Ticker

6/recent/ticker-posts

Matakan Magance Matsalolin Neman Kudi Da Tattali a Kan Intanet

An ciro daga littafin:

BIƊA DA TANADI A DUNIYAR INTANET
(Sana’o’i, Kasuwanci, Ƙwadago)

Na

Abu-Ubaida SANI
Abdulrahman ALIYU

Bida Da Tanadi a Duniyar Intanet (Sana’o’i, Kasuwanci, Kwadago)
Manazartar Littafi: Sani, A-U. & Aliyu, A. (2026). Biɗa Da Tanadi a Duniyar Intanet (Sana'o'i, Kasuwanci, Ƙwadago). Amsoshi Academic Publishers. ISBN: 978-978-62480-1-1. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.21361768

Tuntuɓa Domin Samun Littafi: 
Dr. Abu-Ubaida Sani: Imel - abuubaidasani5@gmail.com | WhatsApp - 08133529736
Dr. Abdulrahman Aliyu: WhatsApp - 08036954354

6.5 Matakan Magance Matsalolin Biɗa Da Tanadin Hausawa a Duniyar Intanet

Ƙalubale da illolin biɗa da tanadi na Hausawa a duniyar intanet ba su samu gatan masana da manazarta Hausa ba. Har ya zuwa yau (2024), babu wadatattun binciken ilimi da aka gudanar game da su. Wannan bincike ya fahimce cewa, lallai ƙalubale da illolin sun kasance kurar gardi. Magance su ko shawo kansu ya fi ƙarfin aikin mutum ɗaya. Akwai rawa da ɓangarorin al’umma ya kamata su taka tun daga kan ɗaiɗaikun mutane da ƙungiyoyi, har zuwa makarantu da kuma gwamnati kanta. A ƙasa an tattauna wasu matakan da za su iya taimakawa wajen magance ƙalubale da illolin da suka dabaibaiye da harkokin biɗa da tanadi na Hausawa a duniyar intanet.

6.5.1 Gurbin Ɗaiɗaikun Mutane

Hausawa suna da rawar da za su iya takawa a matakin ɗaiɗaikun mutane domin kauce wa wasu daga cikin illoli da ƙalubalen da suke tattare da biɗa da tanadi a duniyar intanet. Daga ciki akwai waɗanda tuni sun kasance jiki. Sun haɗa da matsalar wutar lantarki wadda ake bin yanyoyi irin su neman sola domin cajin kwamfuta da sauran na’urori, ko kuma fawa bank domin cajin waya. Wata hanya kuma ita ce ƙulla alaƙa da kafe (cafe) mafi kusa.

Matsalar sabis ma abu ne da ɗaiɗaikun mutane ba su da wani babban yunƙuri da za su iya yi game da shi. Duk da haka, dabarun rage matsalar sun haɗa da tanadin layukan waya daga kamfanoni sama da ɗaya, misali Airtel da MTN da Etisalat da Glo. Gida biyu maganin gobara, yayin da laila ta ƙiya sai a koma basha.

Ɓangarorin da ƙoƙarin ɗaiɗaikun mutane zai iya samar musu da sauyi sun haɗa da:

A – Koyon Zamanantattun Darrusa

A yau lamarin koyo da koyarwa ya kasance al’amari mai sauƙi. Dangane da al’amura da dama, mutum ba ya buƙatar shiga aji domin a koyar da shi. Tuni kafafen intanet da manhajoji da dama suka kasance makarantu waɗanda a koyaushe Hausawa za su iya ziyarta domin kwankwaɗan ilimi. Hasali ma, da dama daga cikin abubuwan da mutum zai koya dangane da intanet da na’ura, bincike da kuma yau da gobe ne za su koya masa, ba wani malami a aji ba.

