Ticker

6/recent/ticker-posts

Samun Kudi Ta Hanyar Koyarwa a Kan Intanet (Online Tutoring)

An ciro daga littafin:

BIƊA DA TANADI A DUNIYAR INTANET
(Sana’o’i, Kasuwanci, Ƙwadago)

Na

Abu-Ubaida SANI
Abdulrahman ALIYU

Bida Da Tanadi a Duniyar Intanet (Sana’o’i, Kasuwanci, Kwadago)
Manazartar Littafi: Sani, A-U. & Aliyu, A. (2026). Biɗa Da Tanadi a Duniyar Intanet (Sana'o'i, Kasuwanci, Ƙwadago). Amsoshi Academic Publishers. ISBN: 978-978-62480-1-1. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.21361768

Tuntuɓa Domin Samun Littafi: 
Dr. Abu-Ubaida Sani: Imel - abuubaidasani5@gmail.com | WhatsApp - 08133529736
Dr. Abdulrahman Aliyu: WhatsApp - 08036954354

4.6 Koyarwa a Kan Intanet (Online Tutoring)

Ci gaban zamani ya samar da hanyoyi daban-daban da ake iya bi domin koyo da koyarwa ba tare da an shiga aji a zahiri ba. Waɗannan hanyoyi sun haɗa da manhajoji da kafafen intanet. Samuwar cutar Korona a watan Disamba na shekarar 2019 da kuma yaɗuwarta a shekarar 2020 zuwa 2021 sun sanya manyan makarantu masu yawa a duniya sun koma tsarin koyarwa ta kan intanet yayin da ɗalibai da malamai suke kulle a gidajensu.

A ɓangare ɗaya kuwa, ana ci gaba da samun ƙaruwar makarantun kan intanet. Ko a nan gida Nijeriya, makarantar kan intanet ta gwamnatin tarayya ba ɓoyayyiya ba ce. Jami’ar Tarayya ta Kan Intanet wato National Open University (NOUN) tana da kwasakwasai masu tarin yawa, ciki har da Hausa.

Akwai manyan hanyoyi uku (3) da ake iya cin gajiyar koyarwa a duniyar intanet. Hanyoyin su ne:

i. Zamowa malami ko ma’aikaci na dindidin ko na wucin gadi a wata makarantar duniyar intanet

ii. Zamowa malami mai cin gashin kansa wanda yake koyarwa a duniyar intanet

iii. Aikin dindindin ko na wucin gadi a matsayin ƙwararre a wata makarantar duniyar intanet

4.6.1 Malamin Makarantar Kan Intanet (Online Tutor)

Yana da kyau a fahimci cewa, makaranta a kan intanet ba ta taƙaita ga jami’o’i da sauran makarantun gwamnati ba kawai. Sun haɗa har da makarantu masu zaman kansu manya da ƙanana. Bugu da ƙari, sukan kasance cikin nau’o’i da sigogi daban-daban. Sun shafi na koyar da ilimin fannonin karatun boko da na addini, har zuwa kan koyar da sauran ilimummuka na rayuwar yau da kullum kamar kwamfuta ko kasuwanci ko girke-girke da dai sauransu. Wannan ma fage ne wanda tuni aka fara samun Hausawa a cikinsa.

Kowace makaranta tana da tsarinta daidai da muradunta. Ana iya nazartar makarantun kan intanet ta fuskoki guda biyu kamar haka:

a. Makarantu

b. Kafafen koyi-da-kanka

A – Makarantu

Akwai makarantun kan intanet masu tarin yawa a faɗin duniya. Waɗansu kuwa, suna da tsarin koyarwa ne iri biyu. Wato suna da tsarin koyarwa na kan intanet, da kuma na shiga aji a duniyar zahiri. Iri-iren waɗannan makarantu ma sun jaddada samar da tsarin shiga aji iri biyu, ɗaya na duniyar zahiri, ɗayan kuwa na duniyar baɗini. Mutum yana iya tura buƙatar neman aiki zuwa ga ire-iren waɗannan makarantu. Wani abin burgewa shi ne, Hausawa a wannan fage suna iya aiki da sama da makaranta ɗaya. Akan samu damar hakan ne kasancewar malami zai riƙa koyarwa ne daga gida, ba tare da buƙatar ɓata lokaci zuwa makaranta ba. Bugu da ƙari, ba sai makarantun da suke koyar da Hausa ba ne kaɗai Hausawa za su iya neman aiki. Hausawa suna iya tura buƙatar neman aikin koyar da duk wani kwas da suka ƙware a kowace makarantar kan intanet. Yana iya kasancewa kwas ɗin harshe ko lissafi ko wani kwas da ya shafi kimiyya da fasaha.

