An ciro daga littafin:
BIƊA DA TANADI A DUNIYAR INTANET
(Sana’o’i, Kasuwanci, Ƙwadago)
Na
Abu-Ubaida SANI
Abdulrahman ALIYU
Talla (Advertisement)
Kalmar talla ba sabuwa ba ce ga
Hausawa. A cikin rubutun Sa’id et al. (2006 sh. 423), an yi bayanin kalmar talla
a matsayin: “(tàllà, sn., mc., jam., tàllàce-tàllàce) (i) yawo da kaya don
sayarwa. (ii) rubuta bayanin wani abu a jaridu, ko maƙala takardu a bango ko jikin wani abu, don neman mai
saye.”
A wannan bagiren, talla tana nufin
tallata haja ko ra’ayi ko aƙidar wani ko waɗansu domin
samun kuɗi. Kusan wannan nau’in talla ba a samun sa a duniyar zahiri – duk da
akan samu makamantansa da ake gudanarwa a gidajen talabijin da na rediyo da
kuma cikin finafinai. A yau Hausawa da dama sun yi nisa a wannan harkar
kasuwanci. Ana gudanar da tallar kan intanet ta fuskoki daban-daban da suka
haɗa da:
i.Talla a kan kafafen
intanet (websites & blogs)
ii.Talla a shafuka da
zaurukan kafafen sada zumunta
iii.Talla ta hanyar raba liƙau
A. Talla a Kan Kafafen Intanet (Websites
& Blogs)
Wanda yake da kafar intanet da ta gawurta,
yana da damar ɗora tallace-tallace a kai. Tallar tana iya kasancewa ta fuskoki
guda biyu, ko dai Adsense[1] ko kuma keɓantattun tallace-tallace.[2] A ƙasa an kawo misalin yadda
aka ɗora talla a kafar Isyaku (www.isyaku.com).
Hoto Na 4.18: Talla a kafar intanet
Madogara:
An
ɗauko daga https://www.isyaku.com/search/label/FADAKARWA
A hoto na 4.18 da yake sama, za a ga yadda
aka ɗora talla a kafar Isyaku. Mamallakin wannan kafa Bahaushe ne ɗan jahar
Kebbi, mai suna Isyaku Garba.
B. Talla a Shafuka Da Zaurukan Kafafen Sada
Zumunta
Waɗanda suke da zauruka da shafuka a kafafen
intanet na da damar ɗora tallace-tallace idan sun cika ƙa’idojin da ake buƙata. Ƙa’idojin sun danganta da kafar da kuma mutum ko mutane ko
kamfanonin da za su ba da tallar. Bugu da ƙari, ƙa’idojin suna sauyawa
lokaci zuwa lokaci.
Hausawa da dama suna samun kuɗi a YouTube da
Facebook da Instagram da TikTok a dalilin irin wannan nau’in tallar. Mawaƙan Hausa na zamani da ‘yan barkwanci Hausawa masu yawa
suna cin gajiyar wannan damar. Tuni masu tsara finafinan Hausa ma suka rungumi
wannan nau’in kasuwanci inda suke sakin finafinansu a kan YouTube tare da ɗora
tallace-tallace domin samun kuɗin shiga. Fitattun finafinan Hausa masu dogon
zango da ake nunawa a kan YouTube sun haɗa da:
a. Amaryar TikTok
b. Asin Da Asin
c. Garwashi
d. Izzar So
e. Kalma Ɗaya
f. Ƙwalla
g. Labarina
h. Sarƙa
i. Zagon Ƙasa
j. Zallar Mata
Sauran ‘yan finafinan Hausa da mawaƙa da ‘yan barkwanci masu yawa suna da tashoshi a kafar
YouTube. Wasu kuwa sun fi bayar da ƙarfi a kan TikTok. Sukan
ɗora tallace-tallace a waɗannan kafafen. Misalansu sun haɗa da:
a. Abubakar Sadauki
(Aibs_Fulani)[3]
b. Ali Muhammad Idris
(Maɗagwal)[4]
c. Bello Galadanchi (Danbello)[5]
d. Mu'azu Muhammad (Bushkiddo)[6]
e. Nazifi Abdulsalam Yusuf
(Nazifi Asnanic)[7]
C. Talla Ta Hanyar Raba Liƙau
Wannan nau’in kasuwancin kan intanet ya shafi
tura saƙonnin talla na wani kamfani a kafafen sada
zumunta ta sigar liƙau.[8] Mai wannan kasuwancin yana ɗaukar liƙau da za a riƙa ba shi a kowace rana (ko
wani lokacin da aka ƙayyade) sannan ya raba a
kafafen sada zumunta irin su Facebook, TikTok, WhatsApp, da sauransu.
Hausawa da dama sun samu riba mai yawa daga
wannan kasuwanci. Duk da haka wannan nau’in kasuwanci tamkar caca yake. Dalili
kuwa shi ne, sau da dama ire-iren waɗannan nau’o’in kasuwanci suna yin ɓatar
dabo na farat ɗaya. A haka ake rufewa da kuɗaɗen waɗanda suka yi aiki ba a biya
su ba, da kuma kuɗaɗen waɗanda suka sanya hannayen jari.[9] Daga cikin ire-iren waɗanda aka ci kasuwarsu
kuma suka watse akwai:
a. Uwork
b. Insme
c. MyBonus
[1] Wannan nau’in talla ne inda ake rajista da
kamfanin Google. Kamfanin na Google ne zai riƙa karɓar tallace-tallace sannan ya riƙa ɗora waɗanda suka dace a kafar wanda ya yi rajistar (ta
la’akari da nau’o’in mutanen da suke ziyartar kafar tasa).
[2] Wannan nau’in tallace-tallace ne da ake
karɓa daga ɗaiɗaikun mutane ko kamfanoni ko ƙungiyoyi. Kai tsaye akan yi ciniki da yarjejeniyar yadda
tallar za ta kasance (kamar abin da ya shafi farashi, da shafukan da za a ɗora
su da tsawon lokacin da za su ɗauka kafin a sauƙe su).
[3] A duba https://www.youtube.com/@abis_fulani.
[4] A duba https://www.youtube.com/@AliArtwork1.
[5] A duba https://www.youtube.com/@bellogaladanchi.
[6] A duba https://www.youtube.com/@Bushkiddo.
[7] A duba https://www.youtube.com/@nazifiasnanic.
[8] A waɗansu lokuta yakan kasance bidiyo ko
hoto ko rubutu.
[9] An samu waɗannan bayanai daga tattaunawa da
aka yi da Hausawa da suka ci irin wannan kasuwa a baya. A. Sani (keɓantacciyar
tattaunawa, 11 ga watan Maris, 2023) ya yi cikakken bayanin yadda harƙallolin suke gudana.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.