“Idan za a sha giya a sha ta dubu!” Duk wanda ya sa biɗa da tanadin duniyar intanet a gaba, yana da matuƙar muhimmanci ya yi yunƙuri a karan kansa wajen samun cikakken ilimi dangane da harƙallar da yake yi. Hausawa za su iya samun cikakkun bayanan da suke nema ta hanyar:

i.Bibiyar tashoshi da shafukan da ake koyar da nau’in abin da yake son ƙwarewa a kai (YouTube da TikTok da Facebook da sauransu)

ii.Yin rajista da makarantu masu zaman kansu da suke koyar da nau’in ilimin da yake son koya

iii.Bincike a kafafen intanet da suke ɗora ire-iren bayanan

iv.Tattaunawa da ingantattun saƙago na ƙirƙirarriyar basira (AI bots)

B – Kiyaye Lafiyar Jiki Da Ta Muhalli

Ya zama dole Hausawa su kiyaye lafiyar jikinsu da ta muhallinsu domin ɗorewar rayuwa mai inganci. Hakan zai faru ne ta hanyar kauce wa duk wasu abubuwan da sukan iya illata lafiya. Sun haɗa da:

i.A guje wa ɗora kwamfuta a kan cinya yayin da ake aiki da ita, ko wasu na’urorin da suke fitar da tiririn radiyeshin.

ii.A yi ƙoƙarin kauce wa ci-da-zuci da hana rai hutu da zummar kammala aiki. Hakan zai taimaka wajen kauce wa kamuwa da ciwon kai na wucin gadi ko matsananciyar gajiya mai illata jiki.

iii.Kauce wa harƙalloli masu zubi irin na caca waɗanda za su kai ga cutuwar ƙwaƙwalwa.

iv.Amfani da dabarar nan ta 20-20-20 domin kauce wa ciwon ido na wucin gadi ko kallo bishi-bishi.[1]

Waɗansu ƙarin hoɓɓasawa da ɗaiɗaikun mutane za su iya yi su ne:

C - Dole ne Hausawa masu harƙalla a kan intanet su naƙalci matakan kare kai daga damfara kamar yadda aka tattauna a baya.

D - Dole ne Hausawa su yi ƙoƙarin sabawa da karɓar sauyi cikin hikima da ƙwarewa. Daga nan kuma sai su bi hanyoyi da matakan da za su iya sauyawa ko jan hankalin kwastomominsu domin cigabansu da na kasuwancinsu ko harƙallolinsu.

E - Yayin da mutum ya ƙware sosai a fannin da ya ɗauka, zai iya neman tallafi ko haɗin guiwa daga kamfanoni da cibiyoyi daga wurare daban-daban.

F - Kasancewar Ingilishi shi ne babban harshen kasuwanci a duniyar yau, yana da kyau Hausawa masu biɗa da tanadi a duniyar intanet su naƙalci harshen. Aƙalla ya kasance sun samu ilimin da zai ba su damar fahimtar dokoki da ƙa’idoji da kuma bayanan kasuwanci da harƙalloli da ake rubutawa cikin harshen Ingilishi.

G - Yana da kyau Hausawa su nemi ƙwarewa a fannin da za a daɗe kafin tasirin zamani ya kashe masa kasuwa. Waɗannan su ne ire-iren harƙallolin da a nan kusa na’urori da ƙirƙirarrun basira ba za su iya maye gurbin mutanen da suke da ƙwarewa a fannonin ba.

H – Yana da kyau Hausawa su nuna kishin bunƙasa al’ummarsu da kyawawan al’adunsu. Waɗanda harƙallolinsu suka shafi ɗora ƙunshiya a kan intanet (online contents) suna da rawar da za su iya takawa ta hanyar ƙara bayyana wa duniya haƙiƙanin al’adu da harshe da adabin Hausawa.

