An ciro daga littafin:
6.4 Illolin Biɗa Da Tanadi a Duniyar Intanet
Yana
da kyau a fahimci cewa, ‘illoli’ a nan suna da bambanci da ‘ƙalubalen’ da aka tattauna a
ƙarƙashin 6.3 da yake sama.
Idan aka ce ‘illolin biɗa da tanadi a duniyar intanet,’ to ana nufin matsalolin
da harkoki da hulɗoɗi da sauran lamuran da suka shafi neman kuɗi da tanadi a
duniyar intanet suke haifarwa. Ma’ana ke nan, wannan ɓangare na bincike zai
mayar da hankali wajen tattauna ire-iren matsalolin da suke aukuwa a sakamakon
lamuran da suka shafi biɗa da tanadi a duniyar intanet, musamman masu alaƙa da Hausawa.
Daga
cikin harkoki da hadahadar kasuwancin intanet akwai waɗanda suke cutar da
muhalli. Misali, haƙon kuɗaɗen intanet irin su Bitcoin yana illata muhalli
matuƙa.
Rahoton Osborne (2022) ya nuna cewa, illar da haƙon Bitcoin yake yi wa
muhalli tana iya kai wanda man fetur yake yi ta fuskar fitar da sinadarin
kabon. Hakan yana faruwa ne sakamakon cewa haƙon Bitcoin yana buƙatar manyan na’urori masu
matuƙar
jan wutar lantarki. Ƙiyasin wutar da ake ja a sakamakon haƙon Bitcoin a duniya, ya kai
wutar da ake sha a illahirin wasu ƙananan ƙasashe. Bugu da ƙari, injuna da kwamfutocin da ake amfani da
su suna fitar da tiririn sinadarai masu illata muhalli. Ayyukan da suka kawo
bayanai game da illolin haƙon Bitcoin sun haɗa da na Truby (2018) da Gallersdörfer
et al. (2020) da Cambridge Centre for Alternative Finance (2025) da
Digiconomist (2025).
A
ɓangare ɗaya kuwa, ayyukan ƙwadagon kan intanet a ƙasashe irin Nijeriya suna
buƙatar
hanyoyin samun wutar lantarki bayan na gama-gari da ake da shi. Wannan ya biyo
bayan ƙalubalen
wutar lantarki da ake fama da shi kamar yadda aka tattauna a sama. Sau da dama
akan yi amfani da janareta domin samun wuta. Shi ma yana fitar da sinarin cabon
wanda yake matuƙar illata muhalli.
Ba
a ci karo da wani bincike da ya tabbatar da cewa yawan kallon sikirin yana
haifar da dauwamammen ciwon ido ba. Duk da haka, masanan ido irin su Dakta
Colman Kraff sun tabbatar da cewa zai iya haifar da matsalolin da suka haɗa da
kallo dishi-dishi da ciwon kai har ma da ciwon wuya idan abin ya yi tsanani.[1] Hakan yakan faru ne musamman idan aka daɗe ana kallon sikirin. A bisa
wannan, yana da kyau Hausawan da abin ya shafa su naƙalci matakan kare lafiyar
idanunsu.
A
ɓangare ɗaya kuwa, na’urori dangin waya da kwamfuta sukan fitar da wani nau’in
tiriri (wanda ido ba ya gani) da ake kira radiyeshin. Binciken Abiola (2021) ya
tabbatar da cewa radiyeshin da yake fita daga jikin kwamfuta yana haifar da
illoli da dama, ciki har da hana haihuwa ga maza. Wannan yakan faru yayin da
ake ɗora kwamfuta a kan cinya idan za a yi aiki, da makamantansu. A wannan
gaɓar ma, yana da kyau Hausawa masu ta’ammuli da na’urori su bi matakan kare
lafiyarsu.
Bayan
waɗannan, ana iya samun matsalar da ta shafi ƙwaƙwalwa sakamakon hadahadar
kasuwancin kan intanet. Akwai hanyoyin neman kuɗi a kan intanet waɗanda suke da
matuƙar
haɗari da ɗaukar kasada. Sun haɗa da nau’o’in kasuwancin kuɗin intanet da na
dauwamammun kadarorin kan intanet. Ana iya samun mummunan hasara ta farat ɗaya.
