𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu
Alaikum Malam Ina kwana ya gida.
Ga tambayata kamar haka; Shin bikin takutaha da ake yi a Kano yana da alaƙa da Addinin Musulunci?
SHIN
BIKIN TAKUTAHA DA AKE YI YANA DA ALAƘA DA ADDININ MUSULUNCI
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus
Salam Warahmatullahi Wabarakatuh.
Bikin
takutaha, wanda ake kira hawan takutaha ko hawan dausayi, al’ada ce da ake yi a
Kano bayan Sallar Idi. Ba ya daga cikin ibadun da Musulunci ya shar’anta. Babu
aya a Alƙur’ani
ko hadisi sahihi da ya tabbatar da cewa Manzon Allah (Sallallahu Alaihi
Wasallam) ko Sahabbai sun yi irin wannan hawa ko biki.
Allah
S.W.T. Ya ce
الْيَوْمَ أَكْمَلْتُ لَكُمْ دِينَكُمْ وَأَتْمَمْتُ عَلَيْكُمْ
نِعْمَتِي وَرَضِيتُ لَكُمُ الْإِسْلَامَ دِينًا
A
Yau Na cika muku addininku, kuma Na cika muku ni’imata, kuma Na yarda muku da
Musulunci ya zama addini. (Suratul Ma'idah).
Addinin
musulunci Allah ya riga da ya cika shi babu bukatar karin wani abu. Mudai aikin
dake gabanmu muyi dukkan abinda Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya
koyar damu. Ba mu kirkiro wani abu daban da niyyar neman soyayyar manzon Allah
(Sallallahu Alaihi Wasallam) ko neman kusanci, Ana neman yaddar Allah da Manzon
Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ta hanyar yin abinda suka umarce mu da hani
akan abinda suka hanemu.
Manzon
Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce
مَنْ أَحْدَثَ فِي أَمْرِنَا هَذَا مَا لَيْسَ مِنْهُ فَهُوَ
رَدٌّ
Duk
wanda ya ƙirƙiro wani abu a cikin al’amarinmu na addini wanda ba ya cikinsa, to an mayar
da shi. (Bukhari da Muslim).
Kaga
kenan duk wanda ya yi da niyyar samun lada babu lada kuma abinda ya yi an mayar
masa dashi.
Idan
aka ɗauki takutaha a matsayin al’adar gargajiya kawai,
ba ibada ba, to ana duba abubuwan da ake yi a cikinta. Idan ta ƙunshi
abubuwan da suka saɓa
wa Shari’a, kamar shaye-shaye, haɗa maza da mata ta hanyar da ba ta dace ba, alfasha,
shirka ko camfi, to waɗannan
abubuwan haramun ne.
Amma
idan al’ada ce kawai wadda ba ta ƙunshi abin da ya saɓa wa Shari’a, ba za a ɗauke ta a matsayin ibada ba kuma babu laifi akan
hakan.
Bikin
takutaha a Kano ba ya daga cikin ibadun da Addinin Musulunci ya shar’anta.
Al’ada ce ta gargajiya da ake gudanarwa kuma bai kamata a ɗauke ta a matsayin wani ɓangare na addini ba.
Allah
ne Mafisani
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.