Ticker

6/recent/ticker-posts

Iyayena Sun Ce Sai Na Yi Masters Kafin Na Yi Aure

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum.

Malam, barka da safiya. Malam, don Allah ina da tambaya: na yi karatu har na gama digiri, to sai iyayena suka ce in je in yi mastas (Master's), kuma Malam ban da aure amma ina da wanda nake so. To Malam, ni dai yanzu aure nake son in yi saboda Malam shekaru na sun ja; yanzu shekarata talatin da ɗaya. Kuma Malam, ba gari ɗaya muke da shi ba. Yanzu idan na je na yi mastas, yana iya yiwuwa iyayensa su ce ba za su yarda ina fitowa kullum ina zuwa makaranta ba, saboda Malam ko lokacin da za a yi mana baiko sai da aka yi rigima iyayensa suka ce ba zan yi aiki ba, tunda ba gari ɗaya ba ne tsakanin inda nake aikin da inda zai yi aure. Haka ya je ya shawo kansu har suka amince.

To yanzu Malam, fi sabilillahi hakan ya dace? Kuma ina jin tsoron kar su ce ban yi musu biyayya ba. Kuma yanzu idan na rabu da shi na je na yi mastas na shekara biyu, ina da tabbacin idan na gama zan samu wani mijin? Kuma Malam, ka duba min wannan al'amari: kafin in gama mastas na cika shekara talatin da uku ban yi aure ba. Kuma Malam, ko lokacin da nake digiri ba wai manema na rasa ba ne, ina jin tsoro ne kar su ce aure nake so, shi ne duk wanda ya zo sai in ce masa sai na gama karatu."

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikis salaam wa rahmatullahi wa Barkatuhu;

Toh sai dai mu ce Allah Ya tsare Ya shirya domin yanzu abun da wasu iyayen suke yi ba su kyautawa Yaran su Mata, kuma ki dage da yin Addu'a Allah Ya fahimtar da su domin su gane abun da suke shirin aikatawa wannan kuskure ne kuma sun tauye haƙƙin ki, kuma akwai cutarwa a cikin yin hakan.

Abun da yakamata ki yi a yanzu, ki gayawa Mahaifiyar ki ta samu Mahaifin ki su yi shawara akan a bar ki yi Auren ki sai ki ba su hujjojin ki na son yin Auren ki, matukar akwai wadda yake son ki da Aure, sa'annan Addinin Musulunci ta amince da a ba shi Auren Mace a ko ina ne, toh kawai a bar ki ki yi Auren ki idan ya so bayan kin yi Auren ki kina gidan Mijin ki sai ki ci gaba da karatun ki ko Professor za ki zama, ki je gidan Mijin ki ki zama professor din yafi dacewa.

Nana Fadima Allah Ya kara Mata yarda ta ce Darajar Mace, Ƙimar ta, Mutuncin ta da Martaban ta shi ne gidan Mijin ta. Ke nan duk Ilmin Mace duk mulkin ta ko mene ne ta zama a duniya indai ba ta da Miji, toh da sauran ta domin Darajar ta bai cika ba.

Sabida haka ki sanar da ita sai ta same shi ta gaya masa ya bar ki ki yi Auren ki, idan kin je gidan Mijin ki yi master ko professor za ki zama ki dai yi Auren tukuna, ki gayawa Mahaifiyar ki sai ta samu Mahaifin ki ta sanar da shi.

Idan kuma ba zai Saurare ta ba ko kuma bakin su ɗaya ne, toh idan kin san a cikin Yan Uwan sa akwai waɗanda yake jin maganar su baya ketare maganar su, toh ki je har gaban su da kanki ki gaya musu matsalar ki da hujjojin ki, sa'annan ki ce su gaya masa ya bar ki ki yi Auren ki in Sha Allah idan kin gaya musu indai yana jin maganar su, za su dauki mataki akai kuma za a bar ki ki yi Auren ki.