Ko bayan haka, a kullum ‘yan kasuwa suna cikin zulumin yadda abubuwa za su
kaya.[2]
Haɗuwar ire-iren waɗannan damuwowi da zulumi suna iya jefa mutum cikin ciwon
tunani ko su jawo masa bugun zuciya na farat ɗaya.[3]
‘Yan
ƙwadagon
kan intanet ba su samun shahara har sai an san su sosai a kan intanet (strong
online presence). Wannan mataki ya haɗa har da yaɗa bayanan tuntuɓa a kan
kafafe daban-daban. Yaɗuwar bayanan tuntuɓar mutum kuwa a har kullum suna ƙara buɗe ƙofofi ga ‘yan damfaran kan
intanet. Suna amfani da su domin yunƙurin damfarar masu su ta hanyoyi daban-daban.
Hausawa
waɗanda bayanansu suke kan intanet suna cikin ƙalubalen fuskantar damfara.
‘Yan damfara a kan intanet sun kasance nau’i-nau’i. Akwai waɗanda za su yi ƙoƙarin damfarar mutum domin
samun kuɗi ko wani abin duniya daga gare shi. Akwai kuma ‘yan damfarar da za su
ba wa mutum aiki alhali ba za su biya shi ba. Ga misali a ƙasa:
Hoto Na 6.6: Misalin Gargaɗi Game Da Kamfanonin Fassara Na ‘Yan
Damfara
Madogara: Kamfanin fassara na ByLanguages (www.bylanguages.com)
ya aiko wannan saƙo ranar 08/11/2024
Kamar
yadda aka gani a hoto na 6.6 da yake sama, ire-iren waɗannan ‘yan damfara sukan
buɗe kafar intanet mai ƙayatarwa. Wanda ya duba zai yi zaton kamfanin fassara ne
na haƙiƙa. Yayin da aka yi musu
aiki, daga nan za a daina jin ɗuriyarsu. Irin wannan nau’in damfara da sauran
makamantansu illoli ne da suka shafi ƙwadagon kan intanet.’
Wani nau’in kasuwancin damfara da ake yi a
kan intanet shi ne na yaɗa
liƙau
ɗin da kamfani zai bayar ko gudanar da wani aiki na musamman (task) a kan
intanet. Wasu daga cikin kamfanonin sukan buƙaci a sanya hannun jari ko
a yi rajista kafin fara kasuwancin. Yawancin waɗanda suka shiga da farko-farko,
sukan samu riba. Hakan zai sa su yi ta tallata abin ga abokansu musamman da
yake ana ba da goro na musamman a duk wanda ya kawo wani sabon kwastoma
(referral). A haka daga ƙarshe ake rufewa da kuɗaɗen waɗanda suka yi aiki ba a
biya su ba, da kuma kuɗaɗen waɗanda suka sanya hannayen jari.[4]
Hausawa masu yawa sun faɗa tarkon ire-iren waɗannan kasuwancin damfara. Daga
cikin waɗanda aka yi a baya, kuma suka gudu da kuɗaɗen Hausawa akwai:
a. Catly
b. Dubai
Gold Souk
c. Insme
d. MyBonus
e. Uwork
Waɗansu
kuwa sukan fito ne da sigar kuɗin intanet (kirifto). Daga ƙarshe sai su buƙaci a saka kuɗi na
kasuwancin a kan bulokcen (gas fee). Yayin da aka saka, sai kuma su yi ɓatar
dabo, ko kuma su fito da wani farashin da ko kuɗaɗen da mutane suka saka ba za
su iya fanshewa ba. A wannan ɓangaren ma an rufe da kuɗaɗen Hausawa. Daga cikin
waɗanda Hausawa suka faɗa tarkonsu akwai:
a. Aqua
Protocol[5]
b. Cold
Wallet
c. Rocket
Rabbit
d. Xblast
Ya
zuwa watan Nuwamban shekarar 2024, akwai kasuwancin kan intanet guda biyu da
Hausa da dama suke gudanarwa waɗanda suke da tsarin damfara. Lokaci ne zai nuna
gaskiyarsu ko koma bayan hakan. Su ne:
a. 52u
b. Anchor
A -
52u
An
fara gudanar da shi a shekarar 2024. Kafar intanet da suke amfani da ita ta
kasance www.52u.today. Bugu da ƙari, suna iƙirarin cewa cibiyar
kasuwancin tana Malesiya.[6] A
bayaninsu, manufarsu ita ce yaƙi da talauci da kuma bunƙasa dogaro da kai.