Misalan makarantun kan intanet waɗanda Hausawa za su iya neman aikin koyarwa a cikinsu sun haɗa da:

a. Cambly (https://cambly.com)

b. iTalki (https://italki.com)

c. Lingoda (https://lingoda.com)

d. National Open University (NOUN) – Nijeriya (https://nou.edu.ng)

e. Outschool (https://outschool.com)

f. Preply (https://preply.com)

g. Verbling (https://verbling.com)

h. VIPKid (https://vipkid.com)

Ko bayan waɗannan kafafen, Hausawa suna iya bincika jami’o’in duniya daban-daban waɗanda suke da tsarin karantantarwa a kan intanet. Ana iya tura neman gurbin koyarwa a makarantun.

A - Kafafen Koyi-Da-Kanka

A intanet akwai kafafe masu yawa da suke matsayin makarantu. Malamai daban-daban sukan rubuta darussa su ɗora a kai. Masu son koyon darussan sukan biya kuɗi kafin su buɗe a kan na’urorinsu. Yayin da suka karance su, akwai jarabawa da aka riga aka tsara game da kowane darasi. Ɗaliban za su rubuta jarrabawar. Idan sun ci, akwai takardar shaida wato satifiket da na’ura za ta tura musu.

Tsarin waɗannan kafafen ya bambanta. Akwai waɗanda malamai suke rubuta kwasa-kwasai sannan su sayar wa masu kafafen. Akwai kuma waɗanda ake hulɗa ta haɗin guiwa tsakanin malamai da masu kafafen. A kafafen da ake haɗin guiwa, duk wani kwas ɗin da aka samu kuɗi daga gare shi, to za a raba ribar tsakanin malamin da ya yi rubutun da kuma masu kafar. Za a yi rabon bisa tsarin kaso (%) da aka ƙulla yarjejeniya a kansa tun farko. Wannan dama ce ga Hausawa domin samun kuɗi tare da koyar da darussa da suka shafi adabi da al’ada da harshen Hausa.

Misalan waɗannan kafafe sun haɗa da:

a. Flowdiary (https://flowdiary.com.ng)[1]

b. Kajabi (https://kajabi.com)

c. LearnWorlds (https://learnworlds.com)

d. Podia (https://podia.com)

e. Skillshare (https://skillshare.com)

f. Teachable (https://teachable.com)

g. Thinkific (https://thinkific.com)

h. Udemy (https://udemy.com)

4.6.2 Malamin Kan Intanet Mai Cin Gashin Kansa (Online Tutor/Freelance Tutor)

Kamar yadda aka bayyana a baya a ƙarƙashin 4.6.1, makarantun kan intanet ba su taƙaita ga na gwamnati ba kawai. Sun haɗa har da masu zaman kansu, manya da ƙanana. A yau Hausawa masu yawa suna cin gajiyar wannan damar da zamani ya kawo. Wasu daga cikin fitattu da ake yawan jin ɗuriyarsu a duniyar intanet sun haɗa da:

a. Manhajojin koyi-da-kanka

b. Koyar da girke-girke

c. Koyar da hada-hadar kuɗaɗen intanet

d. Koyar da sauran nau’o’in ilimummuka

A - Manhajojin Koyi-Da-Kanka

Akwai manhajoji da ake samarwa na koyar da abubuwa daban-daban. A cikinsu akwai waɗanda suka shafi koyar da harshe. Manhajojin sukan ɗauki tsarin kwasakwasai na kyauta da waɗanda sai an biya kuɗi sannan a nazarce su. Misalansu sun haɗa da:

Sunan Manhaja
Koyi Turanci

Manhajojin Koyi-Da-Kanka
Learn Hausa Language

Manhajojin Koyi-Da-Kanka
Learn Hausa with Audio

Manhajojin Koyi-Da-Kanka
Mu Koyi Turanci
Manhajojin Koyi-Da-Kanka

Madogara: Rumbun Manhajoji Na Google (Google PlayStore)

