da J. Abdullahi (keɓantacciyar tattaunawa, 21 ga watan Nuwamba 2024).

[2] An kawo wasu daga cikinsu a babi na huɗu. Sun haɗa da CSS (Cascading Style Sheets) da HTML (Hypertext Markup Language) da PHP (Personal Home Page Tools) da sauransu.

[3] A wannan yunƙuri, NUC ta samar da abin da ta kira ‘Core Curriculum and Minimum Academic Standards (CCMAS) for Nigerian Universities’.

[4] Yana da kyau a fahimci cewa, talauci a nan yana nufin ƙarancin kuɗaɗen da suke hannun al’umma waɗanda ba za su ishe su ba wajen biyan buƙatunsu na yau da kullum har su samu ragowar da za su kashe a kan abubuwan nishaɗi. Bai shafi arzikin albarkatun ƙasa ko wani nau’in arziki da zai iya kasancewa mai yawa a ƙasar Hausa ba.

[5] A ɓangare ɗaya, akwai tasirin ƙarancin ilimin sayayya da gudanar da sauran lamura a kan intanet. Duk da haka, “samu ya fi iyawa.” Masu wadata ba sa rasa hanyoyin da za su bi domin sayan abin da suke muradi a kan intanet.

[6] Domin samun ƙarin bayani ana iya duba Zhu & Zhu (2022) da Rizescu (2024).

[7] Har ya zuwa shekarar 2024, akwai mutanen da suke amfani da samfurin Microsoft Office 2007. Sun ƙi karɓar sababbi da aka samar waɗanda an bunƙasa su sama da na 2007. Wasu da suka karɓi sauyin, sun nuna farin ciki da gamsuwa. Kamar haka abin yake a sauran ɓangarorin rayuwa. Wannan ne ya sa Bahaushe yake cewa: “Sai an gwada akan san na ƙwarai.”

[8] A ƙasashen da suka ci gaba, kusan abu ne da ya zama tilas kowane sashe a jami’a ya kasance yana da kafar intanet (za a iya tabbatar da hakan yayin da aka bincika duniyar intanet). Dangane da sashe-sashen nazarin Hausa, ba haka abin yake ba. Har ya zuwa 2020, wannan bincike bai ci karo da ko da sashen koyar da Hausa a Nijeriya ko Nijar guda ɗaya da yake da kafar intanet tasa ta kansa ba! Wai “wata miyar sai a maƙwabta!” Duk da haka, a yanzu akwai sashe-sashen da suka zabura inda suka fara buɗe kafafen intanet na laburaren sashe ko domin mujallar sashe. Misalansu sun haɗa da www.tasambo.com da www.delac-elibrary.digital (mallakin Sashen Nazarin Harsuna da Al’adu, FUGUS) da www.dundaye.com (mallakin Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, UDUS) da www.yumsuk-hausa.digital (mallakin Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, YUMSUK).

[9] An yi hira da Bunza, (2019) bayan ya dawo daga taron ƙara wa juna sani na ƙasa da ƙasa wanda aka gudanar a Folan. Ya bayyana cewa mallakar kafar intanet dole ne ga malami a ƙasashen da suka ci gaba. Wannan abu ba haka yake ba a ƙasar Hausa. Dangane da abin da wannan bincike ya gano, masana Hausa da suka mallaki kafafen intanet ba su da yawa.

[10] Ɗaliban Hausa sun fi ƙwarewa a kafafen sada zumunta kamar su Fesbuk da Was’af. Sukan ɓata lokaci matuƙa a ire-iren waɗannan shafuka. Da a ce za su mayar da hankali wajen bibiyar shafukan intanet na Hausa, to “da ba kwaɗo ba inji gaya.”

[11] An samu waɗannan bayanai ta hanyar shiga a dama da mai bincike (Participant Observation (PO)).

[12] Masu kasuwancin kan intanet sukan ce ma’aikata ne daga Babban Bankin Nijeriya (Central Bank of Nigeria (CBN)).

[13] Domin ƙarin bayani game da takunkuman da gwamnatin Nijeriya ta sha gindayawa game da hadahadar kuɗaɗen intanet da sauran nau’o’in kasuwancin kan intante, ana iya duba Asu (2024) da Obiezu (2024) da Okamgba (2024) da Onukwue (2024) da Uba (2024).

Post a Comment

0 Comments