Gaskiyar magana yin Auren ki shi ne yafi dacewa domin a wannan zamanin Mace kamar ki a ce wai ta yi Jami'a har ta gama babu Aure a kanta, sa'annan a ce ta je ta yi Master ai akwai matsala sosai wallahi Budurwa fa, matan Aure ma a Jami'a yaya suke karewa balle a ce Budurwa kin gama tsare dokokin Allah da tarbiya da suka ba ki, kin gama jurewa yakamata a ce sun bar kin yi Auren ki a yanzu, na farko ke Mace ce kina da rauni sosai sa'annan kina da Sha'awar ki, duk jurewan da kika yi a Jami'a bai isa ba, yanzu kuma su ce sai kin yi master's wannan akwai cutarwa a ciki, kuma yana ɗaya daga cikin abun da ya sa wasu Yan Mata suke yin duk abun da suke so a Jami'a a yanzu.

Dazun nake bayar da wani mummunar labarin da na gani da Ido na a jiya, Yarinya karama kwata-kwata shekarun ta wlh ya yi yawa ke nan 10, kuma ko nono babu a kirjin ta, amma haka wani ya kwantar da ita tana tsirara shi ma tsirara ya cire azzakarin sa zai sa a farjin Yarinya ko ya sa ne ma sai Allah, kuma Yarinyar tace kuɗi ya ba ta, toh don Allah idan Yarinya irin wannan zatayi haka, ina ga kuma wadda ta mallaki hankalin ta, kuma take da Sha'awa? Wasu Iyayen ba su gane lissafin ai a wannan zamanin ba za a ajiye mace ba tare da miji ba, indai an samu toh yin shi ne yafi dacewa.

Sa'annan kin ga a rayuwar karatun Mace a yanzu, ba kowane Namiji ne yake son ya Auri Macen da ta yi karatu har zuwa Jami'a ma balle a ce har Master's, sai dai idan misalin a ce kun fara soyaya yia da shi tun kafin ki gama secondary school har kina Jami'a har zuwa Master's din a ce kuna tare da shi, toh nan Namiji zai iya Auren ki, amma idan bahaka ba wallahi dakyar ake samun Mace ta yi karatu har zuwa Jami'a ko master's tana Budurwa Namiji ya zo neman ta, ko za ki samu sai kin dauki lokaci sosai, sa'annan ba kowane Namiji ne yake son ya Auri mace ta rika zuwa aiki, ko su Yan Bokon ma irin Prof, ko DR, ko dan Degree din dakyar za ki samu a ce ya Auri mace wadda level nasu ɗaya, kuma a ce tana zuwa aiki wasu ba su son Auren Mace irin wannan wadda level nasu ɗaya, sabida ba zai haɗu ba ne kawai ko an yi ana iya samun matsala sosai.

Waɗanda suke kasa da karatun ki yan secondary school ko ba su yi ba, su kuma suna jin tsoron zuwa gurin ki da sunan neman Auren ki, dalilin shi ne watakila shi NCE ya yi ko kuma karatun sa iya secondary school ko primary School ko Jami'a ke kuma kina da Master's ko Dr, kin ga level naku ba ɗaya ba ne dole ne zai ji tsoron zuwa neman Auren ki, gani zai ko ya zo watakila ba za ki saurare shi ba, sa'annan ga shi shekarun ki sun ja kina da 30 da wani abu, shi kuma watakila 27, sa'annan ko ya zo iyayen ki dakyar za su yarda su ba shi ke domin matsayin karatun ki, na biyu ko an ba shi ke za a yi ta zuga ki a ce kaza a ce kaza a karshe har Auren a fasa shi, sa'annan ga shekarun ki na ja, kyan Halittar ki da komai naki baya yake yi, kyan ki komai naki a kullum chanjawa yake yi, idan a da can Namiji na iya kallon ki sau 1 ya ji sha'awar ki sabida halittar jikin har ya ji yana son ki, toh sai ki ga ko sau 5 zai kalle ki ba ki isa abun kallo ba, balle ace ya yi sha'awar Auren ki.

Sa'annan wasu ba so sun Auren Mace da ta yi Jami'a ko master's wadda za ta zo ta yi aiki a gidan shi, ita tana fita shi ma yana fita, su kuma waɗanda level naku ɗaya ne ko kuma nace kin fi su ko sun fi ki, su kuma dakyar ne za su zo neman Auren ki. Idan ma wasu sun zo neman ki, toh sai dai ki ji suna miki maganar ku yi Zina kuyi rayuwa irin na ma'aurata, a cikin kaso 10 za ki iya samun 8 duk idan sun zo gurin ki maganar Zina ce kawai guda 2 ne kaɗai za su zo su ce Auren ki suke son yi, su din ma da tsoro a tare da su. Domin wasu a fahimtar su shi ne kin yi Jami'a kin zo kin yi master's, toh a nasu tunanin jikin ki ba komai ba ne shiyasa za su yi ta kawo miki maganar Zina kaɗai, sa'annan idan kin samu aikin yi ba ki yi Aure ba bayan gama master's din, nan ma level naki ya sake yin gaba, nan kuma wani case ne daban.