Ko bayan wannan, akwai Hausawan da suka ci gajiyar karatun Hausa ta hanyar haɗa manhajojin littattafai ko waƙoƙin Hausa ko waɗansu abubuwa da suka shafi ilimi. Yawanci sukan samu kuɗi daga gare su ta hanyar ɗora tallace-tallace. Misalan waɗannan manhajoji suna da yawa. Daga ciki akwai:

Sunan Manhaja

Magana Jari Ce Littafi Na Uku

Samun Kudi Ta Hanyar Koyarwa a Kan Intanet (Online Tutoring)

All Hausa Novels

Samun Kudi Ta Hanyar Koyarwa a Kan Intanet (Online Tutoring)

Hausa Novel Lite: Book Media

Samun Kudi Ta Hanyar Koyarwa a Kan Intanet (Online Tutoring)

Ruwan Bagaja MP3 Audio

Samun Kudi Ta Hanyar Koyarwa a Kan Intanet (Online Tutoring)

Magana Jari Ce 1 2 3 by Abdulkarim Nasir

Samun Kudi Ta Hanyar Koyarwa a Kan Intanet (Online Tutoring)

Madogara: Rumbun Manhajoji Na Google (Google PlayStore)

B - Koyar Da Girke-Girke

Wannan wani sabon fage ne da ya samu bunƙasa musamman bayan shigowar manhajar TikTok a watan Satumba na shekarar 2016.[1] Fitattun waɗanda suka iya abinci a cikin Hausawa ‘yammata da matan aure da dama sun buɗe shafuka a TikTok. A cikin shafukan suna gabatar da laccoci inda suke koyar da girke-girke daban-daban. Wani ƙarin abin burgewa shi ne yadda suke yin darussan cikin bidiyo da sautin magana tare da ƙayatar da su ta hanyar sanya maganganun barkwanci.[2]

Daga cikin waɗanda suke koyar da abinci a intanet cikin harshen Hausa akwai waɗanda suka yi matuƙar fice. Shahara da sanuwarsu har ta kai ga ana amfani da waɗansu kalamansu a matsayin sara. Misalan sara da aka samu sun haɗa da:



[1] Domin samun ƙarin bayani game da samuwar TikTok, ana iya duba Tidy & Galer (2020).

[2] Daga cikin masu koyar da abinci da harshen Hausa a TikTok, akwai waɗanda asalinsu ba Hausawa ba ne. Duk da haka, sun taso da harshen Hausa sannan a cikin Hausawa. Ba su da wani harshe in ba Hausa ba. Waɗansu kuwa da suka iya harsuna biyu, sun ajiye nasu harshen sun rungumi Hausa a sakamakon yawan al’ummar Hausawa da suke kan TikTok.

a. Ministan Sharholiya: Take ne wanda Maryam Adam Hamza (Maryama’s Kitchen) mai koyar da girke-girke a kan TikTok take yi wa kanta.

b. Ina za ki? Dawo ki ga abin da na kawo mana!: Kirari ne wanda Hafsat Fulany (Fulany’s Kitchen) take buɗe bidiyoyinta na TikTok da su.

c. Ku dai kun san wanda ya iya ya huta: Kirari ne wanda Maryam Adam Hamza (Maryama’s Kitchen) take yi wa kanta a cikin bidiyoyinta da suke kan kafar TikTok.

Lokaci zuwa lokaci gwanayen girki sukan buɗe azuzuwan koyar da waɗansu nau’o’in abinci na musamman. Misali a lokacin da azumin watan Ramalana ya gabato, akan samu yawaitar azuzuwan koyar da abinci. Za su sanya farashin yin rajista sannan su ayyana ranaku da manhaja da kuma tsarin koyar da abincin. Yawanci akan yi shi a ƙare ne a kan intanet. Sukan ɗan turo hotonu da gajerun bidiyoyin ɗanɗani-haukace a shafukansu domin zaburar da waɗanda ba su yi rajista ba su samu su yi.

A ɓangare ɗaya kuwa, akwai waɗanda suke koyar da girke-girke a duniyar zahiri. Duk da haka, sukan tura sanarwar neman ɗalibai ne ta intanet. Bugu da ƙari, akan yi tururuwa zuwa azuzuwansu ne sakamkon ficensu a intanet (saboda bidiyoyi da hotunan abincinsu da suka karaɗe intanet).

