Ticker

6/recent/ticker-posts

Shawara Domin Zaman Lafiya a Gidan Aure

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum malam khamis Fatan ka wuni lafiya Allah ya ƙara lafiya da nisan kwana me Albarka. Malam khamis dan Allah ina son a ba ni shawarwari akan yadda zan zauna lafiya cikin farin ciki, biki na saura wata huɗu kuma kullum in na tuna irin matsalolin gidajen aure da muke ji yau da gobe sai nake ta jin tsoron auren gaba ɗaya.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumussalam warahmatullahi wabarakatuh.

Ina taya ki murna da samun wannan babban alheri na kusa shiga gidan aure! Abin farin ciki ne, kuma al'ada ce ga duk wani da zai ɗaurawa kansa wannan babban nauyin ya ji fargaba ko tsoro, musamman idan aka duba yadda labaran matsalolin aure suka cika gari a yau.

Kada ki bari tsoro ya kashe miki gwiwa. Zama lafiya cikin farin-ciki a gidan aure yana yiwuwa idan aka gina shi akan ingantaccen harsashi. Ki dena Tsoron Aure. Domin Shi Aure Wata Ibada Ce Mai Zaman Kanta. Allah ne Da Kansa ya yi Umarni da Yin sa Kamar yadda ya yi Umarni da Yin Sauran Ibadu a Cikin Alƙur'ani da Kuma Hadisan Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam).

Ki Shiga auren da niya yiar yin biyaya yia ga Allah da kuma gina iyali na gari. ki Kasance Mai Biyaya yia Sau da Kafa ga Mijin ki. Ki sani za ku fito daga gidaje daban-daban, don haka dole a sami bambancin ra'ayi. Ki Karɓi mijinki da halayensa na kwarai, kuma ki yi haƙuri da kasawarsa.

Gidan aure gidan yafiya ne. Wanda bai iya yafe laifi ba, ba zai daɗe yana farin ciki a gidan aure ba. Ki Zama Mai Hakuri da Kawar da Kai Akan Abinda Mijinki ya yi Miki na Saɓani. Musamman ma Wanda ya yi Miki cikin rashin sani.

Labarin cikin gidan aurenki na daɗi ko na baƙin-ciki ya tsaya tsakaninki da mijinki kawai. Kar ki riƙa kwatanta aurenki da na kawayenki ko na mutanen kafofin sada zumunta (Social Media). Kowane aure da irin nasa jarrabawar.

Ki Zama Mai Tsafta a Gidan Mijin Ki. Domin Rashin Tsafta Yana Mugun Bayar da Matsala a Rayuwar Aure. Kina Kula da Hamatar ki, Gabanki, Kitso Akan Kari, Wanke Kafarki, bakinki, Ki Zama Mai Sanya Turare na Jiki da na Tufafi da na Ɗaki a Koda yaushe. Idan Zai Yiwu Ki Kula da Wanke Kayan/Tufafin Mijinki da zarar ya Fitar da Su daga Jikin sa ki ɗauka ki Wanke Masa.

Ki Rungumi shagwaba, kalamai masu daɗi, da nuna kulawa ta musamman ga bukatun mijinki. Ki Zama Mai Kokarin Wajen Sarrafa Abincin da Mijinki Zai Ci, ya Zama Mai Daɗi da Tsafta.

Ki Kasance Mai Kiyaye Zantattuka na Barkatai. Musamman zugar Kawaye ko Makota ko Zantattukan Gidan Biki ko Suna. Domin Akasari Duk Wata Fitina daga nan Ake Kullo ta.

Ki kiyayi Wayar Hannun ki. Kinga Wannan Wayar da kike gani, Nan da nan Za ta iya Kashe Miki Aure. Mace Rauni ne da ita. Sai kiga ba tare da Kin Ankare ba, Sai Wani Namijin ya ɗauki Hankalinki ta hanyar waya, Akan Abinda ke kina Ganin ba Komi ba ne, nan Kuma Babbar Matsala Ce ga Matar da take Zaman Aure. Kuma nan da nan Sai kiga kin Sami Matsala Tsakanin ki da Mijin Ki.

Idan Zai Yiwu, ki Sami Wata Sana'ar da zakike Taimakon Kanki da Kanki Kuma ki Taimakawa Mijin ki Akan Abinda yafi Karfinsa. Ki yi murna da duk abin da mijinki ya kawo miki, komai kankantarsa ki yi masa godiya. Wadatar zuciya tana kawo albarka acikin gidan aure.

Idan za ki fita ko nan da Makota ne. Ki tabbatar da Cewar da izinin Mijin ki. Kar ki Baiwa Wani Namiji Damar Shiga Gidan Auren Ki, har Sai da Izinin Mijinki. Sai Wanda Kika Tabbatar da Cewar Ɗan'uwanki ne Wanda babu Aure a Tsakanin Ki da Shi.

Ki Girmama Iyayen Mijinki da Kuma Yan'uwansa. Domin duk Lokacin da Kika Sake kika Sami saɓani da Dangin Mijinki. Kamar da Mijinki Kika Sami Matsala. A koda yaushe za Suke zuga Shi Akanki, har Sai ya ji ya Tsane ki. Kinga Kuwa Idan Miji ya Tsani Mace, Sai dai Kuma Rabuwa.

Idan Mijin Ki ya Tashi Kara Aure. Karki tayar da Hankalinki. Ki yi Addu'ar Idan Alkairi ne, Allah ya tabbatar, Idan Kuma ba Alkairi bace, Allah ya Chanja Muku Mafi Alkairi. Domin Wata Matar ta Gwammace da Mijin ta ya Kawo Mata kishiya, Gwanda ya saketa ta Fita ta bar Mata Gidan, ita Kuma ta koma Gidan su ta Kama Zawarci. Wanda Kuma Wannan Shi Ake Cewa "SAKE RISHE KAMA GANYE".

Babu ke babu Harkar Malaman Tsubbu da Bokaye, ko Wata za ta je Miki Kar ki yadda. Ki Riki Allah, Shi ne Kaɗai Zai Baki Kariya, duk Abinda zai Baki, babu Mai Hanawa, haka Duk Abinda Bai Baki ba, babu Wanda ya Isa ya Baki.

Ki rike Addini sau da Kafa, ki Kula da Addu'o'i da Sallolin dare, Waɗanda Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya karantar da Kula da Su. Za su Taimaka Miki Kuma za su kare ki daga Sharrin duk Wani Shaidani na Kusa da na Nesa.

Ina yi Miki Addu'ar dacewar duniya da Lahira, Ina Yi miki Addu'ar Allah ya sa Kin dakko Miji na Kwarai, Mutumin Kirki Mai Addini. Domin Duk Macen da ta Dakko Namiji Mai Bakin Hali, Akwai Babbar Matsala, Sannan Kuma Wannan ba Karamin Barazana ba ne ga Rayuwar Matar da ta Dakko Irin Wannan Namijin da har ya Kasance a Matsayin Mijinta ba. Sabida haka Matukar dai na Gari ne, In Sha Allahu ke Kan ki za ki ji dadin Zama da Shi, Kuma Za a Taya Ki Murna da Farin-Ciki Akan Kasancewar ki tare da Shi.

Zan Ɗan Takaita a nan. Domin Gaskiya Abubuwan Suna da yawa. Wanda na sani in Sha Allahu Idan Kin Riki Waɗannan Shawarwari da na Baki, za ki Zauna Lafiya acikin gidan aurenki. Allah ya Sanya Albarka. Allah ta'laa yasa mudace. Ameen

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam  

Post a Comment

0 Comments