52u
yana da tsarin yin rajista. Matakan rajistarsa guda uku. Yayin da mutum ya yi
rajista, sannan ya biya kuɗi, to 52u za su ba shi aron jari wanda za su saka
masa a akawun ɗinsa domin gudanar da kasuwanci da shi. Yawan kuɗin da za su
saka masa, ya danganta da matakin rajista da ya yi. Matakan rajistan su ne:
a. Basic – dalar Amurka ashirin ($20)
b. Silver – dalar Amurka hamsin ($50)
c. Gold – dalar Amurka ɗari biyu da hamsin
($250)
Duk
wanda ya ya yi rajistar matakin Basic, to za su ba shi dalar amurka ɗari
uku da saban’in da biyar ($375). Wannan bashi zai tsaya a akawun ɗinsa ne, ba
zai iya fita ba. 52u ne za su yi amfani da kuɗin domin yi masa kasuwanci da su.
Kasuwancin an gina shi ne a kan na’urantaccen tsari (automatic). A bisa haka,
mutum ba ya buƙatar yin komai. Kasuwancin da kansa zai gudanar da kansa.
A
kowane wata mutum zai samu ribar da ta kai kimanin dalar Amurka sittin da
bakwai ($67). Da zarar ya fara samun wannan ribar, za a riƙa cire kuɗin da aka ba shi
ba shi (wato $375) har zuwa lokacin da zai biya bashin duka. Idan ya kammala
biyan bashi, to nan ne kuma zai fara cire ribar domin cin gajiyarsu. Mafi ƙarancin abin da za a iya
cirewa shi ne dalar Amurka hamsin ($50).
Shi
ma yana da tsarin gayyata. Duk wanda ya gayyato wani, to zai samu kamasho.
B - Anchor
An
fara gudanar da wannan kasuwanci a shekarar 2024. Kafar intanet da suke amfani
da ita ta kasance https://anchorit.live. Harƙallar Anchor ta haɗa abubuwa daban-daban. Da farko
dai suna da tsarin rajista mai azuzuwa biyu. Wani abu kuma shi ne, duk rajistar
da mutum ya yi, akwai wata garaɓasa da za a ba shi. S. Muhammad (keɓantacciyar
tattaunawa, 24 ga watan Nuwamba 2024) ya bayyana yadda tsarin yake kamar haka:
|
Tsari |
Kuɗin Rajista |
Garaɓasa |
|
Silver |
₦6,000 |
₦6,200 |
|
Pro |
₦8,500 |
₦7,500 |
Wani
abin lura shi ne, mutum ba zai iya cire garaɓasar da za a ba shi ba. A maimakon
haka, za a ajiye su ne a cikin akawun ɗinsa, har sai sun taru. Za su taru ne ta
hanyar sauran jinga da zai riƙa gudanarwa a kan akawun ɗin. Wanda yake Silver sai
kuɗinsa sun kai naira dubu talatin da takwas (₦38,000) kafin ya iya fitarwa.
Wanda yake Pro kuwa, sai sun kai dubu arba’in da takwas (₦48,000).
Jingar
da ake gabatarwa suna da yawa. Sukan kasance cikin tsarin wasannin kan intanet
(online games) da kuma kallon bidiyoyi da kuma tsarawa da ɗora bidiyoyin
tallata harƙallar
Anchor a kan intanet. Bayan haka, akwai nau’o’in jingar da danna kansu kawai
ake buƙatar
yi. Wanda yake Silver dole ne ya hau ya danna da kansa. Wanda yake Pro kuma,
kwamfuta za ta riƙa danna masa. Sauran ɓangarorin da ake samun kuɗi daga
gare su sun haɗa da barin kuɗi masu yawa a akawun ba tare da an cire ba, da
shiga gasa da sauransu.
Bayan
waɗannan, akwai tsarin gayyata. Idan mai Silver ya yi gayyata, za a ba shi
naira dubu biyar da ɗari biyu (₦5,200). Idan Pro ne kuma, za a ba shi naira
dubu bakwai da ɗari biyu (₦7,200). Garaɓasar gayyata ana cire su ne a ranakun
Litinin da Alhamis daga ƙarfe tara zuwa goma sha ɗaya na safe (9:00am – 11:00am).
Mafi ƙarancin
kuɗin da mutum zai iya cirewa shi ne dubu goma (₦10,000).
