Ticker

6/recent/ticker-posts

Yadda Ake Yin Wankan Gawa

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum. A wuni lafiya. Ya ƙoƙari? Allah ya saka da alheri, Allah ya biya ku malam. Dan Allah ina so in san yadda ake wankan gawa. Na gode.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Walaikumus salam Warahmatalahi wabarkatahu;

Al-Imam Hakim ya rawaito hadisi wanda Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) yake cewa, ‘’Duk wanda ya wanke mamaci, kuma ya rufa masa asiri, Allah zai gafarta masa sau arba’in.’’

A wani hadisin kuma Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) Ya ce, "Duk wanda ya wanke mamaci kuma ya rufa masa asiri, toh Allah zai tufatar da shi daga cikin tufafin gidan Aljannah kwarra, (wato launin tufafin).

SHARRUƊAN WANKAN GAWA: Daga cikin sharruɗan wankan gawa sune;

1. Ana bukatar waɗanda za su wanke mamaci su zamanto makusantan sa ne misali Iyaye, kanne ko yaya yie 'ya'yansa da sauran su.

2. Ana bukatar maza su jibinci wanke maza, su ma mata su jibinci wanke mata (sai dai Miji zai iya wanke Matar sa haka ma Mace za ta iya wanke Mijin ta).

3. Ba sharraɗi ba ne lallai sai an yi amfani da ruwan zafi.

YADDA AKE YIN WANKAN GAWA:

Ana yin wankan gawa mara-mara ne misali; Sau Uku (3), ko Biyar (5), ko Bakwai (7), ko Tara (9). Hakan ya tabbata daga Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) a cikin hadisin Ummu Adiya (R.A). Waɗanda za su yi wa mamaci wanka su ne za su yi la’akari su da wanka nawa ya dace su yi masa.

Da farko dai kafin a fara wankan da akwai abubuwa guda Uku (3) da za a fara yi wa mamacin. Sune kamar haka;

1. Za a cire masa suturar da take jikin sa, amma za a sami dan kyalle a rufe masa al’aurar sa ba za a bar al'auran sa a buɗe ba, haka al'auran Mace ma.

2. Sai yi masa tsarki, na ɓangaren mafita guda biyu (Bawali da Gayadi). wato dubura da kuma Farji, ko kuma Azzakari.

3. Idan mace ce, za a tsefe kitson da yake kanta, a wanke kan, sannan ayi Lallabi uku a kanta (wato Kalba guda Uku). Sai a kwantar da Kalbar ta bayan kanta. Idan namiji mai kitso ne sai a warware kitson gaba ɗaya.

YADDA AKE WANKA SAU UKU (3):

Idan masu yi wa mamaci wanka sun zaɓi su yi masa wanka sau uku, toh bayan sun gama abubuwan da suke sama sai su fara wankan.

Da farko dai za su tanadi ruwa kashi Uku (3) ne, kowanne ruwa za a yi wanka ɗaya da shi, (RUWAN FARKO) Wannan wankan za a yi wa mamaci ne wanka irin wankan Janaba.

Da farko za a fara yi wa mamaci al-wala irin yadda kike yin al-wala idan za ki yi Sallah, sai dai wajen, kuskurar baki da shakar hanci za a shafa masa ruwa ne kawai a baƙin da hancin bawai za a buɗe baƙin sa a ce za a yi masa kuskurar Baki da Shaka ruwan ba. Toh bayan an yi masa Al-wala an gama, sai kuma a zuba ruwa a kansa a wanke masa kai har sau uku, sannan kuma a wanke tsagin jikin sa na dama, sannan na hagu.

(RUWA NA BIYU) Bayan an yi masa wanka na sama wato na Janaba, sai kuma a sami Sabulu ko Magarya ko Kanwa, a wanke mamacin da shi. Wato za a sami Soso da Sabulu a cuɗa jikin sa sosai (Kamar dai yadda ake wanka irin na Soso da Sabulu, sai dai za a iya amfani da Magarya ko Kanwa a maimakon Sabulun) Sa'annan ba za a dirje jikin sa da Karfi kamar yadda ke kike yin wankan ki a matsayin ki na wadda take raye ba, za a yi sa soso da sabulu ne ba da karfi ba, toh bayan an gama cuɗa jikin shi, sai kuma a dauraye kumfar da wannan ruwan.

(RUWA NA UKU) Bayan an yi masa wanka na sama, wato na Soso da Sabulu, toh sai kuma a sami ruwa na karshe wato Ruwa na Uku sai a zuba Turare mai kamshi (Sosai) a cikin wannan ruwan, sannan sai a wanke mamaci da shi, an fi son a yi amfani da Turaren Kafur, toh amma idan ba a same shi ba, za a iya yin amfani da duk wani Turare mai kamshi sosai. Bayan an gama wanka da wannan ruwan Turaren, sai a tsane jikin mamacin a sa masa Likkafanin sa.

 😭. Inna lillahi Wa inna Ilaihi Rajee'un, kab din mu fa haka za a yi mana, ki dauka a yanzu kene ake yi wa wannan wankan, wanne aya yiuka kika yi wadda a yanzu da ake miki wanka idan kin je ƙabarin ki ace kin huta?

YADDA AKE YIN WANKA BIYAR (5), KO BAKWAI (7), KO TARA (9):

Idan masu yi wa mamaci wanka sun zaɓi da su yi masa wanka biyar (5), ko bakwai (7), ko tara (9). Toh wanka na biyu (2) wato na soso da sabulu shi za su yi ta maimaitawa ne. Amma dole ne na Janaba shi ne a farko, sannan na Turare shi ne a karshe. MISALIN YADDA ZA AYI WANKAN SAU BIYAR (5).

1. Na farko shi ne na Janaba.

2. Na biyu shi ne na soso da sabulu.

3. Na uku shi ne na soso da sabulu.

4. Na huɗu shi ne na Soso da Sabulu.

5. Na Biyar shi ne na Turare.

Dalilin da zai sa ayi wanka 5 ko 7 ko 9, sabida wani gawar ana iya samun cewa jikin sa akwai dotti sosai ko ya Ɓata jikin sa da ba haya ko jini, kin san wani saban zafin fitar Rai da yake samun su, abubuwa dayawa suke fitarwa daga jikin su, wata kila kuma ya jima ba a yi masa wanka ba a dalilin rashin lafiyar sa bai son taɓa ruwa, kin ga ke nan wanka ukku watakila ba zai sa ya fita tas yadda ake so ba, toh shiyasa Shari'ar Musulunci ya ce ana iya yin ukku, idan ya yi shike nan, idan bai yi ba sai ya zama 5, ko 7 ko 9, fatan an fahimta??

Inna lillahi Wa inna Ilaihi Rajee'un, kab din mu fa haka za a yi mana, ki dauka a yanzu kene ake yi wa wannan wankan, wanne aya yiuka kika yi wadda a yanzu da ake miki wanka idan kin je ƙabarin ki ace kin huta?

YA UBANGIJI KASA MU CIKA DA IMANI AMIN.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam  

Post a Comment

0 Comments