𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamualaikum. Tambayana shi ne na kai shekara ishirin da uku mallam ina da samari amma dukka babu na aure da an yi magana sai ya watse, kuma ni kammamiya ce ban zina ban zuwa fati, ban yawan jin wakoki kawai jarraba ce daga Ubangiji, sannan mallam an kai ni gurin wani mallami ya ce wai na kai agwagwa da kaza za a min aiki wai bakin iska ne dani, shin mallam ya halakta a cikin addinina ko kuwa?
HATSARIN DA KE
TATTARE DA ZUWA WAJEN BOKA KO ƊAN DUBA
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Waalaikumussalamu
Baiwar Allah Baihalatta ba Kuma shi wannan mutumin ba malami bane Kuma
maganganunsa sun tabbatar da cewa boka
ne /Ɗan duba ne. Saboda haka ku kauracewa zuwa gurin irin waɗannan bokayen Sannan
Kuma idan bakusan cewa boka bane kukaje gurin sa, To kuyi gaggawan tuba ku nemi
gafarar Allah. Amma idan kunsan cewa boka ne, amma kuka je gurinsa, to hakika kun kafircewa. Abin da Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya zo da shi kamar yadda ya tabbata a cikin ingantattun hadisai.
Annabi (Sallallahu
Alaihi Wasallam) Ya ce: Duk wanda ya je gurin Ɗan duba ko boka sai
ya kuma ya gasgata abinda yake cewa to
hakika ya karficewa
abinda aka saukarwa Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam). A wani
hadisin kuma cewa yayi; Duk Wanda ya je wajan ɗan duba sai ya tambaye shi wani abu to
ba za’a
karbi sallar sa ba ta
kwana arba’in ba. A wani hadisin kuma cewa yayi “Baya daga cikimmu duk wanda
yake yin camfi ko a ke yimasa camfi ko yayi bokanci ko ake yi masa bokanci, ko
yayi sihiri, ko ya sa ayi mishi sihirin, duk kuma
wanda yaje wajan boka
sai ya gaskantashi a aduk abinda yake cewa to hakika ya kafircewa abinda aka
saukarwa Annabi Muhammad (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi).
'Yan uwa kunji
Hatsarin dake tattare da zuwa wajen boka ko Ɗan duba kuma Yana
kaiwa ga fita daga musulunci domin duk wanda yaje Yana sane ya zama kafiri kuma
gara ya Dena sallah da Azumi. Domin ya kafircewa Allah da manzonsa, kuma Allah
baya karbar sallah da azumin wanda ba musulmi ba.
Baiwar Allah sai ku nisanci zuwa gurin irin waɗannan bokayen kunji dai duk wanda ya je gurin su ya tambayesu wani abu ba za a karɓi sallar sa ta kwana arba’in ba idan kuwa ya gaskata su ya kafirta. Saboda haka saiki godewa Allah Abisa ni'imar da yayi
miki ta samun damar tambaya dangane da wannan al'amari.
Baya halatta ga
maralafiya ya je wajan bokaye da suke ikirarin sanin abubuwan da
ke ɓoye, wai don ya gano
masa rashin lafiyansa, kamar yadda baya halatta ya
Gasganta su cikin abin da su ka bayar da labarinsa.
Sannan kuma yana
dakyau ku sani akwai hanyoyin da shari'a ta amince na neman magani, musamman abinda ya shafi jinnu. Wani abu da mafi yawan Mata basu sani ba shi ne: Babu yanda za'ayi a cire aljani ta hanyar aljani, saidai ma a sake jajibo wasu.
Saboda haka ku nisanci dukkan gurin masu ce muku sai anzo da agwagwa ko kaza ku bakin zakara ko bakar akuya dasauransu. Waɗannan abubuwan duk aljanun ne suke umarta da akawo, kuma duk wanda ya kai ɗaya daga cikin abubuwan, hakika ya bautawa aljanu saboda ya kafirta. Saboda haka ku ziyarci cibiyoyin shari'a ta amince dasu waɗanda suke cire aljanu da ayoyin Alƙur'ani ta hanyar yin ruƙiyya da addu'o'i ba irin waɗannan bokayen ba.
WALLAHU A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Za ku iya samun shafinmu ta wannan hanyar...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.