𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamualaikum warahmatullah inawuni mallam ya jamaah kuma ya aiki mallam dan Allah tambayata ita ce, miji ne ya yi tafiya yabar mata tom sai motarsu ta yi hatsari da ta yi hatsarin kawai sai aka kawo kayansa gida a matsayin ya mutu tinda ita motar taƙone bara agane koma gawarsa baya a cikin motar. Ita matar ta gama takabarta sai aka auramata ƙaninsa kawai sun kusan sati da tarewa sai gashi ya dawo ashe be mutuba, Yanzu shi ƙaninne zai haƙura yabarwa yayan kokuma yayanne zai haƙura yabarwa ƙanin. Kuma dadin dadawa matar ta ce ita ba ta son yayan ta fi son ƙanin tom mallam yanzu ya za a yi?
MIJI YA DAWO BAYAN AN
YI ZATON YA MUTU KUMA AN AURA WA ƘANINSA MATARSA
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikumussalam
warahmatullahi wabarakatuh.
A shari'ar Musulunci,
idan miji ya dawo bayan an yi zaton ya mutu kuma an aura wa kaninsa matarsa,
dole ne ta koma ga babban yayan (mijin farko) saboda auren farko bai mutu ba,
kanin zai rabu da ita ba tare da saki ba, domin aurensu ba shi da tushe a shari'a
saboda mijin na da rai. Don haka kanin ba shi da ikon da zai riƙe matar, dole ya
janye ya fita daga rayuwarsu cikin girmamawa da biyayya ga hukuncin addini.
Kuma dole matar ta koma ga mijinta na farko, ba ta da zaɓi a nan; Dole ne ta
bar kanin ta koma ga mijinta na asali (yaya). Zabin da ta yi na cewa tana son
kanin ba shi da wani amfani a shari'a saboda, ita ba ta da ikon Zaɓi a wannan lokaci.
Alal-Haƙiƙa Malamai Ahlul-Ilmi
sunyi maganganu daban-dabam akan wannan Matsala:
1. Mafi yawan Malaman
dake Mazhabobin SHAFI'IYYA, HANAFIYYA, HANABILA, sun tafi ne akan cewa shi
wannan babban yayan (mijin farko) da ya dawo shi ne Mijinta domin Asali dama
Matarsa ce, don haka auren da'aka ɗaura mata da kanin, to ayanzu sunansa Ɓataccen Aure domin
ba'a buƙatar wai sai ya ce yasaketa, amma idan kanin yasadu
da'ita to shikenan taci Sadaƙinta. Daga nan sai su cigaba da zama
tare da asalin Mijinta (babban yayan) batare da ansake wani ɗaurin aure ba.
Daga cikin Hujjojin
Malaman dake kan wannan fahimta sunkafa Hujja da abinda aka ruwaito daga dukkan
waɗannan Sahabbai:
Usman-Ɗan-Affan, Umar-Ɗan-Kaɗɗab, Aliyu-Ɗan-Abi-Ɗalib, Abdullahi-Ɗan-Abbas, Abdullahi-Ɗan-Zubair. Cewa
dukkansu sunyi hukunci ne akan cewa babban yayan (mijin farko) shi ne Mijinta,
kuma ba'asamu wani Sahabi ko guda ɗaya da ya saɓa musu akan hakan ba, Aʟʟαн(ﷻ) Yaƙara yarda agaresu
baki ɗaya.
2. Mazhabin MALIKIYYA
sun tafi ne akan cewa idan babban yayan (mijin farko) ya dawo bayan Matar ta
gama iddarsa har ta yi aure kuma Mijin yasadu da'ita, to ayanzu kam bashida iko
akanta tunda ta yi aure, don haka sukace kanin da ta aura shi ne Mijinta, amma
sukace idan baikai ga saduwa da'itaba to babban yayan (mijin farko) shi ne yafi
cancanta da'ita.
Saidai magana mafi
inganci anan ita ce, wannan Matar tana ƙarƙashin igiyar auren
babban yayan (mijin farko) da ya dawo, wannan kenan.
To amma idan ya dawo
yatarar har anriga anrabe dukiyarsa amatsayin gado to yanzu ya za'ayi kenan?
Dukkan Mazhabobin nan guda huɗu sunyi ITTIFAƘINE akance za'a dawo
masa da dukiyarsa ne.
To amma idan
yakasance dukiyar ta salwanta fa, yazama babu ita tuni anriga ankasheta? Anan
Sai Malamai sukayi Saɓani, mafi yawan
Malamai sukace sai an rama masa, anbiyashi dukiyarsa, amma Mazhabin HANAFIYYA
sukace babu wata ramuwa da za'ayi masa, kawai abinda yazo yasamu yakarɓa amma wanda
yasalwanta kuma shikenan.
Magana mafi inganci
idan miji ya dawo bayan an yi zaton ya mutu kuma an aura wa kaninsa matarsa, to
dole ne adawo masa da matarsa saboda auren farko bai mutu ba, kanin zai rabu da
ita ba tare da saki ba.
WALLAHU A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.