6.5.2 Gurbin Iyaye

Iyaye a ƙasar Hausa suna da rawar da za su taka a ƙoƙarin haɗa ƙarfi da ƙarfe domin Hausa da Hausawa su hau tudun-na-tsira dangane da gwagwarmayar biɗa da tanadi a duniyar intanet. Wannan ya shafi iyayen da ‘ya’yansu suke kan turbar biɗa da tanadi a duniyar intanet, har ma da waɗanda ba su ba. Iyaye za su iya taka rawa ta fuskoki kamar haka:

A – Tarbiyya

Tarbiyya aba ce mai muhimmanci a al’adar Hausawa da addininsu. Takan gyara tsarin rayuwar mutum domin ya zama mai nitsuwa da sanin ya-kamata. Iyaye suna iya mayar da hankali wajen hana ‘ya’yansu hulɗa da intanet da na’urori ta fuskokin da hulɗar za ta iya gurɓata musu tarbiyya. Bayan jan hankali da addu’a ga yaran nasu, suna iya sanya ido sannan su riƙa bibiyar yanaye-yanayen hulɗar ‘ya’yansu da intanet da na’urori.

Yin irin wannan huɓɓasa zai taimaka wajen ƙoƙarin kare tarbiyyar yaran nasu. A ɓangare ɗaya kuwa, zai kasance ne suna ƙoƙarin dakatar da waɗanda suka riga suka rungumi gurɓata tarbiyya a matsayin hanyar tara mabiya a kafofin intanet. Dalili kuwa shi ne, raguwar masu bibiyar ire-iren shafukan, shi ne zai rage ƙimar shafukan tare da kassara manufofinsu.

B - Tallafi Da Ƙarfafa Guiwa

Yara suna buƙatar tallafi da ƙarfafa guiwa daga iyayensu, musamman a kan al’amuran da suka shafi gobensu. Rawar da za su iya takawa a nan ta haɗa da ƙarfafa wa yaran guiwa da kalaman baki da kuma tallafa musu da kuɗaɗen da suke buƙata domin fara gudanar da nau’in kasuwancin da suke da ƙudirin gudanarwa. Yana da kyau iyaye Hausawa su san da wannan, sannan su yi bakin ƙoƙarinsu don ganin ba a bar ‘ya’yan Hausawa a baya ba.

C – Faɗakarwa

Hausawa suna cewa: “Abin da babba ya hango, yaro ko ya hau Dala ba zai iya hangowa ba.” Sau da dama yara sukan rungumi wani al’amari da tunanin cewa hanya ce mai ɓullewa. Wasu sukan yi hakan ba da wani ilimi ba, sai kawai don sun ga wasu sun samu nasara a sanadiyyar nau’in kasuwancin. Sun manta da cewa idan wani ya yi rawa ya samu kuɗi, wani in ya yi duka yake sha. Yayin da tafiya ta yi tafiya, a nan ne take bayyana musu cewa kallon kitse suke yi wa rogo.

Tun farko iyaye suna iya bibiyar muradun ‘ya’yansu tare da daidaita musu tunaninsu da faɗakar da su yayin da suka yi wani ragon tunani. Haka kuma, suna iya faɗakar da su game da taka-tsantsan da duniya da kauce wa tarkon ‘yan damfara da kuma riƙo da gaskiya da amana.

6.5.3 Gurbin Ƙungiyoyi

Ƙungiyoyin da suke da alaƙa da harshen Hausa suna da rawar da za su iya takawa domin bunƙasawa da inganta harkokin biɗa da tanadinsu a duniyar intanet. Yana da kyau dukkannin ƙungiyoyin Hausa su yi la’akari da zamananci da shirin game duniya a cikin manufofinsu. Bugu da ƙari, ya kamata su gudanar da ƙungiyoyin ta la’akari da zamani da ƙoƙarin kawo nau’o’in cigaba da za su taimaki ‘yan ƙungiyar da al’ummar da kuma harshen kansa. Ya kamata ƙoƙarinsu ya mayar da hankali kan cikakken amfani da lokaci domin yin nasara dangane da muradu na gajere da dogon zango.