A ƙasa an kawo misalan waɗansu Hausawa da suke cin gajiyar koyar da abinci a zamanance:

Jadawali Na 8: Wasu Masu Koyar Da Girke-Girke Da Taimakon Intanet

Suna

Inkiyar Kasuwanci

Gari

Nau’o’in Azuzuwa

A’isha Sulaiman

Yummy Bites

Abuja

Intanet da Zahiri

Aisha Delu Aliyu

Delu Concept Services

Sakkwato

Zahiri (tallatawa a intanet)

Fatima Abdulkadir

Faty AK's Cakes & More

Katsina

Intanet da Zahiri

Fatima Hassan Hamma

Zara’s Food & More

Bauchi

Intanet da Zahiri

Hafsat Fulany

Fulany’s Kitchen

Kano

Intanet da Zahiri

Hajara Adamu Yusuf

Hajjo’s Kitchen

Bauchi

Intanet da Zahiri

Khadija Abbas Sani

Khabs Kitchen

Kano

Intanet da Zahiri

Maryam Adam Hamza

Maryama’s Kitchen

Damaturu

Intanet da Zahiri

Madogara: Tattaunawa da bibiyar bayanai a kafafen intanet

Wannan binciken ya fahimci cewa, tabbas Hausawan da suka zamanantar da sana’arsu ta abinci ta hanyar shiga intanet sukan samu riba sosai ta ɓangaren koyarwa. A ƙasa an kawo ƙiyasin kuɗaɗen da masu koyar da abinci suke karɓa daga kowace ɗaliba.

Jadawali Na 9: Ƙiyasin Kuɗaɗen Da Ake Biya Yayin Shiga Ajin Koyar Da Abinci

Nau’in Ɗalibta

Azuzuwan Kan Intanet

Azuzuwan Duniyar Zahiri

Aji mai ɗalibai da yawa (20 zuwa sama)

N5,000 – N25,000

N5,000 – 50,000

Aji mai ɗalibai kaɗan (ƙasa da 20)

N5,000 – 50,000

N5,000 – 50,000

Ajin ɗaiɗaikun mutane (1-5)

N20,000 – 100,000

N20,000 – 200,000

Ajin manyan mutane na musamman

(Ba a samu misali ba)

N50,000 – 500,000 (wani lokaci har da ƙarin kyaututtuka na alkairi)

Madogara: Tattaunawa da masu koyar da abinci a zamanance da bibiyar tallace-tallacensu a kan intanet[4]

C - Koyar Da Hadahadar Kuɗaɗe Da Kadarorin Intanet

A yau akwai Hausawa da dama da suka duƙufa wajen koyar da hadahadar kuɗaɗe da kadarorin kan intanet. Bayan ita sana’ar kuɗaɗen intanet ɗin kanta, wannan koyarwa da suke yi hanya ce ta samun kuɗi a gare su. Bugu da ƙari, koyarwar tana ƙara nuni da yadda Hausawa suke sake rungumar wannan ci gaban zamani.

A ɓangare ɗaya kuwa, ko bayan kuɗaɗe da masu koyarwar suke samu, suna kuma samun waɗanda za su tura wa liƙau ko lambobin “gayyata” (referral) zuwa ga sababbin kuɗaɗen intanet ko waɗansu manhajoji. Gayyata wani tsari ne da yake ba wa masu akawun a wata manhaja ko kafa damar tura gayyata ga wasu mutane na daban. Yayin da suka yi amfani da liƙau ko lambar gayyatar da aka tura musu domin buɗe akawun, to wanda ya tura musun zai samu wani kamasho. Misali, idan haƙo (mining) suka yi, zai samu wani lada daga abin da suka tara. Idan kuma ruwan kuɗi aka yi musu, to shi ma zai samu kaɗan.[5]

D - Koyar Da Harshe

Masana da manazarta harshen Hausa suna da damar koyar da harshe a duniyar intanet domin a biya su. Mutum yana iya buɗe akawun a ɗaya daga cikin kafofin tallata basira. Masu son a koyar da su wani abu game da harshen, za su tuntuɓe shi yayin da suka ci karo da akawun ɗinsa a kan intanet. Baya ga haka, akan tuntuɓi kamfanonin fassara lokaci zuwa lokaci domin su nemo waɗanda za su iya koyar da wani harshe. Kamfanonin fassarar kuwa za su tuntuɓi ma’aikatansu domin samun waɗanda za su iya aikin.

