𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum, malam. Dan girman Allah, ina da wata tambaya: wai idan mutum ya mutu, ana yi masa tambayar kabari ko ba za a yi masa? Wai mala'iku ba sa zuwar wa mutum cikin kabarinsa; wai idan ya mutu, shikenan sai ranar da za a busa kawo.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikumussalam
warahmatullahi wabarakatuh.
A koyarwar Musulunci,
idan mutum ya mutu aka binne shi, lallai mala'iku biyu (MUNKAR da NAKIR) za su
zo wa mamaci, su zaunar da shi, su yi masa manyan tambayoyi uku Kamar haka:
Wanene Ubangijinka? Menene addininka? Wanene Annabinka? Ko me kake cewa game da
wannan mutumin da aka aiko a cikinku?
Allah zai tabbatar da
harshen Muminai su ba da amsa daidai cikin sauƙi. Bayan sun amsa, za
a buɗe musu ƙofa zuwa Aljanna kuma
kabarinsu zai faɗada.
Munafukai ko kafirai
ba za su iya ba da amsa ba. Za su riƙa cewa "Hah,
hah, ban sani ba." Wannan zai janyo musu faruwar azabar kabari.
Daga nan ne ake nuna
wa mumini ko kafiri makomarsa, kuma ake fara jin daɗi ko azabar kabari
kafin tashin alkiyama. Wannan shi ne abin da aka sani da rayuwar kabari ko
fitinar kabari, ba sai ranar tashin kiyama ba.
Babban ayar da
malamai suka fassara da nuna tambayar kabari ita ce faɗin Allah Ta'ala:
يُثَبِّتُ
اللّٰهُ الَّذِيۡنَ اٰمَنُوۡا بِالۡقَوۡلِ الثَّابِتِ فِى الۡحَيٰوةِ الدُّنۡيَا
وَفِى الۡاٰخِرَةِ ۚ وَيُضِلُّ اللّٰهُ الظّٰلِمِيۡنَ ۙ وَيَفۡعَلُ اللّٰهُ مَا
يَشَآءُ
"Allah Yanã
tabbatar da waɗanda suka yi ĩmãni da
magana tabbatacciya a cikin rãyuwar dũniya, da cikin Lãhira, Kuma Allah Yanã ɓatar da azzãlumai,
kuma Allah Yanã aikata abin da Yake so" (Surah: Ibrahim, Ayat: 27).
An ruwaito daga Sahih
al-Bukhari da Muslim cewa Sahabi Al-Bara' ibn 'Azib ya ce wannan ayah ta sauka
ne game da azabar kabari da amsa tambayoyi (lokacin da aka ce wa mamaci: Waye
Ubangijinka? Me ye addininka? Waye aike zuwa gare ka?). Lokacin da mumini ya
amsa da cewa Ubangijinsa Allah ne kuma Annabinsa Muhammad ne (Sallallahu Alaihi
Wasallam), sai wannan aya ta zama siffar tabbatar masa da gaskiya.
Wata ayar kuma da
malamai ke amfani da ita wajen tabbatar da rayuwar kabari da abin da ke ciki
ita ce ta Surah Ghafir Ayah ta 46 game da nunawa 'yan kabari wuta:
اَلنَّارُ
يُعۡرَضُوۡنَ عَلَيۡهَا غُدُوًّا وَّعَشِيًّا ۚ وَيَوۡمَ تَقُوۡمُ السَّاعَةُ
اَدۡخِلُوۡۤا اٰلَ فِرۡعَوۡنَ اَشَدَّ الۡعَذَابِ
"Wutã, anã gitta
su a kanta, sãfe da maraice, kuma a rãnar da Sa'a take tsayuwa, anã cẽwa, "Ku shigar
da mutãnen Fir'auna a mafi tsananin azãba." (Surah: Ghafir, Ayat: 46).
Wannan yana nuni da
cewa ana nuna musu wuta safe da yamma a rayuwar kabari kafin a shigar da su
azaba mafi tsanani a ranar kiyama.
An ruwaito daga Usman
dan Affan (R.A) cewa: "Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya kasance idan
ya gama rufe mamaci yakan tsaya a kan kabarin ya ce: 'Ku nemawa dan'uwanku
gafara, ku roka masa tabbata, domin shi a yanzu ana tambayarsa'". Wannan
ruwayar tana da tushe a cikin Sunan Abu Dawud, kuma malamai sun zayyana cewa
yana nuni ne ga tabbacin amsa tambayoyin mala'iku MUNKAR da NAKIR.
Sabida Haka Ýan uwa tambayar 'kabari gaskiya ce kuma sai ta tabbata akan
kowa, Kuma duk wanda kukaji yana da'awar cewa Babu tambayar 'kabari, azabar
'kabari ko babu rayuwar 'kabari to shi din munafuki ne ko kuma kafiri ne ko kuma yana shakka akan Manzoncin Manzon
Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) to kunga su kansu masu karyata tambayar
'kabarin koda suna kiran kansu musulmai idan suka mutu a haka da wannan a'kidar
to suma basa daga cikin mutanan da zasu amsa tambayar 'kabari domin munafukai
da kafirai da masu shakka da kokonto basa iya amsa tambaya kabari.
Dukkan mutanen da
suka mutu za a yi masu tambayoyin kabari, amma akwai wasu rukunin mutane da aka
kebe da su ba za a yi masu irin jarrabawar ko azabar da sauran suke fuskanta
ba. Akwai waɗanda aka ambata a
cikin ingantattun hadisan Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) cewa
Mala'iku MUNKAR da NAKIR ba za su yi masu tambaya ba. Allah zai tsare su daga
fitina ko tambayoyin kabari, Wadannan sun haɗa da:
1. SHAHIDI: Wanda ya
mutu a fagen daga yana yaki domin daukaka kalmar Allah, hadisi ya nuna cewa
takobi a kan kansa ya isa jarrabawa, don haka ba za a yi masa tambayar kabari
ba.
2. YARA KANANA DA
MAHAUKATA: Waɗanda ba su balaga ba
ko ba su da hankali a lokacin mutuwarsu, ba su da lissafin aikata saɓo, saboda haka ba a
musu tambayoyin kabari.
3. WANDA YA MUTU
RANAR KO DAREN JUMA'A: Akwai hadisi sahihi da ya nuna cewa duk Musulmin da
Allah ya karbi ransa a ranar Juma'a ko daren ta, Allah kan tsare shi daga
fitinar kabari.
4. ANNABAWA: Malamai
sun ce Annabawa ba a musu irin wannan tambayar ba domin sun riga sun wuce
wannan mataki na jarrabawa.
5. MAI GADIN DOKA
(AL-MURABIT): Wanda yake tsaron iyakar Musulunci a kan hanyar Allah, inda a
hadisi aka ce ayyukansa na cigaba da gudana har zuwa tashin Alkiyama.
Dukkan sauran halitta ban da waɗannan kebabbun
mutane, kowane mutum (Musulmi ko kafiri, mai zunubi ko mai biyayya) za a yi
masa tambayoyi uku a cikin kabarinsa: Waye Ubangijinka? Menene addininka? Waye
a ka aiko muku manzo?
Ya Allah ka ɗauki rayuwarmu muna
musulmai masu imani da Annabinka muhammad {Sallallahu Alaihi Wasallam} ka bamu sa'ar
amsa tambayar kabari. Ameen Ya Hayyu Ya Ƙayyum 🤲
WALLAHU A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Zaku iya samun shafinmu ta wannan hanyar...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.