Ticker

6/recent/ticker-posts

Kasuwancin Kudaden Intanet (Crypto) Wanda Ba Ya Bukatar Uwar Kudi

 An ciro daga littafin:

BIƊA DA TANADI A DUNIYAR INTANET
(Sana’o’i, Kasuwanci, Ƙwadago)

Na

Abu-Ubaida SANI
Abdulrahman ALIYU

Bida Da Tanadi a Duniyar Intanet (Sana’o’i, Kasuwanci, Kwadago)
Manazartar Littafi: Sani, A-U. & Aliyu, A. (2026). Biɗa Da Tanadi a Duniyar Intanet (Sana'o'i, Kasuwanci, Ƙwadago). Amsoshi Academic Publishers. ISBN: 978-978-62480-1-1. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.21361768

Tuntuɓa Domin Samun Littafi: 
Dr. Abu-Ubaida Sani: Imel - abuubaidasani5@gmail.com | WhatsApp - 08133529736
Dr. Abdulrahman Aliyu: WhatsApp - 08036954354

4.4.2.2 Marar Uwar Kuɗi

Bayan nau’o’in kasuwancin kuɗaɗen intanet da suke buƙatar uwar kuɗi (waɗanda aka tattauna a ƙarƙashin 4.4.1.1 a sama), akwai kuma waɗanda ba sa buƙatar uwar kuɗi. A maimakon haka, jarin da Bahaushe ɗan kasuwa yake buƙata kawai shi ne wanda zai sayi kayan aiki. Kayan aikin kuwa sun haɗa da na’ura kamar waya ko kwamfuta da kuma datar burawuzin. Bayan haka akwai samar da tushen caji, kamar biyan kuɗin wutar lantarki ko na man janareta, da makamantansu.

Wannan ma fanni ne wanda ba a bar Hausawa a baya ba game da shi. Nau’o’in hadahadar kuɗin intanet da suke ƙarƙashin wannan rukuni su ne:

1. Haƙo (Mining)

2. Ruwan Kuɗi (Air Drop)

4.4.2.2.1 Haƙo (Mining, Proof-of-Work (PoW))

A bagiren hadahadar kuɗaɗen duniyar intanet, haƙo yana nufin wata tsararriyar hanya da ake bi ta amfani da na’urori da sabis ɗin intanet da manhajoji na musamman domin tara wani nau’in kuɗi ko kadarar duniyar intanet. A Ingilishi ana kiran sa da suna ‘mining’. Wannan kalmar tana ɗaukar ma’anar haƙo ma’adanai daga ƙasa kamar zinariya da azurfa a duniyar zahiri kamar yadda Hausawa suka sani. A haƙiƙanin gaskiya abin da yake faruwa a haƙon kuɗi da kadarorin duniyar intanet ana iya kwatanta shi da haƙon ma’adanan duniyar zahiri. Wani abu da yake ƙara jaddada hakan shi ne yadda Hausawa suke kiran jagaba a dukkannin nau’o’in kuɗaɗen duniyar intanet da suna ‘Sisin Gwal’, wato ‘Bitcoin.’

Ɗanmusa Gombe ya yi waƙa sukutum mai taken Sisin Gwal, inda a ciki yake cewa:

Sisin gwal tsada,

Mai wayo ka saye,

(Musa Muhammad Ɗanmusa: Sisin Gwal)

Hausawa sun yi haƙon kuɗaɗen intanet masu yawa. M.M. Manga (keɓantacciyar tattaunawa, 7 ga watan Nuwamba 2024) ya bayyana waɗansu daga cikin kuɗaɗe ko kadarorin intanet da ake haƙowa kamar haka:

a. Bitcoin (BTC) (https://bitcoin.org)

b. Ethereum Classic (ETC) (https://ethereumclassic.org)

c. Monero (XMR) (https://www.getmonero.org)

d. Litecoin (LTC) (https://litecoin.org)

e. Ravencoin (RVN) (https://ravencoin.org)

f. Zcash (ZEC) (https://z.cash)

4.4.2.2.2 Ruwan Kuɗi (Air Drop)

Wannan hanya ce ta mallakar kuɗi ko kadarar intanet ba tare da buƙatar sanya uwar kuɗi/jari ba, sannan ba tare da an yi haƙo ba. A maimakon haka, za a samu kyautar kuɗaɗen ne tamkar ruwa daga sama. Wannan ya yi kama da yadda abin yake a Ingilishi inda aka kira shi da sunan ‘Air Drop’, wanda zai iya ɗaukar ma’anar jefo abubuwa daga sama.

Yawanci ya fi faruwa ga sababbin kuɗaɗen intanet. Suna iya bayar da kyautar waɗansu sulalla haka kawai. Suna kuma iya bayarwa bayan mutum ya tura musu buƙatar samun kyautar. Ana kuma iya fitar da tsarin waɗansu ayyuka waɗanda idan mutum ya yi su, to za a ba shi kyautar kuɗin intanet. Ayyukan suna iya kasancewa tura saƙonni a kafafen sada zumunta ko buɗe waɗansu liƙau, da dai makamantansu.

M.M. Manga (keɓantacciyar tattaunawa, 7 ga watan Nuwamba 2024) da A. Sani (keɓantacciyar tattaunawa, 7 ga watan Nuwamba 2024) sun tabbatar da cewa Hausawa masu yawa sun amfana da irin wannan tsarin. Misalan kuɗaɗen intanet da aka yi ruwansu sun haɗa da:

a. Ambient (TBA) (https://ambient.finance)

b. zkSync (ZKS) (https://zksync.io)

c. Renzo (REZ) (https://renzoprotocol.com)

d. Marginfi (MRGN) (https://marginfi.com)

e. LayerZero (TBA) (https://layerzero.network)

f. Wormhole (Wormhole Token) (https://wormhole.com) 

Post a Comment

0 Comments