Kafafen da za a iya rajista da su a matsayin malami mai koyarwa a kan intanet sun haɗa da:

a. Freelancer – (https://www.freelancer.com)

b. Guru – (https://www.guru.com)

c. LinkedIn (https://www.linkedin.com)

d. PeoplePerHour – (https://www.peopleperhour.com)

e. TaskRabbit – (https://www.taskrabbit.com)

4.6.3 Aikin Kwangila a Matsayin Masani

Bayan nau’o’in koyarwa da aka ambata a sama, malamai masana suna da damar yin aikin kwangila a ire-iren waɗannan makarantun kan intanet. Lokaci zuwa lokaci makarantun sukan nemi malamai domin su rubuta musu wani kwas ko su yi musu gyare-gyare tare da sabunta kwasa-kwasai yayin da suka samu sababbin sauye-sauye a wannan fannin ilimi. Bayan haka, ana iya neman masanan domin duba ɗalibai a matakin digiri na biyu ko na uku. Misalan kwasakwasan Hausa da masana daban-daban suka rubuta wa Jami’ar Tarayya ta Kan Intanet wato National Open University (NOUN) sun haɗa da:

Jadawali Na 10: Kwasa-Kwasan Da Wasu Masana Suku Rubuta Wa NOUN

 

Kwas

Masanin Da Ya Rubuta

1.

HAU 102: Gabatar Da Tarihin Hausawa (Introduction to the History of the People)

Dr. Aliyu Isa Sulaiman (KASU)

2.

HAU 117: Introduction to Hausa Cultural Studies

Dr. Ibrahim Abdullahi Sarkin Sudan (UDUS)

3.

HAU 210: Morphology of Hausa

Dr. Isah Abdullahi Muhammad (UDUS)

4.

HAU 211: Varieties of Prose in Hausa

Prof. Ibrahim Malumfashi (KASU)

5.

HAU 212: Syntax of Hausa I

Prof. Hafizu Miko Yakasai(BUK)

6.

HAU 214: Hausa Trades and Crafts

Dr. Abdullahi Sarkin Gulbi (UDUS)

7.

HAU 301: Phonology of Hausa II

Dr. Adamu Abdulsalam (FU Kashere)

Madogara: Kafar Intanet Ta NOUN (https://nou.edu.ng)[6]

4.7 Naɗewa

Wannan babi na huɗu ya kawo bayanai game da hanyoyi daban-daban na neman kuɗi a duniyar intanet. Tuni Hausawa suka fara cin gajiyar wasu daga cikinsu. Duk da haka, akwai damarmaki masu tarin yawa da suke wucewa ba tare da an ci moriyarsu ba. Jajircewa domin koyon ire-iren waɗannan sana’o’i da kasuwanci za su taimaka matuƙa wajen rage zaman kashe wando. Za su samar da ayyukan yi masu yawa ga Hausawa matasa maza da mata.



[1] Wannan makarantar a cikin harshen Hausa take.

[2] Domin samun ƙarin bayani game da samuwar TikTok, ana iya duba Tidy & Galer (2020).

[3] Daga cikin masu koyar da abinci da harshen Hausa a TikTok, akwai waɗanda asalinsu ba Hausawa ba ne. Duk da haka, sun taso da harshen Hausa sannan a cikin Hausawa. Ba su da wani harshe in ba Hausa ba. Waɗansu kuwa da suka iya harsuna biyu, sun ajiye nasu harshen sun rungumi Hausa a sakamakon yawan al’ummar Hausawa da suke kan TikTok.

[4] An haɗa waɗannan alƙaluma daga bayanan da suka fito daga Aisha Delu Aliyu (Delu Concept Services) da Fatima Abdulkadir (Faty AK's Cakes & More) da Khadija Abbas Sani (Khabs Kitchen).

[5] A ƙarƙashin 4.4 an kawo misalan waɗannan. A ciki har da makarantun koyar da hadahadar kuɗaɗen intanet da suka haɗa da Arewa Trading Academy da HydarFX Academy Kano da SMT Academy Kaduna.

[6] An ɗauko bayanan a cikin watan Oktoba, shekarar 2024. 

Post a Comment

0 Comments