C -
Tsokaci
Yana
da kyau a lura da cewa, 52u da Anchor suna da zubi da tsari ne
irin na kasuwancin kan intanet na damfara da suka gudu da kuɗaɗen Hausawa a
baya (Misali, Dubai Gold Souk da Insme). Za a iya lura da cewa, duk nau’o’in
kasuwancin kan intanet na damfara suna ƙoƙarin yin amfani da “yarda” wajen yaudarar
mutane. Tsarin gayyata shi ne baban makamin gina yarda da suka yi amfani da
shi.
An
lura da cewa, kafafen intanet ɗinsu ba sa ɗauke da bayanan da ya kamata
kasuwancin gaskiya ya ɗauka. Kafar 52u (https://www.52u.today) kallonta kaɗai zai saka shakku a zuciyar wanda ya san
kasuwannin duniyar intanet. Kafar ba ta tsaru ba, ta yadda har hoton shafin
farko (homepage background image) ya ɓoye ƙunshiyar kafar (menu bar).
Hoto
Na 6.7: Hoton
shafin farko na kafar 52u ya ɓoye ƙunshiya (menu)
Madogara: Kafar 52u (https://www.52u.today)
Wani
abin da ya kamata Hausawa su yi la’akari da shi, shi ne, duka kafafen biyu ba
su da bayanan tuntuɓa. ko Anchor (https://anchorit.live) da ya kawo shafin, lambobin WhatsApp kawai aka sanya
guda biyu. Babu adireshin da za a same su, sannan babu imel ɗin kamfani. A duba
hoton da yake ƙasa:
Hoto
Na 6.8: Shafin
tuntuɓa na kafar Anchor
Madogara: An ɗauko kai tsaye daga
shafin tuntuɓa na Anchor (https://anchorit.live/post/contact-us) (Ranar 2 ga watan
Janairu, 2025)
Duka
kasuwancin biyu an tsara su bisa wani salon da ɗorewarsu zai yi wahala. Dalili
kuwa shi ne, suna da riba mai yawa wadda ba za a iya gamsasshen bayanin
tushensu da ɗorewarsu ba.
6.4.4 Ƙarya Da Farfaganda Da Ɓatanci
Duk
wanda ya dogara da tallace-tallace a kafafen intanet wajen samun kuɗi, to
fafutukarsa za ta karkata kan bin matakan ƙara samun kuɗin shiga.
Waɗanda suka dogara a kan tallace-tallacen sun fi mayar da hankali a kan
abubuwa guda biyu. Na farko shi ne mabiya (misali followers a TikTok ko subscribers
a YouTube, da makamantansu). Na biyu kuwa shi ne yin tsokaci da jinjina ga
abubuwan da mai akawun yake ɗorawa (comment and like waɗanda suke
haɗuwa su bayar da abin da ake kira engagement).
A ƙoƙarin neman mabiya, masu
kafafe da dama sukan ɗora bidiyoyi na labaran ƙarya ko farfaganda ko kuma
ɓatanci. Ko bayan yin ɓatanci a tsakanin taurarin finafinan Hausa da mawaƙa da ‘yan siyasa, abin ya
haɗa har da malaman addini. A taƙaice, akwai ‘yan soshiyal midiya da suka shahara
wajen amfani da miyagun halaye da ɗabi’u domin samun ƙarin mabiya. Misalan
munanan ɗabi’un sun haɗa da:
a. Ɓatanci
b. Cin dunduniya
c. Gulma
d. Ƙazafi
e. Tsegumi
Dangane
da ire-iren waɗannan ne Ɗan’iro Katsina ya yi tsokaci da cewa:
9. Ga
‘yan siyasa ita midiya ku duba,
Nan
ne wurin jawo tsokana da zamba,
Nan
ne wurin ce ma gwaninka bai iya ba,
Nan
ne wurin nuna abin da bai yi kyau ba,
Nan
ne wurin haddasa gardama da gaba,
Dandali ne ake ba na fa’ida ba.
10.
Batu na alkairi ba a son azawa,
Batu
na sharri shi ne abin gwadawa,
‘Yan
mintuka ka gani ya yi zagayawa,
Duk
duniya kowa za ya yo ganowa,
Sirrin
waninka a nan ka yi bayyanawa,
Babu da-na-sani tun da bai gama
ba.
(Ɗan’iro Katsina: Waƙar Soshiyal Midiya Dandalin
Matasa)
A
nan Ɗan’iro
Katsina ya nuna yadda kafafen sada zumunta suka zama wurin yaɗa farfaganda da
sharri da gulma da ɓatanci. Sau da dama ana yin hakan ne domin samun mabiya a
zauruka da shafukan sada zumunta.