Kai tsaye suna iya taka rawa ta ɓangarorin da suka haɗa da:

i.Dangane da matsalar wutar lantarki, suna iya magana da murya ɗaya zuwa ga hukumomi da gwamnatoci domin ingantawa. Haka kuma, suna iya ƙoƙarin samar da wata mafita ta wucin gadi kamar sola a ofishi ko janareta.

ii.Ƙungiya tana iya tara kuɗi ko neman tallafi domin samar wa mambobinta sabis mai ƙarfi. Babban misali a nan shi ne, ƙungiya tana iya yin rajista domin samun sabis ɗin intanet mai ƙarfi kamar na Starlink.[2]

iii.Ƙungiya tana iya yin tsari mai kyau domin koyar da zamanantattun darussa ga ‘ya’yanta, har ma da wasu daga cikin al’umma na kusa da na nesa. Za ta iya yin hakan ta hanyar haɗa kai da masana daga cikinta ko gayyato wasu daga waje. Bugu da ƙari, za su iya taimakon yara da matasa ‘yan makaranta ta hanyar kai musu ziyarar wayar da kai da shirya musu azuzuwa na musamman a lokacin hutu.

iv.Ƙungiyoyi daban-daban suna iya haɗa kai wajen tura kokensu ga gwamnati dangane da wasu takunkumai da suka fahimci ba za su haifar da ɗa mai ido ba.

v.Ƙungiyoyi suna iya faɗakar da mambobinsu da kuma al’umma dangane da abubuwa da dama masu alaƙa da biɗa da tanadi a duniyar intanet. Daga cikinsu akwai matakan kare muhalli da lafiyar jiki da na kauce wa faɗawa homar ‘yan damfara. Za su iya yin hakan ta hanyar tarurruka da rubuce-rubuce a kafafen sada zumunta da kafafen intanet da kuma shirye-shirye a kafafen watsa labarai.

vi.Bunƙasa al’ada da adabi da harshen Hausa yana daga cikin manufofin kusan dukkannin ƙungiyoyin Hausa. Yana da kyau a yau su bi zamanantattun hanyoyi domin gudanar da wannan aikin. Sun haɗa da buɗe kafafen intanet domin samar da kyakkyawa kuma tsaftatatten wakilci ga Hausa da Hausawa. Wani abu kuma shi ne ƙara huɓɓasa wajen faɗakar da yara da matasa domin rungumar sana’o’i da rage zaman banza. Raguwar zaman banza zai taimaka wajen rage ayyukan assha da suke da alaƙa da duniyar intanet.

6.5.4 Gurbin Makarantu Da Cibiyoyin Bincike

Sashe-sashen nazarin Hausa a jami’o’i da manyan makarantu da kuma cibiyoyin bincike su ne suke kan gaba ta fuskar faɗa-a-ji game da abubuwan da suka shafi nazarin Hausa. Suna iya taka rawa a dukkannin ɓangarorin da aka lissafo a ƙarƙashin 6.5.3 da yake sama. Ko bayan waɗancan, suna da muhimman ɓangarori da za su iya bayar da gudummawa. Sun haɗa da:

A – Samar Da Babbar Ƙungiya

Har ya zuwa yau, duk wani yunƙuri na samar da babbar ƙungiya ko wata cibiya da ta haɗa dukkannin sashe-sashe da cibiyoyin nazarin Hausa yana tattare da ƙalubale. A shekarar 2024 an sabunta wannan yunƙuri a lokacin wani taron ƙara wa juna sani na ƙasa da ƙasa da aka gudanar a Jami’ar Ahmadu Bello da take Zariya. An yi ƙoƙarin zaɓen sababbin shuwagabanni da za su jagoranci Ƙungiyar Hausa.[3] A duba hoto da yake ƙasa:

Hoto Na 6.9: Sababbin shuwagabannin Ƙungiyar Hausa da aka zaɓa ranar 30/10/2024

Sababbin shuwagabannin Ƙungiyar Hausa da aka zaɓa rana

Madogara: Takardar rahoton taron Ƙasa Da Ƙasa Na Ƙara Wa Juna Sani Game Da Harsunan Afirka, wanda aka gudanar ranar 29 – 30 ga watan Oktoba ta shekarar 2024 a Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya[4]

