𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum Malam khamis. Mene ne ya haɗa Sallar Azahar da Juma’a? Shin Sallar Juma’a daidai take da Sallar Azahar. Ko kuwa ko wanne matsayinsa dabam? Sannan me ya sa ba a rama sallar juma'a sai ace wai ayi Azahar? shin mutanen da suka rasa Sallar Juma’a za su iya yin jam’in ta a Masallacin ko a’a? Shin dole ne sai antaso masallacin Juma'a sannan mata su yi sallar azahar?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikumussalam
warahmatullahi wabarakatuh.
Babban banbanci
tsakanin Sallar Juma'a da Sallar Azahar shi ne: Sallar Juma'a ta musamman ce da
ake yi a ranar Juma'a maimakon Azahar, tana da Raka'a biyu (2) tare da gabatar
da Huɗuba guda biyu kafin
ita, Ana yin ta ne sau ɗaya a mako a lokacin
Azahar ranar Juma'a kuma wajibi ce a babban masallaci cikin jam'i. Amma Sallar
Azahar tana da Raka'a huɗu (4), ba ta da huɗuba, kuma ana yin ta
ne a kowace rana ta mako (ciki har da ranar Juma'a ga matafiya, mata, ko marasa
lafiya da ba su je masallacin Juma'a ba).
Duk mutumin da ya
rasa Sallar Juma’a domin uzuri da shari’a ta yadda da shi, to zai sallace
Azzahar a mamadin ta kuma a lokacinta ranar Juma’a. Bai halatta ya jinkirta ta
ba har lokacin Azzahar ya fita, balle kuma ya kaita ranar assabar. Wanda kuma bai
yi Sallar Juma’a ba, ba tare da uzurin da shari’a ta yadda da shi ba, to ya yi
gaggawan tuba zuwa ga Allah kuma ya Sallaci Azzahar.
Sallar Juma’a tanada
alaka da azzahar, domin azzahar ita ce asalin sallar Juma’a. kuma ana yin Juma’a
ne a mamadin ta, a cikin lokacin ta. Juma’a tanada ka’idoji da sharudda, duk
mutanen da suka rasa juma’a baza su yi ta ba, saidai su yi azzahar a cikin
jam’i, musamman idan sun taru a wuri guda ko a masallaci bayan lokacin Juma'a
ya wuce ko kuma rashin samun damar yin Juma'ar. Sallar Juma’a tana maye gurbin
azzahar ranar juma’a, amma idan aka rasata, to, sai a sallaci azzahar. Ba a
rama Juma'a da irinta saboda ta rasa sharuddanta da babban aikinta na jama'a da
huduba a babban masallaci, don haka sai Azahar ta maye gurbinta.
Abinda ya sa ba a
rama juma’a da sallar juma’a shi ne ita juma’a tanada manufofi da dalilan da
shari’a ta shar’anta ta. Irin taruwan jama’ar gari guri guda, fadakarwa, sannaya
yia da taimako, bugu da kari dunkulewa da yenta a guri daya kuma lokaci daya
wata alamace daga cikin alamomin musulunci.
Juma'a ta na da
sharudda da manufofi na musamman kamar taruwar jama'a da kuma huduba, yayin da
Azahar ke da nata tsarin na raka'a hudu ba tare da huduba ba.
Ba dole ba ne mata su
jira har sai an idar da sallar Juma'a a masallaci sannan su yi sallar Azahar.
Suna iya yin sallar Azahar tun lokacin ta ya shiga, wato da zarar rana ta wuce
tsakiya. Mata ba su la'akari da Juma'a a matsayin sharadin Fara lokacin Azahar
dinsu. Ba a buƙatar su tsaya suna jiran fitowar maza daga masallaci.
Allah shi ne mafi
sani.
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.