6.4.5
Gurɓata Kyawawan Al’adu
Daga
cikin hanyoyin samun kuɗi da ake da su a kan intanet akwai waɗanda suka shafi
ɗora bidiyoyi da sautuka da rubuce-rubuce. Idan aka ɗauki bidiyoyi a matsayin
misali, suna iya kasancewa waƙoƙi ko barkwanci ko koyar da wani nau’in al’ada (misali
abinci) da makamantansu. Akan samu gurɓatar al’adun Hausawa yayin da Hausawa
suka yi riƙo
da baƙin
al’adu a kafafen intanet ko kuma suka gina ƙunshiyar shafukansu a kan
munanan al’adu (misali batsa ko ɓatanci da makamantansu). An kawo hakan a waƙar Soshiyal Midiya inda
ake cewa:
3. A yaɗa alkairi kar a yaɗa zamba,
A
nan ake mai da kaɗan ta zamma babba,
A
nan ake haddasa ƙi a rai da gaba,
A
nan ake tarbiyyar da ban faɗi ba,
A
nan ake wargaza tarbiyyar su baba,
Duk a nan midiya in ba kus sani
ba.
5. Waɗansu
ko lamarin ba ni son tunawa,
Irin
abin da idanu suke ganewa,
Waɗansu
hoto na tsiraici za su sawa,
A
midiya nan ne dandalin gwadawa,
Kowa
irin mai halinsa zai kulawa,
Wa ya ce watta rana ba sa haɗe
ba?
(Ɗan’iro Katsina: Waƙar Soshiyal Midiya Dandalin
Matasa)
Hausawa
sukan ɗauki al’adun wasu al’ummu musamman Turawa da Indiyawa da Larabawa.
Mafiya yawan waɗannan al’adu sun ci karo da na Hausawa. Gurɓatattun al’adu da
ake ɗauka a intanet sun fi shafar halayya da tufafi. Tasirin intanet a kan
al’adun Hausawa ya ja hankalin manazarta da marubuta da dama. Daga cikin
rubuce-rubucen da suka fito da bayanai game da wannan batu akwai Magaji (2018)
da Almajir (2009) da Shehu & Aliyu (2019) da Shehu & Rambo (2019) da
Sani (2022).
Ɗora ire-iren waɗannan munanan al’adu yana da illa ga
Hausa da Hausawa ta fuskoki guda biyu. Da farko yana janyo taɓarɓarewar
tarbiyya a tsakanin al’ummar Hausawa. A yau mata Hausawa masu yawa sun bi sahun
ɗora bidiyoyi a TikTok da sauran kafafe ɗauke da maguzantattun ƙunshiya. Illa ta biyu kuwa
ita ce mummunan wakilcin al’adun Hausawa a idon duniya. Abubuwan da suka
bayyana a ire-iren bidiyoyin ga al’ummar duniya, su za su riƙe a matsayin al’adun
Hausawa na haƙiƙa.
A
ɓangare ɗaya kuwa, ayyukan kan intanet irin su fassara da gyaran rubutu sun ba
da dama ga waɗanda ba Hausawa ba su wakilci Hausawa. Mutane masu yawa sun yi
rajista a matsayin masu fassarar Hausa a kafafen baje kolin fasaha irin su Proz
da Translation Directory. Sau da dama akan ci karo da ayyukan fassara da
aka gudanar waɗanda kai tsaye za a fahimci cewa ba Hausawa na haƙiƙa ba ne suka yi su. Hakan
yakan kai ga samar da gurɓatattun bayanai game da harshe da al’ada da adabin
Hausa.
[1] Domin ƙarin bayani, a duba Kraff
(2021).
[2] Wannan ya danganta daga
mutum zuwa mutum. A bisa tsarin halittar ɗan’adam, wasu sun fi wasu jure wa
damuwa da zulumi.
[3] Domin ƙarin bayani, a duba
Sergeenkov (2024).
[4] An samu waɗannan bayanai
daga tattaunawa da aka yi da Hausawa da suka ci wannan kasuwa. A. Sani
(keɓantacciyar tattaunawa, 11 ga watan Maris, 2023) ya yi cikakken bayanin
yadda harƙallolin
suke gudana.
[5] Farko ya fito ne da suna
“Gleam.” Daga baya ne suka mayar da sunansa “Agua Protocol.”
[6] Suna da ofishi a
Constitution Road, 2nd Floor, KC Holding Building, Opposite Shema Filling
Station, Kaduna.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.