Wannan shi ne matsalar da ake samu shiyasa Mace za ta gama karatun ta, amma wallahi Mijin Aure zai gagare ta domin irin waɗannan abubuwan, sa'annan kuma Siffofin jikin ki da zai dauki hankalin Namiji har ya ji yana kaunar ki, toh yanzu duk sun chanza ga yawan shekarun ki watakila kin girmi wadda ya zo neman Auren ki, idan ma zai neme ki shi ma iyayen sa su ce ta yaya zai nema sa'ar Mahaifiyar sa? Da sauran su.

Shiyasa mace a yanzu a wannan zamanin da muke ciki da babu tsoron Allah, toh wallahi indai mace budurwa ta gama secondary school, idan akwai mai son ta tsakanin sa da Allah da zuciya ɗaya kuma Shari'ar Musulunci ta amince da a ba shi auren mace a ko ina ne, toh wallahi yin auren ta shi ne yafi dacewa, idan ma zatayi karatun jami'a ko master's ko prof. ta je gidan Mijin ta ta yi sa a can indai ya bar ta, amma idan Mace ta sake damar ta a lokacin da Maza suke da burin su Aure ki, suke yawan zuwa gurin ki da sunan Auren ki za su yi, amma iyayen ki suka ce a'a karatu za ki yi, wai sai kin gama degree za ki yi Aure, ko kuma sai zuwa master's, toh ana iya samun matsala sosai wallahi za ki iya gama karatun, ki samu abun da suke so ki samu burin ki ya cika, amma kuma Mijin Aure ya zama miki tashin hankali sosai wallahi ga Sha'awa na damun ki.

Sa'annan kuma a wannan zamanin namu da babu tsoron Allah a gurin wasu Lecturer, babu tsoron Allah gurin wasu Daliban, babu tsoron Allah a gurin wasu ƙawayen da Samari, sa'annan ga wasu kungiyoyi da suke shiga cikin Jami'a a yanzu da sanun samawa Yan Mata yancin su ko wanin sa, su zo su yi ta lalata rayuwar Mace, Mace ta je Jami'a a mutumiyar kirki ce ga irin tarbiyar da iyayen ta suka ba ta sosai za ki iya sa mata yatsa a baki ba za ta ce miki komai ba, amma sai ki ga ta lalace yanzu Zina kam ya zama kwalliya gare ta ba ta jin kunyar kowa, kuma ko a jikin ta tana school amma tana fita ta je ta yi duk abun da ta ke so, iyayen ta suna sake da Baki cewa Yar su tana karatu a Jami'a, ba su san cewa Yar su babu irin Iskanci da ba ta yi ba, wallahi wani Voice kwanaki aka tura min na wasu Yan Mata da suke karatu a Jami'a suna Hostel na Mata, idan kin ji abun da suke aikatawa wallahi idan Yaran ki suna Jami'a a take za ki cire su sun karatun gama ke nan har abada sai dai ki yi musu Aure, domin idan kin ji irin abubuwan da suke aikatawa wallahi sai hankalin ki ya tashi. Toh, irin waɗannan suna da yawa a jami'a. A yanzu, rayuwar wasu mata budurwa sai wadda Allah Ya tsare ta kuma ta tsare kanta ne kawai, amma idan ba haka ba, irin rayuwar da wasu suke aikatawa a jami'a, wallahi, da iyayen su suna gani da idon su, ba za su taɓa yarda a ce har yanzu ba su aurar da su ba.

Sabida haka ki samu Mahaifiyar ki sai ki sanar da ita komai kada ki Ɓoye Mata, sa'annan ki bata hujjojin ki akan wannan, ta samu Mahaifin ki ta yi masa magana, idan kuma ba zai saurare ta ba sai ki samu wadda yake jin maganar su a cikin Yan Uwan sa ko abokan sa ki yi musu bayanin komai in Sha Allah idan sun same shi sun yi masa magana komai zai zo da sauki. Da fatan kin gane ko?

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam  

Post a Comment

0 Comments