Akwai buƙatar ƙarfafa wannan yunƙuri domin kafa ƙungiyar da za ta zama uwa ga dukkannin masana da manazarta Hausa. Ƙarfin faɗa-a-jin da za ta samu zai taimaka ta fuskoki da dama da suka haɗa da:

i.Za ta iya magana a gwamnati dangane da wasu hukunce-hukunce ko ƙa’idojin da suke da illa ga Hausa da Hausawa.[5] Bugu da ƙari, suna iya tura buƙatun samun damarmakin da za su iya bunƙasa Hausa, musamman ta fannonin da suka shafi biɗa da tanadi a duniyar intanet.

ii.Za ta samar da hanya mafi sauƙi na yanke hukunci dangane da wasu abubuwan da suke da ruɗani ko janyo saɓani a nazarin Hausawa. Sun haɗa da fassarar kalmomin fannu da abin da ya shafi hanyoyin gudanar da bincike da ƙa’idojin rubutu da sauransu. Ta haka ne kuma za a samu hanya mafi sauƙi na yanke hukunci game da matakan da za su taimaka wajen inganta lamuran da suka shafi biɗa da tanadin Hausawa a duniyar intanet.

B – Zamanantar Da Harkokin Koyo Da Koyarwa

Ko da ma dai, sabon tsarin koyarwar da aka kawo na Core Curriculum and Minimum Academic Standards (CCMAS) ya mayar da hankali sosai a kan zamanantar da harkokin koyo da koyarwa.[6] Akwai buƙatar sashe-sashen nazarin Hausa da kuma cibiyoyin bincike su yi amfani da wannan dama domin sanya zamanantattun kwasakwasai waɗanda za su taimaki ɗalibai a gwagwarmayar biɗa da tanadi na duniyar intanet. Wani abin da zai ƙara taimakawa shi ne rage ba da ƙarfi a kan haddace batutuwa. A maimakon haka, a himmatu kan gina tunanin ɗalibai da koya musu dabarun amfani da fikira da basira wajen fara ayyukan dogaro da kai.[7]

6.5.5 Gurbin Gwamnati

Gwamnati ita ce uwa uba a duk wani cigaba ko sauyi da za a iya samu. Ita take fitar da dokoki tare da zartar da su dangane da fannonin rayuwa daban-daban, ciki kuwa har da lamuran da suka shafi ilimi. Da goyon bayanta ne kawai za a iya samun sauyi mai amfani da zai kai ga bunƙasar hanyoyin dogaro da kai na zamani. Gwamnati tana da muhimman rawa da za ta iya takawa da suka haɗa da:

i.Gwamnati za ta iya mayar da hankali kan inganta wutar lantarki tare da fito da tsare-tsare da za su ba wa ƙananan sana’o’i damar samun intanet mai inganci. Wannan zai taimaka musamman a masu harkokin da suka shafi biɗa da tanadi a duniyar intanet. Haka kuma, za ta iya ƙara mayar da hankali a kan tallafa wa masu ƙananan sana’o’i da suke da alaƙa da biɗa da tanadi a duniyar intanet.

ii.Gwamnati za ta iya ci gaba da haɗa kai da manazarta da makarantu domin ƙara zamanantar da kwasa-kwasai. Hakan zai tabbatar da ana yaye ɗalibai masu wayewar kai game da hanyoyin dogaro da kai a zamanance. Haka kuma, tana iya fitar da shirye-shirye a gidajen rediyo da kafafen talabajinin da tarurrukan ƙara wa juna sani masu manufar cusa wa mutane ɗabi’ar son karɓar sauyi. A ɓangare ɗaya kuwa, wannan yunƙuri zai iya ɗaukar manufar faɗakarwa da koyar da hanyoyi da matakan kauce wa matsalolin da suke tattare da biɗa a duniyar intanet. Matsalolin sun haɗa da waɗanda suke illata lafiya da muhalli da fuskantar damfara da kuma abubuwan da suka shafi gurɓacewar al’adun ɗa’a da mutunci.

iii.Wani babban gudummawa da gwamnati za ta iya bayarwa shi ne tabbatar da janye duk waɗansu takunkumai marasa ƙwaƙƙwaran tushe waɗanda suke daƙusar da harkokin biɗa da tanadi a duniyar intanet.

6.6 Naɗewa

Duk da ɗimbin alfanun da suke tattare da harkokin biɗa da tanadi a duniyar intanet, lallai suna dabaibaye da wasu illoli da ƙalubale waɗanda suka keɓanta ga Hausawa da waɗanda suke gama-gari. Illolin kuwa sukan shafi lafiyar jiki da ƙwaƙwalwa da muhalli, har ma da zamantakewa. Waɗannan matsaloli ba za a iya shawo kansu ba har sai an samu sa hannun ɓangarorin al’umma daban-daban. Sun haɗa da ɗaiɗaikun mutane da iyaye da ƙungiyoyin ɗalibai da manazarta Hausa da kuma makarantu da cibiyoyin bincike, har ma da gwamnati kanta. Gyaruwar lamura a wannan fannin abu ne da zai yi matuƙar taimakawa. Ko bayan kare kyawawan al’adu, za a samu ayyukan yi da raguwar zaman banza. Hakan kuwa zai samar da bunƙasar tattalin arziki da raguwar ƙanana da manyan laifuka da kuma cigaban ƙasa baki ɗaya.


[1] Wannan hanya ce da masana kiwon lafiya suka samar domin kare ido yayin da ake aikin da ya shafi kallon sikirin. Yadda ake yi shi ne, a duk bayan mintuna ashirin (20) da aka yi ana kallon sikirin, to a kalli wani abu da yake da tazarar ƙafa ashirin (20) daga wurin da ake. Za a kalle shi ne na kimanin tsawon sakanni ashirin (20). Wannan yana taimakawa wajen wartsakewar ido da hana shi tara gajiya. A duba Marcin (2017).

[2] Starlink sabis ne na intanet wanda yake tashe yau a duniya. Mallakin kamfanin SpaceX (Space Exploration Technologies Corp.) ne wanda yake ƙarƙashin jagorancin Elon Musk. Ya zuwa shekarar 2024, SpaceX sun tura satilayit sama da dubu huɗu (4,000) zuwa sararin samaniya. Suna kuma ƙoƙarin tura ƙarin wasu domin inganta ƙarfin sabis ɗin intanet da suke samarwa a faɗin duniya. Domin ƙarin bayani ana iya duba eoPortal (2024) da Starlink (2024).

[3] M.S. Wali (keɓantacciyar tattaunawa, 24 ga watan Disamba 2024)

[4] A duba Department of African Languages and Cultures, Ahmadu Bello University (2024)

[5] Misalansu sun haɗa da mayar da darasin Hausa na zaɓi a makarantun sakandare. Wani misalin shi ne tilasta wa masu son karantar Hausa a jami’o’i zana Adabin Ingilishi (English Literature) a jarabawar JAMB (Joint Admissions and Matriculation Board).

[6] A duba NUC (2022).

[7] Ƙasashen da suka ci gaba sun fi mayar da hankali a kan bunƙasa basirar ƙirƙira sama da haddace batutuwa da bayanai. Hasali ma, akwai masana da suke ƙalubalantar tsarin jarabawa a makarantu. Suna da fahimtar cewa, jarabawa ba ta ƙara komai face taƙaita tunanin ɗalibai zuwa ga ƙoƙarin cin jarabawa a maimakon fahimtar kwas da amfani da hikimomin da suke cikinsa domin inganta rayuwa. Domin ƙarin bayani, ana iya duba Pantami (2022) da Stellar (2022).

Post a Comment

0 Comments